P-5
Page🟧5
----------Da sauri Halima ta kalli Hajiyar Maska,saboda babu abinda taƙi jini a duniyarta irin ayi mata gorin haihuwa,ita a ganinta Haihuwar nan ba don Allah ya tsaneka bane baya ba ka ba,kawai dai Allah ya jarabceka ne don yaga yadda zakayi,tunda Allah bai bawa Uwar mumunai ba,to waye ba zai jarabta ba?ko so take tayi hauka tunda bata haihu ba?ita a ganinta tunda tana da Baby wani kukan Haihuwa za tayi?a ganinta bai kyautu tayi wani kuka ba,tunda har tana da Baby yarinya me nutsuwa,yarinyar da har yanzu bata yarda ba ita ce mahaifiyarta ba,tasha kama Baby tana kuka idan ta tambayeta dalilin kukan sai ta ce,Wallahi Momy ni bana son ana cewa ba ke ce kika haifeni ba,idan ma ba ke ce kika haifeni ɗin ba a'i kin haifi,tunda tun ina jaririya ke kika kula dani har girma na,to kuwa idan na butulce miki a'i kai na na butulce wa.
Tana cikin wannan tunanin taji MD na cewa"Hajiya zamu tafi,sai Allah ya kaimu gobe zan leƙo In sha Allah".
Hajiyar Maska ta ce"Allah ya kaimu ta wuce abinta zuwa sashen Mijinta,don Allah ya sani ko fuskar Halima bata son gani,saboda ta tsani yarinyar duk ta mallake mata ɗa,komai Halima!Halima kafin ya kira sunanta sau ɗaya,ya kira sunan matarsa shiyasa abin yake dagula tunaninta baki ɗaya.
A kaf cikin ƴaƴanta tafi son Muhammad,kawai dai tana cewa tafi son autanta saboda kada Halima taji daɗi ta miƙe ƙafafunta,shiyasa take nunawa agabanta ta tsani Halima.
Baby kuwa ko sallama bata yiwa Hajiya ba,saboda sam yanzu ta tsani matar sai dai babu yadda za tayi da ita tunda dai kakarta ce,sai dai addu'ar da take a kullum shine Allah ya dawo da hankalin Hajiya kan Mominta,ta dinga sonta kamar sauran surukanta.
Baby ta kalli Abbanta sannan ta ce.
"Dady".
A hankali ya kalle ta Amman bai ce mata komai ba,da yake mutunne me saurin sauka ko da ma ace yayi fushi,ta cigaba"Dady bamu shiga part ɗin Hajiya ƙarama ba,kuma bamu shiga part ɗin Hajjiya kaka ba."
A hankali ya ce"muje tare nima ban shiga ba."
Halima dai na jinsu amman bata tanka musu ba,saboda yadda kanta ke matuƙar sara mata,bata son tashin hankali ko kaɗan a duniyarta,bata son duk wani abinda xai shigar mata rayuwa ya hanata rawar gaban hantsi,sam bata son zuwa gidan Hajiya saboda tashin hankalin dake gidan,tun tana amarya har yanzu,da sahu ya fara daɗewa amman Hajiya na nan akan turbarta ta tsanar Halima,ita ta rasa dalilin wannan tsana,ko da ake bata labarin surukai ita dai bata taɓa ganin irin tata ba,Hajiya ko atamfa taga Halima ta saka to tabbas,sai ta saka ɗanta ya siyo mata,a faɗarta wai Halima na tatsewa ɗanta tattalin arziƙi,kullum cikin hidimta mata yake da ƴan uwanta.
Kuma Allah ya sani Halima bata taɓa roƙar wani abu a wajen MD ba,shi dai da kansa yake dubawa yaga ya cancanta daya bawa ƴan uwanta wani abu,duk da suma fa ba baya bane wajen kuɗi,don daman cen karayar arziƙi ce ta samu mahaifinta,amman babu wanda bai san kuɗin da mahaifinsu yake dashi ba,ko kama ƙafarsu gidansu Muhammad basuyi ba,tunda su gidansu Muhammad duk ma'aikatan gwamnati ne,ita kuwa mahaifinta babban ɗan kasuwa ne kuma ɗan siyasa,babu wanda bai sanshi ba mahaifinta bai taɓa roƙar wani abu gun mijinta ba,ko kuma ya sata ta roƙar masa ba amman duk da haka Hajiyar Maska bata ƙyale ta tasha ruwa ba,kullum cikin masifa da hantara da zagi,ko kishiyarta bata yiwa haka ballantana ita da take matar ɗanta,abin yana damunta sosai gashi Halima tana da zurfin ciki,don duk wannan abinda ke faruwa iyayenta basu taɓa sani ba,saboda macece me zurfin ciki sosai,don ko mahaifiyar Baby ba halinsu ɗaya ba,don ita tana da zafi sosai don itama sunsha yi da Hajiyar,sai dai da taga mahaifiyar Babyn ba baya bace wajen masifa itama,sai ta haƙura sai data bari zamanin Halima yazo sannan ta ɗora,bayan ta gane matsanancin haƙurin da Halimar ke dashi.
Kuma daman idan aka ga kana da haƙuri to ko wani kashi sai a ɗebo azuba a kanka,sai dai fa haƙuri shi kansa baiwa ne ba kowani ɗan adam ke dashi ba,sai wanda Allah ya bawa haƙuri rahama ne.
Sashen Hajiya Ƙarama suka fara shiga,babu kowa a falon sai Karimatu da Rabiah sune ƴammatan Hajiya Ƙarama,kishiyar Hajiyar Maska yaran suka taso da gudu suka rungume Halima.
Halima ta saki murmushi wanda ya ɓace a fuskarta tun bayan shigowarsu gidan Hajiya,sai yanzu tayi murmushi ta shafa gefen fuskar Rabiah ta ce"kai lallai Autar Hajiya wannan man ya karɓeki,nima a faɗamin sunanshi in siya".?
Da sauri kuwa Karimatu ta ce"yauwa Anty yi mata faɗa dai,mutun yana ɗan baƙi yace wai shi sai yayi fari?a ina aka taɓa yin haka?mu dai tunda farare ne ayi haƙuri a zauna haka,kada a canja halittar Allah."
Sai kuwa Baby ta ce"a'i kuwa dai Little momy man yayi miki kyau,Allah yasa Yaya Abbas ya gani"?.
Sam su Rabiah basu kula da Babban yayan nasu ba,dai da sukaji ya wuce ɗakin Hajiya sannan dukansu suka kama bakunansu,tare da zaro idanu suna magana da hannu sa idanuwa,wai yaushe yazo?ko tare suke ne"?.
Halima tayi murmushi sannan ta ce"tare muke mana a'i yana jinku,kinga ke Autar Hajiyar ta kanki za'a fara"?.
Ta nuna Rabiah wacce ta fito da idanuwa waje,ƙwalla ta cika idanuwanta don aƙwaita da saurin kuka,ga tsoro kamar farar kura sai kuwa ta ce"Don Allah Anty Halima ki bashi haƙuri,don wallahi daman haushina yake ji,tun wata biyu da suka wuce daya ganni da Aliyu a Wani Shopping,kuma kinsan baya son Aliyu saboda halayensa,ni kuma wallahi Antu shi nake so whith all my heart(da dukkanin zuciyata)."
Halima ta kalle ta da tausayin Rabiah aranta,don a sha'anin gidan sam basa son bawa bare ƴaƴansu,sun fi yin auren zumunci,don gidansu Aliyu duk da iliminsu har yanzu ƴan gargajiya ne,kamar suna garinsu Maska don itama abinda yasa Hajiya ta ƙara tsanarta kenan saboda ita ba ƴar uwarsu ba ce,bare ce ita shiyasa suka tsane ta,don bayan Hajiya har ƴan uwan Hajiyan ba sonta suke ba,don tasha zuwa biki a danginsu a wulaƙantata,inda dai take samun sauƙi awajen ƴan uwan mahaifin Aliyu,don su dai sun san darajar ɗan adam sosai,sai kuma wajen Hajiya Ƙarama kishiyar Hajiyar Maska,itama macece me son mutane,kuma babu ruwanta macece me sauƙin hali da kuma haƙuri,don idan banda haka bata isa ta zauna da Hajiyar Maska ba,don mai zama da Hajiyar Maska sai ya shirya,don Hajiyar Maska aƙwai faɗa tare da son ƙuntatawa mutum.
-----*****-----
. . . .Indo na fita kai tsaye dandali ta wuce,tana tafe tana wani yauƙi da ƙwarƙwasa,don Allah ya zubawa Indo iya tafi salo salo,gashi Allah yayi mata halitta me kyau da tsari,don irim matan nan ce ƴan duma duma,don ma ta saka fitina aranta don sai tafi haka girma.
Tana zuwa taga kowa yayi tagumi a Dandalin,ta kallesu kallon ƙasa da sama ɗinnan sannan ta ce"kai Lafiyarku kuwa?kamar an ce muku me gari ya mutu?alhali yanzu naga me Gari ya babbake ƙatuwar Rigarsa yana zaune ƙofar gidansu Hanne,ƴar zamanin taƙi fitowa sai ta gama ƴan ƙwanasa sannan ta fito?kai Allah na gode maka daka kawo me cin gidansu Megari".
Dariya ce ta kufcewa kowannensu,don daman zamanda sukayi na rashin Indo ne,suna masifar son Indo duk da faɗanta amman indai kana kusa da ita ka dai na shiga ƙunci.
Sosai samarin da ƴammata suke ihu tare dayi mata kirari suna ce wa.
"She Indo Me maganin ƴar banza da ɗan banza,ƙadaran kan dutse baki fito she da kika shirya."
Wani irin juyi tayi sannan ta fara kallonsu a nutse,ta ƙurawa wani waje ido sannan ta ce"wai Inna Surbajo ne?yau bata zo bane?me ya hanata zuwa?ince dai wannan kawun nata ɗan gajere me wandon saƙa,shine ya hanata zuwa ko?to Alƙur'an indai shine She nayi maganinshi,me ƙaton ciki kamar tulu yau he na sakashi yayi rawar banjo".
Ƙwashewa sukayi da dariya,suka cigaba dayi mata kirari,sannan ta zaɓo ƴan mata biyu acikin ƴan dandalin,Harda aminiyarta Bintu da yake tsoro ne da ita sai zare idanu take tana ce wa.
"Allah ni dai Indo ki barta?tunda dai bata zo ba,a'i shikkenan ko?mu ba iyayenta bane ballantana mu ɗakko ta tazo nan,don Allah Indo ki barta tunda Kawunta ne ya hanata."
Indo ta juyo a hankali,ta juya mata kyawawan idanuwanta,masu kama da madarar Luna ta ce"ke Mage koma don Allah,sai shegen tsoro kamar wacce ta daɗe acikin daji,koma kada ki ɓata mana shiri ƴar ruwa kawai".
Da sauri Bintu ta koma,don tsaf tasan halin mutuniyarta,yanzu sai a biyo su ta tsere su ta barsu suci na jaki,ita kuwa Indo shegen gudu gare ta kamar barewa,shiyasa sam bata son Indo taja ta ayi wata ta'asar.
Tun daga ne sa ta hango Kawun Surbajo,ta sheƙe da wata munafukar dariya,don ta shirya tsiyar da za tayi masa,don Kawun Surbajo tuni ta daɗe da gane Inda ya dosa,don haka yau ba sai gobe ba za tayi maganinsa.
Suna zuwa Indo ta wuce gaba,ta ɗan ɓoye fuskarta ta tura Hanne sannan ta juya bayanta.
Hanne ta shiga gidansu Surbajo,ita kuma Indo tana ganin haka taga wani yaro yazo wucewa ta ce"kai yaro don Allah je ka cikin waɗancen masu zaman banzan kace wai,Baffan Surbajo yazo"?.
Yaro ya tafi da sauri,yana zuwa ya faɗi abinda Indo ta faɗa masa,sannan ya tafi Shi kuwa Kawun Surbajo jin ance mace ke kiransa,a'i tuni ya jishi a kogin murna,sai washe jajayen haƙoransa yake,daman Malum Malun ce ajikinsa,gashi ɗan gajere kamar wada ɗan kuyat dashi,ya sanya zororuwar hularsa kamar zashi fadar sarki.
Indo kuwa ce wa take,He ge gajere sai sauri yake zaizo wajen Budurwa,baka san ƙwahe ka zamuyi ba.
Indo na ganin ya taho ta wuce da sauri zuwa Dandali,Ita kuma Hanne ta shiga ta fito da Surbajo suka gudu,daman sun san indai yana ƙofar gidan ba yarda zaiyi Surbajo ta wuce ba,shiyasa su Indo suka haɗa wannan dabarar. . . .✍🏾