AUREN SIRRI PG9-10
AUREN SIRRI
๐๐๐
๐๐๐๐๐
AYSHA A BAGUDO
Page 9-10
Zeenat kwance a bedroom din ummi hannuta rike da wani English novel face to face tayi zurfi cikin karatun novel din saboda yadda take enjoy din novel din ya .
DEENI ne yashigo gaishe da ummi kafin yafita aiki ,byn sun gaisa ne ummi tace "har ka shirya fita kennan ?
Yace mata "eh sannan yaja ya tsaya yayi shr ya zubawa ummi idanunshi .
ummi ta dubeshi tace" da magana ne ?
Tunda ta rigada tasan muddin yayi shr irin haka to da magana a bakinsa.
koda yake tasan dai zance nasa bai wuce maganar zeenat bane " Kuma daman tana son zeenat din tajima kunneta idan ta amince ruwanta "
dan haka ummi ta kalleshi da kyau tana nazarinsa ta numfasa sannan tace " kayi shr alhalin nasan da magana abakinka .
, muryasa a shagwabe yace "first lov kan dai maganar zeenat ne ,dan Allah first lov, ba yabon kai ba "ina da qualities din da za'a bani auren kowace irin mata nake so" Kuma ko Yar gidan waye "
"Yar taki ma daba wani kyau ne daita ba" dan ma zan taimaka mata "ya fadi haka fuskarsa a hade ,.
ummi tace "duk da haka dai bazan bada diyata ba kaje waje ka gwada sa'a r ka" wai ma in tambayeka DEENi ya maida hankalinsa sosai ga ummi" kai da kake damun kanka da zance nan kullum , kasamu ita yarinyar da maganar ,kun daidaita kanku ne ?
DEENI yace" uhmm kece dai zaki sanar mata, ummi ta nuna kanta da dan yatsanta, "nice ma zan tayaka yakin nemar maka soyayyarta?
" lallai ma bason auren nata kakeyi ba" ka share zance kawai tunda baka shiriya neman aure ba.
yace "to ni first lov in na fada sai naga tamkar Raina ne zatayi, ummi tace" kunji girman kan ba ?
a hassale ummi tacigaba da mgn " ni dan Allah kayi hakuri ka bar zance nan, haba duk kabi katadda hankalinka da nawa. yarda ne dai ba zanyi ,
dan haka kayi hakuri kabar zancen nan kwata kwata dan ba yarda zanyi ba .
DEENI daya gaji da yiwa ummi magiya ya hakura ya ficewarsa ,yana jin takaici kansa, tun daga lokacin da zeenat taji DEENi ya ambaci sunanta ta mike zubur zaune daga kwanciyar da tayi, hankalinta a tashe jikinta har rawa yake tsabar rudewa.
" ita zeenat din DEENi yake nufi ko wata daban?
ahankali ta furta in ko ita yake nufi dakuwa ta more a rayuwarta, dan gaskiya DEENi ba irin namijin da mace zatace bataso bane , ahankali ta sake furta A'a dan Allah ummi kada kimin bakinciki mana.
tana jin fitarsa ta fito da sauri daga dakin tana kallon ummi dake zaune tana jan carbi, zatonta ko ummi zata mata maganar ne, Amman sai taga sabanin haka .
dan kuwa ummi ko kallon inda take tsaye batayi ba.
dan ta rigada tasan taji komai" to Kuma bayanin me zata tsaya yi mata. Ta dai yi shr ne taga yadda zata dauki lamarin .
Can kuma, ummi ta dago tana duban zeenat din tana nazarinta" yayinda zeenat din itama ummi take kallo" har zuwa lokacin ummi ba tace komai ba .
sai ma kau da kanta gefe datayi , ganin ummi bata da niyyar ce mata komai ,yasa zeenat kira sunan ummi" ta juyo tana duban zeenat din da kyau".
ahankali cikin sanyi murya tace ummi wai wata zeenat din yaya DEENi ke so ?
Ummi ta dan tabe baki sannan tace'" dan Allah rabu dashi wai ke yake nufi "da sauri zeenat tasa hannuwanta duka ta dafe kirjinta dasu tana zaro idanu waje "tace da gaske ni yake so ummi?
ummi tace" zan miki karya ne" zeenat ta marairaice murya tace" shine Kuma ummi zakice masa baki yarda ba.
ummi tace "to may kike nufi ,kina son kice min kina son DEENi kennan ? Zeenat Tayi shr dan bata da amsar bawa ummi dan gabadaya ilahirin jikinta bbu inda bai dauki rawa ba.
ummi ta sake yin magana daman kina son DEENi ne naga duk kin tada hankalinki haka ?
zeenat tace "nifa bance ina son shi ba Amman ke me yasa zakice A'a, Kuma ma mayye dalilin dayasa kika ki amincewa ,ummi tace" ok tutseni zakiyi" kan naki yarda ko yaya ,? zeenat tace "ba haka bane.
ummi tace" tsaya ma kiji abinda yasa naki yarda, DEENi "d'a" nane' ni haife shi da cikina sannan ke ma kinsa halinsa sarai da shege miskilanci da saurin jin haushi mutun ,abu kankani ke hassalashi ga tarin girman kan tsiya, zeenat ta tsugunna gaban ummi hade kamo hannuwan ummi duka cikin nata ,muryarta a sanyaye tace "haba ummi dan kawai saboda wannan halin nasa ne ,zai sa kiki amincewa , in dai dan haka ne' ni na amince da aurensa kinji .
ummi tace "duk kinbi kin koma kalar tausayi wai ma me ya birgeki da DEENi ne naga duk jikinki ya dauki rawa haka ?.
Zeenat tace "ai gaskiya yaya ba irin mutunmin da za'a tsaya cewa ba,aso bane ni dai na amince ,ummi tace ko kin amince, ni nace A'a ban yarda ba ,.
Zeenat ta mike cikin fushi tayi bedroom din ummi .
da kallo ummi tabi bayanta dashi ,ummi taji matukar mamakin ganin reaction dinta musamman da tasan zeenat din ,bata fiyye nuna fushinta akan abu ba .
Koda tashiga dakin ma waje tasamu ta zauna abunta tayi tagumi batayi aune ba, kawai taji hawaye na silalowa mata.
ita kanta tasha mamakin ganin hawayen na zuba a idanunta "ta tambayi kanta to daman can tana son DEENI ko yaya? domin abun itama yayi maseefar daure mata kai .
kuka take sosai da iya karfinta hade da ganin laifin ummi ,to me yasa ummi zatace batason aurenta da yaya DEENi byn ita tasha kisma haka a ranta .
ta ci kukanta sosai har sai da taji alamun kanta ya fara mata ciwo sannan ta runtse idanunta ta kwanta nan a gefen bed din ummi ta cigaba rera kukanta kasa kasa .
Yinin ranar tayi shi ne cikin daki hade da tunanin DEENi da kitsima kalar rayuwar da zatayi a gidansa,
Da zarar taga ummi kuwa take hade fuskarta saboda jin haushin abinda tayi " .
kusan zuwa Maryam uku gidan "Amman zeenat taki saukowa kasa" dan gabadaya ta kasa samun sukuni gabadaya haushin kowa take ji
,ita kuwa ummi sai binta take da idanu dan kasa magana tayi , gashi ranar Sam DEENi ma kin dawowa yayi da wuri sai wajen shabiyu na dare .
haka ma washegari tun da asubar fari yabar gida , ya dai shigo ya gaida ummi a tsaitsaye.
,byn ummi ta idar da sallah ne kafin ta soma lazimi , ta dubi inda zeenat ke kwance akan bed , idanunta a runtse tamkar mai bacci Amman Kuma ba baccin take ba .
ummi takira sunanta kusan sau uku Amman tayi mata shr alhalin tana jinta.
ummi ta sake kiran sunanta "zeenat nasan kina jina Kuma idanunki biyu Amman kika min banza , hade da ganin laifina .
"bakomai yasa kika ga naki yarda da maganarki da DEENi ba" nasan halin DEENi ciki da bai bashida dadin sha'ani kwata kwata gashi da bakar zuciya tsiya azo ayi auren nan yazo yana gana miki azaba, .
"ni.. nasan abinda nake gudar miki Amman inda kinkiji ke kika sani , kije Allah yabada sa'a .
Amman ki sani idan akwai wanda zai ji dadin aurenki da DEENi a bayana yake, Amman duk da hakan bazai hanani fadar gaskiya ba idan tazo.
Kuma shawarata gareki ki rage rawar kai dan idan ya fahimci haka zaki sha wulakancin, da karshe km mutuncinki ya zube a gurinsa.
ga zaton ummi zata ji zeenat din tace ta hakura da auren DEENi din , Amman sai ganinta tayi ta duro daga kan gado ta zube gabanta durkushe.
tace "idan dai har kin amince ummi inshallahu bbu abinda zai faru sai alkhairi .
Ummi tayi shr tare da tsura mata idanu tana kallonta sannan tace" kina nufin kin amince zaki auri DEENi kennan da wannan halin nasa ? Zeenat tayi shiru ta kasa cewa komai , sai karyar da wuya da tayi , ummi ta sake duban tace" ke..bafa zan yarda da auren nan ba .
take zeenat ta fashe mata da wani irin kuka tana bata hakuri ta amince dan Allah, abun ma ya daina bawa ummi mamaki , yadawo bata tsoro ,.
Cikin kuka zeenat ,tace" ai shi yace yana sona " to ta yaya ke zakice A'a ummi ta bita da wani irin kallo tausayi , aranta kuma tace ya'yan yanzu sam basu da kunya .
wani irin son zeenat din ne taji yana ratsa ko wani part na jikinta.
ga tarin tausayin yarinyar dake matukar damunta ,Amman hakan ba zai sa taji zata iya amincewa da muradinsu ba .
ta kau da tausayin yarinyar a ranta ta hade fuskarta tamau ,sannan tace "ke dan ubanki akan na hana aurenki DEENi ne zaki ta sani gaba da kuka "dan bakisan ciwon kakin ba ?
dan ma ke shashace ko shi dayace yana son naki" ba wai damuwa yayi dake ba.
tunda har zuwa yanzu bai kawo kansa gareki ba.
sai kece zaki wani damu mutane da kuka akanshi ,cikin wani irin sabon kukan zeenat tace "bagashi ke yayi miki maganar ba .
Ummi tace " OK dan yayi min maganar shine me?
" ni zai aura ko ke ?
da kyar ta iya sausauta kukanta tace "ummi dan Allah ki amince mana tunda day har shi ya furta da kanshi".
ummi taja tsaki ta mike tsaye tace ni matsa ban waje tun banyi ball dake ba shashar bazan kawai
ta wuce parlour
ta barta zeenat nan durkushe aiko zeenat na ganin haka ta sake fashewa da wani kukan har da shesheka .
*****
Da daddare misalin karfe tara ,DEENi zaune a parlour shida ummi suna kallo Amman jifa jifa take sako masa hirar duniya "
shi dai jinta kawai yake , yayi tamkar bbu abinda ke damunsa Amman shi kadai yasan abinda yake ji aransa' zeenat ta hado masa coffee tazo har inda yake zaune ta ajiye masa nan kusa dashi, ta juya zata bar gurin ko kallo bata ishe shi ba ballanantana yasan ko ita wacce, hakan da yayi ne yasa ummi taji ba'adadi aranta .
muryasa a kwasashe yace ke.....ta juyo ahankali hade da zuba masa idanunta , shima ita yake kallo da rikitattun idanunsa ,yace "dawo ki dauki abinki konace miki ina bukatane?
da sauri zeenat ta girgiza masa kai, ya kau fuskarsa kmr bashi yayi maganar ba .
bai sake cewa komai ba ,km bai kalli inda ummi ke zaune ba, ya mike kan three site yayi kwanciyarsa " aransa yace akanki zan dinga huci takaici abinda ummi tamin.
"tunda tace bazata auramin ke ba,
nima na hakura da auren naki" sai ta jikaki tayita tasha .
kunya ne tattare da tsoro suka taru suka ma zeenat rubdugu , taji gabadaya kakafunta sun Gaza d'aukarta "
ana cikin haka shemah ta shigo da sallamarta "kai tsaye wajen ummi ta nufa ta zauna tana gaishe da ummi "
Ummi ta amsata cikin sakin fuska ,
sannan ta juyo tana kallon inda zeenat ke tsaye kikam tamkar an dasata' km sai a lokacin idanun shemah ya Kai ga DEENi dake kwance idanunshi a lumshe.
itama idanu ta zuba masa tana kallonsa , tana jin wani irin ajikinta yayinda gefe daya na zuciyarta ke wani irin dokawa da sauri " shi km kwata kwata bai ma san Allah yayi ruwan mutun a gurin ba " ahankali ya mike tsaye yana wa ummi sai da safe .
a ciki ta amsa masa dan takaici abinda yayiwa zeenat " suna hada ido da ummi ya sakar mata murmushin gefen baki hade da kashe mata idanunsa daya wanda ita kadai ta gani , da sauri ya haye step ,.
yana barin wajen .
atare suka sauke ajiyar zuciya daga zeenat din har shemah " .
dan har gara shemah ma akan zeenat din, dan ita gabadaya a frigice take "idanunta ta dan juya da niyar satar kallon inda ummi take , ai ko take suka hada ido daita, take ummi ta watsa mata harara dan gabadaya ta gama bata haushi .
yana shiga dakinsa ya fada kan bed dinsa ya jawo system dinsa kennan idanunsa ya Kai ga phone dinshi dayaga almost 12 miss cal da sauri yasa hannu ya dauki wayar yayi dealing number daya Gani bugu daya biyu "fk ya dauka yace" ka kyauta angon zeenat" bukatarka ta biya, ai dole kashare mutane.
DEENi yaja tsaki sannan yace dan Allah ni rabani da wannan zancen naka na banza" haka kurum kasa mutun a one chance,.
gashi kaja wa mutun wulakancin kawai ,fk yace wulakancin Kuma a gurinwa ?
DEENi ya tabe baki tamkar fk din na ganinsa yace "a gurin ummi mana.
" to meyya faru?
inji cewar fk.
sai da DEENi ya jima bai yi magana ba kafin daga baya ,yaja wani irin numfashi yace "ummi fa taki amincewa da shawarka ,sai ma wani yawo ake min da hankali kmr za'a bani gold.
fk ya kwashe da dariya yace "mutumina ko dai ka zurma ne, irin wannan jin haushi haka?
DEENi yace "kai nifa na hakura da yarinyar nan wlh ,dan gaskiya bazan jura wannan wulakancin ba .
ga mata nan dayawa a waje suna bina kmr su lashe ne " fk yace" tsaya ranka ya dade ba haka za'a yi ba, bari zamu samu big dady da zance nasan komai zaizo da sauki ,
kai me zai hana kasumu zeenat din da kanka.
DEENi ya sake jan tsaki yace "maganar bazan kennan ai inda takaicin yake kennan, haba ai kauyancine a wajena na tsaya ina fad'ar kalmar so ga karamar yarinyar .
fk yace "kaji irin ta ko kana son yarinya Amman girman kanka na neman cutar da kai "
DEENi ya katseshi da hanzari " hade da cewa "kai fa dan matsala ne , na sha gaya maka ka daina cewa ina son yarinyar nan, zan dai aureta ne kawai.
fk yace "Shikenan ajiye wannan zance,
bari gobe inshaallahu zanzo muje gurin big dady a San abun yi DEENi bai ce komai ba ya katse wayarsa .
MMN SUDAIS CE