P-8
Page⬜8
---------Da sassafe Halima ta tashi,ta shiga kitchen da kanta ta girka musu abincin karyawa,ƙamshi ya fara tashi kai kace gidan amare ne.
Ummita tana ganinta duk abinda take yi,ta cije leɓenta sosai ganin Har Halima ta sauke ferfesun kaza,wanda yake ta tashin ƙamshi gwanin sha'awa yasha kayan ƙamshi.
Halima ta sauke ta zuba komai acikin foodflask me kyau,wacce ba sai an gaya maka ba kasan ta masu kuɗi ce sosai,ta gama jera abincinta akan dining,sannan ta wuce ɗakinta don shiryawa don yau ma MD ya shaida mata da wuri zai fita,saboda ƴan jam'iyayya na nan suna jiransa ta shiga ɗakinsa don tayar dashi.
Ummita na ganin ta shiga ɗakin,tayi wuf ta fito ta shiga kitchen ta duba sosai ta samu gishiri,tayi wata irin muguwar dariya sannan ta ɗakkoshi ta cika chokali har guda biyu ta zuba a farfesun,ta ɗan juya kaɗan yadda babu wanda zai fahimci abinda aka saka.
Da sauri ta koma ɗakinsu,ta iske Khairat tana azkhar,jikinta Ummita yayi sanyi sosai ta sunkuyar da kanta ta wuce.
Khairat ta bita da kallon takaici,don tasan duk yadda akayi wani abin take son a'ikatawa,don tasan halin ƙanwarta aƙwaita da mugun hali.
Halima ta matse sosai acikin ƙananan kaya,tayi kyau sosai daman gata irin siraran mutane ne,irin ƙirar turawa silindium amman Halima nada shape ɗinta dai dai gwargwado.
MD ma yayi kyau cikin manyan kayansa,shadda fara sol sai walƙiya take,yadda kasan wata acikin zarah,Halima sai kallonsa take saboda yadda yayi mata mugun kyau.
Ya riƙo hannunta sannan ya hure mata idonta ya ce"habibty kallon yayi yawa haka?".
Murmushi kawai Halima tayi ta wuce ba tare da ta ce komai ba,suka zauna kan dining Halima ta buɗe komai,ƙamshi ya bugi hancin MD ya lumshe idonsa sannan ya ce"i'm really miss this delicious food Halima".ya faɗi hakan yana janyota zuwa kusa dashi.
A hankali ya fara kurɓar ruwan shayin,sannan ya fara cin farfesun cikin nutsuwa,sai dai yana kaiwa bakinsa yaji wani irin mugun gishiri me firgita harshe.
Da sauri ya furzar sannan ya goge bakinsa da tissue ya kalli Halima wacce itama shi take kalla saboda yadda taga hankalinsa a tashe,uwa uba ma bata san abinda yasa ya furzar da abincin ba.
Baban Baby lafiya kuwa ka zubar da abincin?ko baiyi daɗi bane?".ta faɗi hakan hankalinta a tashe.
Ganin hankalinta ya tashi ne yasa ya ce"next idan zaki zuba gishiri ko magi adanga kula,don gishirin yayi yawa Halima kamar zai cire harshe".
Da sauri Halima ta ce"gishiri kuma Baban Baby?wallahi ni ban ma zuba gishiri ba,magi ne kawai ma sanya?".
Ta faɗi hakan da tsoro fal akan fuskarta,don dai tasan ita bata zuba gishirin ba.
A hankali ya shafi kumatunta sannan ya ce"muje ki rakani Halima don mutanen nan sun dameni,don tun ɗazu suke ta bugomin waya".
Halima ta tashi ta wuce ɗakinta,ta ɗakko jalbab ɗinta ƙato har ƙasa sannan ta rakoshi har waje,sai da securities ɗinsa suka shir shiga motocinsu sannan ta dawo.
Jikinta har yanzu a matuƙar sanyaya yake,gani take tamkar cin fuska MD ke son yi mata,to idan banda cin fuska yaushe ma da ta saka gishirin ita kanta a girkin?saboda ja mata kunne da likitoci sukayi akan ta daina cin gishiri sam,saboda hawan jinin daya sako ta a gaba,sannam sunce matuƙar tana son ta samu ciki to ta ƙauracewa cin gishiri,don yawan cin gishiri yana kawo ruwan mahaifa,daga nan kuma sai kaga cikin yaƙi samuwa.
Ta tashi a hankali ta buɗe foodflask ɗin ta fara shan farfesun,da sauri ta furzar saboda mugun gishirin daya ziyar ce ta,ta goge da tissue tana kallon farfesun cikin mugun tsoro,don ita dai tasan bata zuba gishiri cikin abincinta ba.
Hankalinta ya tashi sosai,ta leƙa kitchen ɗin ta ɗakko gishirin tana dubawa,yana nan a yadda ta ajjesa,mamaki ya kamata sosai to ko dai ta zuba ta manta ne?.
Kasa tuna hakan tayi ta fito ta zauna shiru kan rantsatsun kujerun falon,tana cikin wannan halinne Baby ta fito daga ɗakinta,da kayan bacci ajikinta cikin shagwaɓa ta taho ta ɗora kanta akan cinyar Halima.
Baby ta ce"mom good morning"?.
Halima ta shafa kanta sannan ta ce"ɗazu kin shiga kitchen ne?".
Baby ta lumshe idonta sannan ta ce"No mom".
Halima ta faɗawa Baby duk abinda ya faru,Baby ta ce"Mom kuma su Ummita basu tashi ba"?.
Sai lokacin Halima ta tuno dasu.
Sannan ta ce"gaskiya ko da ace sun tashi bana tunanin zasuyi haka gaskiya,sai dai ina ganin ni ce na sanya gishirin na manta."
Baby ta ɗaga kai kawai,sannan ta shiga ɗakinsu Ummita dukkansu yanzu bacci suke,don Khairat tana gama Azkhar ɗin ta samu kanta a wani irin bacci,sai kuwa ta hau barci duk da tana tunanin tashi ta girka wani abin,amman kuma tana tunanin yin hakam tunda matar gidan bata bada dokar a dafa komai ba.
Baby taga suna barci don haka ta fito daga ɗakin.
Duk abinda ake Baby na jinsu,don har kitchen ɗin da Halima ta shiga ta ganta,sai dai da taji motsin tafiya sai ta koma da sauri,yanzu ma da taga Baby ne yasa ta koma da gudu ta fara barcin ƙarya,zuciyarta fes saboda ganin abinda ya faru,tsakanin Baban Baby da Halima.
Ta tashi ta rufe ƙofar sannan ta hau tsallen murna,tuni ta fara hango kanta acikin wannan tafkeken gidan a matsayin matar aure,matar ma kuma matar Baban Baby kyakkyawan soja,ne cikar haiba da ƙwarjini.
-----*****-----
. . . .Sailuba ta kalli Indo tana zaro fici ficin idanuwanta sannan ta ce"Na higa uku na ni Sailuba?me Sunusi yake shirin ɗakkomin daya fi mutuwa"?.
Indo ta ɗan juya tayi dariyarta son ranta sannan ta juyo..ta haɗe fuska tayi kamar za tayi kuka,ta kalli Bintu ta karkatar da baki gefe sannan ta ce"Bintu in faɗa?ni na kasa faɗa Bintu ke ki faɗa mata"?.
Bintu ta zaro ido waje,Indo na son jaza mata masifa don dai tasan ita bata san wani abin kunyar da Sunusi yayi ba?ita dai tasan tunda ya taɓa Indo baza ta barshi haka banza ba,sai ta horar dashi kafin daga bisani a gane manufarta.
Bintu ta kalli Indo da mamakinta sannan ta ce"ni Indo ban. . . ."
Da sauri Indo ta katse ta da ce wa"to na gane Bintu,kema bakyason faɗar wannan maganar,amman ni dole in faɗawa matarsa don kada abu yayi nisa."
Sailuba ta waro idanuwa tana kallon Su Indo.
Indo kuwa ta gyara zamanta sannan ta ce"daman ɗazu ne da muka taho muka ga Sunusi awajen Lami,suna taɗinsu Kuma ba wannan ce rana ta farko da muka ganshi ba,mun daɗe muna ganinsa kullum idan muka dawo daga Dandali,shine muka yanke shawarar zuwa mu gaya miki,don wallahi Lami iccen kabari ake ce mata,indai har ta shigo gidanka to fa sai ta lalata komai,sai ta sakaki kinyi yawo tsirara Allah idan baki tashi tsaye ba,kika bari aka auro miki ita to alƙur'an kin kaɗe har ganyenki".
Da sauri Sailuba ta tashi tsaye tana ƙunduma ashar kamar bamagujiya.
Indo ta miƙe tsaye tana cewa"to mu dai bari mu tafi,kada yazo ya same mu yace mun kawo miki gulma".
Indo ta faɗi hakan tana wa Sailuba gwalo,irin gwalon nan na sokuwa ce ke.
Sailuba ta ce"na gode muku sosai ƴammata,Allah yabar zumunci yau sai ƙauyen nan ya tashi baki ɗaya,don wallahi idan har na bari aka auromin Lami hegiya nake."
Su Indo suka fara shirin fita,sai kuma ta dawo da baya ta ce"am idan yazo ki faɗa masa Indo da Bintu ne suka gaya miki,don kada yace zai musa miki don nasan yanzu bazai yarda ba,gaddama zaiyi miki don yasan baida gaskiya.
Suna fito Indo ta tintsire da dariya sannan ta ce"a'i wallahi Sunusi zai san ni ya taɓo,da zai kama ni ya hau duka kamar ya samu jaka,a'i yanzu kinga haɗa masa abinda zai zo yana da nasanin yimin wannan dukan".
Bintu ta ce"ni dai ban yafe ba Indo,don me zaki dinga sanya ni acikin masifa?ke aka daka ko ni?da zaki dinga sakani cikin masifa?Allah ni dai Indo na kusa raba hanya dake don ni dai wallahi indai har baki canja hali ba,Allah zan yi hannun riga dake duk kuwa da son ƙawancen da muke.
Indo ta ce"to sai me Bintu?ga hanya nan a'i?ke da kanki ke son ƙawance dani don daman ke ce kika laƙemin kamar mayya,amman mi kinsan ko ajikina,tunda idan ma nayo tsokanar inada ƙarfin ƙwatar kai na."
Bintu tayi hanyar gidansu,don dare har ya fara yi don goma ma ta wuce. . . . . .✍🏾