MATAR MAMMAN.

chapter three

by @maikosai53

Page 5_6.


Bisimillahir_rahmanir_raheem.


Da hannu ɗaya ya damƙota . ƙwallace ta cika mata idanuwa tabbas tasan yau ta shiga uku.

  " Wai me ya sa ita bakinta baya iya yin shiru ne??"

  ta tambayi kanta da kanta.

 "Maimaita kalamanki na ji"

 Ya ce da ita fuskarnan a murtuke tamkar damamiyar fura.

Turo baki ta yi kafin ta ce,

 "Ni fa ba abin da na ce wallahi, ka tambayi Baba ma ka ji ."

 "Ba wannan na tambayeki ba, za ki maimaita abin da kika ce ko saina ɓaɓɓallaki kamar yadda ake karya kara".

 Ya faɗa yana mai murɗe mata hannunta ta baya, wanda har sai da ta saki ƴar ƙara.

  "Yarinya kaɗan kika gani ma, ke ba jurinki rashin kunya da fitsara ba?, wallahi na kuma ji ma kina ke sunanki *matar Mamman* saina zubar miki da haƙoran gaba ,sai kin zama baki da haƙora sai dai ki dinga mamul-mamul kamar yadda tsofaffi ke yi"

  Jin za'a mayar da ita tsohowa ya sanyata yin wiƙi-wiƙi da idanuwa.

  "Dan girman Allah ka yi min rai, wallahi ban shirya zama tsohowa yanzu ba, kana kallo ko Mamman ɗina ban aura ba balle na haifa........"

 Maganar ta sake katsewa sakamakon fyalle mata baki da ya yi da ƴan yatsunsa biyu.

  Riƙe bakin ta yi tare da sakin ɗan marayen kuka.

  "A'a auta waya taɓamin ke kuma? Me ya faru?"

 Suka tsinkayi muryar Ammi lokacin da take ƙoƙarin ƙarasowa wajensu.

 Jin muryar Ammi ya sa ya yi saurin sakar mata hannu, galla mata harara ya yi yana mai wucewa ciki.

Ammi ce ta ƙaraso .kallonta ta yi kafin ta ce,

 "Ɗiyar albarka waya taɓamin ke ?,ma za faɗi ko waye yanzu yasha kashi".

Shagwaɓe fuska ta yi jin Ammi na daɗa shagwaɓata.

  "Ammi ba yaya mugu ba ne ya fyallemin baki, kinga fa harda jini saura ƙiris haƙorana na gaba su zubo"

Ta ƙarashe faɗa tana mai nuna mata bakin.

 "Kai!kai! gaskiya yaya mugu ya yi rashin kyautatawa muje ciki na same shi"

Ammi ta ce, tana mai riƙe hannunta zuwa ciki.

 Baba mai gadi yana hango diramar da akeyi duk da baijiyo me suke cewa ba ,amma yasan tabbas ya mata wani abun.dariya ya yi yana mai ƙara jinjina yarinta da wauta irinta Ramlat.

Su Rahma ne suka sakko ƙasa jin muryar Ammi na ƙwalawa Mamman kira .

  "barka da zuwa Ammi"

 Saudat ta ce.

"yawa barka dai, sannunku da gida?"

 Ammi ta ce tana mai ci gaba da ƙwala masa kira.

Shi kam gogan naka ya na ji ya yi shiru, dan yasan ba akan komai take nemansa ba sai akan waccar figigiyar yarinyar da ta gama haɗa ƙaryayyakinta ta faɗa mata.

  "za ka sakko ka same ni ne, mugun banza"

 Ammi ta ce.

Kallon junansu su Saudat suka yi game da taɓe baki. 

  "Lallai yarinyar nan wato sharrin nata ya barmu ya koma kan babban yaya, cab! ai kuwa kin ɗakkowa kanki aiki"

 Saudat ta ce a hankali.

"Ammi muje ki huta mana daga dawowarki za ki dakatata wannan mara kunyar yarinyar?"

  Cewar aunty Rahma da ta ke ƙoƙarin amsar jakar hannun Ammi.

 Kamar wacca take jiran ƙiris a taɓota ta fashe da kuka game da faɗin,

 "Kinji ko Ammi, wallahi daman tunda kika fita suke ta dukana, gaba ɗaya su duka suka yi mini taran dangi aka"

  Ramlat ta faɗa tana goge ƙwallar da ta zubo mata.

Cike da mamakin kalmominta suke kallonta.

Ammi kuwa haɗe fuska ta yi kafin ta ce,

 "Wato taron dangi kuka yiwa ɗiyar tawa?, lallai ba shakka yanzu na tabba tar ko mutuwa na yi ba zaku iya riƙemin ita ba, balle ko tare mata wani abun ko?"

 Aunty Rahma ce ta matso daf da inda Ammin take kafin ta ce,

"haba Ammi me ya sa za ki yarda da zancan wannan yarinyar?, ya kamata ace tunda daɗewa kinganota da irin sharrin da takewa mutane, meyasa zamu mata taran dangi akan me Ammi?"

 "Ni dai na faɗa muku duk randa wani ya kuma gigin dukar mini ita wallahi sai ransa ya ɓaci"

 Ammi ta ce, cike da faɗa.

Ba ta kuma bi ta kansu ba ta wuce part ɗinta, wanda ya kasance a ƙasa.

Mara mata baya ta yi dan tasan muddin ta tsaya zasu iya yimata wani abun.

Tana shigewa ɗakin ta faɗa kan gadon Ammi tare da faɗin,

 "Wash! Allah na, wallahi yau naci azabar ƴan uwa"

Kallonta Ammi ta yi tare da faɗin,

 "Kul! banason na kuma jin kince haka, sufa ƴan uwanki ne akan me zasu azabtar da ke,kema fa bakyajin magana Ramlatu"

Turo baki ta yi kafin ta ce,

  "Allah Ammi babu wanda na yiwa sharrifa , bakiga yadda suka kumburamin jiki ba."

 "Shikkenan koma dai menene dai kar na kuma ji kinji ko, ki rage tsokanar nan ".

Gyaɗa mata kai ta yi alamar to.

  "Yawwa ko kefa, tashi ki haɗomin ruwan tea banda madara"

 Ammi ta ce mata.

Miƙewa ta yi tare da ficewa daga ɗakin.

Ammi kam girgiza kanta ta yi, tana mai kuma mamakin yadda kullum Ramlat ke mayar da kanta baya tamkar ba ta girma.

  "Lallai ba shakka da wuri zan aurar da ke ɗiyar nan."

Ammi ta ce, tana mai miƙewa tare da faɗawa bayi.

Ramlat kuwa na fita kai tsaye kitchen ta nufa, tana shiga ta soma dube-duben abin da za ta haɗawa Ammi tea da shi.

Kaf lokar kitchen ɗin ta hau binkicewa, duk a domin neman kayan tea ɗin.

 ya jima yana kallonta, cikin zuciyarsa kuma tambayar kansa yake ,

 "Me take nema kuma?"

 Tamkar daga sama ta jiyo sautin muryarsa na faɗin,

 "Uban me kike nema ?, duk kika hargitsawa mutane waje haka?"

  Ya tambayeta yana mai matsowa kusa da ita.

Jin muryarsa ya sanyata fara rawar mazari, tasan shi kenan ruhinta ya fara motsin tafiya daga jikinta, kasheta kawai zai yi.

 "Uhmmm! dama-dama-dama uhmmm!".

Gaba ɗaya ta rikice tama kasa magana.

 Tsawa ya dakamata kafin ya ce,

 "Tambayarki na yi bawai inda-inda na ce ki yi mini ba malama."

  "Uhmmm ! daman Ammi ce ta ce na haɗo mata tea"

 Ta ce a hankali.

"Shi ne ki ka bi kika hargitsamana kitchen ɗin haka?"

  Ya tambayeta cike da tsawa.

Raba idanu ta somayi, take hantar cikinta ta soma kaɗawa, ruwan hawaye ya cika idanuwanta taab!.

 Hannayenta ta haɗe waje guda, cikin firgici da tsoro ta soma faɗin...