MATAR MAMMAN.

chapter five

by @maikosai53

Page 9_10


Bismillahir_Rahmanir_Raheem.


Da ƙarfe Ammi ta ce,

 "What! ??, me kuke cewa haka?"

Cikin razani da firgici Aunty Rahma ta soma faɗin,

 "Ammi suma ta yi amma yanzu za ta farfaɗo insha Allahu, plz calm down"

Cikin fushi da faɗa Ammi ta soma faɗin,

 "Ɗiyar tawa ba ta numfshi kice na kwantar da hankali na? ku faɗamin me kuka yi mata wallahi ko na ci mutuncinku, da man tun ɗazu ina jiranta ashe ku kuka tsareta da bala'in ku shiyasa ba ta dawo ba, ku gayamin waye ya taɓamin ita??"

Wuri-wuri suka shiga yi da idanuwansu kowannensu yana fargaba da tsoron faɗa mata ,

 "MAMMAN ne."

"Sai na ci mutuncinku za kuyi magana ko kuwa?"

Ammi ta faɗa cike da faɗa.

Baba Mai gadi ne ya yi gyaran murya kafin ya ce,

 "Hajiya ki kwantar da hankalinki ba wani hatsari ne babba ba tunda madam ta ce za ta farka, yanzu muyi haƙuri a fara mata taimakon dan Allah"

 Ya faɗa cikin tattausar murya.

Sauke ajjiyar numfshi Ammi ta yi ,ba ta ce musu ƙala ba ta neme waje kan kujera ta zauna, zuciyarta fal cike da assasa irin abin da za ta musu na hukuncin abin da suka aikata.

Ganin hakan ya sanya Baba yiwa Aunty Rahma nuni da ido alamar ta soma aikin nata.

Taimakon gaggawa ta shiga yi mata, cikin hukuncin Allah taja dogon numfshi kafin ta sake shi.

Gaba ɗayansu murna suka shiga yi tare da godewa Allah ganin ta dawo hayyacinta.

Cikin sauri Ammi ta matso kusa da ita tare da riƙe hannayenta kana ta ce,

 "ƴa ta sannu, miƙe zaune muga, sannu kinji"

Binso ta soma yi da ido ,ɗaiɗai take kallon su kamar wacca ba ta taɓa ganin su ba, cikin abin da baifi minti biyu ba ta fashe da kuka.

Ganin hakan yasa Ammi janyota ta mannata da jikinta ta soma ɗan dukan bayanta a hankali-a hankali.

  "Yi shiru ɗiyata ,ki daina kuka ,ki nitsu ki faɗamin waye ya miki haka cikinsu?"

 Ammi ta tambayeta.

Sassauta kukan nata ta yi cikin shassheƙa ta soma faɗin,

 "Ammi mutuwa zanyi ,bayana ,ƙafafuwana ,kwankwasona Ammi mutuwa zan yi ke taimaka mini"

 Lallashinta ta ke yi sosai cikin san kwantar mata da hankali ta ce,

 "ki yi shiru ɗiyata ki nutsu ki faɗamin me ya faru da ke?"

Miƙewa ta yi zaune daga jinginan da ta ke jikin Ammin ,langwaɓar da kanta ta yi kana ta ce,

 "Ammi duka ƴan gidan nan basa sona, wallahi so suke suga na mutu, a gaban Yaya Saudat akai komai amma taƙi taimako na har sai da ya aiwatar da mummunan nufinsa a kai na"

Ta ke ƙirjin Ammi ya hau bugawa fat-fat, cikin sauri ta ɗaga ta tsaye tare da faɗin,

  " janye min siket ɗinki ma za"

Aunty Rahma da ta fahimce abin da Ammi ke nufi ta yi saurin dakatar da ita ta hanyar faɗin,

 "Ammi ki kwantar da hankalinki bafa abin da kike tunani ba ne, kawai Yaya ne ya sanyata tsallen kwaɗo shine fa ta suma, kinsan dai daman ita jurin ta fitsara amma ba jarumta"

Ji Ammi ta yi kamar ta ɗauke Aunty Rahma da mari dan haushi sai dai wannan sam ba ɗabi'ar ta ba ce,hakan ya sanya ta galla mata harara kana ta ce,

 "Ke kuma jurinki gulma ba, wai yaushe za ku so yarinyar nan ne? wallahi akanta zan iya ɓatawa da kowa, shi kuma mara kunyanya na ina??"

Juyawa ta yi ta kalli Saudat kana ta ce,

 "Maza ki haura saman ki kirawo min shi, kuma ƙafarki ƙafarsa"

Ko ida zance Ammi ba ta yi ba ta juya ta soma tafiya, cikin zuciyarta ta kissima irin faɗan da Yayayn na su zai sha yau.

Tana shiga ɓangaren na sa ta taddashi zaune yana kallo a system na shi, bayan ta yi sallama ne ta sanar da shi saƙon Ammi.

 " Kije ga ninan zuwa"

Raurau ta yi da idanuwanta kafin ta ce,

 "Yaya dan Allah ka zo muje ,wallahi haka ta ce ƙafata ƙafarka"

Harara ya galla mata kafin ya miƙe, ko amsa bai ba ta ba ya wuce gaba.