P-7
Page🟩7
------------Ummita ta sau baki da hanci tana kallon MD,ta kasa ɗauke idonta a kansa,har Khairat ta fito ta samu ƙanwata acikin wannan halin,da sauri ta riƙe hannunta suka shiga ɗakinsu,don gudun kada kowa ya ganta,don tasan hakan da ƙanwarta tayi zai fassara komai.
Khairat ta ɓata rai sannan ta ce"Ummita wai meye hakanne?kin san kuwa abinda kike a'ikatawa?kina son su koremu daga wannan gidan?gaskiya Ummita ki canja halinki,don wannan sam ba haline me kyau ba,mace da mijinta ki nemi yi mata ƙwace har kina kallon mijinta haka?yanzu da ta shigo ta ganki fa?me kike son a ɗaukemu?".
Ummita ta fisge hannunta sannan ta fara magana cikin faɗa"kinga Khairat ki fita daga sabgata?ita zuciya ba'a canja ta,tun lokacin da naga wannan bawan Allahn sonsa da ƙaunarsa ya ɗarsu azuciyata,tun lokacin da na ganshi a hoto naji ina masifar sonshi,don haka Khairat ki sakamin ido kawai,amman fa zuciyata ba zata daina son bawan Allahn nan ba."
Tana faɗar hakan tayi hanyar fita daga ɗakin.
Da sauri Khairat ta dawo da ita tana ce wa"wallahi tallahi baza ki fita ba,kina son ki koma ki cigaba da kallonsa kamar mayya?haba Ummita a'i ana barin halas don kunya ko?".
Ummita ta buga mata wata muguwar harara za tayi magana aka turo ƙofar.
Baby ta kallesu ganin kowaccensu ta harzuƙo kamar za suyi faɗa,Baby ta ƙel ƙele da dariya sannan ta ce"ikon Allah sister's faɗa za kuyi ne?haba don Allah cool down mana,kada kuyu faɗa ku fa ƴan uwa ne?don Allah kada kuyi kunji?Momy ta ce ku fito ku gaisa da Dadyna".
A'i Ummita na jin anyi maganar Dady da sauri ta fice,ba tare da ta jira abinda Babyn zata faɗa ba,Khairat ta bita dana mujiya kawai tana mamakin ƙanwarta,daga zuwa gidan mutane kawai sai kiga mijinta kice kina sonta?ita abin ma mamaki yake bata,sai dai tasan duk abinda Ummita tayi niyya babu wanda ya isa ya dakatar da ita,daman ita haka take tun tana ƙarama,kuma laifin mahaifiyarsu ne don ita ce ta shagwaɓa ta.
Ummita na fitowa ta kusa sandarewa a wajen,biyo bayan abinda idanuwanta suka gane mata,Halima ce zaune akan cinyar mijinta tana feeding ɗinsa gwanin sha'awa,shima yana ɗakkowa yana bata sai abin ya bata mamaki,taji wani irin mugun mashi ya dako zuciyarta,sai take jin kamar taje ta shaƙe Halimar ta mutu,sai dai ta kasa control ɗin kanta kai tsaye tayi wajen,ranta a matuƙar ɓace ga wani irin mugun kishin MD daya cika mata zuciyarta.
Dai dai lokacin su Khairat suka fito Khairat ta ce.
"Ummita!".
ta ɗan faɗi hakan da ƙarfi Sai ta fara yi mata magana da yarensu na shuwa,Ummita ta tsaya cak amman idanuwanta cike suke da ƙwalla,tana ji kamar ta ɗaga hannu tayi ta zunduma ihu.
Khairat ta tsugunna ta fara gaida MD,ya amsa ammanfa ko kallon inda take baiyi ba,ba don girman kai ba a'ah sai don matane bai kamata ya kallesu kallo me yawa ba,don MD aƙwaishi da kiyaye gani da kuma ji,don duk zamanda yake a ƙasashen turawa bai taɓa ko da budurwa ba,ballantana kuma ya nemi matan banza ba,ƴan matan dai sunsha kawo kansu har inda yake,amman ko kallo basu ishe sa ba abinda kullum yake cewa shine,baya shiga gonar da duk ba tashi ba,har sai muharramarsa matarsa.
Itama kuma Halima ta yarda da mijin nata ɗari bisa ɗari,babu ruwanta da zarginsa ko damuwa idan baya nan,ko tayi tunanin yana cen da wata bata tama yin hakan ba don ta yarda da mijinta sosai.
Ummita ma ta gaishesa,sai dai tana gaishe sa ɗin ta wuce da sauri,sai dai da yake duk suma mutanen wajen hankulansu basa wajen basu lura da yanayin nata ba,Sai dai Khairat na lura da yanayin ƙanwarta Ummita,da sauri itama ta bita ɗakin don ganin halin da ƴar uwarta ke ciki.
Tana zuwa ta isketa a ƙwance a bakin gadonsu,ta haɗa kanta da guiwa ta shiga rera kukanta da ɗan ƙarfi,jin zuciyarta take kamar zata fashe,tun kallon farko da ta yiwa bawan Allahn taji soyayyarsa na nuƙurƙusar zuciyarta,tabbas son Mahaifin Baby ya kama zuciyarta sosai.
Khairat ta sanya hannunta ta ɗago kan Ummita a hankali,ta ɗora akan cinyarta sannan ta shiga yi mata nasiha akan rayuwa,tare da haƙuri akan ta cire mahaifin Baby aranta,saboda wanda take don shima bai san tana yi ba.
Da sauri Ummita ta miƙe tsaye ta nuna Khairat da hannunta ta ce"Na fahimce ki Khairat,wato in daina sonshi ke ki soshi ko?to bari ki ba zan dai na sonshi ba,sai dai duk abinda za kiyi kiyi,don haka wallahi tun wuri ki fita daga harka ta,tunda bazaki goyamin baya ba,goyon bayan wata kike a madadin ƙanwarki."
Khairat tayi tagumi tana kallon ƙanwarta Ummita,sai take ganin Ummita nan gaba fin ƙarfin kowa za tayi,don tun yanzu gashi ta fara nuna hakan.
Khairat ta tashi a hankali sannan ta kalli ƙanwarta ta ce"babu komai Ummita,tunda haka kika ɗauka cewar nima ina sonshi ne,to ki cigaba da ɗaukar hakan amman ko yarda ko kada ki yarda gaskiya ce sai na faɗa miki,kuma ina fatan Allah ubangiji ya shiryar dake shirin addinin musulunci.tunda ke har yanzu baki san annabi ya faku ba."
Ummita ta wuce da sauri banɗaki ta bar Khairat awajen,Khairat ta zauna tayi tagumi sosai ta tsunduma a kogin tunanin halin da zasu tsinci kansu a wannan,da kuma yadda matar gidan zata kallesu,don ba iya Ummita zata kalla da laifi ba,har ita saboda tare suke kuma yayar Ummita ce.
Halima kuwa tana cen wajen mijinta,bata san ma abinda ke faruwa ba da yake MD mutunne mara ruƙo don haka tuni ta rarrashi abinta,suka cigaba da soyewarsu don MD ko bature haka ya barshi ya ƙyale.
Ashe Ummita na da aiki babba,don indai tana gidansu Halima to sai zuciyarta ta kusa fashewa,don ko agaban Baby ne basa kunyar yin soyayyarsu,don Baby ma bata ɗauki wannan abin a matsayin wani abu ba,tunda dai mata da miji ne don ita an nuna mata cewar matuƙar mijinta ne duk abinda zasuyi lada zasu samu,matuƙar bai take hukuncin Allah ba,kuma an nuna mata haramcin yin hakan ga wanda ba muharraminka ba.
-----*****-----
. . . . .Indo kuwa sam hakan baya damunta,don ita daman ta tsani wani namiji yace yana sonta,to tabbas sai taji tamkar an gingima mata wani dutse aranta,ta rasa dalilin hakan sai dai tasan komai lokaci ne wataƙil nan gaba idan ta samu wanda take so ta dai na jin hakan.
Bayan an tashi daga gaɗar dare,Suna tafiya suna hira ita da Bintu don hanyar gidansu ɗaya ne.
Har sunyi hanyar gida sai kuwa Indo ta chono baki gaba ta ce"Bintu don Allah ki rakani wani waje mana"?.
Bintu ta zaro ido sannan ta ce"haba Indo yanzu fa dare yayi?kuma kinsan faɗa za'ayi min don Allah mu tafi gida Indo,ni dai bana son ki tsokano wani da daddaren nan gwara mu tafi gida"?.
Indo ta juya idonta ta kalli wani layi sannan ta ce"Bintu zaki rakani ko baza ki rakani ba"?.
Bintu tayi shiru bata ce komai ba,Indo ta ce"to aradun Allah idan baki rakani ba sai ki gane kurenki Allah,don duk ranar da aka biyoki na daina tsarw miki faɗa".
Bintu ta ce"Indo muje don ni nasan halinki ba iya tsaremin faɗa zaki dai na ba,nasan sai kin ɓaromin wata wutar muje Indo".
Indo ta sheƙe da dariya sannan ta ce"muguwa Bintu wato baki son in miki tallan silili ko?".
Bintu dai bata ce komai ba,don ita yanzu Indo ma tsoro take bata,don idan tayi wani abun kamar ba ita kaɗai tayi ba.
Suna zuwa ƙofar wani gida Binti taja ta tsaya sannan ta ce.
"Ayya Indo yanzu don Allah bazaki kyale Sunusi ba?ni daman nasan gidan nan zamu zo?abinda yayi miki fa ya kai sati?haba don Allah ke kuwa Indo ki kyaleshi mana?ki dinga yafiya don Allah Indo"?.
Indo tayi mata wani kallo sannan ta ce"to uwar wa'azi,ki kyaleni don wallahi sai na rama abinda yayi min,har sauran duk sai sun gane kurensu don wallahi tallahi bazan barsu ba,tsabar mugunta ban shiga harkarsu a gari ba,sai su saka ayimin wannan ɗan banzan dukan?don sun san Baffana baya nan?Alƙur'an sai na rama da kai na shima me garin zai gane kurensa".
Bintu dai bata ce komai ba,suka shiga gidan Suna shiga suga dinga sallama amman ba'a amsa musu ba,Indo ta ƙare gwale bakinta tayi sallamar da ƙarfi.
Sailuba ta tashi a firgice,ɗanta dake gefenta yana shan mama ta cireshi ta tashi ta fito daga ita sai ɗaurin ƙirji.
Ganin ƴammata a tsaye yasa ta ce"lafiya dai ƴan mata?".
Indo tayi murmushi sannan ta ce"haba baiwar Allah a'i kya bamu waje mu gaisa ko?don mudai ba cutar dake mukazo yi ba".
Ta faɗi hakan tana yiwa Sailuba gwalo.
Sailuba ta ce"kuyi haƙuri ga tabarma nan ku zauna."
Indo ta ɓoye fuskarta tana mata gwalo,sannan ta ƙara gaishe da Sailuba kamar abin arziƙi ta fara ce wa.
"Don Allah kece Sailuba matar Sunusi?".
Sailuba ta gwalo ido waje ta ce"eh ni ce?lafiya dai ko,Allah yasa ba wani abinne ya samu Sunusi na ba?don wallahi ba nida kowa kaf duniyar nan,sai Sunusu don iyaye na sun mutu."
Indo ta langaɓe kai kamar mutuniyar kirki sannan ta ce.
"A'i gwara ma mutuwar Sailuba,da abinda Sunusi yake shirin ɗakko miki" . . . . .✍🏾