chapter nine
by @maikosai53
Page 17-18
Bisimillahir rahmanir raheem.
Ramlat na shiga ɗakin Ammi ta fashe da wani matsanancin kuka dan ƙafar ta ce garin gudun neman tsira ta buge da ƙofar shiga ɗakin ba ta yi tsammani ba.
Durƙushewa ta yi a wajen tana mai ƙara ƙarfin kukan nata tamkar wacca ake zarewa rai .
Ammi da tun ɗazu da ta shigo ɗakin ta tarar ba tanan ya sata wucewa ainihin ɗakin da take ɗan hutawa kasancewar cikin ɗakin ɗakuna uku ne, ɗaya mai ɗauke da bed ,ɗaya kuma kawai kujerune da shirginta, ɗayan kuma shi ne wanda takan huta aciki idan buƙatuwar hakan ta taso.
Firgigit ta farka jin amon muryar kukan Ramlat a kunnenta ,miƙewa ta yi ta fito daga ɗakin zuwa inda ta jiyo sautin kukan na ta.
Durƙushe ta iske ta sai faman kirari take "za ta mutu acece ta"
Ammi ce ta ƙaraso inda ta ke tare da dafata da hannu ɗaya kana ta ce,
"Ke kuma lafiyar ki ƙalau me ya faru Ramlat??"
Ramlat jin muryar Ammi kusa da ita yasata ƙara tunzura da kukan nata.
Ammi kam duk ta bi ta ruɗe matuƙa.
"Wai mene ne Ramlat ,me ya faru.??"
Ɗan tsagaitawa ta yi da kukan kafin ta ce,
"Ammi ƙafata wayyo zan mutu, ki ceceni dan Allah"
Ammi ta sanya hannu tare da jan ƙafar a hankali .
"Me ya faru da ƙafar me yasa meta??"
"Auch! wayyo Ammi da zafi ƙafata"
Ramlat ta ce, fuskar nan cike gwaranye da ruwan hawaye.
"Ammi wallahi inaga karyewa na yi, ita ce ma wallahi Ammi, shi kenan nasan na riga na zama gurguwa ko Ammi"
Duk da cewa Ammi na tausaya mata amma sai ta waske dan abin na Ramlat ya fara mata ciwo yanzu da ban haushi.
"Dalla rufemin ba ki, wayace ki fita daga ɗakin, ba sai sa nace kada ki kuskura ki fita ba shi ne saboda ke ba kijin magana kika sa ƙafa kika fita, sai yanzu da kika jiyowa kanki rauni za ki wani dami mutane, in na kuma jin bakinki a nan sai na hanɓareshi yasin"
Ammi ta faɗa a zafafe.
Maganar da Ramlat ke shirin yi ta haɗiye maƙwat sakamkon kallon da Ammi ta bita da shi.
Ammi kam miƙewa ta yi ta ƙarasa bedside ta ɗau wayarta ta shiga latsa kiran MAMMAN.
______________
MAMMAN__________
Mamman kam yana zaune cikin motarsa da ya faka gefen titi, bakomai ya ke ba illa kawai tunanin yadda zai saitawa Ramlat hankali.
Iskar bakinsa mai huci ya kuma furzarwa a karo na uku tare da dukan sitiyarin motar.
Daidai nan kiran Ammi ya shigo cikin wayarsa, har ya yi banza tamkar ba zai ɗaga ba sai kuma ya dubi kan screen ɗin wayar ganin sunan Ammi ne ya sashin sauri ɗagawa tare da mannata a kunnensa.
"Kai kana ina ne kai maza ka dawo yanzu ina son ganinka"
Ammi ta faɗa bayan ta ida sallamarta.
Ko jiran amsar sa ba ta yi ba ta katse kiran nasa.
Mamman kam mamaki da ta'ajibin kiran da Ammin nasa ta yi masa na gaggawa haka,
"Allah yasa lafiya dai"
Ya furta a hankali .
Ƙafafuwansa ya mayar da su cikin motar ,ya sanya hannunsa ya murza mukullin da ke jikin motar ya soma janta a hankali zuwa gida kamar yadda Ammi ta buƙata.
_______________
RAMLAT_____________
Ammi kam tana kammala wayar ta koma kan Ramlat da har yanzu ke durƙushe ƙasa idanuwan nan nata sai ci gaba da ambaliyar ruwan hawaye suke.
"Ta shi ki sauya rigar jikin ki maza."
Ammi ta ce.
Ramlat na san faɗawa Ammi cewar ba za ta iya ba amma babu hali, haka ta dake ta soma ƙoƙarin cire rigar da ke jikinta ba tare da ta miƙe ba.
Ganin haka yasa Ammi juya mata baya.
___________
MAMMAN_________
Ya daidaita parking ɗin motar tasa bayan Baba ya buɗe masa ya shigo.
Kai tsaye ɗakin Ammi ya wuce ƙwaƙwalwarsa fal cike da tunanin me ya sa Ammi ke san ganinsa a yanzun?
Yana shiga ya iske Ramlat zaune fuskar nan shaɓe-shaɓe da hawaye wasuma har sun soma bushewa.
Kauda kansa ya yi tamkar baisan da zamanta a ɗakin ba.
Ammi da firowarta kenan daga ɗaya ɗakin, kallonsa ta yi kafin ta ce,
"Yaushe ka shigo?"
Ya ɗan riasinar da kansa kana ya ce,
"Yanzu na shigo Ammi"
"Ok ka ɗauki yarinyar nan ka kaimin ita asibiti ko wajen mai gyara a duba mini ƙafarta ina tunanin targaɗe ta yi"
Ammi ta ce da kakkausar murya.
Mamman da kansa ke sunkuye ya ɗago ya kalli Ammi kafin ya ce,
"Ammi wannan sukurkutacciyar ƴar ta ki fa bai zama lallai cewa targaɗan ba ne kawai gata da san jiki ne ya sa ............"
"Nifa ba cewa na yi ka tsaya kana min wasu surutai ba, in ba zaka ba sai ni naje ai Allah ya horemini ƙafafuwa"
Ammi ta ce.
"A'a Ammi me ya yi zafi kuma?, Allah ya huci zuciyarki"
Bai bari Ammi ta ba shi amsa ba ya kalli Ramlat da tun shigowarsa ta sunkuyar da kanta ƙasa ya ce,
"Tashi muje, ki sa meni a mota"
Ya sanya kai da nufin ficewa daga ɗakin.
"Dawo nan ka ɗauketa ai baza ta iya takawa ba"
Ammi ta ce.
Jiya yi wani ƙululun abu ya tokare masa maƙoshi saboda maganar da Ammi ta yi.
Cikin zuciyarsa ke ayyana masa
"Me ya sa Ammi kesan bayar da shi gaban wannan kuchakar yarinyar da ko ƙirgar danki ba ta kammala ba"
Ba yadda zai yi haka ya juyo ya sungumeta a kafaɗar sa ya yi waje da ita.dan shi kam bazai iya musawa umarnin Ammi ba.
Yana ji tana ta batu akan,
"Ya kular mata da yarinya, kada ya kuma ji mata wa ni raunin amma ya yi shiru tamakr bai ji ba.