MATAR MAMMAN.

Eleven

by @maikosai53

Page 21-22


Bisimillahir rahmanir raheem.


Ammi ta wuce ɗakinta kai tsaye ba tare da ta jira ta cewar Aunty Rahma ba.

Aunty Rahma kuwa mamaki take ta yi akan maganar da Ammi ta ce.

Tana nan tsaye Ammi ta fito .

 "Mu je ko"

Ammi ta ce.

Gaba Aunty Rahma ta yi, cikin zuciyar tana daɗa sakaya mata me yasa mi Ramlat ɗin .

Kai tsaye wajen motarta ta wuce tare da buɗewa Ammi gidan baya, Ammi ta shiga itama ta shiga taja motar.

Daidai wajen Baba suka tsaya Ammi ta ce,

 "Baba ka kula da gidan dan ba kowa sai Saudat a ciki zanje asibiti ne autata ba lafiya"

Baba ya ce,

"To Hajiya Allah ya kiyaye hanya, ya ba ta lafiya"

Da "ameen" su Ammi suka amsa.

Shi kam Baba shima mamaki yake yi akan rashin lafiyar da aka ce Ramlat tana yi, yini ɗaya me ya faru da ita?.


_________

 ASIBITI_________

Sai bayan minti goma sha biyar Mamman ya dawo office ɗin nasa, ko da ya shigo bai wani tsaya tambayar ba'asin mene ne matsalarta ba illa kawai faɗin da ya yi,

 "Ina take ka sallameta mu wuce"

Dr Jawad yaja tsaki kafin ya ce,

"Ammi ta kirawo kuma na amsa na sanar da ita halin da ake ciki, saboda mun bawa Ramlat gado dan tana buƙatar hutu domin kuwa karaya ce a ƙafarta "

Mamman ya yatsina fuska tare da faɗin,

 "And so what, malam ka sallameta mu wuce ni ina da abin yi"

Jawad ya maka masa harara kana ya ce,

 "Lallai ba shakka yau na kuma tabbatarwa baka da imani, to sai dai ka fasa yin koma mene ne, kuma na tabba ta Ammi tana nan tafe"

Mammn ya ja dogon tsaki .

 "Shashashan banza kawai, kai me ya sa baka da aikin yi ne sai munafurci "

Jawad ya ce

 "Oho! kuma mene ne da na faɗa ka iya tafiya"

Bai tanka masa ba yaja kujera ya zauna tare da zaro wayarsa ya soma lallatsata.

Shima Jawad ganin haka ya sa ya ci gaba da abin da ya ke yi.


___________

  AZARE__________


Ni'imar da Allah ke sanyawa a tsakanin al'ummarsa ita kaɗai ta ishe kowa hisabi.

Sassanyar iskar da ke kaɗawa haɗi da sanyin da ke busowa ya sanya ta tattara komatsanta zuwa ɗakin nata.

Baba Hadiza kenan tsohowa mai ran ƙarfe ,dashen Allah .

 "Ahmad Ahmad wai ina ka shiga ne?"

Ta soma ƙwalawa mai sunan kira tare da tambayarsa.

 Jin ƴar tsohowar ta sa na antayo masa da kiran gaggawa ya sanya shi tsayar da abin da ya ke yi, cikin hanzari ya ƙarasa ɗakin da ya jiyo sautin muryarta yana faɗin,

 "Ga ni a nan kakale"

Daƙuwa ta jefo masa da yatsu biyar game da faɗin,

 "Ka ci gidan ku na ce, amshi wannan"

Dariya ya yi ƙasa-ƙasa kafin ya ce,

 "Wai dan na ce kakale, to da kuma cewa na yi kakus fa?"

"Lallai ya yi maka kyau ka ce tsohowa mai ragargazazzan ƙashi wanda ya kusa daina aiki ma man, ja'irin banza, ni zoka shimfiɗa min wannan bargon"

Ahmad ya matso inda take nuna masa bargon yana ta dariyarsa.

"Wato ba za ka tsayar da wanann mahaukaciyar dariyar ta ka ba"

 Kakale ta ce.

Ahmad ya ɗan getta gefen ta yana mai ƙoƙarin shimfiɗa bargon ya ce,

 "Na daina ta Mamman bada kan ki asare, kije gida ki ce ya faɗi"

"Zan damƙeka ne ja'iri mai gira ɗaya a goshi"

Ƙyalƙyalewa ya yi sa dariya kafin ya ce,

 "Au kakale girar ma agoshi ta ke?"

"Ban sa ni ba ɗan banza zo ka fice min daga ɗaki bana so"

 Kakale ta ce cikin faɗa .

"Afuwa Hajjaju na daina"

Nan ya shiga ƙoƙarin saita mata bargon dan ya yi daidai a kan gadon.

"Wai Kakus yaushe su yaya zasu zo ne?, ni kam na gaji da rashin ganinsu a cikin idanuwa na"

Kakale ta damƙa masa daƙuwa da yatsu goma ta ce,

 "Kiransu za ka yi ka tuhumesu ka ji"

ya yi ƴar dariya kafin ya ce, 

 "To Kakus wane laifi suka yi mini da zan ce zan tuhumesu kuma ni ɗan nan?"

"Zan ci mutuncinka wallahi Ahmadudu tam ,zo ka fice min daga ɗaki maza"

Ta faɗa fuskarta a haɗe tana mai saita masa hanyar waje .

Ficewa ya yi yana dariya ƙasa-ƙasa dan yasan ta shaƙa iya matuƙa.


____________

  ASIBITI____________

Sanda su Ammi suka isa Ramlat ta farka daga baccin hutun da take yi, Ammi na shiga ta ƙarasa inda take tare da rankafo kanta saman kafaɗarta.

Ramlat kuwa ƙafar nan saƙale jikin ƙarfe wacca aka mata aikin.

Ammi ta shafa kanta tare da faɗin,

 "Sannu ƴa ta, ya ƙafar sannu kinji"

Ramlat kuwa shagwaɓe fuska ta yi tamkar za ta yi kuka cikin salon taɓara ta ce,

 "Ammi ina jin tamkar mutuwa zanyi, har fa fitsari na yi a wando, shi kenan na zama gurguwa mara ƙafa ko Ammi na shiga uku"

"Kul kar na kuma ji, waya ce mi ki haka ? za ki tashi ki yi tafiya fiye da mu kin ji ko"

 Ammi ta ce.

"Da gaske Ammi, da gaske ki ke zan yi tafiya da ƙafufuna?"

Ramlat ta tambaye Ammi cike da zumuɗi.

Ɗaga mata kai Ammi ta yi kan ta ce,

 "Ƙwarai ma kuwa sosai ma, yanzu dai ki kwantar da hankalinki ki nutsu ki tsaya ki sami lafiya kinji ko"

Ramlat ta gyaɗa kanta alamar "to"

"Yawwa ko kefa, yanzu me ki keso me ki ke da buƙata?"

Ammi ta tambayeta.

"Uhhmmm! uhhmmm! Ammi ni farfeson kaza na ke so"

Ramlat ta ce tana lashe ƙasan laɓɓanta tamkar tsohowar mayyar da ta jima tana neman abin hari sai yanzu ta samu.

"Iya shi kawai ba wani abun?"

Ammi ta tambayeta.

Ɗaga kai ta yi sama alamar ehh.

Aunty Rahma da tun shigowarsu ba ta ce komai ba saboda tattaunawar da suke yi da Ammi, jin abin da Ramlat ɗin ta faɗa ya sanya ta matsowa daf da Ammi ta ce,

 "Amma Ammi inaga yanzu a fara jira likita ya duba ta tukun, kinsan suma fa masu rauni a ƙafa ba komai suke ci ba"

Ramlat da tunda Aunty Rahma ta soma magana ta fahimci inda ta dosa dan kar ace ta je ta mata yasata marairaice fuska ta ce,............