MATAR MAMMAN.

Sixteen

by @maikosai53

Page 31-32.


Daf da za su shiga cikin kitchen ɗin Ramlat ta fito a guje tana tari game da ƙwala ihu.

Aunty Rahma ta kutsa kai ciki sai dai da sauri ta yo baya saboda hayaƙin da ya mata katutuwa ya hanata ƙarasawa ciki.

Saudat kam komawa ta yi falon tare da dosar ɗakin Ammi tana haki ta shiga rattabawa Ammi abin da ke wakana.

Da sauri Ammi ta biyo bayanta, ganin abin da ya ke faruwa ya sanyata sanya salati tare da fitowa farfajiyar gidan dan neman a gajin su Baba.

Ko da ta sanar da Baba abin da ke faruwa da sauri ya miƙe ya iske Mai bawa fulawa ruwa ya sanar masa da abin da ke wakana ,take suka rankayo zuwa sashen in da abin ya ke faruwa.

taimako da ƙoƙarin tsayar da hayaƙin su ka yi da ƙyar aka samu a ka shiga aka kashe gas ɗin tukunyar kuwa ba a maganarta.

Kowa yana zaune a falo in ka cire Abi da Mamman da basa nan.

Ammi ta kalli Aunty Rahma ta ce,

 "Garin ya akayi hakan ta faru?."

Aunty Rahma ta kalli Ammi ta kalli Ramlat kana ta ce,

 "Ammi sai dai ki tambaye Ramlat, itana gani a kitchen ɗin."

Ammi ta kalli saitin inda Ramlat ta ke zaune ta ce,

  "Ramlat kuma?"

Auntu Rahma ta gyaɗa kai tare da furta,

 "Ƙwarai Ammi."

Ammi ta kuma kallon Ramlat ta ce,

 "Mai ya kai ki kitchen?, Kuma garin ya hakan ta faru?"

Ramlat ta soma raba idanuwa kafin ta ce,

  "Ammi ni ma ban sani ba ki tambaye Aunty Rahma, ita ce na gani ɗazu tana girki akai Kuma ni bacci ma na ke yi yasin."

Ammi ta fusata ƙwarai cikin fushi ta ce,

 "Zanci mutuncin ku wallahi, ya ina magana kuna rainamin hankali ne."

Aunty Rahma ta kalli Ramlat a ƙufule tana mai ƙyasta mata yatsu biyu, ta juyar da kanta ta kalli Ammi kana ta ce,

 "Tabbas Ammi na je na yi girki kuma na kammala lafiya harma na ci abin da na dafa ni da Saudat. Ban san ya aka yi hayaƙi ya turnuƙe kitchen ɗin ba saboda ni dai na gama komai lafiya kuma na fito na bar Ramlat a ciki."

Ammi ta ce,

  "To ya aka yi hakan? , Mai ya kai Ramlat kitchen?"

Aunty Rahma ta ce,

  "Ammi wallahi ban san yaya a ka yi hayaƙi ya tashi cikin kitchen ba, Ramlat kuwa na ganta tana bacci kan loka, dana mata magana sai ta ce, ke ki ka ce ta tafi kan bola ta ci gaba da kwana acan kin sallameta shi ne ta zo za ta fita wai Baba ya ce ta dawo ta kwana cikin kitchen ko lambu shi ne ita kuma ta zaɓi kitchen."

Tun da Aunty Rahma ta soma zuba jawabinta Ammi ta saki baki galala tana binta da kallo.

Ammi ta ce,

 "Innalillahi wa'inna ilaihir raji'un yanzu ni Ammi da baki na na ce ki tafi kan bola ki ci gaba da kwana ?"

Ta ƙarasa tambayar tana kallon Ramlat da ta yi wuri-wuri da idanuwa sai raba su ta ke yi.

A hankali ta furta,

  "A'a Ammi daman-daman fa kawai dai da ki ka ce na-na-na-na....... "

 "Yi min shiru ai dole ki kasa magana mana, ni ban san me zan ce miki ba amma Allah dai ya shirya min ke, maza wuce ɗaki kan na iso gareki."

Ammi ta faɗa a fusace.

Aunty Rahma da Saudat kam sai faman dariya suke yi ƙasa-ƙasa jin yau rana ta haɗosu da aminiyar ta ta.

Kallonsu ta yi tare da furta,

  "Ku kuma ku ta shi ku bani waje."

Sum-sum suka miƙe tare da barin falon.

Ramlat na zaune ƙasan falon Ammi ta rakuɓe ,shigowar Ammi ya sanyata tsandara ihu tare da faɗin,

  "Dan Allah Ammi ki min rai wallahi ban shirya mutuwa dan Allah ki ƙyaleni kada ki karya ni."

Ammi ta daka ɓata tsawa ta hanyar furta,

  "Rufemin baki sakaryar banza."

Ɗif Ramlat ta yi ta haɗiye yawu ji ka ke "Maƙuuut".

Ammi ta kalleta kana ta ce,

 "Yanzu abin da ki ka yi kinyi daidai? In da ace gobara ta tashi fa ta kama da ke ko da gidan gaba ɗaya fa? Sai ki ce me? Mai ya sa har yanzu ba za ki gane Annabi ya faku ba iye Ramlat? Ina rabaki da kiwon kyalla kina kyalla ta haihu ko? Ki nutsu tun wuri tun kan raina ya kai maƙarar ɓaci."

Duk abin da Ammi ke cewa bawai tana jin sa bane hasalima hankalinta ya karkata ga tatanahiyar.

Har sai da Ammi ta lura da hakan ta miƙe ta wuce ɗaki ba tare da ta tanka mata ba.

Sanda ta dawo duniyar ta lura Ammi ba tanan falo ta miƙe a hankali ta salallaɓa ta fice daga falon  Kai tsaye lambu ta wuce tana yi tana waiwaye.