MATAR MAMMAN.

chapter eight

by @maikosai53

Page 15-16.


Bisimillahir rahmanir raheem.


Cikin san salon bagarar da Saudat ta ce,

 "Dan Allah da gaske ki ke ? Allah sai na gaya ki da Ammi"

Tuntsurewa Saudat ta yi da dariya haɗi da faɗin,

  "Yarinya ai duk wani iskancinki na dameshi in ba ki faɗa to ba ke ba ce ba, shashasha mai kama da ifiritiya"

Yamutsa fuska ta yi kafin daga bisa ta yi kamar za ta yi kuka.

"Dan girman Ubangijin da ya ara miki numfshi har ki ke komai ki yi haƙuri ki ceci marainiyar Allah ki mata rangwame"

Habawa mai Saudat za ta yi inba dariya ba,ta ke kuwa ta shiga ƙyalƙyalewa da dariya, harda riƙe ciki.

 "Au to yau kuma marainiya a ka koma to ikon Allah, da yaushe ki ka zama marainiyar dare ɗaya ko kuma safiya ɗaya ke ko rana ɗaya faɗi na ji?"

Kuka Ramlat ta fashe da shi, sunkuyawa ta yi ta riƙo ƙafafuwan Saudat bakomai ta ke hangowa ba illa kawai irin yayyanka tan da zai yi in ya ji abin da ta shuka.

 "Dan Allah Aunty Saudat ki yi min aikin gafara wallahil azeem bazan kuma ba kinji ma na rantse"

Saudat ta yi murmushi kafin ta ce,

 "Miƙe tsaye, zan haƙura zan goge amma da sharaɗi "

Da sauri ta miƙe tsayen kamar yadda yaya Saudat ɗin ta ce.

Ɗaga kai ta shiga yi kamar jemage yaga nama, 

 "Na ji na amince koma mene ne zanyi wallahi"

Saudat ta tafa hannu kafin ta ce,

 "To ikon Allah, tun ma baki san mene sharaɗin ba well"

 Ta yi rau-rau da idanuwanta ta ce,

"Ni dai na amince koma mene kawai ki faɗa."

 Saudat ta ce,

   "Alright sharaɗina guda ɗaya ne zuwa biyu, zan haƙura da kunna mai recording ɗin amma sai kin amince za ki gyara ɗakin nan na kwana biyu, sannan za ki wankemin kaya na na kwana uku, in kin amince to in kuma saɓanin haka ki ka ɗauka to shi kenan da zarar ya shigo sai na ba shi ya saurara"

Ramlat ta yi saƙaƙe tana nazari akan abin da saudat ta ce, wata zuciyar na ba ta shawarar ta bijirewa sharaɗin nata, wata kuma na ce mata ta amince kawai shi ne mafita.

 "Ya ya dai, ko ba za ki iya ba ne??"

 Saudat ta ce cike da gadara.

"Uhmmm! zan yi amma dan Allah ki sassauta min, kinga dai ni na farko ban iya wanki ba kuma ban ma iya gyaran ɗaki ba, ban san ta ina zan fara ba dan Allah"

Saudat ta aza hannunta ɗaya kan kafaɗar Ramlat kana ta ce,

 "Ai ni ma ba na ce wai kin iya ba ne so na ke ki koya daga yanzu, ko haka ki keso akai ki ɗakin MAMMAN ɗin ba ki iya komai ba"

 "Shi kenan na amince tunda ba za ki tausayawa marainiyar Allah ba"

  Ramlat ta ce kamar za ta fashe da kuka.

"Yawwa good girl, sai kuma sharaɗi na ƙarshe shi ne, ko da wasa in Ammi ta ji wallahi sai na saɓamiki kamanni kuma sai na kunna masa ya ji"

Saudat ta ce tana mai jan kunnen Ramlat ɗaya.

Cikin sauri Ramlat ta ce,

  "Ni wallahi na amince da koma mene ne in dai har za ki goge"

"Zan goge amma sai kin kammala aikin idan ki ka yi kuskure ɗaya aiki ya ruguje"

 Saudat ta faɗa.

Ramlat ta gyaɗa kai .

 "Na ji na yarda"

Ta fara ƙoƙarin raɓawa za ta fice daga ɗakin.

Cikin sauri Saudat ta ce,

 "Ina kuma za ki , ai daga yanzu aikin zai fara dawo"

Wiƙi-wiƙi ta shiga yi da idanuwanta haɗa hannayenta ta shiga yi tare da ƙoƙarin furta,

 "Dan Allah ki yi min rai wallahi gaba ɗaya gaɓoɓina ciwo suke yi min ,ki ba ri zuwa gobe dan Allah"

Abinka da jini ɗaya sai ta ji tausayinta ya kamata .

 "Shi kenan je ki, amma ki tabbbatar aiki ya fara daga gobe"

"To Aunty Saudat na gode Allah yabar zumunci"

 Ramlat ta ce.

"Ah! ikon Allah yau kuma aunty na koma gaba ɗaya to kar dai a manta da matsayina na yaya,zumunci kuma ameen, za ki iya tafiya"

Kamar daman jira ta ke aba ta umarni ta fice da saurinta kamar za ta tashi sama.

Saudat kam zubewa ta yi kan gado tare da fashewa da wata iriyar dariya, 

 "Kai lallai yaro yaro ne, yaro man kaza"


  _____________

   RAMLAT_____________


Tana fita daga ɗakin ta tsaya daidai matattakalar tana mayar da numfshi tare da tsinewa yaya Saudat yafi ba adadi.

Sauka ta shiga yi a hankali tana gwaggwale idanuwa da nufin hangen wani ta ke yi.

Daidai ƙarshen matattakalar suka yi ido biyu da Aunty Rahma da ta fito daga ɗakinta hannunta ɗauke da plate da alama mai da shi kitchen za ta yi.

Kallonta Aunty Rahma ta yi tare da yatsina fuska ta yi gaba za ta wuce.

Da sauri Ramlat ta ida sakkowa ƙasan tabar kan matattakalar cikin ɗaga sauti tamkar ba a kusa da juna suke ba ta ce,

 "Aunty Rahma"

Aunty Rahma jin an ambaci sunanta ya sanya ta cakewa a wajen ba tare da ta motsa ba.

A haka Ramlat ta ƙaraso ta tarar da ita.

 "Aunty Rahma wai dan Allah da gaske yaya ya fita baya nan??"

Aunty Rahma ta kafeta da idanuwanta na wasu ƴan mintina kafin ta ɗauke kana ta ce,

 "Injiwa ya ce miki ya fita? Bari ki ji yana can yana shirya yadda zai karairayaki ne ba ke jurinki rashin arziƙi ba, karki manta yaya ba sa'anki ba ne ba, kuma indan iskanci ne da fitsara ba wanda ya kaishi gwanancewa, ni wallahi har na fara tausaya miki sai na ji dama na yi miki kuka koda sau ɗaya ne"

Tsoro, fargaba da tararrabi tuni suka mamaye zuciyar Ramlat gaba ɗaya jikinta ya ɗau haramar fara kakkarwa.

Ta matso daf da Aunty Rahma ta sanya hannunta cikin nata kafin ta ce,

"Dan san da kike yiwa Annabi Aunty Rahma ki ceci ne kada ki bari yaya ya taɓa ni ko da sau ɗaya ne, wallahi na tuba na daina bazan kuma ba"

Aunty Rahma ta janye hannunta cikin na Ramlat daga bisa ni ta ce,

 "Wah! ni rufa ni ki saya sanda za ki yi rashin kirkin na ki kin tambaye ni ne, ko so ki ke ni ya huce a kaina, tun wuri ki nemi mafakar ɓuya dan gamuwar ku baza taa yi da kyau ba"


Gaba ɗaya idanuwanta sun kawo ruwa sun cika tab ƙiris ya rage ta fashe da kuka, ganin hakan ya sanya Aunty Rahma faɗin,

 "Barka da fitowa yaya"

Habawa ƙafa me na ci ban baki jin hakan ya sanya Ramlat kwasa a guje tamkar babu wani ciwo a ƙafarta ta yi ɗakin Ammi.

Ita kam Aunty Rahma ƙayalƙyalewa ta shiga yi da dariya kafin ta wuce kitchen abinta.