P-9
Page🟨9
---------Ummita bata bar Halima ba,ta shiga shirya mata munafunce munafunce,duk don dai ta haɗata faɗa da mijinta,sai dai fa duk abinda tayi sai taga cikin lokaci ƙanƙani an manta komai,sosai abin ya baƙanta ranta har ta shiga wani hali,ta shiga yin zazzaɓi sosai a lokacin kuma MD yayi tafiya,daga Su sai halinsu Suka kai Ummita asibiti,sai dai tashi ɗaya likitan ya gano Ummita na da hawan jini.
Sosai Halima ta tsorata,ƴar wannan yarinyar da hawan jini?Bayan sun dawo gida Halima ta shigo har ɗakinsu Ummita,ta same ta a bakin gadonsu ta zabga uban tagumi.
Sosai tausayin yarinyar ya dirar mata,ta ƙarasa da karsashinta ta ɗaho fuskar Ummita sosai tana kallon nata face ɗin ta ce"Ummita don Allah ki faɗamin abinda ke damunki?bana son wannan abinda kike?tun da kuka zo gidan nan nake kula dake,bakya walwala ba kamar ƴar uwarki ba,ko bakya son nan gidan ne?ko kuwa wani abin ake miki wanda yake baƙanta ranki?".
Ummita taji Halima kamar ta soka mata wani irin mashi,taji tamkar ta shaƙe ta kallon fuskar Haliman da take,amman sai ta goge hawayenta ta ce"ba komai Anty kawai dai gani nake kamar kina cikin damuwa ne,saboda yawan tafiye tafiye da mijinki yake yi,dubi fa wannan zuwan da yayi bai fi sati biyu ba,amman har ya koma ya barki ke kaɗai?gaskiya maza ba suda tausayi".
Ummita ta faɗi hakan tana hararar Halima ta gefe,bata san ma me yasa yanzu take ganin Halimar muguwa ba,don gani take kamar tana yiwa mijinta asiri,saboda yadda ko da ta haɗasu faɗa sai taga kuma sun shirya.
Halima taji son yarinyar ya ƙaru acikin zuciyarta ta ce"Ummita dole zan damu mana,amman tafiyarsa itace mafi alkhairi agare ni dama shi kansa ɗin,saboda matsalar da muke ciki ni dashi".
Ummita ta zaro ido waje ta ce"wata matsala kuma Anty"?.
Don tana son jin matsalar da take haɗa Halima da romio ɗin mijinta MD,don a ganinsu babu abinda zai haɗasu kuma duba da yadda suke ƙaunar junansu,gwanin ban sha'awa don yadda suke soyayyar yana ƙona mata rai sosai,so take taga duk wannan son ya tafi sai kuma ƙiyayya don wani buri nata da take son cikawa.
Halima ta share ƙwallar da ta taru a idonta ta ce"Ummita mahaifiyarsa baza ta taɓa bari mu zauna Lafiya ba,kullum naje da problem ɗin da zata zo min dashi,Musamman idan taga yana gari amman yanzu kinga idan yayi tafiyarsa shikkenan."
Ummita na jinta,ta ɗan matso hawayen munafurci ta ce"Allah sarki Anty,gaskiya cikib matsala babba sai dai Allah ya fitar dake."
Halima ta ce"amin Ummita,yanzu dai tashi muje fali muyi hira tunda dai kin samu lafiya,kuma yau dai naji damuwarki".
Ummita ta ce"to Anty".
Amman fa ba don taso hakan ba,Halima ta wuce gaba itama ta biyo ta a baya,tana jin kamar ta tsire Halimar kowa ya huta.
Hira ake sosai,ammanfa ita hankalinta yaba kan wani ƙaton hoton MD wanda yayi kyau matuƙa gaya.
Khairat ta fuskanci abinda take kallo,ta juya ta kalli Halima da Baby taga hankalinsu baya wajensu,sai kuwa ta taso da sauri ta rufe idon Ummita,ta raɗa mata wani abu acikin kunnenta sannan ta buɗe mata idon.
Ummita ta galla mata harara,sannan ta tashi ta shige ɗakinsu don ita shi kansa gidan ma ta tsaneshi don bata samu abinda take so ba har yanzu.
Khairat na ganin hakan tabi ƴar uwarta ɗaki,tare da rufo ƙofar don kada ma su Halima su biyo su,duk tasan ba lallai suyi hakan ba don Halima bata fiya shiga ɗakinsu ba.
Baby ce daman me yawan shiga,don Baby aƙwaita da son hira sosai.
Ta harɗe hannayenta a ƙirji,tana tsaye bakin ƙofar ɗakin bayan ta rufe,tana hango ƙanwarta tayi ruf da ciki alamar tana tunanin nata da ta saba.
Ta ƙarasa har inda take sannan ta ce"Ummita wai meye ribar wannan halinda kika saka kanki ne?me yasa kike son janyo mana masifa haka?kina tunanin idan kika cigaba da hakan mutanen gidan baza su gano halin da kike ciki ba?ko kuma an gaya miki ba suda ƙwaƙwalwar da zasu gano hakan?gaskiya Ummita wannan ƙazamar rayuwar da kika jefa kanki tayi miki tsauri da yawa,ki sassautawa kanki ki cire mutumin nan aranki,tunda shi bai ma san kina yi ba abinda ya sani kawai shine matarsa da ƴarsa,kuma kinga alkhairan matar nan awajenmu bai kamata muci amanarta ba,mu zamo masu cika alƙawari ba masu Butulci ba". . . . . . . . . . . .
Tun kafin ta ƙarasa Ummita ta daka mata wata irin tsawa,wacce tasa Khairat gimtse maganar ba tare da tayi niyya ba.
Don ita a halin yanzu ma ta fara tsoron Ummita,tamkar dai Ummita ɗince yaya ita kuma ƙanwa,don daman can ba'a nunawa Ummita yiwa yayarta biyayya ba,saboda ita ƴar so ce shiyasa ba'a koya mata hakan ba.
"Khairat na gaya miki ki fita harkata ko?don me ba zanso shi ba?saboda matarsa?to bari kiji indai har kika ga ban auri Baban Baby ba to mutuwa nayi,don Wallahi kinji na rantse ko ta wata hanya sai na aure shi.
Khairat ta ce"Ummita kin san abinda kike faɗa kuwa?kina son ki jefa kanki cikin masifa ko?wannan wani irin so ne haka?don ni dai a tarihi ban taɓa jinsa ba."
Ummita ta juya abinta ta cigaba da aikin tunaninta,ta bar Khairat anan tsaye tana tunanin halin da Ummita ke ciki.
Suna hirar Halima ta neme su ta rasa,Baby ta ce"Momy aƙwai abinda kike nema ne?".ta faɗi hakan tana kallon Halima wacce ke ta kallon gefansu,don dai tasan anan ta bar su Ummita yanzu kuma taga ba ta gansu ba.
-----*****-----
. . . .Suna cikin hirar suka ga Sailuba ta fito daga cikin gidan cikin mugun fushi,daga ita sai ɗaurin ƙirji sai kuma zanin da ta goya ɗan ta,wanda yake barcinsa hankalinsa ƙwance.
Indo ta tintsire da dariya ta ce"haka nake so Sailuba,so nake taje ta tarwatsa wannan nishaɗin,ta haukace masa yadda zai kasa gane komai,ta yadda zan sanya musu rigima me ƙarfi a tsakaninsu,sai yazo ya dafa ƙafa ta ya ce don Allah Indo ki yafe min,don kinsan tunda ya taɓoni sai yasan ya taɓoni don wallahi bazan yarda yaci bulus ba.
Bintu ta ce"Hmm ke kam Indo kin fi ƙarfina wallahi,ni ban ma san abinda yasa na tafi gida na dawo wajenki ba?".
Indo ta kyalkyale da dariya sannan ta ce"hegiya Bintu wato kin gano amfani ko?daman idan kaga kare na shinshina takalmi to yasan abinda ya hango,da bani da amfani da tuni kin fita a harkata."
Bintu taja hannun Indo wai au tafi gida,Indo ta fizge hannunta ta ce"ke Bintu kyale ni a'i dole sai naje naga yadda abin zai kaya,ko so kike in tafi gida banga yadda zasu kaya ba"?.
Ta fisge hannunta tayi gaba abinta,Bintu ta kalli ƙawarta kallon tausayi don ita yanzu Indo tausayi ma take bata,ayi mutum bai da aiki sai tsokanar mutane da son tashin hankali?ita Indo wacce irin mutum ce?babu yadda zatayi da halin Indo,kuma baza ta iya rabuwa da Indon ba don son Indo azuciyarta yake,sai dai kullum addu'arta Allah ya shirye ta.
Sailuba na zuwa ƙofar gidansu Lami ta hango mijinta Sunusi,sai tsara Lami yake ya kafo hularsa a gaba yana mata daɗin baki.
Sailuba ta wuce ta tsaya a tsakiyarsu tana kuka ta ce"wallahi She Allah ya kamaka mugu azzalumi kawai,macuci maci amana yau Allah ya toni asirinka."ta faɗi hakan tana kuka sosai,jin tana kuka sai ɗan tama ya fara kukan sosai.
Sunusi yayi tsuru,kamar kazar da ƙwai ya fashewa aciki,ya buɗe bakinsa xaiyi magana Sailuba ta ce"yimin shiru Sunusi,babu abinda zaka ce min ashe daman wajen wannan ƴar iskar karuwan kake zuwa?wajen wannan shaiɗaniyar ka tare?so kake ka ɗebomin masifa da ƙazanta ka kawo min gida?Allah ya wadaran Halinka Sunusi".
Sunusi ya kasa magana,saboda iya kunya yau dai ya jita kuma yasan halin Sailuba da mugun taurin kan tsiya,ba tafiya za tayi ba tunda taja ta tsaya ɗinnan.
Lami ta kalli Sailuba kallon sama da ƙasa ta ce"kan uba ni kike antayawa zagi haka?to wallahi baki isa kisha ruwa ba yau,sai na cire miki haƙoranki kaf kin kasa tauna ko da abinci ne,tunda ke agidanku ba'a koya miki tauna magana ba".
Ta kawowa Sailuba wani mugun naushi,don Lami irin manyan matan nanne masu ƙiba ta ko'ina.
Da sauri Sunusi ya kai hannunsa don ya tare dukan da Lami ta kaiwa Matarsa Sailuba,ji kake ƙum-ƙum an buge Sunusi a bakinsa.
Indo ta sau dariya a inda take har tana riƙe ciki tana ce wa"Hegi Sunusi yau sai anyi maka ruwan zafi". . . . . . . . .✍🏾