MATAR MAMMAN.

Seventeen

by @maikosai53

Page 33-34.

A hankali ta miƙa wuya tana hangen ko wani na biye da ita.Ganin babu kowa ya sanyata saurin shigewa cikin lambun.

Saɗaf-saɗaf ta ƙarasa gaban shukar Ayaba da Mamman ya shukata dan a rayuwarsa yana san Ayaba da kankana da abarba.

Hannu tasa ta soma tsigarta a hankali.

  "Aikin banza ba malam ace ga kayan daɗi iya daɗi amma ba za a bawa mutum ba,ai wallahi ko ba lada sai na ci."

 Tana tsiga tana sambaɗar surutanta har saida ta tsigo guda biyar.

A baza ta ta jiyo sautin murya na faɗin,

 "Lalala mai na ke gani haka?, Ayabar tasa ki ke cirewa?"

Juyowa ta yi ta kalleshi tana mai ɓoye huɗu a bayanta ta ce,

  "Kai innalillahi ɗaya fa na tsiga kuma yanzu na cire ta ,to kai mene ne naka ma acikk tunda dai ba kai ka shukaba."

Ta ƙarasa tana mai murguɗa masa baki.

"Ehhhh! na ji ba dai ni na shuka ba amma ai ni ne mai alhakin kulawa da ita ko? Bari gogan ya dawo tas a kunnensa kamar a gabana a kayi komai zan shaida masa."

"Dan Allah ka fi ƙuda gudu, kai ne ma Ammi da Abii ,an gaya maka ni ina tsoran karta-kwana ne ,ai ni ce na yankewa tsoro cibi dan kar ya addabi sashen rayuwata."

 Ramlat ta ce.

"Haka ki ka ce?"

  Ya tambayeta.

"Ahh! haka na ce."

  Ta ba shi amsa tana mai matsawa daga wajen.

Saitin kan kashu ta matsa ta sanya hannu tana ƙoƙarin cirarsa, take mai kula da wajen ya matsa yana faɗin,

  "Kul a hir ɗinki alƙur'anin Allah ba ki isa ba."

Taɓe baki ta yi gami da faɗin,

  "Kamar ya ban isa ba ? Ni da gidan ubana kayan ubana a hanani tsiga."

Wata sanda ya ɗakko da take jingine gefe ya nunata da ita kana ya ce,

  "Wallahi kina sanya hannunko ina rafka miki wannan."

Ƙyalƙyalewa ta yi da dariya kana ta ce,

  "Ai shi kenan, na dai ƙyaleka ba yanzu ba amma gaba in na dawo ba za ta maka da kyau ba."

 "Ƙaryar banza ce da burgar wofi a she ki cire ki ga ni."

  Ya ce.

"Ka dai ci sa'a yau watan mutuncina ya kama, amma duk randa ya fita ka fara hawaye yasin."

 Ta ce tana mai ficewa daga lambun.

Shikam dariya ma ta ba shi, girgiza kai kawai ya yi ya koma inda ya fito a ransa yana raya ƙarfin hali irin na yarinyar amma sai shegen tsoro.

Ramlat na fita ta wuce wajen Baba mai gadi, zaune ta iske shi yana jan casbaha.

Kallon s ta yi bayan ta zauna gefen bencin da ya ke zaune ta zuɓe Ayabar da ta tsinko a lambu.

  "Wash! Baba yasin naa gaji"

Baba ya kalleta kana ya ce,

  "Ɗiyata me kika yi haka da ya sanya ki gajiya."

Ta yi murushi kana ta ce,

  "Yanzu saboda Allah baba ba za'a ragwanta mana ba a ciro komai na lambu a ajjiyeshi kawai ɗauka za mu riƙa yi, amma sai an bari har munje da kanmu an hawalar damu, yanzu ba ka ji yadda ƙashin kafaɗata ya ke ciwo ba akan waɗannan Ayabar guda biyar."

Baba ya dubeta sosai yana jinjina kalmominta kana ya ce,

 "Gaskiya ne ɗiyata ya kamata a cirosu a ajjiye saboda hakan kada ki zo ki rafke da ciwo."

Ta gyara zamanta sosai akan bencin tana faɗin,

 "Yawwa babana na kaina, kaga abin da za ayi ka sami shi wancan mai fuskar banɗashe ka masa bayani na san zai ji maganarka."

Baba ya riƙe baki gami da gwalo ido waje ya ce,

 "Wa ni rufani ki saya, au banɗashe ma yana da fuska ɗiyata?."

"Hmmm! Baba baka sani ba ? Cab aikam ka riƙa lura da kyau,uhmm! ni dai bari na tafi kumafa ba sanmaka zan ba dan kadama ka sa rai yasin."

Baba ya yi ƴar dariya kana ya ce,

 "Ina ni ina sanya rai ɗiyata, maza kije ki sha kayarki."

"Ah! to ya ma dai fi Baba".

  Ta faɗa tana mai miƙewa.

Ammi kam tana fitowa daga ɗaki ta iske ba ta falon, girgiza kai kawai ta yi tare da mata fatan samun shiriya daga wajen Ubangiji mahalicci.

Tana shigowa babban falo ta yi bayan kujera ta tsugunna ta cusa Ayabar ƙarƙashin kujerar kana ta nufi ɗakin Ammi.

Duk abin da ta yi Saudat na kallonta, tana barin wajen ta iso inda ta ganta a tsugune ta sanya hannu ta zaro Ayabar da Ramlat ta ɓoye.

Mamaki ya cikata tare da tambayar kanta da kanta "A ina ta samo su? Badai a lambu ba? waya ba ta?"

Ganin ba ta da mai ba ta amsa ya sanyata kwashesu gaba ɗaya ta haye sama abinta.

Ramlat na shiga falon Ammi ta iske ba tanan, sauke ajjiyar zuciya ta yi ta neme gefen kujera ta rakuɓe ta sanya hannu ta dangwalo yawu ta shafa akan fuskarta wanda ya je har ƙasan idanta alamar kuka ta yi, sai ta langwaɓar da kai tamkar mai bacci.

Ammi ce ta fito da shirin fita za ta unguwa, kiciɓis ta yi da Ramlat na baccin ƙarya ga hawaye saman fuskarta da ya soma bushewa.

Mamaki fal ta cika da shi har yaushe ta shigo? Ta yi kukan? Kuma ta yi baccin?

Matsawa ta yi inda amlat ɗin ta ke ta sanya hannu ta taɓata, abinka da wacca daman na lamɓone da kuma shiri sai ta razana ta sanya ihu tare da faɗin,

  "Ammi ki yi haƙuri ba zan kuma ba dan Allah kada ki dake ne "

Ammi ta dafa kafaɗarta tare da riƙota ta ce,

 "To mene ne na kukan kuma? ,Yaushe kika shigo?"

Ramlat ta buɗe baki ta ce,

 "Ammi ba kice kika yi mini tsawa ba kuma kika ce na fitar miki daga ɗaki, kuma shi ne za ki dake ne."

"Na ji yanzu ba wannan na tambaye ki ba ,ca na yi yaushe ki ka dawo falon, kuma ina ki ka je?"

 "Ammi na jima a nan, fitsari na je na yi fa"

 Ramlat ta faɗa a sanyaye.

"Ok good ya yi, kada ki kuma sa ƙafarki ki fita daga ɗakin nan, zanje unguwa saura kuma na ji ance kinyi wani abun in na dawo."

 Ta yi rau-rau da ido kana ta ce,

 "Ni ba abin da zanyi Ammi, amma ki ce musu kada wanda ya dake ne."

"A kan me za su dake ki, sai dai in laifi ki ka yi musu."

"Kada na ji wani zance kuma."

Ammi ta ce tana mai ficewa daga ɗakin.

Baifi minti uku da fitar Ammi ba ta buɗe ƙofar ta fito a hankali tana leƙen taga ko ba ta fita ba.

Jin tsit a falon ya sanyata danna kai ciki, in da ta yi ɓoyarta ta wuce kai tsaye.

Tana zira hannu ta ji wayam babu komai, hakan ya sanyata furta,

 "Kan bala'i, wallahi yau gidan nan a kwai damuwa acikinsa kowa sai dai in tasa ta fissheshi."

Ta buɗe murya tare da faɗin,

 "Ku na ina kowa ya fito wallahi yau akwai yaƙin.........."

Maganarta ta katse sanda idanuwanta suka hango mata Mamman tsaye da shigowarsa kenan.