MATAR MAMMAN.

chapter seven

by @maikosai53

Page 13-14.


Bisimillahir rahmanir raheem.


Ran Ammi ya ɓaci ta kuma kafeta da idanuwanta, matsowa ta yi daf da ita kamar za ta da keta, komai ta tuna koma oho.

 "Yanzu nan Ramlat duk abin da kika faɗa ƙarya ne??"

Ramlat ta yi wiƙi-wiƙi da idanuwanta kafin ta ce,

 "A'a Ammi banda fa abin da ya yi mini, kawai na yanzun ne na yi ƙarya kuma fa ni dan duk ki ramamin ne, kuma ba kiga yadda fa ya tsorata ba, kinga yadda idanunwansa suka yi ja kamar zai yi kuka, ni na maso ya yi kukan fa wallahi musha kallo........."

Cikin zafin nama Ammi ta ce,

 "Rufemin baki ,wai ke me ya sa har yanzu ba zaki san kin girma ba? Ramlat shekarunki fa 14 amma ace har yanzu kina abin da ko ɗan shekara 9 ba zai yi ba, to bari ki ji duk abin da ya sameki ke da shi ba ruwa na ko kasheki zai yi ya yi daman nima na gaji da zamanki a gabana kinga shi kenan ai kowa ma sai ya huta da ƙaryarki"

 Fashewa ta yi da kuka cikin sauri ta riƙo Ammi da take ƙoƙarin fita daga ɗakin.

 "Dan Allah Ammi kada kice ya kasheni wallahi na dai na bazan kuma dan Allah wayyo Allah na Ammi ta daina so na"

 Ta rushe da wani irin gigitaccen kuka kamar wacca za a yanka.

Ammi ce ta juyo ta zuba mata idanu cikin abin da baifi sakan uku ba ta janye kallon da ta ke mata.

Rungumota ta yi "Shi kenan yanzu dai ki yi mini shiru, abu na biyu kuma ki yi min alƙawarin kin daina yarinta da rashin hankali, ba kuma za ki sake tsokanar kowa ba agidan nan"

Da sauri ta ce,

  "Wallahi Allah Ammi na daina bazan kuma ba na tuba ki yafeni"

"Ya isa haka, ta shi kije ki watsa ruwa kizo ki yi sallah, ki kwanta ki yi bacci kar na ganki a waje."

 "To Ammi ta Allah ya tsundu maki a aljanna, ina sanki Ammi"

Ta kai mata sumbata a saman goshinta, kafin ta shige bayin tana ɗingisa ƙafarta.

Ammi girgiza kai kawai ta yi tana mai kuma nemawa ɗiyar tata shiriya wajen ubangijinmu.


 ______________

  MAMMAN____________


Tunda ya shiga ɗakinsa zuciyarsa ke masa wata irin suka ,ji yake dama ya sa ni ya kakkaryata sanda ya je ajjiyeta ɗakin Ammin.

Hannunsa ya doka cikin ɗayan ya fuzar da hucin iska daga bakinsa mai zafi.

" Lallai ba shakka sai na koya mata hankali "

Ya ce a hankali.

Bayi ya wuce ya sakarmawa kansa shower nan ya fara jin wani sanyi na ratsashi kasancewar ruwan sanyi ya sa ki.

Ko da ya fito canza kaya kawai ya yi ya fice daga ɗakin, parking space ya wuce ya shige cikin motarsa ya tada ta.

Baba na zaune ya hangi fitowarsa da kuma shigarsa motar hakan yasa shi miƙewa ya wangale masa gate ɗin gidan.

A 360 ya bar harabar gidan na su.

 "An taɓo ran maza"

Baba ya ce, yana mai mayar da gate ɗin ya rufe.

Komawa ya yi mazauninsa ya kunna redionsa ya ci gaba da sauraran shirin da akeyi a cikinta.


_____________

  RAMLAT___________


Ko da ta fito ba ta iske Ammi zaune cikin ɗakin ba, hankan ya ba ta damar ficewa daga ɗakin cikin sanɗa.

Daƙyar kamar tashowar mayya na san samu abin da takeson lasa ta ke hayewa saman duk da zuciyarta cike take fal da tsoro.

A hankali ta tura ƙofar ɗakin na su, ba kowa aciki, cikin sanɗa ta ƙarasa ciki daidai inda sif nata kenan ta tsaya tana mai buɗe murfin ta.

Ƙarar buɗe ƙoface ya sanya ta juyowa da sauri.

Saudat ce ta fito daga bayi jin motsin mutum cikin ɗakin.

"Ke kuma lafiya kika shigowa mutane ba sallama sai kace wata ɓarauniya"

Ɗan raurau ta yi kamar ba ita ce keyin tsokana ba ta ce,

 "Dan Allah yaya Saudat ki yi a hankali kar wani ya jiyo mu, kaya na zo ɗauka fa za ki wani cemin ɓarauniya"

 Duk zancan da ta keyi tana yini cikin raɗa-raɗa.

Fashewa ta yi da dariya kafin ta ce,

"Yo to Allah na tuba ni me ruwana ,infact ma me ya haɗani da wani da har zai hanani ɗaga sauti, hmmm yarinya man kaza sanda za ki yi iskancin na ki me ya sa ba ki ji faɗuwar gaba ba sai yanzu za ki wani tsorata, tsoran banza kenan ma, ai wallahi ki yi kuka da kanki dan na san muddin kika sake ki kayi ido biyu da shi hmmm yasin karya ki zai yi kuma babu wani tsoro a tattare da shi,to Allah na tuba dame ki kai kama inba da sigar ɓarayin ba kin shigowa mutane ɗaki ba sallama wanann ai ɗabi'ar ɓarayi ce"

Sosai Ramlat ta tsorata da jin kalaman Saudat, cikin san dakewa da san nuna ita ɗin jaruma ce ta ce,

"Amma dai ai bai isa ya kashe ni ba ko, kuma Ammi nasan ma ba za ta taɓa bari ya yi min haka ba, kuma wallahi ni ba tsoransa na ke ji ba, yazo ɗin ma na"

 Ta ƙarashe tana murguɗa bakinta.

"Ohh! yarinya haka kika ce, to albishirinki da man da zai fita sai da ya sa ni wani aiki, ya ce na naɗemasa sautin muryarki cikin wata ƴar ƙaramar recorder ya ji wani iskancin kika kuma shiryawa ,bari ya dawo sai na kunna masa ya saurara wato ba kya tsoran sa ko hmmmmm!"

Jin hakan ya sanya Ramlat tsurewa take jikinta ya fara kakkarwa cikin salon san yiwa Saudat dabara ta ce,...