AUREN SIRRI PG 7-8
AYSHA A BAGUDO
Page 7-8
Har DEENi yazo gida tunanin yake akan shawarar da fk ya bashi." anya kuwa zai iya amincewa da auren zeenat ? Lokacin da ya shigo d'akin ummi yayi daidai da zeenat ta bare magani tana mikawa ummi ,
ta amsa ta apa, zeenat ta Mika mata ruwa cikin cup ,yayinda shi km yake tsaye jingine da jikin kofar shigowa rungume da hannuwansa duka a kirjinsa yana kallonsu, take zuciyarsa ta dinga ingizashi akan lallai bbu wace ta dace ya aura sama da zeenat bisa ga hujarsa ta cewa ,bazai taba samun matsala daita gurin kula da mahaifiryarsa ba, saboda irin soyayyar dake tsakaninsu "
yasan ko yana nan ko baya nan zeenat zata kula daita, umminsa zata zamo a karkashin kukawarta tunda zeenat bata da wata uwar data wuce ummi, tunaninsa ya katse lokacin da ummi takira sunansa' " son karaso mana yayi frigigit ya dawo natsuwarsa ahankali ya shiga takowa har inda ummi take ,ya zauna.
zeenat ta gaidashi ta mike zata fice daga dakin bai amsa mata gaisuwar data masa ba ,sai dai yabi bayanta da kallo" ummi ta kalleshi ta kauda kanta, yace "first lov ya jikin naki? ummi ta danyi murmushi hade daura hannuta kan sumar kansa tace "naji sauki sosai , ahankali ya sauke ajiyar zuciya, ko bai ce komai ba, ummi ta fahimci yaji dadin yadda ya ganta .
yana nan zaune , Sam ya kasa yiwa ummi zance yana son auren zeenat din ,daga karshe ma tunani yayi kawai gara ya samu ya mahamud da zance dan gaskiya kunya yake ji yayiwa ummi maganar da kansa .
Da yammacin ranar byn ya dawo daga office yaje har gida ya samu ya mahamud da maganar, ya ji dadi kwarai da gaske, har ya rasa inda zai sa DEENi dan farinciki dan shima da kansa ya matsu yaga DEENi ya ajiye iyali kmr kowani magidanci , yace Shikenan sai ka samu yarinyar da zance, ku daidaita kanku DEENi yace" A'a ina ganin basai na sameta ba in dai first lov ta amince ai Shikenan .
yaya mahamud yace ummi bazata taki ba Amman dai kasan kaidar auren gidanmu kennan bbu dole a ciki "muddin kuka daidaita kanku na iyayenmu mai sauki ne, idan Kuma ita ummi ta amince ita yarinyar tace bata sonka fa? DEENi yaji haushi da takaicin maganarsa sun kamasa, a lokaci guda yace" ai nima ba wai ina sonta bane kawai dai zan aureta ne.
Yaya mahamud yace "shirme bazan kennan kai yanzu idan anzo meeting cewa zakayi basonta kake yi ba ,za dai ka aureta ne ?
DEENi yayi murmushin gefen baki har dimple dinsa ya lotsa sannan yace " cewa kurum zanyi ina son zan aure zeenat ne ' Yaya mahamud yace "to Allah ya mana zabi na alkhari kabari zanje gurin ummi tukun duk yadda mukayi daita zakaji . DEENi yace Shikenan ya mike ya fice ,a office ma koda yaje aikinsa kawai yasa gaba .dan shi gabadaya ya manta da wani zance aure .
Mahamud ya samu ummi cike da karfin gwiwa" ganinsa ba wanda zai kai ummi murna tunda daman burinta kennan na ganin auren DEENi, Amman ga mamakinsa yana gama labarta mata abinda yakawo shi, sai yaga ummi tayi kicin kicni da ranta tamkar bata taba sanin wani abu farinciki ba "sai da gaban Yaya mahamud ya fadi ,dan ganin yadda ummi tayi da fuska tamkar yazo mata da zance mugun abu.
" tace kai ne kaga sun dace kaba shi shawara ya nemi aurenta ko Kuma shi da kansa ya sameka da zance ?
Da sauri yaya mahamud yace A'a shine dai yazo min da zance ummi ta sake daure fuska, sannan tace" ka koma ka fada masa ban amince ba ,kace masa akwai sauran mata a gidan nan yana da damar zabar duk wacce tayi masa, idan ma ya canza ra,ayinsa na kin auren family' to yaje waje ya nemi matarsa can itama Allah zai bata nata mijin, Amman Sam ni ban yarda da wannan hadin ba " tayi shiru na wani lokacin kana ta zubawa Mahmud idanunta tana kallon yanayin daya shiga .
,ahankali ta numfasa sannan tace "kana iya wucewa idan kana da abinyi ka manta da wannan shirme na DEENi . Yaya mahamud yayi kasa da kansa Sosai cikin muryasa can kasa da alamun rarrashi yace "dan Allah ummi ki amince da auren nan bazan iya tunkarar DEENi da maganar ba.
duk da bansa dalilinki nakin amincewa ba.
ummi ta dan saki fuskanta ba kmr dazu ba tana mugun son mahamud tamkar dan da ta haifa acikinta tana jinsa har cikin zuciyarta .
" bawai ina kin hadin bane Muhammad duk duniya idan akwai wanda zai so auren DEENi da zeenat a bayana yake ,
na farko dai kaima kasan halin DEENi da dan bazar zuciya , ga saurin fushi ga maseefar miskilanci , ga jin kai, sannan da bakinsa yasha gayamin cewar shi bazai taba yin auren family ba sannan shi mai digiri yake so ya aura ,shine km yanzu zai zowa mutane da wani salo.
nida tawa iya secondary kadai ta tsaya" ai kai da jin zancensa ma kasan akwai wani makircin daya shirya "dan nace yayi aure ai bance lallai sai ya aure tawa yarinyar ba , Muhamud yace "ummi ki duba lamarin tunda shi da kansa ya furta cewa ita tai masa,ai Ina ganin ba za'a samu wata matsala ba ,.
ummi tace "Sam ban ba yarda da wannan tsarin ba " Ni dai yaje gaba ya nema, hakurin duniya nan bbu wanda yaya Muhamud bai bawa ummi ba amman taki amincewa ,duk ta inda ya bullo mata sai itama tabiyo masa ta wata hanyar, har ran yaya mahamud yasoma baci ,yaji haushin abinda ummi tayi dan haka ya hakura ya fice ransa abace .
DEENi zaune a office dinsa ya dukufa wajen tura sakwanni a yanar gizo ,hankalinsa kwance yake bin komai daki daki , yaji daya daga cikin wayoyinsa ,daya ta dauki karar sauti mai dadi ,ya d'auke idanunsa daga kallon system , yasa hannu ya dauki wayar yana dubawa ganin sunan dake yawo akan screen din ne" yasa yayi sauri dagawa ya kara a kunnenshi hade da yin sallama" kana ina muryar Yaya mahamud yaji ta daki dodon kunnenshi cikin sanyi murya DEENi yace ina office yace" ok idan katashi ka biyo inason ganinka sannan ya kashe wayar .
DEENi zaune a gaban Yaya mahamud kansa sunkuye a kasa yayinda idanunshi ke kallon zarazaran yatsun kafafunsa yana sauraron sakon da ummi tabayar a sanar dashi,
a gurin deeni sam bai tsammaci jin haka daga umminsa ba .
ga mamakin Yaya mahamud sai yaji deeni yace Shikenan babu komai Allah yasa haka shine mafi alkhari .
ya mahamud yace" ka hakura kennan da aurenta?A Nashi ganin ba zai damu dan ummi ta hanashi auren zeenat ba , dan haka Yace " eh "tunda daman ba wai ina sonta bane"
nan dai suka bar zance aure suka shiga wata hirar daban a inda Yaya mahamud ya tashi yaje ya kwaso wasu takardu da file files ya zubesu nan a gaban DEENi yace "yasa masa hannu ciki " kai tsaye DEENi ya zaro wani hadadden Biro daga gaban aljihun rigarsa yasoma cike gurraren da akeso yayi sign,
dan gabadaya dukiyar DEENi , sulaiman da Muhamud ne akai, su suke kula daita kuma komai na tafiya daidai " domin dukkannisu abu guda ne a gurin ummi dan ma idan ba'an gaya maka zaka dauka duk ummi ce ta haife su .
Sai da DEENi yagama sign din takardu ,sannan yaya mahamud hada da mishi bayanin companies din da suke son budewa a kasar American, sun turo musu da sako akan suna da bukatar mutun daya daga cikin masu company din yazo interview, dan haka shi ya wakilta sulaiman yaje , DEENi yayi murmushin yace "Shikenan bbu komai duk yadda kukayi daidai ne Allah ya taimaka .
byn DEENi ya koma gida ya dingawa umminsa wani irin kallon, wanda shi kansa ya kasa gane dalilin yin haka, yana son yi mata magana Amman yayi shr ,yayinda zuciyarsa ke kwabarsa akan ya share kawai ai baita kadai bace mace a duniya" daman ai dan ita yake son ya aure zeenat din ,da yaje waje ya aure wata wacce bai san halinta na boye ba ai gara zeenat din amman tunda bata so shima ya hakura .
Da misalin karfe goma na dare ranar DEENi sanye da rigar wanka dan fitawarsa kennan daga bathroom ,ya tsaya gaban dress mirrow yana karewa jikinsa hade da zare rigar wanka dake jikinsa" ya saura daga shi sai boxer , yabi koina a jikinsa da turaren Hamilton 27.
sai daya kammala da komai na al'adarsa da ya saba yi kafin ya kwanta sannan ya hau kan royal bed dinsa ya lumshe rikitattun idanunshi, alamun yana son yayi bacci' sai dai baccin yaki zuwa kawai ya tsinci kansa da tunanin zeenat.
ya rinka jinta ajikinsa , yadda yake jinta a halin yanzu bai tsammaci abin har ya zai Kai haka ba ,,
Sosai ya tsinci kansa cikin damuwa ko baya son yarinyar hakika ya tsananta da son aurenta, yayi shr yana tambayar kansa abinda ummi take nufi da kin amincewar da tayi.
"shi ya guji big dady da maganar a tunaninsa sai umminsa tafi kowa murna da jin dadi 'ya dauki tsawon lokacin kwance kafin bacci barawo yayi gaba dashi .
Byn kwanaki , DEENi ya kasa hakuri da maganar zeenat din kmr yadda yaso ,shima ya share da zance kawai ya manta dasu "
Amman ya kasa, ya samu ummi da kansa a wata safiya dayazo gaisheta byn yayi shirinsa na zuwa aiki cikin kakinsa dake kara masa kyau tamkar dan shi kadai akayi,sai kamshin yake zubawa ta koina ,gashin kan nan nasa kwance luf luf luf dasu , duk da ba cika yawa sukayi ba ,saboda yanayin aiki "Amman dayake Allah yayi mishi suma takoina ajikinsa ko yayi askin ma baya wani dadewa ,gashin zai sake fitowa, sosai yayi kyau matuka ,ita kanta ummi satar kallonsa take har yagota ya sakar mata murmushi tace" son kayi kyau sosai fa, uniform din nan na kara maka kyau .
ya dage mata girarsa daya yace "Allah first lov ?" ai daman can ni mai kyau ne sannan duk maccen datayi dacen samuna , ta gama samun duniyarta sai dai ta nemi lahirarta kawai " ummi tayi dariya sosai ya kamo hannun ummi cikin nasa muryasa a shagwabe hade da dan karyar da wuyansa, yace "first lov da kanki ma kin yaba dani "tace uhmm yabon gwani yazama dole "yace to meyasa bazaki bani auren zeenat ba ?
Ta lissafomasa dalilinta kmr yadda ta sanarwa Muhammad ta Kuma sake jaddada masa yaje gaba ya nemi mata Amman banda diyarta ranshi ya baci matuka Amman ya share sai dai take Yar fara'a dake fuskarsa ta dauke " sai dai bai nuna ba , cikin sanyi murya yace "to Shikenan ummi na hakura, dan bazan taba zuwa koina neman aure ba" saboda banida nagartar daza'a soni har a bani aure" ummi tace "ba fa haka nake nufi ba" yace "haka ne mana first lov" ina da munanan halayen da ban cancanci abani mata aure ba. ummi tayi murmushi tace "nifa bance haka ba"
" haba first lov kince mana gashin nan kema da kanki kin hanani taki Yar , to waye zai amince ya bani yana kaiwa nan ya cire hannun ummi cikin nasa ya mike cikin sanyi jiki tamkar bai damu ba ,gabadaya jikin ummi yayi sanyi ita bawai auren ne bata so ba halinsa take gudu ta yaya zata yarda ta aura masa marainiyar Allah yazo yana cutar mata da yarinya .
Abin mamaki duk a tunanin DEENi ba zai shiga damuwa ba akan kin amincewar ummi ba,sai gashi dumu dumu cikin tashin hankali kullun sai yayiwa ummi naci da magiya akan ta bashi auren zeenat ,ita kuwa ummi duk lokacin data ga ya dauko mata zance sai ta share hade da bata fuska .