GABATARWA.
WATA ZUCIYAR lamarin ta sai Allah, halayyar mutane yanzu butulci yayi yawa yayinda halacci yayi kaɗan, hassada, kyashi sun mamaye zuciyoyin mu, yayinda son ganin juna a tsakanin ƴan uwa Musulmi ya zama wani abu mai sauƙi, son ɗaukar fansa akan wani ƙaramin laifi.
WATA ZUCIYAR labarin wani attajiri wanda yake zagaye da maƙiya ta kowanne ɓangare daga cikin abokai, ƴan uwa, abokan kasuwanci sai dai Allah ya azurta da jajirtaccen yaro wanda ya tsaya tsayin daka don tabbatar da cewa ba su samu nasarar cika burin su akan mahaifin su ba, yayinda ya samu taimako mai tarin yawa daga wajen wata yarinya wacca itama a ƙoƙarin ganin bayan mahaifin wannan bawan Allah aka yi ƙoƙarin kawo ƙarshen dangin ta gaba ɗaya a duniya,harda mahaifin ta amma sai dai cikin iko da ƙaddarar Ubangiji hakan bata yiwu ba, sai gashi sun ƙara haɗuwa gaba ɗayan su a matsayin iyali.