chapter six
by @maikosai53
Page 11-12
Bisimillahir rahamanir raheem.
Suna nan zaune kamar yadda Saudat ta tafi ta barsu sai dai saɓanin Ammi da keta safa da marwa a tsakiyar falon.
Hangoshi da ta yi tafe cikin sanyayyiyar tafiyarsa yasa ta ƙara tunzura wato shi ko ajikinsa ma.
"Dan ubanka ba za ka ɗago ƙafa ba ne ko kuwa ni na ƙaraso inda ka ke"
Ammi ta ce cikin hasala.
Kowa na wajen sai da ya tsorata ganin yadda Ammi ta ɗau zafi akan abin da bai taka kara ya karya ba.
Shi kam gogan naka ko ajikinsa illa kawai zuciyarsa da ta shiga zulumin zagin da Ammi ta auna masa, jiya yi kamar ya sanya ƙafafuwansa ya tattake yarinyar.
A hankali ya ƙarasa inda take ya sunkuyar da kai ƙasa kafin ya ce,
"Ammi ki yi haƙuri"
Ammi cikin fushi ta ce,
"Da haƙurin ya mutu sadakar nawa ka bani, me ta maka da har ka illata ta haka??"
Ɗago kansa ya yi ya kalli Ammi idanuwansa duk sunyi jajawur kamar garwashi.
"Ammi ki tambayeta mana"
Ya ce cikin sanyayyiyar murya.
"Daga bakinka nakeso na ji, ko zaka nuna min aikina ne??"
Ammi ta ce.
"No ba haka nake nufi ba Ammi, bansan me ya sa kike san mara mata baya ba bacin ko kaɗan ba ta da kunya ga munafurci kala-kala"
Ammi ta kuma fusata jin an ambaci ɗiyar tata da Munafuka.
"Wallahil azeem zanci mutuncinka Mamman za ka faɗamin abin da ka mata ko sai na mauje ka anan wajen"
Tuni sauran annurin da ke shimfiɗe saman fuskarsa suka baje ,bai taɓa jin faɗa daga wajen Ammin sa ba sai yau ,yau ɗinma akan wannan figaggiyar yarinyar lallai ba shakka sai ya gyara mata zama.
"Ammi ki yi haƙuri, kamata na yi da laifi dumu-dumu shiyasa na mata hukunci daidai da abin da ta aikata,ki tambayeta ai ita tasan me ta yi"
Ya ƙarashe faɗa yana mai nuna Ramlat da yatsansa ɗaya.
Cikin marairaice murya Ramlat ta ce,
"Wallahi Ammi bafa abin da na yi, kawai na je ina haɗa miki tea ne fa da kika ce shi ne ya tsareni a kitchen ɗin wai lallai saina dafa mai indomie ni kuma kinsan.........."
Saurin haɗiya kalmomin da take shirin furtawa ta yi ji kake maƙuut, sakamakon kallon da MAMMAN ya watsa mata na zamu haɗu da ke.
Ammi ta juya ta kalleshi daidai da ɗaukewar idansa akanta kana ta ce,
"Koma dai mene ne na rantse ka kuma aikata makamancin hakan sai na karya maka ƙashin baya ka kasa tafiya, ka ji ko"
"Na ji Ammi, insha Allahu ba za a kuma ba"
"Sai ka riƙe wannan ,kada ka sake mu kuma gamuwa"
Ta juya ta kalli Ramlat ta ce,
"Ke kuma ta shi mu je"
Ramlat ta miƙe dama Allah-Allah ta ke subar wajen, ƙara ta saki sakamakon riƙewar da ƙafarta ta yi.
"Ammi wallahi ba zan iya ba"
Ta ce.
Kallon Mamman Ammi ta yi da shikam har ya juya zai koma inda ya fito.
"Kai dawo nan"
Ya jiyo muryar Ammi na faɗin haka.
Juyowa ya yi ya dawo inda ta ke tsayen.
"Ga ni"
Ya ce ataƙaice.
"Ɗauketa ka kaimin ita ɗaki"
Ammi ta ce .
Jiya yi zuciyarsa na masa wata iriyar tafasa, kan kace me ya sungumeta a kafaɗarsa ya yi hanyar ɗakin Ammi.
"Tafi min da ita a hankali, in ka jimata wani ciwon sai ranka ya ɓaci"
Ta juya ta kalli su Saudat da ke tsaye ta ce,
"Ku kuma wallahi ku fita daga ido na"
Ta juya ta bar wajen.
Baba ma ficewa ya yi daga falon zuciyarsa cike da mamaki irin hali na Ramlat, bacin abin da ya faru amma har ta sami ƙwarin gwiwar shirga wannan uwar ƙaryar.
Su Aunty Rahma kuwa kasa cewa komai suka yi ,kowacce ta juya ta kama gabanta, sai dai kowacce zuciyarta cike fal da tausayawa Ramlat akan irin aika-aikar da ta tafka.
Shikam Mamman yana shiga ɗakin ya direta ƙasa a tsaye ba tare da ya yi tunanin ko za ta ji wani rauni ba.
"Auuch"
Ta ce, tana mai rau-rau da idannuwanta.
Bai ko kalleta ba ya fice daga ɗakin, zuciyarsa a cunkushe.
Itakam faɗawa ta yi kan gadon Ammi tana mai mayar da numfshi tare da godewa Allah akan baice mata komai ba.
"Wayyo Allah, na shiga uku"
Ta miƙe zumbur tamkar doki daga kwancan da ta ke.
"Shi kenan nasan in ya kamani kasheni zai yi ko? wayyo Allah na!"
Ta ƙarasa tana mai dafe ƙirjinta tare da fidda idanuwanta waje.
A haka Ammi ta shigo ta risketa, ƙarasawa ta yi inda ta ke ta riƙo hannayenta kana ta ce,
"Ramlat me ya faru? wani abun ya kuma yi miki??"
Ramlat ta girgiza kai kafin ta ce,
"Ammi duk abin da na faɗa ɗazun ƙarya na ke daman dan dai kada ........"
Ta haɗiye ƙarashen zancen sakamakon irin kallon da Ammi ta kafeta da shi.