RASHIN SANI…

62

by @hauwaausmanjiddarh

_*RASHIN SANI.......*_





*HAUWA A USMAN*

    _JIDDARH_




'''Wattpad:HauwaAUsmanjiddarh'''





6⃣2⃣





Cikin zunzurutun tashin hankali Khulud ke kallan Sanah tana girgiza mata kai,

jikinta na rawa da kerrrrma ta nufi Sanah dake tsaye idonta kanta,

ta dafa kafad'arta tace " no..! please karki yi min haka dan girman Allah,

ta fad'a yadda babu mai jin abinda take cewa,

murmushi tayi tare da cewa " dole nayi miki haka,

lokacin dana so rufa miki asiri ni tuna min nawa kikayi,

lokacin dani na nemi taimakonki k'in taimako na kikayi,

" wai yama zakice karka nayi miki haka....!?


"So kike nayi ta zama da auren wanda bai sani ba a kaina.....!?


" Ko so kike yi ni rayuwata ta k'are a haka ba tare dana mori komai daga gare ta ba....!?


"Ko kina nufin nayi ta zama da aure har k'arshen rayuwata....!?


" Dan girman Allah ki rufa min asiri,

wallahi a yau zan saka shi ya sake ki,

amma dan Allah karki tona min asiri,

" kiyi hak'uri Khulud hakan ita kad'ai ce mafita,

hakan ne kad'ai zai kawo k'arshen komai,

ya kuma bayyanar da gaskiya,

ta yadda kowa da zai san meke faruwa a tsakanin mu,

duk irin shak'uwar dake tsakanin d'a da mahaifi amma Dide da Juju kasa tantace Khulud d'in gaskiya suka yi،

haka ma Abbu da Mamu kwata-kwata basu gane Sanah ba,

cikin rawar murya Abbu yace " wai meke faruwa ne....!?


"Ke wacece، daga ina kuma kike....!?


Ya fad'a yana kallan Sanah,

murmushi tayi gami da kallan Sir Moli،

dake tsaye hard'e da hannuwanshi a k'irjinshi,

yayi mata alama data cire fuskar da voice maker,

babu musu Sanah ta cire fuskar da voice maker d'in,

ai sai lokacin suka k'ara shiga cikin rud'u da tsantsar tashin hankali,

saboda tsabar tsoro Jaddah bata san sanda ta soma hawaye ba,

Halan ta kalli Mamu tayi mata alama da kinga ni ko...!?


Itama Mamu Abbu ta kalla wanda ke tsaye tamkar an dasa shi,

gumi ya gama jik'a shi sharkaf,

Dide kam shiru yayi ya kasa koda motsi haka ma Juju,

Sanah tayi murmushi had'i da cewa " yau in sha Allah gaskiya zatayi halinta,

sirrin b'oye zai fito fili, kowa zai san gaskiyar al'amari,

cikin nutsuwa Sir Moli yayi gyara murya,

" dan Allah kowa ya zauna akwai sauran bayanan da zamu tattauna,

jiki babu kwari duk suka zauna,

yayinda Ziyad ya rarrafa ya rab'e jikin Halan,

Hanash ko motsi ya kasa yi balle ya samu damar zama,

Sir Moli ya kalle shi yace " dan Allah ka zauna Hanash...!

gumi na ketowa Hanash yace " cigaba please,

yayi kamar wani sokoko,

ganin yanayin dayake ciki yasa Sir Moli mai da kanshi ga sauran jama'ar,

had'i da yin gyaran murya a karo na biyu,

ya d'aga diary d'in Papu yace " wannan shine littafin aje muhimman bayanai na Marigayi Alhaji Waseef,

wanda a turance ake kira da diary,

mamallakin littafin Marigayi Alhaji Waseef Papu yayi rubutu kamar haka,

_" ni Waseef na d'aura auren d'ana Hanash Waseef,_

_da 'yar aminina Sanah Hamraz na d'aura musu aure a yau ranar 10/ May/2018 wanda yayi dai-dai da hijira ta 1439 5 ga watan Shawwal,_

_akan sadaki naira dubu d'ari 100k,_

_a gaban shaidu mutum shida bayan ni waliyin Sanah,_

_da Malam Udu driver na wanda shine yayiwa Hanash waliyanci,_

_bayan na tabbatar da Sanah ta yarda ta kuma amince,_

_shima kuma Hanash ya amince akan zan aurar dashi,_

cikin rud'u Hanash ya sunkuya gami da dafe kanshi yana tuna lokacin da Papu ya kira shi kan maganar aure.


Shekara d'aya da watanni da suka wuce a baya


Bayan Khulud da Sanah sunzo kan maganar auren Hanash da Sanah,

Papu ya kira Hanash parlor'n shi,

Papu da Hanash zaune cikin parlor,

Papu ya kalli Hanash yace " gaskiya Hanash hankalin mahaifiyarka ya tashi sosai akan rashin haihuwarka,

dan haka ina son ka k'ara aure,

a razane Hanash ya d'ago kanshi ya kalli Papu tare da cewa " aure fa kace Papu....!?


"Eh...! aure nace Hanash, matuk'ar kasan ba kai ne keda matsala ba,

dan hakan shine kad'ai zai kawo zaman lafiya da masalaha,

gami da kwantar da hankalin mahaifiyarka da kuma tawa mahaifiyar,

saboda suna cikin tashin hankali kan rashin haihuwarku,

gwara ka k'ara ko itama kanta Khulud d'in ta huta hankalinta ya kwanta,

cikin marairaice murya Hanash yace " dan Allah Papu kayi hak'uri,

amma ni bani da shawa'ar tara mata,

ko yin mace fiye da d'aya, 

" Hanash dole ka k'ara aure,

kodan cikar kamalarka da mutuncinka,

ka sani babban burin kowanne mutum a duniya bai wuce yaga yayi aure ya samu zuri'a ba,

Annabi SAW da kanshi yace kuyi aure ku hayayyafa dan nayi alfahari daku ranar alk'iyama,

kamalar mutum bata gama cika har sai yana da iyali da zuri'a,

" ni dai dan Allah Papu ka barni dan Allah bazan iya k'ara aure ba,

matata d'aya ta ishe ni 

cikin zafin rai Papu yace " yanzu Hanash ni ke yi maka magana kana yi min musu da gardama...!?


Kanshi ya sunkuyar cikin girmamawa yace " kayi hak'uri dan Allah,

" to ba shawarka nake nema ba,

umarni na baka, dan haka yau ka fito da matar da zaka aura idan kuma baka da ita,

ni zan zab'a maka,

kanshi k'asa yace " bani da ita, ka zab'a min d'in،

" ka yarda na zab'a maka na aura maka ko wacece...!?


Eh..! kayi komai kawai, duk abinda ya dace kayi ba saika shawarce ni ba,

na bar maka komai a hannunka,

" kai da bakinka kace ka yarda na aurara maka kowacece ko....!?


"Eh...! na yarda na amince kayi min aure,

" Allah yayi maka albarka ka baka zuri'a ta gari,

"amin ya Rabbi.


Cigaba.....


Tunowa da wannan yarjejeniyar tasu yasa Hanash dafe kanshi,

a hankali Sir Moli ya taka gaban Abbu da Dide ya mik'a musu diary d'in,

hannun Dide na rawa ya amsa,

daga k'asa yaga sa hannun Papu da stamp d'in company shi,

cikin sanyin jiki ya mik'awa Abbu,

shima ya kalla, ya mik'awa su Zafran, wannan mik'awa wannan,

haka sai da kowa ya gani, kana Sir Moli yayi tattaki gaban Hanash ya mik'a mishi,

hannunshi na rawa ya amsa,

tabbas wannan sa hannun Papu ne,

da kuma company stamp d'in su,

duk parlor'n aka yi jugum-jugum,

kowa da abinda yake sak'awa cikin ranshi,

cikin zafin rai Hanash ya mik'e tsaye gaba d'aya gumi ya gama jik'a shi sharkaf,

yana k'ok'arin yin magana,

 Sir Moli yayi murmushi yace " koma ka zauna me akayi, ai da saura....!?


A harzuk'e Hanash yace " waya baka dama da izinin d'aukar diary Papu...!?


A hankali Sir Moli ya ciro ID card d'inshi ya nuna mishi gami da cewa " I have a right na shiga gidan kowa nayi bincike,

hukuma da doka sun bani damar yin hakan,

" waya baka details d'in mu....!?


Hanash ya fad'a muryarshi na rawa saboda tsananin tashin hankali,

" kwantar da hankalinka، ka koma ka zauna na baka labari,

Hanash zayyi magana Mimmee ta kamashi ta zaunar danta fahimci baya cikin hayyacinshi.


Labarin baya.....!


Kasancewar a cikin labarin da Sanah ta bawa Sir Moli ta sanar dashi,

cewar lokacin data haifi Sultan Papu yaje hospital kuma har yayi musu video,

yasa Sir Moli zurfafa tunaninshi ta yadda zayyi ya samu wayar Papu da kuma diary shi,

danya tabbatar zai samu wani abu cikin diary'n da zai iya taimakonsu,

tsayar da tunanin shi yayi kan mai gadin gidan,

dan haka batare da b'ata lokaci ba ya fita ya hau motar shi ya nufi gidan Papu،

a k'ofar gidan yayi parking gami dayin horn mai gadin ya lek'o Sir yayi mishi alama da yazo,

ba musu mai gadin ya k'arasa ya tsaya daga d'an nesa da Sir Moli,

cikin nutsuwa Sir Moli ya k'are mishi kallo,

ya gano abubuwa da dama dama a tattare da mai gadin ciki kuwa harda tsananin tsoron dayake ciki,

" ka saki ranka taimako na zakayi dan Allah,

" ba damuwa ina jinka, cewar mai gadin,

Sir Moli yace " kana shiga cikin gidan nan part d'in Marigayi Alhaji Waseef....!?


"Malam lafiya me kake nema....!?


Murmushi Sir Moli yayi kana yace " ni lawyer ne kuma ina bincike ne,

d'an shiru mutumin yayi idonshi kan Sir Moli,

kana yace " tayaya zan yarda da kai....!?


ID card d'inshi ya ciro ya nunawa mai gadin gami da cewa " ka iya karatun boko.....!?


"Eh...! na iya,

" tom karb'i ka duba, amsa yayi ya duba kana mayarwa da Sir Moli,

amma duk da haka bai gama yarda da Sir Moli ba,

dan har lokacin a tsorace yake,

yace " to yanzu me kake so....!?


"Taimako na zakayi, Sir Moli ya bashi amsa,

cikin rashin fahimta yace " wanne irin taimako....!?


"Dan Allah ka taimaka min ka shiga part d'in Marigayi Alhaji Waseef ka d'auko min wayarshi da diary'n shi,

wani irin kallo mutumin yayiwa Sir Moli kana ya juya yana niyyar tafiya,

da sauri Sir Moli ya bud'e motar ya fito ya tari gaban mutumin,

" dan Allah Malam ka taimaka min mana,

wallahi ko nawa kake so zan baka,

" kana san kaja min matsala, ka jefani cikin masifa da bala'i ko....!?


"Ko kana san na rasa aiki na ne....!?


" A'a babu d'ay, idan sun kore ka ko an samu matsala kazo zan baka wani aiki,

ko na baka jari mai tsoka, yanzu ma d'an jira ni na soma baka na shan drink,

cikin motarshi ya koma ya d'auka bundle na 100k guda biyar make 500k,

ya mik'awa mai gadin yace " ga wannan ka soma maneji dashi kafin ka kawo min,

hannunshi na rawa ya amshi kud'in ya k'ank'ame su tsam bakinshi har kunne yace " duk wannan nawa ne....!?


"Eh...! naka ne na kuma baka su kyauta,

idan ka gama aikin dana saka ka zan kuma baka wasu،

kamar yadda idan suka kore ka daga aiki zan baka wani aikin,

washe baki yayi yace " to madalla...! yanzu me kake so ayi.....!?


"So nake ka samo min diary'n Papu da wayarshi,

" indai wannan ne babu damuwa gobe ka dawo ka amsa,

" to tayaya zaka samo dan bana san a samu matsala fa....!?


"Karka damu cikin gidan nan nake zaune da me d'aki na Maman Lailah a BQ,

kuma ita keyi musu aikin cikin gida,

duk bayan kwana biyu uku tana share part d'in ta gyara dan karyayi k'ura,

shiru Sir Moli yayi kana yace " ka tabbatar babu matsala....!?


"Eh....! in sha Allah babu wata matsala,

godiya sosai Sir Moli yayi mishi kana ya juya zai tafi,

mai gadin yace " dan Allah ka tabbatar ba cutar da mutanen gidan nan zakayi.....!?


"Ba cutar dasu zanyi ba, dan ni ba macuci bane,

" haka ne, nagode sosai,

bayan kwana biyu Sir Moli ya koma ya karb'i diary da wayar.


Cigaba....


Idonshi kan Hanash yace " to kaji yadda akayi na samu diary da wayar Papu,

bayyi magana ba da ido kawai yake bin Sir Moli,

cikin nutsuwa Sir Moli ya juya yayi connecting system d'inshi da micro led tv dake parlor'n,

take videon da Papu ya d'auka a hospital lokacin da aka haifi Sultan ya bayyana,

dai-dai inda Papu yace " masha Allah kamarshi d'aya sak da ubanshi,

sai dai yafi Hanash fari ya biyo su Abbu, amma bakinshi irin na Sanah ne,

Sultan Papu ya mik'awa Sanah ta amshe shi hawaye na zubo mata,

duk maganganun da sukayi a lokacin tsakanin Papu, Sanah da Khulud sai da ya bayyana, 

har zuwa lokacin da Sanah ta dank'awa Khulud kyautar Sultan,

da maganar suka fad'awa junansu,

duk sai da kowa ya gani,

(Wanda ya manta abinda ya faru a lokacin ya duba page 53),

yana k'arewa Sir Moli ya kuma connecting system d'inshi da camera،

video da Sanah taje gidan Khulud ya bayyana tun daga farko har k'arshe،

har zuwa wajen da Sanah tayiwa Khulud tambayoyi tana bata amsa.


Gaba d'aya parlor'n gaurayewa yayi da maganganun mutane wasu na salati,

wasu na jimami da tafa hannu,

Hanash ko dashi da babu duk d'aya ne,

dan kwata-kwata bai ma san a duniyar da yake ba,

Khulud ji tayi yadda kasan an zare mata ranta da rayuwarta gaba d'aya,

lokacin d'aya komai nata ya tsaya cak,

harta jinta da ganinta d'aukewa yayi,

bata tab'a tsammanin wannan bak'ar kuma mummunar ranar tana zuwa ba,

shiyasa koda wasa bata tanaje ta ba,

duk inda kake tsammanin tsantsar tashin hankali to Khulud tana cikin shi,

shiru kawai tayi tana tunanin ta inda zata b'ullowa al'amarin,

jikinta ba b'ari ta rarrafa taje gaban Sanah,

muryarta k'asa-k'asa yadda babu mai jin abinda zata ce...!

ta soma yiwa Sanah rad'a " kin cuce ni kin tarwatsa min yau da gobe ta,

amma ki sani kema bazan tab'a barinki ki rayu cikin salama da kwanciyar hankali ba,

kamar yadda kika kunya ta ni,

kema sai na kunya ta ki....

kamar yadda kika tozarata ni cikin jama'a,

bazan tab'a mutuwa batare danaga ke kema kin tozarta ba,

kin wulak'anta ni kin ci min mutunci sannan kin tona min asiri,

wallahi tallahi ko zan mutu kema saina wulak'anta rayuwarki,

gobenki da duniyarki.....!

cikin zallar bak'in ciki da takaici hawaye suka soma suntirin zubowa daga idanuwan Sanah,

tace " dama alkhairi ya kan iya izama sharri....!?


"Dama taimako yana iya komawa butulci....!?


" Dama soyayya da k'auna suna iya rikid'ewa lokaci d'aya su koma zallar k'iyayya...!?


"Dama kana iya bawa mutum farin ciki ka sanya rayuwarki cikin farin ciki da walwala shi kuma ya rink'a k'ok'arin jefaka a bala'i, da bak'in ciki....!?


" Dama kana iya k'untata rayuwarka da duniyarka dan ka haskaka ta wani, shi kuma ya butulce maka ya jefa ka cikin uk'uba da rad'ad'in rayuwa....!?


"Duk so da k'aunar dana yi miki da abinda zaki saka min dashi kenan Khulud.....!?


" Ki tuna a kanki fa na lalata rayuwata da gobe na, 

na kuma ci amanar iyaye na da masoyi na,

a kanki ke d'aya tak na jefa dubban mutane cikin k'unci da azabar rayuwa,

a kanki babu abinda banyi ba Khulud,

amma ni kike nema da sharri kike bibiyar rayuwa ta da mugun nufi da bala'i.....!?


"Me nayi miki a rayuwa, why Khulud....!?


" Soyayya fa kad'ai na nuna miki,

na kuma nuna ina san farin cikin ki fiye da nawa,

daga haka me nayi kuma.......!?


"A kanki na maida kaina sakarai shasha sannan hotiho,

na maida kaina tamkar wacce bata san abinda take yi ba,

wacce bata san ciwon kanta da zafin rayuwarta ba,

na mayar da kai na mahaukaciya dabba kuma jahila mara wayo,

duk fa dan kiyi farin ciki,

saboda baki da cikekkiyar lafiya,

murmushi Khulud tayi tace " waya ce miki bani da lafiya.....!?


" A gaba na nurse tace baki je amsar magani ba,

daga baya dana tambaye ta tace min kina da hawan jini da ciwon zuciya,

idon Khulud kan Sanah tana murmushi,

tace " kin san wani abu.....!?


Da ido kad'ai Sanah ke bin Khulud,

tana murmushi tace " wannan ma k'arya ne, setup ne,

ni na bawa nurse d'in kud'i na kuma fad'a mata haka nace ta fad'a miki.....!

bakin Sanah na rawa tace " meyasa......!?


"Saboda na rink'a juya ki san raina,

ta yadda duk abinda nace kiyi ko na sakaki zakiyi babu musu,

batare da gardama ba, haka ma maganar dana fad'a a labour room lokacin da kina labour'n Sultan itama k'arya ne,

setup ne, na fad'a ne danna tabbatar kina ji na, maganar kuma zatayi tasiri a zuciyarki,

saboda nasan kina so na, sannan......!

" dakata ya isa please....! Sanah ta fad'a tana kuka,

" idan na fahimce ki da soyayyar da nake yi miki kika yi amfani wajen cimma burinki ko.....!?


"Wow so brilliant girl shiyasa nake sanki saboda kina da kwakwalwa,

da saurin gane wasu abubuwan,

to kusan hakan d'inne, but never trust anybody in life kodan gaba,

continue play the game bari muga waye loser waye kuma winner,

sa ido kiga wani sabon salon nawa,

ta fad'a tana mik'ewa, kasancewar maganganun da akeyi a parlor'n ya d'auke hankali da idon kowa,

dan haka babu wanda ya lura da abinda ke wakana tsakanin Sanah da Khulud,

cikin makirci Khulud ta d'ora hannu a ka gami da kurma ihuuuuun kuka,

" wayyyo na shiga uku yau naga tuggu da makirci,

way.......!

a hankali Sanah ta mik'e idonta d'auke da hawaye ta nufi Hansh dake zaune k'asa ya d'ora kanshi saman cinyar Mimmee,

duk ilahirin jikinshi na kerrrrma da tsuma,

hak'oranshi na kafffff-kafffff,

a hankali ta durk'usa a gabanshi had'i da jefa idonta cikin nashi,

suna had'a take gaba d'aya tsikar jikinshi ta mik'e,

yaji wani yarrrrr tun daga cikin kwakwalwarshi har zuwa tafin k'afarshi,

gaba d'aya parlor'n tsit akayi kowa ya zuba musu ido yana jiran abinda zai biyo baya,

har ita kanta Khulud d'in shiru tayi tsaye hannunta aka, tana kallansu,

cikin nutsuwa da muryar kuka Sanah ta soma magana ,

*MAN....!* kanshi ya dafe da duka hannayenshi biyu، saboda barazanar tarwatsewa daya soma yi,

ta cigaba da magana " ka tuna daren farkon mu.....!?


"Kai da bakinka kace abinda ya faru a lokacin yayi kama da kayi disvirgin mace،

kace abinda ya faru a wancan lokacin yayi kama da ka cirewa cikekkiyar budurwa burcinta ka tuka......!?


" Ka tuna ihunnnnn kuka da dana rink'a yi a lokacin da maganganun dana rink'a fad'a maka......!?


"Kai da kanka a lokacin cewa kayi impossible،

ka tuna kace tabbas ka karb'i budurcin mace a ranar.....!?


" Ka tuna kace kayi abinda babu wani d'a namiji daya tab'a yi a rayuwarshi، kayi disvigin mace d'aya sau biyu.....!?


"Ka tuna lokacin dakake cewa ka jiyo shashshekar kuka daga cikin bathroom har kake k'ok'arin shiga.....!?


" Idan baka manta ba a ranar kuka je dubo ni a hospital bani da lafiya,

Hanash k'addara ta riga fata,

k'addara mace ce mara tabbas da a koyaushe tana iya canjawa,

Destiny....! Lots of folks confuse of bad management with destiny,

destiny is no matter of chance it's matter of choice's،

It's not a thing to be waiting for, it's a thing to be achieved،

our destiny change with our though,

ka tuna munyi wannan maganar da kai Man......!?


" Ka tuna sanda nace maka rabuwa ta zama dole a tsakanin mu, ko kana so ko baka ko, saboda ni matafiya ce , ba madauwamiya bace, dole akwai ranar rabuwa ta har abada......!?


" Zaka iya tuna lokacin da Jaddah taje gidan nake ce maka ina da gadon gidan dan nafi iko da gidanka akan gidan uba na.....!?


"Farin ciki kai ne baiwa zuciya,

bak'in ciki in tai ka saka ta dariya,

dana gane ka sai inji nazam sarauniya aure da kai ba wanda zai san dashi,

ka manta kana k'arasa min da koda baki nan kina nan zuciyaaaaa....!,

na kulle ido na akan so da k'auna kuma bar kira na ni ita kad'ai na gano,

dake zani zauna in morewa rai na,

ka tuna wannan wak'ar.....!?


Ido Sir Moli ya lumshe hawaye na zubo mishi,

ganin irin kallan da Sanah ke yiwa Hanash,

shi kad'ai ya san me gani cikin kwayar idanta,

da irin kallon da suke jefan junansu dashi,

wanda shi yasan ya rasa Sanah kenan har abada,


" Ka tuna ranar daka je gidan mu ni da kai muka kasance a parlor'n har tsakiyar dare......!?


"Ka tuna sanda kaje gidan mu Yaya Ziyad ya biyo ni da gudu nayo wajenka ina kiran sunanka Man.......!?


" Ka tuna iya yawan ce maka kayi min alk'awarin zaka kula da abinda ke cikina, zaka rik'e shi bazaka tab'a bari yayi kukan maraici da kewar mahaifiyarshi ba, zaka bashi ingantacciyar tarbiyya......!?


"Nace maka ka zame mishi uwa kuma uba, danni bazan rayu dashi ba,

nace maka ka kula dashi sosai ka zame mishi garkuwarshi......!?


Man! ka tuna.......! cikin rud'u da kerrrrma jiki Hanash ya mik'e yana dafe da kanshi,

idanuwanshi sun kad'a sunyi jajir kamar gauta,

yayinda gaba d'aya ilahirin jikinshi ke rawa yana tsuma da b'ari,

while yana jin zuciyarshi kamar zata fasa k'irjinshi ta fito,

mak'ogwaranshi ya bushe, yawon bakinshi ya koma mishi tamkar mad'aci,

a hankali ya sanya hannunshi d'aya ya dafe k'irjinshi,

gaba d'aya gumi ya gama jik'a mishi jiki,

yace " stop....! please ya isa haka,

na yarda....! na kuma amince cewar ke MATATA CE........!

ssakamakon mahaukacin ihuuuuun da Khulud ta fasa yasa Hanash yin shiru,

while yana tsayen ya d'an rankwafa,

hannunshi na dafe da k'irjinshi,

cikin ihuuuuun kuka Khulud tace " wallahi Allah k'arya take makirci Sanah ta shirya danta raba ni dakai,

Sir Moli tsaye yayi yana kallan Khulud cike da tsantsar mamaki da al'ajabi,

dan tunda yake bai tab'a ganin mutum irin Khulud ba,

duk da halin dayake cikin na hango wani abu cikin kwayar idon Sanah,

bai hana Sir Moli taraddabi ba,

kai Hanash ya shiga girgizawa " a'a Khulud kece ke k'arya kuma kece ke shirya makirci,

please let the game over here,

wasan ya isa haka please,

idan k'arya Sanah take ya akayi tasan abubuwan dake baki san su ba......!?


"Idan karya take ya akayi tasan wasu sirrika na.....!?


" Ya akai tasan abubuwa da dama a kaina.....!?


"Ya akayi ke ko sau d'aya baki tab'a kira na da Man ba....?


" Wallahi k'arya take yi Hanash ka saurare ni please,

murmushin takaici da bak'in ciki yayi yace " tsakanin ku wacece ta rarrashi ni lokacin mutuwar Papu.....!?


"Ni ce, Sanah ta bashi amsa, kallanshi ya mayar ga Khulud yace " naji Sanah k'arya take yi,

amma ko zaki iya fad'a min maganganun da mukayi dake ranar......!?


"Good...! Sir Moli yace yana murmushi,

" uhunnnn hummmm am....am...am,

hannu ya d'aga mata yace " ya isa Khulud,

cikin nutsuwa Sanah tace " ka fad'a min cewa " Papu ya baka amanar su Mimmee da Jaddah, 

ya kuma yi maka nasiha sosai akan ka kula da ahalinshi,

sannan na baka hak'uri na tunatar dakai k'addara, ko ba haka bane.....!?


Khulud na k'ok'arin yin magana Ziyad ya mik'e a fusace ya kifa mata gigitattun marika,

kamar suna jira Zarfan, Aarib da Idrak duk suka mik'e suka shiga dukanta yadda kasan sun samu jaka,

kafin kace me sun had'a mata jini da majina sunyi mata laga-laga,

fata-fata kanta da bakinta suka fashe sai jini suke zubarwa,

Abbu, Dide, Mamu, Juju, Hamraz, Nisah, Erum, Gahez, Halan, Jaddah, Mimmee, Zohal da Wajnah da sauran jama'ar dake parlor'n duk suka yi shiru cikin jimami da al'ajabi kowa yana cike da tsantsar mamaki,

saboda yadda k'attin maza har gudu hud'u suke dukanta yasa cikin k'ank'anin lokaci suka sab'ata mata kamanninta,

lokaci d'aya ta canja, tun Khulud na ihuuuuun kuka tana neman ceto harta ta daina iya koda d'aga hannunta,

cak numfashinta ya d'auke ta sume a wajen,

amma saboda tsabar bala'i maimakon su zuba mata ruwa ta farfad'o,

sai suka cigaba da dukanta, kamar yadda duka ya sumar da ita,

haka duka ne ya farfad'o da ita,

duk cikin parlor'n babu wanda yayi k'ok'arin dakatar dasu,

sai da suka kaji dan kansu suka kyale ta,

cikin rawar murya Dide ya kira sunanta,

Khulud.....! ko motsa kasawa tayi saboda tsabar wuya,

bai damu da halin datake ciki ba,

ya cigaba da magana " idan har nine mahaifinki, wanda ya haife ki, a yau a yanzu yanzun nan na baki umarnin ki fad'i gaskiya, 

matuk'ar kika b'oye dai-dai da kwayar zarra daga gaskiya Allah ya isa ban yafe miki ba,

kuma wallahi tallahi saina tsine miki anan take a gaban kowa,

Juju na kuka sosai tace " wallahi nima idan baki fad'i gaskiya ba,

Allah ya isa tsakani na dake kuma ban yafe miki shayarwar danayi miki ba...........!


Cikin matsanancin kuka da bak'ar wuya Khulud ta rarrafa ta rik'e kafafun Dide,

cikin zafin rai yayi ball da ita ,

zaki fad'a ko saina tsine miki, cikin kuka Khulud ta soma basu labarin duk abunda ya faru tun daga farko har k'arshe,

ta kwashe komai kaf ta fad'a musu batare data rage komai ba,

Dide na k'ok'arin yin magana aka ji timmmmm.....! juyawar da zasu sukaga Hanash ya fad'i k'asa,

a sume wani irin barin abu yana fitowa daga bakinshi (dafarar mutuwa),

idanuwanshi suka kakkafe, cikin tashin hankali Sanah tayi kanshi,

ta soma girgiza shi tana kiran sunanshi a haukace "HANASH.............!








MOMYN ZARAH     'YAR BAIWA