MATAR MAMMAN.

Chapter two

by @maikosai53

Bisimilillahir_Rahmanir Raheem.


Page 3_4.


Tunda daga nesa ya hangota ta nufo wajenshi a guje, dariya ya yi tare da girgiza kansa cikin zuciyarsa yana mai addu'ar "Allah ya shiryeta ta sami nutsuwar sanin cewa ta girma".

  Tun kafin ya ida maganarsa ta iso sai faman haki take, sunkuyawa ta yi game da ri'ke gwiwowinta duka biyun da hannayenta.

  Cikin hakin ta ce,

   "Wai kai Allah ya temakeni ai da kasheni za ta yi nasan inta kama ni"

 Baba Mai gadi da tun isowarta ya ke kallon yadda take ta faman fidda numfashi da sauri da sauri ya ce,

  "A'a Matar Mamman Me ya faru haka naga kina ta haki?, ince dai ba tsokanar taki da kika sabayi kika yo ba?"

  Ya tambayeta.

Sai da ta mi'ke tsaye daga sunkuyen da ta yi fuskarta d'auke da dariya ta ce,

 " Hmmmm! Kai dai yau Baba ka tayani murna waccan mai jikin 'karfen ba ta kamani ba"

 Sai da ya dara kana ya ce,

 "Tofa Matar Mamman wace haka ??"

 Ya tambaye ta.

Benchin dake gefenta ta samu ta zauna tana mai gyara zamanta sosai kana ta ce,

  "Caab! Baba baka san muna da mai jikin rodi anan gidan ba, wallahi karka bari Allah ya had'aka da ita, dan mazga d'aya za ta ma kajika a lahira. "

 ta sake numfasawa kafin ta d'ora da fad'in,

  "Bakasan yaya Saudat jikinta irin na rodi ba ne, kaga yadda ta biyo ni d'in nan hmm! da takamani da tuni ai yanzu kuna shirya kai gawata kabari"

Dariya ya yi sosai irin tasu ta manya kafin ya ce,

  "Yanzu Ramlat au Matar Mamman yayar taki ce mai jikin rodi??"

 Zaro idanuwanta ta yi komai ta tuna kuma sai ta ce,

 "Ah Baba baka fahimta ba ne, amma Allah kuwa in ta masgeka ko sai ka ce daman bakasan ta ba"

 "To ni in banda abinki ma me zai had'ani da ita tsofai_tsofai da ni da har za ta mazgeni" Baba ya ce.

  Sai da ta d'an yi jim tamkar wata mai nazari kafin ta ce,

 "Au haka ne kuma fa haka ne, ni ce dai yau Allah ya ceta, yanzu kai komai za ka ce mata ba za ta masgeka ba ko?"

Murmushi ya yi kafin ya ce,

 "To ni mema zan mata bacin kullum hirar arzi'ki ce da abin alkhairi ke rabani da ita" 

 Baba ya ce.

Turo baki ta yi kana ta ce,

 "Wallahi Baba ka ki ya yi yaya Saudat uhmm! Kwanciyar makafi ta ke maka, wata rana sai dai kaji ta maka qwamas ka suma"

Dariya sosai zancen na ta ya bashi sai dai gudun rigimarta ya sanya shi shanye kayarsa. .

 "To Matar Maman, kema in kika daina tsokana ba wanda zai ta'ba ki balle ya sumar da ke"

 Baba ya ce.

"Caab wallahi bazan dai na ba, nifa sai dai su gaji dan kansu su barni, dan ni daman nan gani nan bari ce takalmin kaza"

 Tana gama fad'i ta mi'ke da nufin barin wajen tare da fad'ar,

 "Ni dai Baba na gayamaka wallahi ka yi taka tsam_tsam da ita dan wataran Hmmmm!"

Shi dai Kawai dariyarsa ya yi, 

   "kullum dawo wa baya take kamar ba 'kara girma ta ke ba"  ya ce.

 Ba cikin gidan ta koma ba ,'bangaren lambu ta wuce kai tsaye.

Can wajen da Mamman ya ware yake kiwon sa ta wuce.

Kallon d'awisun da ya kuma ri'ka ta yi kafin ta ce,

 "Hohoho! ga nama iya nama amma a hana mutum, wallahi in aka kaini bango duka sai na sa muku guba kun mutu"

Kamar sunji me take cewa d'aya daga cikin su ya zuro kansa ta cikin ragar.

 "Ehh! Kalleni da kyau fara nake tas yaro ,wallahi Sa'arku d'aya ina tausaya muku ne shi yasa, amma duk randa kuka kaini bango saina karya qashin bayan ku ".

Matsawa ta yi gefen su kafin da d'ebi 'kasar dake wajen ta watsa musu .

  " 'Yan banza sai taurin rai gareku"

  Ta ce tana mai tsaki.

  Daidai lokacin mai kula da lambun ya 'karasu wajen, ganin ta Wajen ya yi mamaki dan tabbas inka ganta wajen to *Mamman* ya mata fad'a ko an 'ba ta mata rai ta zo hucewa akan kiwonsa da yake yi.

 " A'a Ramlatu lafiya kuwa??"

  Ya tambayeta.

Jin muryarsa wajen da kuma sunan da ya ambaceta da shi yasanyata had'e fuska kafin ta ce,

  "Wai kai me ya sa sai kullum an nanata maka abu ne, na sha gayamaka ni ba sunana Ramlatu ba, in ba za ka ce "Matar Mamman" to ka barshi gwara ka ce mini keee ai".

 Shi ma had'e fuska ya yi daman sun saba duk sanda tazo sai sunyi chakwakiyarsu.

  " kinga yarinya ga sunan da nasani na ki amma bawani kakale da kike yi ba, in ba za ki amsa ba shi kenan, ni fa shi ya sa ba naso ki shigo nan balle mu had'u ma"

  Ya ce da ita.

 "Lallai ma Lawandin nan, kai ko kunya bakaji ba ka zo gidan ubana sannan ka ce bakason mu had'u to wallahi ka fita ido na , kai tsayama ni fa batun yau na gama fahimtar ka da ace za'a d'au wuqa a baka nasan fa kashe ni za ka yi, daman kwanaki na ta'ba kamaka da wuqa akaina za ka yankani da badan 'karfin addu'ar da nake da kuma ihun da na sa maka ai da tuni ka dad'e da aikani lahira, to wallahi a hir d'inka Ehhh!"

Cike da mamakin yadda take zaro zan tukan nata kamar gaske ya ce,

 "Ke! Ramlatu ki ji tsoron Allah, da yaushe na sanya miki wuqa a wuya??"

 "To zan maka qarya ne??"

  Ta ce masa.

"Shi kenan bari yayan naki ya dawo Sai na fad'a masa kinzo kina cutar masa da kiwon sa"

  Ya ce yana mai kallon ta.

Murmusawa ta yi kafin ta ce,

 "Dan Allah in baka fasa ba ba sunanka Lawandi ba ,ni kuma wallahi sai na ce, "na kama ka kana 'ko'Karin yanka masa guda d'aya, shi ne ka ri'ka ro'kona akan na rufa maka asiri, ka ce kuma za ka sammin in dai ban fad'a ba"

 Zaro ido ya yi,

   " ya ilahi! lallai wannan yarinya ta fi ni hatsabibanci"

 Ya ce a hankali yadda ba za ta jiyoshi ba.

 Bai tanka mata ba ya ra'ba ta gefenta ya wuce, dariya ta yi kafin ta ce,

  "Ai da ka kuma magana kaga aiki da cikawa"

tana fad'a tana mai 'ko'karin barin wajen.

  *******

Mota 'kirar corola ce ta danno kai cikin harabar gidan, sai da ta 'karasa daidai parking space sannan ta yi parking , wata dattijowar matace wacca a shekaru ba za ta haura 65 ba ta fito daga cikin motar 'bangaren mai zaman banza.

 Daidai lokacin Baba Mai gadi ya iso wajen Bayan ya mai da gate d'in ya kulle.

 "Hajiya sannu da zuwa"

 Ya ce yana mai 'ko'karin sunkuyowa dan d'aukar jakar kayan da wanda ya tu'ko motar ya fito da ita daga bayan motar.

  "Yawwa sannu, ya gidan?"

  Ta fad'a game da tambayarsa.

  "Lafiya Lau Alhamdulillah"

  Ya ce yana mai wucewa cikin gidan.

  A daidai lokacin ne kuma Matar Mamman ta fito daga lambun da taje, hango Baba da jaka tasan lallai Ammi ta dawo, da saurinta ta 'karaso inda ya ke kana ta ce,

  "Yanzu Baba saboda Allah wani mara imanin ne ya had'aka da wannan jakar wacca da 'kyar ma kake jan numfashi?"

 Murmushi ya yi kafin ya ce,

 "Haba mi ye abun nauyi a nan d'iyar albarka??"

 Da saurinta ta ce,

  "Wallahi da nauyi Baba Kawai tsabar rashin imani ne irin na 'yan Adam , amma dube ka fa yadda duk kake numfashi sama_sama kamar ana zare maka rai ace zuciyar Mutane ba imani haba"

  Har Baba ya bud'e baki zai yi magana ya ga tsayuwar Mamman ya had'e fuska tamkar Mala'ikan mutuwa wanda hakan ya tabba tar masa da cewa lallai yaji duk abin da take cewa.

Hango Baba na qoqarin magana ya sanya Mamman dakatar dashi ta hanyar samasa yatsa a saman le'ban sa tare damai alamar ya tafi.

 Ba yadda zai yi haka ya ajjiye jakar ya juya.

  "Yawwa Babana dire masa shi yazo ya d'auka ko yaji yadda akeji a cikin nauy........."

 Ma'kale sauran maganar ta yi a maƙoshinta saboda ganinshi da ta yi tsaye a gabanta kamar an cilloshi , tuni ta fara raba idanuwa 'kafar nan ta fara rawa. 

  "tabbas tasan yau me ceton ta sai Allah, shawara d'aya ce ta san na yi kawai"

Ta ku d'aya ta yi ya sanya hannunsa ya dam'ko ta ji ka ke luuuuuuuu tayo baya.

To fa! kome zai faru??? Ku biyoni dan jin yadda za taa Kaya, shin za taa Ku'butan ko kuwa????.