Fourteen
by @maikosai53
Bisimllahir Rahmanir Raheem.
27-28
Ranar da suka isa Azare zo kuga farin ciki wajen ahlin na su.
Kowa murna ya ke yi da ganinsu. Musamman ma Ahmad da ya haɗu da abokiyar ƙiriniyar ta shi.
Tun a ranar Ramlat ta zame jiki ita da aminin na ta Ahmad suka antaya ta su sabgar.
Ko da sauran jama'ar suka ƙyalla ido suka ga ba tanan dariya kawai suka yi musamaan da su kaga har Ahmad ba ya nan sun san sun tafi ta su sabgar ne.
Kwanansu uku a garin, ranar Ramlat sun fita da Ahmad,kan hanyar su Ramlat ta jangwalo tsokanar da har saida aka biyosu har gida.
abin da ya faru shi ne;
Ramlat suna tafe suna hirarsu kamar yadda suka saba yi cike da shewa da annushuwa. Kamar daga sama Ramlat ta hangi wani bawan Allah tafe da ɗan jakinsa ya yo ice akai.
Matsawa ta yi daf da mutumin ta kalle shi kafin daga bisa ni ta kwashe da mahaukaciyar dariya.
Sosai mutumin ya sha mur fuskar nan babu alamun wasa ya kada baki ya ce:
"Ke kuma malama me kike yiwa dariya?."
Ramlat ta kuma bushewa da dariya kafin daga bisa ni ta ce:
"Ah! ni ba abin da na kewa dariya . Kawai dai wallahi malam tunbin ka ne ya burgeni da alama dai kullum tukunya ɗaya ka ke kwashewa a gidanku ko?."
Jin abin da Ramlat ta ce, ya sanya mutumin shan mur sosai tamkar bai taɓa sanin mecece fara'a ba ya ce:
" A'a buhun shinkafar na ke haɗiyewa."
Ramlat ta kuma bushewa da wata iriyar dariya kana ta ce:
"Haba ni kam naga alama wallahi, yasin wannan tumbin ba iya buhu ɗaya ne ba. Cab yaya Ahmad dan Allah wannan tumbin ba sai ya ci buhun hatsi ashirin ba?. Ai kaga hatta da makekiyar fuskarsa ma sai da ta nuna yanayin cinsa ko yaya?."
Ta ƙarasa tana me kallon Ahmad.
Ahmad ya tunstire da tasa dariyar kafin ya ce:
"Ai wallahi rabin raina wannan ya fi ƙarfin hatsi ashirin. Ba kiga yadda tumbin ya kumbura ya yi suntum da shi ba sai ka ce tukubar tsire."
Gaba ɗaya fuskar mutumin ta haye da wani irin ɓacin rai wanda bai musaltuwa, jiya yi zuciyarsa na tafarfasa da jin irin kalaman da suke furta masa.
A fusace ya kallesu kana ya ce:
"Dan ubanku ai tumbin uwayenku ne a haka. Shegu ƴaƴan matsiyata masu yawo tsirara."
A ƙufule Ramlat ta ce:
"Dakata malam. Iskancinka da rashin arziƙinka ya tsaya iya nan wallahi banda sako iyaye. Mu da muka maka abin arziƙi sai kuma tsiya ta biyo baya,dan an ce mai ƙaton tumbi to ba gaskiya aka faɗa ba."
Kafin mutumin ya yi magana Ramlat da danƙi ƙasa a hannunta ta watsa matsa shi da jakin, take suka rantama a guje suna faɗin:
"An faɗamai tumbin tukubar tsire.
Ikon Allah ya kiyaye mutumin ta hanyar yin ƙasa da ido da ya yi. Take ya shiga kwashewa su Ramlat albarka.
Sai da ya san yadda ya yi ya samo gidansu shi ne fa abin da ya kawo lamarin tsokanar gida.
Sanda su AMMI suka ji abin da ya faru gaba ɗaya hankalinsu ya tashi. Nan su Abii da Mamman suka shiga baiwa Mutumin haƙuri da ban baki ,wanda da ƴa ce:
"Ya haƙura." ya tafi.
Ko da ya fita Aunty Rahma janyo Ramlat ta yi ta rufeta da duka.wanda da ƙyar Saudat ta ƙwa ce ta,Shi ma sai da su Ammi suka yiwa Rahman tsawa.
Cikin fushi Ammi ta ce:
"A kan me za ki rufemin yarinya da duka?. Ke ta yiwa laifin kome? da har za ki mata wannan ɗan banzan dukan?."
Ran Kakale ya ɓaci jin abin da Ammi ta yi, cikin fushi ta ce:
"Yanzu dan ta ladaf tar miki da ƴar shi ne abin tada jijiyoyin wuya. Inda ace mutumin ne ya damƙeta a hannu fa, sai ki hango ai irin abin da zai mata. Haba yarinya ba faɗa ba kwaɓa."
Ammi ta wuce ɗaki fuuu alamar ta ji haushi.
Abii ya kalle Kaka ya ce:
" Dan Allah gwaggwo ki yi haƙuri.Komai ya wuce ai itama yarinyar ba laifin ta ba ne harda shi wannan ƙatan banzan."
Ya ƙarasa yana mai nuna Ahmad.
Ahmad ganin an nuno shi ya sanya shi wucewa ɗaki simi-simi.
Kakale ta soma faɗa akan lallai gobe su koma inda suka fito gudun jan wata rigimar.
Jin haka ya sa kowa jin haushin Ramlat .Musamman yadda su suke san zaman ƙauyen suke kuma jin daɗain zamansa.
Kamar yadda Kakali ta ce kam haka akayi washe gari bayan la'asar suka tarkata komatsansu suka baro ƙauyan,duk yadda Ahmad ya so biyosu Kakale hana shi ta yi.
Yana ji ya na ga ni suka baro Azare,Ramlat kuwa harda kukan munafurcinta har sai da Mamman ya daka mata tsawa tukunna ta yi shiru.