MATAR MAMMAN.

Thirteen

by @maikosai53

Page 25-26


Bisimillahir rahmanir raheem.


Cikin hukuncin Allah cikin Munawwara ya cika wata biyar cif ,duk wani lokacin ya kan canza mata ya nayi na rashin jin daɗi.

Yayin da Mamman ke ta faman shan karatun sa a makarantar da aka sanya shi, ƙwazansa ya sa malaman ke matuƙar ji da shi duk da ba wani daɗewa ya yi a makarantar ba.

Mahaifinsa kuwa wanda suke kira da ABII Allah ya ci gaba da hore masa hanyoyin arziƙi fiye da da.

Malam Mamman tsufa yana ta tahowa, a yanzu kam baya fita waje karatu ba wai jikin ne ba a'a Yusif ya karɓe masa komai da komai.

Rayuwa suke yi yau da daɗi gobe babu, yau cikin farin ciki gobe saɓanin hakan, a haka har cikin Munawwara ya cika wata bakwai da sati ɗaya.

A lokacin ne kuma ya fara mata wani irin laulayi kai ka ce haihuwar za ta yi.

Ganin ba sarki sai Allah ya sanya Abii sawa a kaita asibiti.

A she ɗan ne ya juye kuma cibiya tananaɗe shi, to sai an mata aiki dan cetan ran sa.

Haka Abii ya biya kuɗaɗen da za a mata duk da cewa suma su malam ɗin bawai rasa kuɗin suka yi ba.

A lokacin da aka kammala aikin wanda ya sami nasarat ciro santaleliyar yarinyar sai aka sami saɓanin hakan daga wajen ita mahaifiyarta ta, dan alokacin ta soma fitar da numfashi mai sarƙewa.

Nan hankulansu ya tashi sosai duk da irin ƙoƙarin da likitocin ke yi amma Allah baisa Khadija za ta rayuwa, ko daidai da ganin yarinyar ba ta yi ba Allah ya amshi kayarsa.

Mutuwa kenan mai raba ɗa da mahaifa, mai raba masoyi da masoyi wannan mutuwa tata ya sanya Yusif cikin kaɗuwa sosai, gaba ɗaya ya zama so silent.

Bayan sadakar bakwai ne Aisha wacca su ke kira da Ammi ta ce aba ta yarinyar suka kuma raɗa mata suna Ramlat.

Badan ya so ba dan ya nasan jin ɗumin ƴarsa kusa da shi amma haka ya ɗauki ƴar ya ba ta koba komai ya san za ta kula masa da yarinyarsa.

Malam Mamman da a yanzu bai da lafiya sai ya zamana mutuwar ta matuƙar gigi ta shi, dan yana ƙaunar Khadija ya na jinta tamkar ƴar sa.

Haka ɓangaren Yusif shima dan kuwa jinya ya ke matuƙa.

Lokacin da Ammi ta amshi Ramlat Saudat na da wata shida a duniya,haka ta zo ta haɗasu ta cigaba da rainon yaran nata.

Ramlat na da wayo sosai dan lokacin da ta isa wata uku ba ta ma fara ƙoƙarin rarrafe ba sai ma miƙewa da ta ke yi da ƙafafuwanta.

Mamman kam a yanzu ya sami promotion dan yana aji ɗaya a secondary lokacin da ƴan aji uku za su zana exam shugaban makarantar ya bawa Abii shawara akan ya barshi ya yi jarrabawar tunda yaran yana da fahimta kuma yana da ƙwaƙwalwa.


__________

 AZARE____________

Rashin lafiyar malam ta fara gigita su dan yanzu ta kai ba ya iya yin wasu abubuwan da kan sa, duk an tabba tar musu da cewar ciwon ƙoda ne yana buƙatar hutu kuma zai iya wuya ya kai wasu shekaru dan duka ƙodar ta sa sun lalace yanzu dashe za ayi masa.

Yusif shi ya bada ta sa inda za ayi aikin nan da kwana bakwai.

Cikin ikon Allah mai hikima da buwaya, kuma mai yadda ya so sai a ka waye gari Allah ya amshi ran malam ashe dai ba sai an masa ma aikin ba.

Wannan mutuwar ta gigita ahlin gidan matuƙa, wannan sukan su matan sai da suka kwanta rashin lafiya.

Ranar sadakar ukun sa suka kuma ta shi da wani rikirjitacceb al'amari inda suka kuma rasa wani sashe na gidan wato Mama Hindatu.

Haka wannan ahlin gida ya kasnce cikin alhini na rashin mutanen biyu da aka yi.

Haka rayuwa ta ci gaba da tafiya, yau cikin jarrabawa mai daɗi wani lokacin kuma saɓanin haka.

Bayan Shekara ɗaya da wata bakwai.

Abubuwa da dama sun faru ciki kuwa harda mutuwar Yusif, da ƙannen sa mace ɗaya ƴa ga Mama Hindatu wacca tabar yaro ɗaya mai suna Ahmad.

Gefe guda kuma wayan Ramlat ya kuma fitowa sosai 

hakan ya sa Abi itama ya sanya ta a makaranta.

Sai dai Ramlat ko kaɗan ba ta jin magana duk da ƙanƙancin shekarun na ta, tsokana kam ba a magana dan sai ta sa wanda ya girme ta ma kuka.

A haka harta ta ida Nursery ta shiga Primary, lokacin kuma Mamman ya ta fi SS three yayin da Aunty Rahma ke Jss three.

A yau su Mamman suka kammala secondary inda sakamako ya fito kuma ya sami kyakkyawan sakamako, take Abi ya sama mi shi karatu a fannin likitanci.

Haka abubuwa suka ci gaba da faruwa ,inda kusan duk sati biyu sai Abii ya ɗau ƴaran na sa ya kai su Azare dan ganin ahlin su.

Duk da a yanzu shima zaman na sa ya fara yin kaɗan, dan in aka yi sa'a akan turashi wata ƙasar kuma ya kan shafe wata ɗaya zuwa biyu kafin ya dawo.

Rayuwa mai kyau, tsaf, soyayya da ƙauna ahlin ke ta ginawa, arziƙi kam wajen Abi ba'a magana, dan yanzu shike ɗaukewa ahlinsa da na su Ammi komai, duk da cewa shi baida iyaye ma saɓanin Ammi da ta ke da ɗaya a raye wato mahaifiya.


BAYAN SHEKARA BAKWAI.


Mamman ya kammala karatunsa na likitanci, yayin da Rahma ta fara karatunta itama na fannin asibiti inda take karantar ɓangaren Haƙori.

Ramlat kuwa tun daga aji ɗaya na secondary aka cireta sakamakon yawan tsokanar da take da shi har ta fasawa wata yarinya kai, lokacin Ammi ta tsorata shi ne ta ce in ta kuma girma a mayar da ta sannan ta ƙara hankali may be kuma ta daina abubuwan da take yi.

Saudat kuwa na ajin ƙarshe na secondary na ta inda ya rage wata huɗu su yi canday.

Haka abubuwa suke ta tafiya yau ga shi satin Mamman uku da dawowar sa, nan Abii ya shirya musu tafiya Azare dan ganin kakar ta su da kuma ragowar ƴan uwa.

Sosai suke murna da hakan musamman ma Ramlat dan a cewarta "Yaushe raban ta da kakus ɗin ta"

Shiri suke yi sosai na musamman tun a na saura kwana biyu tafiyar Abii ya kammala komai ,duk wani abu da ya ke musu ya tattareshi ranar kawai su ke jira.

Ramlat kuwa murna ta ke akan za taje taga Azare da abin da ke cikinta, da kuma tada ƙiriniyar da ta jima tanasan tado ta.