AUREN SIRRI

AUREN SIRRI PAGE 3-4

by @ayshaabagudo

๐Ÿ’—๐Ÿ’—๐Ÿ’—

 AUREN SIRRI

   ๐Ÿ’–๐Ÿ’–๐Ÿ’–

๐Ÿ’—๐Ÿ’—๐Ÿ’—๐Ÿ’—๐Ÿ’—



Aysha A bagudo



Page 3-4


Sai da ta gama kallonta tsab ,Sannan ta canza Chennal ta  shiga kitchen dan dyaura abinci abincin dare ,

bakin kofar kitchen din ta dawo tayi tsaye abunta tana cigaba da kallonta Chennal din data canza, ajima ajima  tana zuwa tana duba abinda ta daura.


Karar bell taji ba kaukautawa da sauri  taje ta Bud'e , gudun maseefar DEENi dan tasan muddin yana  gida baya son yawan hayaniya , yanzu ne zai gama daita,  Maryam  ta gani tsaye da wasu yan school dinsu su biyu  , tuni murna ya kama zeenat ,ta rungume su daya bayan daya tana musu sannu da zuwa hade da basu hanya suka shigo har cikin main parlour .


waje ta nuna musu da hunnu "ku zauna mana suka zauna ita kuma ta koma kitchen ta duba abinda ta d'aura taga yayi ta kashe gas din ,sannan ta dawo inda ta barsu hade da kawo musu drunks mai tsanyi da snacks ta ajiye a gabasun .


gabad'aya hayaniyya ce ta barke a atsakaninsu da murna ganin juna ,zeenat ta kalli su Sumayya hade da yin kasa da muryata tace " kuyi magana ahankali fa,  sannan tacigaba da magana cikin ruwan sanyi " kun kyauta sai yau kuka ga damar zuwar mana ?

Sumy tace" ba gara mu ba muna zuwa time to time.

kufa sai aikin sa rana  kullum, hira suka shiga yi,

Yayinda Maryam ta dube zeenat tace "wai nan fa IV suka kawo mana na birthday din rukky, zeenat ta zaro idanu waje "I ....me kika ce ?

Maryam tace " IV "

zeenat Tayi dariya had'e da cewa "uhmm ba dani ba,kema kinsa sarai baza'a taba barinmu zuwa wani birthday party ba


Sumy Tayi murmushi sannan tace "ai sai da na gayawa rukky Amman tace "ga zance ga magana " gashi nan, ni ai nasan baza kuyi attending birthday party dinta ba ,da day itace sarkin shishigi da neman suna .


zeenat tace "kmr kinsani ,duk abinda ya wuce cikin gidan nan namu "ta girgiza mata kai baza'a taba barinmu ba ,ki bata hakuri kawai Amman wlh har ga Allah naso zuwa ko dan rukky , Sumy tace " why nut ku sace hanya kuje a boye batare da sanin kowa ba ... zeenat ta kalli Sumy fuskarta a had'e " kefa kin cika matsala wlh,

kmr bada hausa nake miki magana ba ,

ta sake bude bakinta da niyar sake balbale summy,

sai ga DEENi ya sake fitowa  parlour, jikinsa sanye da jallabiya marun colour ,may maseefar kyau sai kyalli take , ga kamshin ni'imantaccen turarensa mai mugun sanyi dadi ,wanda tun tasowar zeenat ta sanshi da turaren Hamilton , har yanzu fuskarsa a daure take tam ,kmr koda yaushe " 


take ta hadiye maganarta batare da tasan Tayi hakan ba ,ta zuba masa idanu tana kallon kwayar idanunshi, sai da ya hararata, sannan  ta dauke idanunta ,ta maida kallonta da hankalinta kacokam a kansu Sumy dake zaune surusuru tamkar ruwa ya cinyesu .


Maryam kuwa duk ta fisu tsurewa ko dan ita Yar gidan ce oho.. ?

 cikin wata irin murya mai sanyi dadi tamkar ba soja ba yace "ke......ta juyo ahankali ta sake zuba masa idanunta dan tasan dai daita yake dan haka ta bada dukkan attention dinta garesa,

"   bakisan ki bawa mutun abinci bane ?

Dan iskanci sai an roka ?


zatayi magana ya katseta a fusace , "ai ba tun yanzu nasan ke muguwar rowa ce dake ba ,Tayi surusuru da idanu ,da  sauri tace "kayi hakuri dan Allah nayi zaton ko kana azumi ne, "naga kullum kana yi.


yace "oh "dama kinsa min ido ne har kinsa cewa azumi nake kullum ?

Jikin Maryam har rawa yake ,a hankali tace" wayoo Allah ashe ya dawo ,bari in gudu tun bai gama daita ya da kanmu ba , zeenat tayi shr har sanda  ya sake maimaita tambayarsa hade da cewa "dan ubanki ba da ke nake magana ba kike bina da idanu kmr zaki cinyeni?


ta sake   girgiza masa kai,. Tana bashi hakuri

 "marowaciyace banza kawai mai mugun gado, shiru yayi na d'an wani lokaci hade da sauke numfashi .l,

Sannan yace "ai idan bakiyi rowa ba sai Allah ya tambayeki" km baza'asan ke...Yar uncle Habib bace ,

"kin taba ganin barewa Tayi gudu danta ya kasa rarrafe?


"zeenat ta sake girgiza masa kai da sauri ,yace "OK ashe dai kema kinsa gaskiya dole kiyi gadon rowa.

Ganin haka yasa su sumy suka nemi sulalewa duk yana kallonsu, sai daya ga Maryam na shirin gudu itama dan har summy ta d'aura hannuta kan handle din kofar ,ya dakatar dasu da hannusa , sannan yacigaba duban zeenat yace "barikiji da kyau yana mai nunata da yatsansa" nan ba gidan marowata bane gidan masu bayarwa ne aci ," me nace ? 


Da sauri tace " gidan masu bayarwa ne"

"gud daga yau bama ni ba ,ko wani ki kaga yazo gidan nan , ki bashi ruwa da abinci yaci dan ba naki bane.

ya sake jiho mata wata tambayar on-expecting "ko abincin naki ne?

da sauri ta girgiza masa kai , dan gabadaya ta sure ta kasa kwakwaran motsi sai ajiye zuciya kawai take yi .


yace" baki da baki ne kike kadawa mutane kai , tace "naji kayi hakuri dan Allah, Sannan ya juya kansu Maryam da kadan ya rage ta fashe da kuka tsabar tsoro , ya zuba musu rikitattun idanunsa da suka fi kama dana mage masu saurin raunana mutun kai tsaye .

"  ku kuma en iskanci banza kun wani cikawa mutane kunne  da hayaniya tamkar kuna club ,kallo daya yayi musu kowace tabawa kafarta iska yaja tsaki ya juya  ya nufi d'akinsa.


ahankali zeenat take sauke ajiyar zuciya hade da dafe kirjinta , bata.san meyasa ba ,idan har DEENI yana guri Sam bata samun cikakkiyar natsuwa "sai tarinka ganin duk yacika guri ga tsananin tsoransa da take ji yana mamaye zuciyarta . 


Maryam har da kuka tayi byn sun fita dan daman can ita haka take ,shegen tsoro gareta  aiko, su sumy suka ce me zasu ba dariya ba, dariya suka dinga yi har da rike ciki suna nuna ta aiko tace "yau sai da kuyi ta zama a estate din dan bazan rakaku gun securities ba, sai da sukayi ta bata hakuri sannan suka jera suna hirar abunda ya faru. 


Ko lokacin da ummi ta dawo, tuni murna da farinciki Ganin tilon "dan " nata ya mamayeta zuciyarta.


nan suka zauna a parlour suna hira cikin hirar ne ummi take masa maganar aure in da tace masa "yakamata ya nemi mata yayi aure " kasan shekararka nawa kuwa yanzu ?

yayi murmushi ai "dole nasan shekaruna ,muke nan kullum cikin rubuta date of birth ,talatin da biyu ne kawai fa ummi Tayi dariya 32 din ne kawai ?

" kusan duk sa'annin haihuwarka duk sunyi aure acikin estate din nan , gasu yasir nan ma duk ansa musu rana dan haka kaima ka fidda mata kafin azumi .


DEENI yazaro idannu yana bin ummi da kallo a shagwabe yace "haba first love dan sunan da yake kiranta dashi kennan tun tasowarsa .


"ni din guda nawa nake da zakice inyi wani aure yanzu?

" Dan Allah kiyi hakuri my first lov zuwa wani lokaci ,duk hirar da suke zeenat na zaune tana jinsu haka kawai taji gabanta na faduwa lokacin da taji abinda ummi tace ,Amma jin amsar da DEENI ya bata yasa taji wani irin sanyi na ratsa zuciyarta .


 kmr ance ya dago idanunsa suka had'e cikin nata harararta yayi yace" kallon fa kin wani tsare mutun da idanu?


ummi tace "uhmm kafa dawo kennan karka takuramin yarinya ,

ya langwabar da kansa yana maida idanunsa kan ummi cikin sanyi murya yace " haba first lov baki ga irin kallon da take bin mutune dashi bane,?

" kmr bata san mutun ba , ummi tace" kai da wani idanu ka kalleta har kasan tana kallonka?

" kuma ma ni banga komai ba kai dai

takurace kawai da kai indai kana gida, baka barin yarinya nan ta huta ta sarara , ya dubi ummi ya tabe baki , Sannan yace" ke....kawo min coffee ,ta mike taje ta hado coffee din ta kawo masa, gabanta na wani irin faduwa ta durkusa har kasa ta ajiye masa tayi gaba .


******

Adaidai wannan lokacin ne zeenat ta kammala karatunta na secondary school , ta fito da sakamakon mai kyau domin ta samu almost 7 credit masu kyau .

shi kansa DEENI yaji dadi Sosai sanda ummi ta nuna masa, Amman da yake miskili ne, sai cewa" yayi Sam shi bai ga wani kokari da Tayi ba tunda bata cinye duka ba .


ummi Tayi murmushin tace" kai ne dai bakaga kokarin ta ba,Amman ni nagani km nasan Tayi kokarin Sosai .


" Ina laifi duk cikin wayanda suka rubuta jarabawa tare bbu wanda yakaita marks ,.

yace "ok inda ta cinye duka ne zan iya cewa Tayi kokarin ai wayanda suke cinye 9 credit ba finta brain sukayi ba./,

Ita dai wasa da kallace kallacen banza tasa a gaba.


ummi ta hade fuska tana harararsa ya cigaba da zagin zeenat ganin yadda ummi Ta canza fuska ne ,yasa yabar maganar , ummi ta sake duba result din tana shafawa hade da kwallawa zeenat data tashi tun sanda taji DEENi yasoma zaginta  ,ta karaso cikin sanyin jiki  ta tsaya kusa da ummi DEENi ya dauki wayarsa yana daddannawa bai ko kalli inda take ba , ummi ta mika mata slip din tana murmushin tace "kinyi kokari sosai yarinyata Allah yasanyawa karatu albarka , zeenat ta karba tare da cewa "ameen ummina , ta juya ta bar gurin dan bazata iya zama a duk inda yake ba .


ummi ta dubi DEENI tace "yanzu kuma sai aure zanwa yarinyata .

DEENI ya juyo a sukwane yace" wani irin aure kuma first lov da rana tsaka , ku dai Bari yarinya ta cigaba da karatu kawai" dan yanzu kai yawaye , an daina irin wannan auren na iya secondary .


"ummi ta dubesa da kyau ta numfasa Sannan tace "ni tawa iya secondary zan aurar daita ,dan ma taki sauraran masu sonta , itama shegen iyayi ne daita ,kuma dai  kasan matan wannan family din basa wuce secondary ake musu aure .


Kasan baza'a fara karatun jami'a daga kanta ba, "kai  nima nafi son na aurar da abita a iya secondary. 


DEENI ya tabe baki Sannan yace "Allah ya kyauta ,ni ko zanyi aure bazan  auren Yar secondary  ba wlh , sai wacce tagama jami'a, mai tarin illimi ,kuma ba auren family zanyi ba dan baya birgeni, yakarasa maganar yana dan murmushi .


ummi tace to Allah yabaka sa'a. amman ni tawa aure zan mata da wuri .

kai kasan halin big dady bazai taba barinka kayi aure a waje ba ,

Wlh naso a hada aurenka dana su yasir "uhmmmm fist love su dai yi nasu ni sai nan gaba .


******

A wata yammacin DEENI zaune akan dadduma  awajen a lambun dake cikin estate din, shi da abokansa wad'anda duk kusan family ne ,zagaye dashi, gefe guda kuma flasks ne cike da ruwan zafi da kananan cups , hira suke sosai atsakaninsu ,Amman banda DEENI ,dan shi gabadaya daukar hirar tasu yake shirme ,dan duk zance nasu akan maganar aurene ,wanda shi kuma Sam baya kaunar ji , dan haka ya sharesu ya cigaba da lasalasar wayarsa 

,ya kai hannunsa daya ya dauki cup din coffee wanda orready fk ya tsiyaya masa, ya kai bakinsa yasha hade da rufe rikitattun idanunshi wanda yazame masa jiki .


fk ya kalli yasir da faysal dake tawowa inda suke, ya kwashe da dariya har suka karaso bai bar musu dariya ba ,fk yace "sannuku da karasowa Mayan angwane kunsha kamshin !kunsha kamshin !!,faysal yace "kai dai anyi dan iskan yaro , kai baka tsaya ruwan ido ba kana biyewa wannan ya nuna DEENI da yatsa.


fk yayi murmushi yace "yayi  an gwanen bana, wannan karon gabadaya suka dara hannu suka bawa juna suka gaigaisa har DEENI.


yasir ya dube fk yace" ai gara muyi aurenmu tunda muna son juna kai ka zauna kar kayi har mahdi ya bayyana ,fk yace  "A'a nifa bance saboda  me zakuyi aurenku ba . Amman gaskiya zaku takura kanku ne kawai yanzu da wani aure wayannan kananan bbys din.


  DEENI ya tabe baki Sannan ya dube fk yace "shiyasa rawar kan yaran ke kara yawa ba tunda sunga ana saurararsu da sunan zance ,dukkansu suka sa dariya suna cikin dariyar  fk har da rike ciki ,sai gasu zeenat da suka taso daga islamiyya su biyar suka jero kowace sanye da hijab dinta raudat da shemah da samiha da Maryam sai zeenat dake tsakiyar su dukkansu kyawawane kuma yanuwan juna .

da hannua fk  yake nuna musu inda suke Sannan ya dakata da driyarsa  , ya kalli inda DEENi ke zaune tamkar bai san abinda ake ciki ba ,asslima ko kallon inda suke bai yi ba, yacigaba  da sarrafa wayarsa .


fk yace" kai gaskiya bbys din nan fa su hadu dayawa fa , nima ko zan dan shiga daga ciki ne?


yasir yace "dako ka huta , kabar wannan ya nuna DEENi, fk ya cigaba "ina ai bazan barsa ba tare zamuyi namu auren , ko yakace mutumina?

" kaga Shikenan mun huta da surutu jama'a .


DEENi ya kallesa a kaikaice  yace" A'a ku dai da kuka ji zaku iya kuje kuyi Tayi ,

Amman ni ya nuna kansa da yatsansa hade da tabe baki, ba yanzu ba"  har sanda su zeenat suka zo suka wuce . Suna hirarsu suna dariya Maryam ce ke basu labarin abinda ya faru jiya bbu wanda bai dara ba har ita zeenat din raudat tace wa zeenat "wallahi  ke kika daukar masa , kuma yarinka yi miki kennan ina ma nice daya gane kuresan suka sake yin dariya .


Tun lokacin daya dawo zance sa da ummi bai wuce DEENI kayi aure , fito da mata cikin yan,uwanka kayi aure hirar kennan sai dai idan basu zauna ba .


*******

Yau takama walimarsu zeenat ta saukar alqur'ani mai girma wanda aka shirya musu anan islamiyyarsu dake cikin estate din ,su kusan goma , anyi taro walima lfy yayinda zeenat ta karbi kyaututtuka da dama saboda kokarinta har kuka ummi Tayi sakamakon tunowa da da er'uwarta, taro ya watse lfy kowa yakama gabansa ,byn sun gama hirarsu da ya zame musu jiki suka fara hada kujerun da akayi walimar dasu  .   sun fito kennan suka ga DEENI da wani abokinsa zaune  akan kujera guda biyu  suna hira ,take suka ja birki samiha ta cewa zeenat "jeki amso wadan can kujerun, cikin zolaya tayi mata maganar dan tasan yadda take jin tsoronsa.


zeenat tace" uhmmmm ku dai kuje "suka sa mata dariya ke wlh muguwar matsoraciyace wlh ki rage tsoransa shiyasa yabi duk ya renaki ,Tayi  sororo tana kallonsu , Sannan tace to bari naje na amso Tayi tafiya kmr zata isa gurinsa sai kuna ta juyo da sauri" aiko suka sake kwashe mata da dariya .


muryashi ce ta katse musu dariyar tasu lokacin daya suke kallonsa a frigice" yayinda gaban zeenat  ya soma faduwa yace "ke....da hannu ya nuna musu alamun suzo suka nufo inda 

Yake cike da tsoro ya zuba musu rikitattun idanunsa yana kallonsu daya byn daya yana nazarinsu Sannan yace "da ganinku akwai alamun rashin gaskiya atare daku 'ya nuna su da dan yatsansa zeenat Tayi saurin cewa "A'a cikin inda inda  " bbu komai fa, Ta fadi hk gudun Kar wata cikinsu ta fada masa ,shiyasa Tayi saurin yin magana ",to menene na inda inda wama ya tambayeki ?


Tayi shiru tamkar ruwa yacinyeta, Sannan ya juya ya kalli abokin nasa da ya zubawa zeenat  idanu yana kallonta , kafarsa daya  yasa ya take kafar manir dashi ,sannan manir ya dawo natsuwarsa ya maida hankalinsa kan DEENi .

DEENi ya nuna su zeenat da samiha hade da shemah da Maryam yace gasu nan  ," bansa inda sauran suka nufa ba, manir yace "ina ta yaku murna walima saukar alqur'ani mai girma, Allah yasa na tsoron Allah ne ,suka hada baki wajen cewa Ameen , kallonsu kawai DEENi yayi jikinsu har rawa yake suka bar wajen.


 manir yabi bayansu da kallo yace " kai sisters din nan naka fa akwai kyau DEENi ya kallesa yana watsa masa harara" ok iskancin naka kuma yau agidanmu zai Kare?


manir yayi murmushi yace "Allah barin ma wace ta tsakiyarsu gaskiya duk tafiso haduwa DEENi ya kalli inda ya nuna sai yaga zeenat yake nufi take yaja tsaki manir yace" dama ita ka zaba wlh dan nasan karshe ma auren zumunci za'a maka.


DEENi ya sake jan tsaki "dan Allah malam karka dameni da wannan shirme bazan ,manir bai daddara ba ya sake cewa Allah dama tsayawa kayi akayi Yar gida tunda duk tarin matan dake sonka baka kallonsu , a fusace DEENi yayi magana" dan me zan kallesu alhalin ban da abinyi dasu?


manir yayi murmushi "ina ma ni ne kai wlh tsayawa zanyi na kwashi gara son raina har sai nagaji in more kuriciyata , DEENi yace "ai kai dan iskanci ne lamba daya , wlh ka guji abinda kakewa ya'yan

mutane "ko dan gaba .


  "ka dauki neman mata tamkar wani abinci, manir ya dan daki kafadar DEENi yace "ai sun fi abinci dadi ,.

Amman Allah koni ina son na daina bin matan bazan wallahi , abun ne da kmr wuya Amma kacigaba da yimin addu'a . 


DEENi ya nuna sa "kai zanwa addu'a saboda ban da abinda zan roka  Allah ,?

manir ya dage masa gira daya "yes meye dan kamin addu'a kaga idan Allah ya shiryani sai kabani wacce Yar dimadimar sister din taka na aura .

bai kulasa ba sai canza zance da yayi nan dai suka cigaba da hirarsu har zuwa sanda sukayi sallama da juna  .


Abinda zai daure maka kai  bai wuce yadda ummi ke sake bawa zeenat kulawa ta musamman ba ,ta kowani part tana kokarin ganin ta fito da diyarta ta tsab, zeenat bata rasa komai ba tun daga dangin sutura da mayuka shafe masu tsada zuwa kayan kwalliya ana cikin haka tafiya takama ummi zuwa India ,dan haka ta tasa diyarta gaba suka tafi  ,zeenat taji dadin zuwansu India tamkar karta dawo ,watan su daya suka tattaro suka diro Nigeria saboda bikin family dinsu ya kusa, koda ta dawo ma su Maryam sun dinka mata duk anco din da aka fidda, tunda damar suna da telansu da yake zuwa har gida ya karba dinki,.


biki akayi sosai bakama hannu yaro an kashe kudi tamkar ba'asan ciwonsu ba ,bidia iri iri kuma duk anan cikin estate din akayi komai, daga karshe akayi walima washegari ranar Sunday aka daura auren en mata biyar, haka ma samarin ,aka dan kowace a gidan mijinta, ya saura mutun uku cal suka rage da basu yi aure ba, Maryam da shemah sai zeenat, amaza kuma fk da DEENi sai kamil .



MMN SUDAIS CE