MATAR MAMMAN.

Twelve

by @maikosai53

Page 23-24


Bisimillahir rahmanir raheem.


"Wallahi Ammi ana ci dan fa kawai kar ki ce ta je tayo mini ne shiyasa fa ta ke san waskewa"

Aunty Rahma ta galla mata harara kafin ta ce,

 "Dalla rufemin baki , kina nufin ni ban san aiki na ba ne kome?"

"Ni dai dan Allah Ammi ayo mini farfeson kaji, yinwa nake ji plz"

 Ramlat ta ce cikin shagwaɓe fuska.

Ammi ta kalli Aunty Rahma kafin ta ce,

 "Ma za ki kirawo mini Saudat yanzu a waya ki ce tayo mata ta kawo, ke kuma ki wuce na ki wajen."

Aunty Rahma ta ce,

 "To Ammi"

Ta soma dailing lambar Saudat, bugu biyu ta ɗaga ,nan ta shiga isar mata da saƙon Ammi.

Saudat da ke kwance saman gado tana karanta wani littafi ta ajjiye shi gefe ta turo baki tana magana ƙasa-ƙasa.

"Lallai yarinyar nan wata kam ni ta raina ma za ta ce a bani nayo mata ko? tabbas zan yi maganinki wallahi"

Ta faɗa tana mai sakkowa ƙasa dan aikata abin da Ammi ta ce mata.

Ɓangaren su Ammi kuma cewa ta yi ba za ta koma gida ba har sai taga abin da ya turewa buzu naɗi, Aunty Rahma kam sallama ta musu ta wuce nata aikin dan har an soma kiranta a waya.


________

 OFFICE ƊIN DR JAWAD_________

Mamman zaune ya na mai ci gaba da latsa wayar ta sa tamkar babu shi a cikin office ɗin.

Jawad ya miƙe tare da faɗin,

 "Bari na je ɗakin na dubo ta ko"

Mamman bai tanka masa ba, shi kam da yasan ma ba amsa masa zai ba ya sanya shi ficewa daga office ɗin.


________

 WAIWAYE__________

Malam Muhammad Nuradden Mamman shi ne cikakken sunan Malamin da ya yi fice a cikin garin Azaren, shi ne malamin tsangayar tasu.

Mutum ne mai dattako, ƙima da sanin ya kamata ,kyautatawa ga uwa uba ilimin Addini har da na boko.

Wannan malantakar ta shi shi ma ya gaje ta ne wajen mahaifinsa Nuradden inda shi ma ya gada daga wajen mahaifinsa Muhammad Mamman.

Malam Muhammad wanda shi ma suke ce masa MAMMAN kasancewar sunan kakan nasa ya ci, yana da shekaru 65 kuma ɗan asalin garin Azare ne haifaffan nan ne, yana da mata biyu Maryam da Hindatu.

Inda Maryam ta ke uwar gida yaranta biyu Aisha(Humaira) da Yusif.

yayin da Hindatu ke da yara mata biyu Asma'u da Zainab.

Waɗannan su ne yaran malam Mamman kuma gida ne mai cike da tsafta babu dattin ƙazantar kishi ko kaɗan cikinsa.

Malam Mamman ya ta so cikin san ɗora yaransa kan abin da yake da shi na ilimi musamman YUSIF da ya kasance namiji cikin su kuma yakeso ya gaje shi.

Alhmadulillah kamar yadda ya ke so ɗin kuwa hakan ce take faruwa domin kuwa Allah ya bawa Yusif fikira da basira duk wani karatu da za ayi masa zai iya ɗauke shi a ƙwaƙwalwarsa ko da abun yana da nauyi .

Ganin haka ya sanya malam Mamman zage damtse wajen ganin ya horar da shi akan abubuwa da dama na amfanin kai da rayuwa.

Cikin hukuncin Allah Malam Mamman na da shekaru 72 ya aurar da yaransa mata kaf ɗin su, yayinbda shi kuma Yusif yaja ragamar karatun malam ɗin.

Sannu a hankali komai yake tafiya daidai fiye da zatan malam Mamman ,sosai yake jin daɗin hakan.

Yusif na da shekara 42 hankalin malam ya fi karkata akan lallai cewa yaga ya yi aure tunda ya ɗakko hanyar manyan taka shima, duk da cewa shi Yusif ɗin ya ce,

 "Ai aure nufi ne na Allah, kuma shi baya damuwa da rashin yin auren na sa, dan kuwa har yanzu bai ga matar aure ba"

Duk da wannan furucin nasa malam Mamman kam tunzurashi akan lallai sai ya samo matar aure ko kuma ya masa auren haɗi da koma wacece.

Shi dai Yusif ba shi da wani zaɓi, dan acewarsa kam,

"Har yanzu bai hangi matar auren sa ba"

Wasa-wasa tun abin bai ɗagawa malam Mamman hankali har ya soma damunsa, dan yau ga shi Yusif na da shekara 46 amma yaƙi mayar da hankali wajen yin aure .

Wannan ya sanya malam yanke hukuncin haɗa shi aure da ɗiyar Amininsa.

Hakan kuwa akayi inda aka ɗaurawa Yusif aure da Khadijatul Munawwara ƴar wajen aminin malam, yarinya mai hankali da nutsuwa.

Zu kuga murna wajen malam da farin ciki cewar ɗansa ya yi aure shi ma.

Kowa na cikin gidan yana murna da hakan hatta shi kansa angon wanda acewarsa

"Ya rasa farin cikin mene ne shima".

Nan Khadija ta tare a gidan Yusif, zama suke cikin so da ƙauna wanda suka samar da shi ta hanyar auren.

Cikin ikon Allah watan su huɗu da auren Khadija ta sami juna biyu na tsawan sati biyu, zo kuga murna da farin ciki wajensu.

A wannan lokacin ne kuma mijin Aisha ƙanwar sa yasamu ci gaba daman ma'aikaci ne yana Abuja to yanzu an dawo da shi Kano cikin gari wannan yasa ya ce

 "Zai ɗakko matarsa su dawo nan da zama"

An musu murna sai dai duk wanda ya ji cewar za su tashi sai su ji babu daɗi, a lokacin kuma tana da cikin wata bakwai da sati uku, bayan yaye Rahma da ta yi mai shekara ɗaya da rabi wand a yanzu yaranta biyu Muhammad Mamman da kuma Rahma.

Haka suka tattara komatsan su suka dawo cikin garin kano da zama,babu wanda baizo yaga gidan na su ba masha Allah.

Khadija kuwa ta so zuwa ganin gidan Allah bai nufa ba kasancewar fama da laulayin da takeyi wannan yasa kowa ya ce,

 "Ta zauna"

in ta sami lafiya ta je, ba yadda ta so haka ta haƙura.

Da daɗi da babu daɗi ta ci gaba da rainon cikinta har Allah yasa ya shiga wata ɗaya cif, sai kuma Allah yasa ta ɗan sami sauƙin laulayin da takeyi akai-akai.

Su Aisha kuma ƙanwar Yusif sanda suka koma makaranta aka samawa Mamman suka sanya shi, da yake yaran yana da kaifun ƙwaƙwalwa har ya zarce kowa ma na ajin da ake san sanya shi hakan yasa sai aka sanya shi a primary four wannan yasa mahaifinsa jin daɗi da alfahari da shi.

Itama nan ta ci gaba da rainon cikinta wanda yanzu yake da wata takwas da sati biyu.