MATAR MAMMAN.

Fifteen

by @maikosai53

Page 29-30.

Dukkansu fushi suke da Ramlat in ka cire Mamman da shi ko ta kan sabgarta ma ba ya cika bi.

Ammi kam sai wani faman shagwaɓata ta ke yi tamkar jinjira.


 ****

Ramlat ce ta fito da gudu hannunta ɗauke da kwalin charcolate fuskarta duk ta jagwale da charcolate ɗin.

Saudat ce ta biyo ta a guje tana faɗin,

 "Dalla malama ki tsaya, wallahi na kamaki sai na karya miki ƙafa."

Ramlat ta tsaya dai-dai ƙofar ɗakin Ammi ta sanya yatsa ɗaya ta kwaso charcolate ɗin ta miƙowa Saudat da nufin ba ta.

Da sauri Saudat ta matso da ɗan gudu-gudunta da niyyar amsa.

Ganin hakan ya sa Ramlat shigewa ɗakin Ammi da saurinta. Saudat na matsowa ta jita gwaram ta buge da ƙofar da Ramlat ta turo .

Ihu Saudat ta sa ki tare da zubewa a ƙasa tana rusa kuka.

Jin ihunta ne ya sanya mutunen gidan fitowa ciki harda Mamman da ya ke kwance ya na bacci.

Cikin tsawa ya ce,

  "Kinga ki yi mana shiru ko na fasa miki baki, uban me aka yi miki ki kewa mutane kuka?"

Cikin shassheƙar kuka ta ce,

 "Ba Ramlat ba ce ta kwashemin charcolate ɗita bayan ta shanye ta ta, shi ne kuma ta gwara ni da garu na buge"

Mamman ya ja tsaki kafin ya ce,

 "Shi ne ki ke mana ihu kamar mahaukaciya. Kin san halinta sarai ai ba hankali gareta ba ki ke biye mata."

Yana gama faɗin haka ya haura sama abinsa, Aunty Rahma kuwa ɗaga Saudat ta yi suka kama hanyar ɗakinta.

Abii kuwa murmushi kawai ya yi yana mai faɗin,

 "Kema kin san ai sai da haƙuri da Ramlat ki daina biye mata."

Wani kallo Ammi ta jefe shi da shi. Shiru ya yi yana mai murmushi ƙasa-ƙasa.

Zuciyar Saudat kam sai tafasa ta ke ganin yadda duk aka goyi bayan Ramlat ita ba za a ba ta haƙuri ba ko a mata sannu.

Ramlat kuwa tana shigewa ɗakin ta haye kan gadan Ammi ta hau kwamacalarta da charcolate ɗin da ke hannunta.

Gaba ɗaya ta ya mutsa zanin gadon da ke shimfiɗe kan gadon, yayin da ya ji gwagwarmayar charcolate.

Ammi ce ta turo ƙofa ganin aika-aikar da Ramlat ta mata ta sanyata turkewa a wajen kamar bishiyar da aka dasa.

Salati ta shiga rattabawa game da ƙarasawa inda Ramlat ɗin ta ke.

Hannu ta sanya ta fizgota zuwa ƙasa, zuwa yanzu ita kanta fitinar Ramlat ta soma damunta.

Cikin fushi da faɗa ta ce,

 "Wai ke yaushe za ki yi hankali ne? Ke ce daga wannan sai wannan."

Jin abin da Ammi ta ce da irin hantsalowar da aka mata ƙasa ya sanyata fashewa da kuka.

Cikin kuka ta ce,

 "Haba Ammi yanzu kawai dan ina wasa na shi ne za ki jefo ni ƙasa mene ne laifina ni kuma?."

Jin hakan daga bakin Ramlat ɗin ya sanya ran Ammi kuma ɓaci, charcolate ɗin ta fisge daga hannunta ta yi wurgi da ita, sannan ta damƙo gashin kanta wanda daman babu ɗan kwali a kan na ta .

Ihu ta sa ki kamar gyare.

Cikin ƙaraji da fushi-fushi Ammi ta daka mata tsawa.

  "Rufemin baki mahaukaciyar banza ,muddin ki ka kuma shigowa ɗakin nan ma sai na karairaya miki ƙafafuwa ma za fice min a ɗaki."

Tun kan Ammi ta ida zancanta ta yi hanyar ficewa daga ɗakin da sauri har tana tuntuɓe.

Tana zuwa bakin ƙofar dab da za ta fita ta juyo da sauri ta yi ma za ta durƙusa ta ɗau charcolate ta miƙe ta fice da gudu tana mai ɗaga sautin kukan da ta ɓarke da shi.

Ba ta zarce ko'ina ba sai kitchen.

Ammi kam tsaki ta ja tana mai tattare zanin gadon zuwa bayi.

Tana isa kitchen ɗin ta haye kan wata ƴar ƙaramar loka da ke zaune gefe wacca suke saka shirginsu ciki.

Zama ta yi daram akanta ta fidda charcolate ɗin daga dunƙuletan da ta yi daga hannunta ita a zummar ɓoyeta ta yi ta soma shan kayanta.

Ta jima tana tanɗe-tanɗenta kafin bacci ya yi awon gaba da ita.


Bayan Awa Uku.

Aunty Rahma ce ta shigo kitchen ɗin dan dafa Noodles da ƙwai.

Sosai ta ke hada-hadarta. karaf idanuwanta suka hango mata mutum a rakufe ya yi lamo da shi yana sheƙar baccinsa.

Matsawa ta yi daf da inda Ramlat ta ke tana baccinta hankali kwance.

Dai-dai sai tin fuskarta ta sanya hannu ɗalle fuskar.

A razane Ramlat ta farka tana waige-waige ganin ko wane ne.

Ganin Aunty Rahma tsaye gabanta ya sanya ta taɓe baki ta yi komawarta .

Aunty Rahma ganin hakan ya sanya ta faɗin,

 "Ke lafiyarki ƙalau? Me ya kawo ki nan? Baccin me ki ke yi?"

Ramlat ta gyara zamanta kan lokar sosai ba tare da ta kalli Aunty Rahma ba ta ce,

 "Ammi ce ta ce na fice mata a ɗaki na tafi kan bola na ci gaba da kwana, shi ne har na zo zan fita Baba ya ce ai gwanda na je kitchen ko lambu na kwana, shi ne ni kuma na ce bari na zo nan."

Aunty Rahma ta yi saƙaƙe tana mai bin Ramlat da kallon mamakin jin abin da ta ke cewa.

 "Ammin ce ta ce ki tafi bolar?"

Ta tambayeta.

"To zan mata ƙarya ne ,ki je ki tambayeta za ki sami wasu ƙarin kanun labaran."

  Ramlat ta ce tana mai jingina da jikin bangon kitchen ɗin.

Kafin Aunty Rahma ta yi magana Ramlat ta katseta da faɗin,

  "Ni dai kinga kawai ki ƙyale ni ki yi tafiyarki bacci na ke ji."

Jin hakan ya sanya Aunty Rahma barin wajen ba tare da ta ce mata komai ba.

Har ta kammala dafa abincin ta fice daga kitchen ɗin Ramlat na nan zaune ko motsawa ba ta yi ba.

Aunty Rahma na fita Ramlat ta diro daga kan lokar ta matsa daf da gas ɗin ta soma ƙoƙarin kunna shi.

Tukunya ta samo ta ɗakko Noodles ta fasata ta juyeta a tukunyar ko ruwa ba ta zuba ba ,ta zuba maggi da gishiri sai kori sak irin abin da taga Aunty Rahma ta yi. Sannan ta kunna gas ɗin ta ɗora ta yi komawarta inda take ta yi kwanciyarta.

Cikin abin da bai fi minti goma sha biyu ba hayaƙi ya soma cika kitchen ɗin.

Saudat da fitowarta kenan daga ɗakin Aunty Rahma hancinta ya jiyo mata ƙauri da kuma warin gas tuni ta koma ɗakin Aunty Rahma ta shiga sanar mata da abin da ta ji.

Nan su ka ɗunguma zuwa kitchen ɗin dan san sanin me ke faruwa.