MATAR MAMMAN.

chapter ten

by @maikosai53

Page 19-20.


Bisimillahir rahmanir raheem.


Suna isa inda motarsa ya ke ya balle murfin motar da hannu ɗaya ya watsa ta ciki tamkar kayan wanki.

Har yanzu takaici yake cike da abin da Ammi ta masa akaro na biyu gaban wannan yarinyar.

Dan ba yadda zai yi ne ita ɗin mahaifiyarsa ce amma tabbas da ace wata ce daban to ba shakka da ya maƙureta numfashinta ya fita.

Zagayawa ya yi mazaunin driver ya shiga sai da ya kwashe wajen second biyar kafin ya ja motar ya bar harabar gidan.

Ammi kam tana hangen duk wani motsinsa har ya bar harabar gidan.

Ƙwafa ta yi kafin ta ce,

 "Za ka dawo ka iske ni ne ai"

Ta zuge labulan dake saƙale jikin tagar ta koma ta zauna.

 "Lallai lokaci ya yi da zan ɗauki shawararka Abiin yara".

Wayarta ta ɗauka ta shiga calender tare da duba ta kafin ta ajjiye gefe.

 "Da sauran lokaci dai, tabbas lokaci ya kusa kam"



________________

  MAMMAN AND RAMLAT____________


Tunda suka fita take wani ɗan marayan kuka kamar wacca aka cirewa wani abu  

Juyowa ya yi ya watsa mata wani kallo da ya sanya numfshinta kusan ɗaukewa.

"In kika kuskura na kuma jin bakinki wallahi sai na fasa shi ya yi jini a nan, sokowar banza kawai".

Ya faɗa a ƙufule.

Jin hakan ya sanya ta yin tsit, duk da irin raɗaɗin da ƙafarta keyi amma haka ta shiga ƙoƙarin shanyewa.


_____________

  ASIBITI_______________


Kai tsaye asibiti suka wuce ,da yake akwai wani friend na shi da suka yi school tare da shi to shi sai ya tafi fannin likitan ƙashi, shi kuma Mamman ya wuce ɓangaren likitan mata wato gani.

Office ɗinsa ya wuce kai tsaye da yake kowa ya sanshi ba tare da anmasa wani shamaki ba ya wuce.

Yana tura ƙofar ya iske shi zaune yana duba wani file da ke gabansa.

Miƙa masa hannu ya yi alamar musabaha bayan ya yi sallama cikin office ɗin .

Cike da murmushi shima ya miƙa masa hannun.

 "Ah! ikon Allah yau kai ne a ɓangaren na mu"

Haɗe fuska Mamman ya yi kafin ya ce,

 "Ni matsala ta da kai rashin nutsuwa wallahi,shekaru na yi ko kuma tafiya na yi ta dindin din?"

Dariya ya yi ɗayan kafin ya ce,

 "Zaɓi wanda ranka keso mutumina"

"Kaga Jawad ya isa haka sokwancin, wata bahamagiyar mara lafiya za ka duba min"

Mamman ya ce.

Jawad ya yi murmushi kana ya ce,

 "Alright, tana ina??

Sai a lokacin ma da Jawad yake tambayarsa ya tuna ya barta amota.

Miƙa masa key ɗin motar ya yi kana ya ce,

 "Plz sa wasu ƴan uwan ta mata su shigo da ita".

Jawad kam sanin halin Mamman ya sa bai wani furta kanzil ba illa kawai amsar key ɗin da ya yi yana me fita daga office ɗin.

Wasu Nurse ya yi wa magana tare da basu key ɗin akan suje su shigo da ita .

Ko da suka iske motar Ramlat har ta gaji da kukan da takeyi na azabar ƙafar ta soma bacci.

Jin motsin mutum wajenta yasa ta buɗe idabuwanta.

Ganinsu ya sanya ta gyara zaman ta cikin motar.

 "Zamu wuce da ke ne ciki, bisa umarnin likita"

"Uhmmm wata kam ma ba zai iya ɗaukar ta ba shi ne zai sanya wasu kinkimarta"

 Ta ce cikin zuciyarta.

Zuro ƙafar ta yi a hankali tare da ƙoƙarin miƙewa.

  Da sauri ta koma ta zauna dabas saboda zugin da ƙafar ta mata.

"Bazan iya tafiya ba wallahi"

 Ta ce a hankali .

Ɗaya daga cikin su ce ta ce,

 "Kinga kije ki turo gado sai mu ɗauketa anan, gaskiya naga ƙafar ta kunbura sosai"

"Ok"

Ɗayar ta ce tana mai komawa ciki.

Itakam ɗayar sai faman sannu take jerawa Ramlat.

A kan gadan marasa lafiya suka miƙa Ramlat izuwa ɗakin duba marasa lafiyar.

Ɗaya daga cikinsu ce ta wuce ta sanar da Dr Jawad sun kaita.

Jin hakan ya sanya shi miƙewa zuwa ɗakin, duba ta ya fara ƙoƙarin yi, take ya gano karaya ce ba targaɗe ba.

Nan ya shiga ƙoƙarin gyara mata, Ramlat kuwa tun tana daurewa har ta fara fidda kukan azaba.

Cikin sa'a uku aka kammala komai, ɗakin hutu a ka wuce da ita, dan tana buƙatar hutawa.

Ko da ya koma office na shi bai tarar da Mamman ba ciki, shima hakan bai wani ɗaga masa hankali ba dan ya jima da sabawa da kowane irin hali na MAMMAN.


_______________

 AMMI____________

Sai faman safa da marwa take yi a tsakiyar falon cikin gidan, hankalinta duk a tashe na rashin sanin halin da Ramlat ke ciki.

Ta kira Mamman yafi sau nawa amma wayarshi ta ƙi shiga not reacherble.

Aunty Rahma ce ta fito daga ɗakinta ,jikinta sanye da kayan asibiti sa alama fita za ta yi.

Ƙarasowa ta yi inda Ammi ta ke kafin ta ce,

 "Ammi lafiya kuwa, me ke faruwa??"

Duka ta jero mata tambayar lokaci ɗaya.

Ammi ta ɗanja guntun tsaki kafin ta ce,

 "Yo inafa lafiya? tun ɗazu suka fita basu dawo ba"

Aunty Rahma da ta gaza gane zancan Ammi ta ce,

 "Ammi su waye basu dawo ba, Abii ne ya ce zai dawo?"

Ammi ta tsaida tafiyar da take ta kalli Aunty Rahma kafin ta ce,

 "Ramlat ce ba lafiya, nasa Yayanku ya kaita asibiti har yanzu basu dawo ba, na kira wayarshi taƙi tafiya, hankalina sam ya gaza kwanciya"

Aunty Rahma ta bayyana mamakin ta a fili jin cewa wai Ramlat ce ba lafiya.

 "To da yaushe kuma ta soma rashin lafiyar, ko kuma ta soma rashin lafiyar ƙarya ne dan kare kai"

 Ta tambaye kanta da kanta.

Ta kalli Ammi kana ta ce,

 "To Ammi bari na kira shi muji ko ni zan same shi"

"Yawwa maza ki kira mini shi"

 Ammi ta ce, tana mai zaman kan kujera.

Aunty Rahma ta sanya hannunta cikin jaka ta zaro wayarta ta shiga latsa kiran yayan nasu.

Cikin hukuncin Allah wayar ta shiga.

Har ta katse ba a ɗaga ba, sai da ta kuma kira tana kan hanyar yankewa sannan aka ɗaga.

"Yawwa ga shima an ɗaga Ammi"

 Aunty Rahma ta faɗa tana mai miƙawa Ammi wayar.

Amsa ta yi tare da karawa a kunne, cikin faɗa-faɗa ta ce,

"Me ake ciki ne baka sanar da ni ba?"

Daga ɗaya ɓangaren wanda dr.Jawad ne ya ɗaga ya ce,

 "Ammi an yini lafiya, baya nan ya bar wayar a office ɗina"

Ammi ta ɗan rage fushin na ta kana ta ce,

 " Lafiya lau Jawad, ina ƴata, wani hali ta ke ciki?"

Jawad ya ɗan muskuta zaman nasa kan kujerar da ya ke zaune ya ce,

 "Tana lafiya lau Ammi, sai dai zamu riƙeta har na tsawan sati guda saboda ta sami karaya ne a ƙafar tata yanzu dai an ɗorata kuma yanzu haka ma tana ɗakin hutu"

"Me kake cewa ƴar tawa ce ta karye garin yaya? To gani nan zuwa"

 Ammi ta ce tana katse kiran na sa.

Jawad kam da yasan yadda take ririta ƴar tata hakan yasa kawai ya yi murmushi.

Ammi kam kallon Aunty Rahma ta yi kana ta ce,

 "Maza muje ki ajjiyeni a asibitin yayan ku"

Aunty Rahma ta nisa kana ta ce,

 "Ammi lafiya kuwa, me yake faruwa?"

"Bari na ɗakko mayafi na, koma mene ne in munje kyaji"

Ammi ta ce tana mai wuce ɗakin ta kai tsaye.