INDA BA ƘASA!!!

P-6

by @rabiattu0444

Page🟦6


-----------Kareematu ta ce"wallahi Anty Rabiah baza ta gane bane,amman Aliyu mayaudari ne sosai,yanzu ya iya zuwa sai abu yayi nisa ya ce ya fasa aurenta,idan akayi la'akari da shekarun Rabi'ah da kaɗan fa ta girmi Baby,yanzu shekararta 17 Baby kuma 16 ni kuma 19 to don Allah idan ya yaudare ta sai ya tafi ya barta da ciwo,amman sam idon Rabi'ah ya rufe saboda yana da kyau,auren namiji me kyau a'i masifa ne,don duk inda yayi idon mata yana kansa,shiyasa shima Aliyu ya fake da kyau yake cutar ƴaƴan mutane,indai halayyarsa yaudarar yaran mutane insha Allah shima sai anyiwa ƙannensa ko ƴaƴansa."



da sauri Rabi'ah ta miƙe tsaye sannan ta ce"look Anty Kareematu,idan ma baƙin ciki kike min saboda ke bakiyi aure ba,insha Allah sai nayi na barki sai inga ta baƙin ciki".


Kareematu za tayi magana Hajiya Ƙarama ta fito ita da MD, kuma duk sunji abinda ya faru.


Tuni cikin Rabi'ah ya ɗauki ruwa,Kareematu kuwa harda hawayenta na baƙin ciki,don tunda take ba'a taɓa gaya mata magana irin wannan ba,tunda take ita da ƙanwarta basu taɓa shiga irin wannan yanayin ba,sai akan saurayi kuma itama a yanzu haka tana da saurayinta wanda yake sonta,abokin Yaya Muhammad ne amman babu wanda ya sani,ta bari sai abu ya fito sannan kowa ya sani.


MD ya ce"Rabi'ah daman bakida mutunci?ina ganin ki kamar me hankali?Aliyu ne dai baza ki aure shi ba,idan haɗiyar zuciya zakiyi ki mutu sai ki mutu,kuma yayarki da kike wa gori itama ayanzu haka tana da wanda yake sonta tsakani da Allah,kuma nan ba da daɗewa ba zata tafi ta bar miki gidan."


Yana faɗar hakan ya fice abinsa,ya bar Baby da Halima awajen,Rabi'ah ta ce"don Allah anty ki bishi ki bashi haƙuri,wallahi nasan nayi laifi kuma bai kamata in faɗi hakan ba".


Wata irin tsawa Hajiya Ƙarama tayi mata,wacce duk sai da ta razana mutunen wajen,don ita Hajiya Ƙarama macece me sauƙin hali da kuma sanyi,sai ka rantse ma bata faɗa,sai an kai ta ƙarshe sannan ake ganin ɓacin ranta.

Ta ce"yimin shiru mara kunyar banza da hofi,Kareematu ba yayarki bace?amman saboda rashin kunya har kike iya gaya mata magana?to bari kiji a satinnan za'a saka ranar Kareematu,kinga sai ta baki waje kiyi yadda kike so tunda daman kin tsane ta".


Sosai Rabi'ah ta fashe da kuka sannan ta rungume ƴar uwarta tana ce wa.


"Don Allah Anty Kareematu ki yafemin,don Allah kada kiyi aure ki barni,wallahi na saba dake bazan iya rabuwa dake ba,ina jinki har acikin jinina don Allah kice ayimin ɗaki agidanki".


Sosai suka saka dariya su dukansu,don autancin Rabi'ah ya motsa in banda haka a'i bata yi wannan maganar ba.


Tuni idanuwan Halima ya ciko da ƙwalla,tunowa da ƴar uwarta mahaifiyar Baby ta sanya bayan hannunta tana gogewa,tana tuno irin shaƙuwar da sukayi,da kuma son juna amman yau babu ita,ta tuna ranar da Allah ya ɗauki ranta,Halima na riƙe da hannun yayarta Allah ya ɗauki ran mahaifiyar Baby,wannan abu yana matuƙar girgiza tunaninta,tabbas ɗan uwa yana da daɗi,yanzu ba tada abokin shawara don sauran ƴan uwanta duk maza ne,daman su biyu ne mata ita da mahaifiyar Baby.

Tana cikin goge hawayenta taji hannun Hajiya Ƙarama a fuskarta ta ce"Halima bai kyautu ace har yanzu baki fara sabawa da halin Hajiyar Maska ba,ki rage kuka da kuma tunani kinga kuwa yadda kika koma?ina tsoron kada hawan jini ya kamaki Halima,don Allah ki manta da duk wani abinda ta taɓa yi miki sai ki zauna Lafiya".


Da sauri Baby ta ce"Allah Hajiya mun daina zuwa gidanku,tunda idan ma mutum yazo kullum sai an saka Momyna kuka".


Ta faɗi hakan cikin shagwaɓa wacce ta zamar mata tamkar jiki,don Allah ya zubawa Baby shagwaɓa.

Hajiya Ƙarama ta ce"Baby ke da momyn naki duk zuwa gidan nan ya zamar muku dole,sai dai kuyi haƙuri dukkanku sannan ku zama masu toshe kunnuwansu a koda yaushe,idan kukayi hakan sai kuga kun zauna lafiya."


Halima ta tashi a hankali sannan ta ce"Hajiya ni bama wannan nake wa kuka ba,kawai dai wani abu na tuno ne,kuma in sha Allah zanyi amfani da shawarar da kika bani,bari muje ɓangaren Hajiya Kaka don nasan yau tana fushi damu,tunda bamu fara zuwa ɓangaren ta ba."

Hajiya Ƙarama ta miƙawa Halima wata leda,ta turarukan wuta dana jiki,sannan ta rakosu har waje Halima kuwa tana sawa azuciyarta da ma Hajiya Ƙarama ce surukarta da ta more rayuwa.


Suna zuwa wajen Hajiya Kaka suka tarar da MD,yana kallon Halima sai ya juya abinsa ya cigaba da tsokanar Kakar ta sa.


Hajiya Kaka ta ce"kai Me sunan manya gaskiya baka da ta ido,au shine dana tambayeka da tsohuwata kazo kace min a'ah,to a'i gata yanzu tazo sai ka ɗauke ta ka komar da ita gida ko"?.

Halima ta sunkuyar da kai ta zauna tana gaida Hajiya Kaka,da fara'arta ta amsa mata sannan ta ce"a'a uwata me ya samu idonki yayi ja haka?ince dai ba waccen guzumar bace ta ɓata miki rai ba?don nasam zuciyarta kamar ta fir'auna take".


Da sauri MD ya ce"Hajiya kaka bana son wannan zagin da kike?tsakani da Allah idan Hajiya bata ci darajar kowa ba,a'i zata ci darajarmu mu ƴaƴanta,amman sai kiyi ta zaginta agaban kowa,ni gaskiya bana so don Hajiya ko kunama ce ita,a'i haka kawai ba zata hau faɗa ba,don haka Hajiya Kaka ki kiyayi zagin Hajiyata a gabana".

Hajiya Kaka fara salati tana ce wa"Muhammada ɗan Abdalla yau naga abinda yafi ƙarfin idanuwa na,yanzu Me sunan manya ni kakewa wannan idon kamar ƴarka?to wallahi bari ƴaƴana suzo,sai na faɗa musu sun ƙwato min ƴan cina,kuma wallahi sai ubanka ya zaɓa ko ni ko waccen iblishiyar makira me haɗa ɗa da uwa".


Ta faɗi hakan tana han hawaye harda Majina,Baby kuwa ta dinga dariya ƙasa ƙasa don tafi kowa sanin masifar Hajiya kaka,don idan ta bushi iska tana zuwa ta daɗe a wajen Hajiya kaka.

MD ya fita daga sashen nata cikin ɓacin rai,Halima na ganin ya fita itama ta tashi zata bishi, Hajiya Kaka na kuka kamar ƙaramar yarinya ta ce.


"Ke ƴar nan dawo kiji in faɗa miki wani abu,Allah mijin nan naki ya iya tsare gida,ki dinga kula dashi sosai,don irinsu sai da rarrashi kinji".?


Halima bata yi niyyar dariya ba,amman sai da ta dara sannan ta ce"to Hajiya kaka,in sha Allah yadda kika ce haka za'ayi."


Baby ta kaiwa Hajiya kaka kiss(sumba) ta ce"by my yarinya ta".


Hajiya kaka ta daɗawa kukanta sauti ta ce"wayyo Allah na,kaji tsabar ma an wulaƙantani shine za'a ce min ƴar yarinya?babu komai ƴaƴana ne suka bada ni shiyasa duk hakan ta faru."sai ta ƙarawa kukanta sauti tana yi tana ɓantarar goronta,abin tausayi abin dariya kuma abin baƙin ciki.

Halima na fitowa ita da Baby suka hango Alhaji mahaifin MD suna tattaunawa a harabar gidan,inda yake saka kujerarsa me kama da gado ta shaƙatawa.


Halima ta ƙarasa har gabansa ta gaishe sa,ya amsa cikin mutunci da mutuntawa saɓanin Hajiyar Maska da gaisuwarma masifa take komawa.


Har mutanen gidansu da iyayenta sai daya tambaye ta,sannan da zasu tafi ya kira Baby ya aike ta sashensa,sai gata ta fito da jarkoki manya guda biyu,na madarar sa(fresh milk)tayi sanyi sosai acikin free suna cikin leda fara sol,ana hango komai ya amsa ya miƙawa Halima ya ce"gashi ƴata kullum ku dinga shanta da sassafe magani ce sosai a jikin ɗan adam,idan ta ƙare zan aiko muku da wata."


Sosai Halima tayi godiya,don shi MD tuni ma ya daɗe da shiga mota.

Ko acikin motar ma bai yadda ya kalle ta ba,Halima tayi shiru don arayuwarta ta tsani wani abu ya haɗa da mijinta,abin sonta kuma farin cikin rayuwarta,ta kasance aduk sanda taji muryarsa ko ta kallesa sai taji duk baƙin cikinta ya ye,tana masifar sonshi har ma bata san yadda zata iya nuna hakan ba,tabbas ya zamar mata dole ayau ta ƙara bashi haƙuri indai tana son ta tarbeshi yadda take so.


Suna isa aka buɗe musu tangamemen gate ɗin nasu,tun daga baƙin ƙofar gidan sojoji suke sara masa,gwani sha'awa yana ɗan ɗaga musu hannu har motar ta tsaya.


Daman shi al'adarsa ce bai fiya zama sai an buɗe masa murfin mota ba,don a ganinsa girman kai ke kawo hakan,yana fitowa kai tsaye ya shige part ɗin Halima don anan ya saba sauka,kuma baya son Baby ta gano yana fushi da Mahaifiyarta,har sai Halimar ta kawo kanta ɗakinsa,sannan zai ƙara nuna mata kuskurenta na raina masa uwa.

Ummita na zaune a falon,ta rafka uban tagumi don ganin daɗewarsu Halima basu dawo ba,don a ganinta ai filin jirgin ba shida nisa,ballantana tafiyarsu ai sunyi awa biyu ko uku,don har magriba ta fara yi.


Ƙamshin turarensa ne ya riga shi zuwa,Ummita ta yi wata sanyayyiyar ajiyar zuciya,jin turaren daya saka zuciyarta acikin nishaɗi.


Da sallamarsa ya shigo,duk da yasan babu kowa acikin falon,don haka kai tsaye ya wuce dining table don cika tumbinsa.


Ummita ta sau baki da hanci tana kallon kyakkyawar fuskar MD,wanda tsabar kallonsa bata san lokacin da ta tashi tsaye ba.



*INDO ƳAR CASKALE*😂😩



  -----*****-----


. . . . .Indo ta falfala da gudu,ita dasu Surbajo da Hanne sai gasu a Dandali.


Aka saki ihu da shewa,ana cewa"sai Indo,Me maganin ɗan banza da ƴar banza,Indo Ƴar caskale me maganin me taurin kai".


Indo ta nitse cikin ƴan mata aka fara wasan dandali da ƴammata,Indo ce saurauniyar gaɗa,Surbajo kuma Autar ƴammata,Bintu kuma Ƴar gatan samari haka sukayi ta yin gaɗarsu gwanin ban sha'awa,samari na zuwa suna zaɓar ƴammata,ita kuwa Indo duk wanda yazo ma da sauri yake juyawa,don su kansu samarin suna mamakin Indo,don duk lokacin da suka kalleta da fuskar soyayya sai suga ta koma musu tamkar zaki. . . . .✍🏾


Hmm wannan sirrine tsakanin indo da Baffanta zakuji ko menene sai nan gaba.