AUREN SIRRI

AUREN SIRRI PAGE 5-6

by @ayshaabagudo

AUREN SIRRI

   ๐Ÿ’–๐Ÿ’–๐Ÿ’–

๐Ÿ’—๐Ÿ’—๐Ÿ’—๐Ÿ’—๐Ÿ’—





Aysha A bagudo




Page 5-6




Zeenat na da kyau sai dai ba can ba" fara ce Sol Amman bata da dagon hanci ,wannan bai sa fuskarta muni ba" haka idanunta matsakaita ne ita mutun ce mai tsananin son kwalliya wanda ko alwala Tayi sai ta sake yin wata sabuwar kwalliya, haka nan ummi bata gajiya da siya mata kayan kwalliya iri iri sannan bata ganin aibunta a duk lokacin da zata 'bata a gurin yin kwalliyar .



abinda kawai ummi bata so kuma bata yarda dashi ba, shine a yi mata d'inkin da zai bayyana surar jikinta ,nan ne fa tace bazata bada goyon baya gurin bata kamasho yad'a zina ba , dan a cewarta shigar da yawancin ena'mata keyi a wannan zamani itace ke sake haifar da fashadi a doron kasa.


 zeenat akwaita da saurin sabo da mutane sannan km tana da son kawaye ita da Maryam dan ko yanzu suka san mutun  ko km kuka had'u dasu sanadin wata kawar, Shikenan sun zama kawaye , shiyasa suka fi dukkan sauran yn'uwansu  jama'a dan daga waje ma zuwa ake gurinsu sa'banin sauran"


 kullum kaga ana rikinci a bakin get da sune , gurin shigo da baki  most especially ma na school dinsu ,abinda ummi tafi tsana kennan daga gareta yawan tara kawaye gata da matukar son gayu ,da son kallace kallacen film's ,muddin tana gida kuwa bata da aikin yi sai na kallo ,daga wannan Chennal zuwa wata ,sai dai duk da wannan halin nata Allah ya bata illimi sosai both arabic & school.


Daidai misali  Allah yayi mata farin jinin samari masu sonta daga waje ma biyota akeyi, sai dai bata fita, dan ummi taki yarda ta fara zance da wuri sai data kai ss2 kuma duk masu zuwa gurinta da aure suke sonta "amman matsalar dai d'aya ce family dinsu basa yarda da  auren wajen, Amman sukan bar namiji .


 Sannan duk masu son nata bataji son su har cikin ranta 'har wani lokacin ummi kesata gaba da fad'a "tace maza ki tsaya ruwan ido daga karshe kirasa kowa kizo kina nema ,yawon yi mata fad'an da ummi keyi ne yasa ta tsaida kamil dan gwaggonta" yayar mahaifinta da suke uwa guda uba guda .

 shima bakowa yasan suna tare dashi ba , dan bata gama tantancewa aurensa ba" kuma shi bai fiyye zama a garin ba yana aiki ne a abuja ". haka kawai taji idan bata samu wanda yafi shi ba , zata iya aurensa dan shima ba laifi .


Jiki da jini wata safiya ummi ta tashi da ciwon ciki , wasa wasa tun tana d'aurewa har abun yafi karfinta gabad'aya tafita haiyacinta' hankalin zeenat yayi mugun tashi dan bazata manta yawan labarin da ummi ke yawan bata na mahaifiyarta da irin wahalar da tasha kafin mutuwarta ba ,ciki har da cewa mata Tayi ta bud'e ido ta zabi miji wanda zai san mutuncinta kar taje gurin ruwan idonta ta kwashi gaibu ,shiyasa take massefar jin tsoron haihuwa da mutuwa arayuwarta ,dan ta kudircewa ranta ta amince da mutuwa tunda tasan muddin kwanakinta suka Kare Shikenan "amman ita kam bazata yarda da haihuwa ba ,ganinta garata tasha wahala d'aya .


wunin ranar da ciwo ummi ta wuni can kuma ta samu sauki  ,dare nayi ciwo ya sake dawowa zeenat taso zuwa ta sanar da DEENi Amman ummi taki .



 washegari DEENi ya shigo da shirin fita aiki dan bai san bata da lafiya ba, koda yashigo d'akin yayi matukar girgiza da ganinta kwance cikin bargo da kyar take iya magana a rud'e ya karaso inda take yana  tambayarta ba lafiya ne ? 


Ummi tace "eh tun jiya yace "meyasa baki sa an tashe ni ba ,ya kalli inda zeenat ke ruku'be kusa da ummi duk tazama wata kalar tausayi.


"ke....Wace irin" sakariyace da baza ki iya zuwa kisanar min ba ?

da kyar ummi ta iya bud'e baki ,tace "ni na hanata ya furzar da huci ta bakinsa had'e da cire hular kansa yayi wurgi dashi gefe ,take ya Ciro waya cikin aljihun bayan wandonsa yakira family doctor dinsu wanda side dinsu kawai yake dubawa.


 mintina kad'an sai ga likinta da yake bai da Nisa dasu cikin sauri yashiga duba ummi sosai har drip aka sawa ummi a ranar DEENi kasa fita yayi koina, byn likinta ya wuce ne, ya kirasu yaya Mahmoud ya sanar masu da ummi fa ba lfy .


 idanunta ta zuba mashi tana kallon bakinsa yadda yake maganar ne tamkar wata mace shi yafi d'aukar hankalinta, 

bata ta'ba jin DEENi ya birgeta ba irin na yau.


 duk wunin ranar kusan shi yayiwa ummi komai hatta magani da abinci a baki ya bata sai gurin la'asar su Yaya Mahmood sukazo tare da matansu ,  zuwansu ne ma yasa mutane cikin estate din suka sani  dan DEENi bai sanar da kowa ba, shi dai ta mahaifiyarsa kawai yake.


Ai kafin kace me tuni side din ummi ya cika da jama'a, haka suka dinga shigowa duba ummi har dare DEENi na tare da ummi yana bata kulawa. duk yayi wani iri cikin lokaci kad'an ya fita haiyacinsa zeenat na zaune a gefe guda tana jiyo hirarsu, rokonsa ummi take akan yayi aure a hankali ta kira sunansa NASURULDEEN ....abinda ya sake tada ma DEENi hankali kennan yaushe rabon da yaji ummi ta kira complete name dinsa , ta cigaba "ban rasa komai na rayuwar duniya ba, ina da tarin dukiya da kadaroro wanda ni kaina basan iyakarsu ba ,burina da muradina a halin yanzu bai wuce inga aurenka ba, Amman na fuskanci kafi son sai na mutu sannan zakayi aure .


 Jikin DEENi ya d'auki rawa hankalinsa ya sake tashi matuka, ta sake kiransa cikin tattausar muryar had'e da rarrashi" DEENi banida kowa daga kai sai zeenat ,sai kuma d'an uwana wanda yake wata uwa duniya ,idan ba kayi aure ka taramin jikoki masu albarka ba mezakayi min naji dadi ?

" ina ji ajikina sai na mutu zakayi aure .


a rud'e yace"no first lov ki daina cewa haka, zanyi inshallahu, kina raye ma ,Tayi murmushin karfin hali tace "kullun haka kake cewa, ni tuni na fidda raina ka tashi ka tafi Allah ya maka albarka ... Amman yarinyar nan zeenat na rokeka dan Allah ko ban tashi ba kada kabari ta koma hannun mahaifinta, na damka amanarta a hannunka ,bata da kowa duk duniyar nan daga ni sai kai ,ka rike min ita a hannunka har zuwa lokacin da zata samu miji . 


DEENi yakamo tafin hannun ummi cikin nasa ahankali yasoma magana muryasa cike da rauni da fargaba, "haba first lov ki daina maganar mutuwa nan kece zaki aurar daita da hannuki kuma kina raye inshallahu ,ta girgiza kai ita kad'ai tasan abinda take ji ,cikin muryarta irinta marasa lfy tace "Shikenan tashi kaje ka kwanta , hankalinsa a tashe ya fice daga d'akin..


 zeenat ta mike daga inda take idanunta na zubda hawaye ta taimaka mata suka kwanta tana kuka kasa kasa ummi tace "lfy zeenat?


" ummi . .... ummi..... cikin sheshekar kuka "banason naji kina cewa zaki mutu ki barni dan Allah ,ummi  tace "ko fa ban fada ba mutuwa ta zamemin dole ,sai dai idan ajalina bai zo ba . zeenat ta saki kuka had'e da kamkameta ummi a jikinta , ta cigaba da kuka mai cin rai had'e da cewa "ummi bazaki mutu ba inshallahu da kanki zaki aurar dani ga duk wanda kike so da kyar bacci ya d'auketa yayinda ummi Tayi nisa a bacci .


Shi kuwa DEENi tunda ya koma dakinsa ya kasa zaune ya kasa tsaye sai zariya yake daga farkon dakin zuwa karshe, kafin daga baya ya nemi gurin ya zauna.

 yayi tagumi da duka hannuwansa yayi zurfi cikin tunanin yadda zai yi lallai ya zama dole ya nemo mata domin cikawa umminsa burinta. sai dai shi matsalarsa bai san ta ina zai fara ba "

 "Bai ta'ba yin buduwar ba ballanantana wata aba soyayya, shi duk a tunaninsa raini hakan zai jawo masa idan yaje yace yana son budurwar .

ya kamo gefen lips dinsa ya dan cizawa a hankali har daga karshe ya yanke shawara zai nemi fk da zance, a nan ya sulale ya kwanta rigingine idanunsa na kallon celling d'akin .

yayinda ya rungume hannushi a saman kirjinsa yana aiyana irin type din maccen dayake son ta mallakesa, kuma wacce ya dace ya aura cikin sanyi jiki ya runtse idanunsa gam, take ya soma zaiyano irin type dinsa kyakkyawa dogowa mai dirin jiki , choculate colour, mai dara daran idanu sannan educated mai wushiryar haka dai ya rinka yi har dare ya sula bai samu wani ishashen bacci ba.


 koda asuba kafin ya tafi masallaci sai da ya fara shiga Bedroom din ummi ya sameta tana sallah ya sauke ajiyar zuciya sannan ya wuce , ganinta tsaye tana sallah yasan Allah ya kawo mata sauki .


A masallaci DEENi suka had'u da fk byn an idar da sallah "yajashi gefe guda, da idanu fk yake binsa da kallo "abinda bai ta'ba faruwa ba kenan ,saboda DEENi daya idar da sallah yayi yan addu'oinsa yake wuce wa gida .


 fk ya dube sa da kyau yana nazarinsa kafin daga baya yace lfy kuwa naganka haka ? Gabadaya fk yagama tsurewa da ganin yanayinsa sai da ya sake maimaita tambayar sannan DEENi yace "ina fa lfy jiya ummi kwana Tayi ba lfy har tana barmin wasiya burinta da muradinta yanzu bai wuce nayi aure ba.


 fk yayi shr yana jin DEENi har sanda yagama bayaninsa sannan yace ba ita kad'ai ba har big dady ma burinsa kennan dan ko jiya sai da ya min maganar nida kai , Amman tunda kai ummi ta damu ta tsananta gara kayi kawai ku rabu lfy .


DEENi yace "ai ba san inda zan nemo matar ba nifa gabadaya en,mata family din nan basu min ba , sannan kuma sun min kankanta da aure .

 fk yace "A'a bawani kankanta da sukayi " mace nawa namiji kankanta da aure ne ? "kaine dai kawai kake ganin haka ,ni  yanzu na yanke shawarar zan tsaida shemah kawai tunda na dade ina sonta ni da zakaji shawarata ma , da zeenat ka aura .


 DEENi ya mishi wani irin kallon baka da hankali sannan yaja tsaki yace "haba dai zeenat , fk ya cigaba" yarinyar akwai hankali wlh ,ba kmr wancan banzar uban nata ba, da yake duk sun tsani halinsa.

  kaga kawai sai a had'a bikinka da nawa kawai kaga zeenat bata da matsalar, km ko ba komai ummi zata ji dadi Sosai da wannan hadin.


 DEENi yace" Amma ban ta'ba jin koda alamar digon sonta ba, kuma ni gaskiya ina ganin tamin yarinta dayawa duk fa shekarunta sha bakwai zuwa shatara ne fa. nafison mutua girl wace ta mallaki hankalin kanta tasan yadda zata kula dani a kan bed ,amman wannan Yar bbyn maimakon ta kula dani ,ni ne zan koma renonta.

 fk ya dubesa a kaikaice yace" lallai ,yaran zamanin da  kasani haka , Amman banda na yanzu, na yanzu sai su maka abinda manyan matan baza su iya ba, kana rai nata ne kawai ,karka yi mamaki kaga mararta ta d'aukeka tsab,.


DEENi yaja tsarki" kai ban son iskanci ,shawara nake so , ba wani shirmen bazan  ba .


fk ya kada kafad'a yace "well tunda kaga bata maka ba kana iya duba wasu acikin gari .

DEENi ya kalleshi yana watsa masa harara "kai fa dan iska ne, dan kaga nazo maka da maganata shine zaka rainawa kanka hankali " sai kuma yayi kasa kasa da murya yace "kasan Allah ni fa ko a waje ba wai ina kallon mata bane, fk yace to ka tsaya akan zeenat din kawai,duk inda ake neman mace mai natsuwa yarinyar nan ta kai ,DEENi ya sake jan tsaki yace "ai inda takaicin yake kennan sai kuma na kirata ince ina sonta ...?

ya fad'a yana ta'be baki "hade jin takaici da haushin shawarar da fk ya kawo masa " 


fk yace "ida bazaka iya ba kabi ta sama mana , ma'ana ka samu big dady da maganar kawai, ka sanar dashi kana sonta nasan zai ji dadi Sosai .

DEENi ya sake watsa masa wata harara yace "dan Allah malam ya zaka da meni da wannan shirmen haukan , ina ganin fa kmr ka fara samun ta'bin hankali , wa yace da kai  ina sonta "zan dai yi aure ba dan ina so ba ,ya juya ya bar fk nan tsaye  yana binsa da kallon mamaki.


 yace "ai kaine babban mahaukacin  d'an iskan kawai , sai iskanci fall ciki ,shi bai ga laifinsa da yace ba zata iya d'aukarsa a bed ba sai nawa ,sai kuma ya kwashe da dariya .




MMN SUDAIS CE