eighteen
by @maikosai53
Page 35-36.
Da sauri ta juya za ta shige ɗakin Ammi. Taku ɗaya ya yi ya damƙota da hannunsa ɗaya hakan ya sa ta ƙwala ƙara.
"Rufemin baki"
Ya daka mata tsawa.
Ba shiri ta yi gum da ita.
Kallonta ya yi kana ya ce,
"Uban me kike cewa?"
Cikin in ina ta ce,
"Uhmm! uhmm! uhmm! wallahi ni ba abin da na ke cewa."
"Well kada ki faɗa"
Ya furta a hankali. Janyota ya yi ya dangwarar da ita kan kujera ya sanya ƙafarsa ɗaya ya tokareta kana ya ce,
"Ko ki maimaita ko yanzun na cire miki kunne ɗaya."
"Wallahi ba wani abun na ceba haka na ce yau gidan nan akwai tijara."
Ta ƙarasa tana shassheƙar kuka.
"Me aka yi miki da za ki yi tijarar?"
Ya tambayeta tare da kafeta da idanuwansa.
"Babu komai walahil azeem babu komai, dan Allah ka rabu dani ka yi haƙuri na tuba."
Ramlat ta ce.
"Wallahi yaya ƙarya ta ke yi, zuwa ta yi ta ciro maka Ayabarka wacca ta nuna ta zo za ta sha"
Saudat ta faɗa tana mai ƙarasa sakkowa daga kan matattakalar benen.
Kallon Ramlat ya yi da ta fara raba idanu.
"Haka a ka yi da gaske ko kuwa?"
Wani yawu ta haɗiye ji ka ke maƙuuuut kafin ta ce,
"Ni ma-ni ma-ni ma in zuwa na yi wucewa na ganta a ƙasa in ƙarya na ke ka tambaye Baba ka ji"
Mamman ya tafa hannayensa kafin ya ce,
"Baban ubanwa zan tambaya shi ma ai duk tawagarku ɗaya, da gaske kin ɗaukarmin Ayaba ta ko kuwa?"
Ya shiga ƙoƙarin zare belt ɗin da ke jikin wandansa.
Ganin hakan ya sanyata faɗin,
"Ehh! haka ne kam da gaske ne, dan Allah ka yi haƙuri."
Bai amsa mata ba har sai da ya zare belt ɗin gaba ɗaya .Lokaci ɗaya ya kaishi jikinta ji ka ke shuuul.
Ƙara ta sa ki tare da furta,
"Dan girman Allah ka yi haƙuri, wallahi ba zan kuma ba na tuba na bi Allah da ma'aiki"
"Yi mini shiru, daga yau in na kuma ganin ƙafarki a bakin lambu ko ta yi hanyar lambu sai na ɓalla ita ƙafar gida ɗari yadda ko an ta shi jonata ba za ta jono ba, kin ji ko?"
Ya faɗa cikin daka tsawa.
"Ehh na ji ba zan kuma ba dan Allah."
Ramlat ta ce cikin kuka.
"Ta shi ki bani waje."
Ya ce yana mai sauke ƙafarsa daga kan kujerar, ya juya tare da haurawa sama.
Ramlat kam kallon Saudat ta yi ta gyaɗa kai.
Saudat kuwa kwashewa ta yi da dariya tare da furta,
"Gobe ma kya kuma, in kunne ya ji jiki ya tsira".
Ramlat ba ta ce mata komai ba ta wuce ɗakin Ammi zuciyarta fal cike da ruwan kalar muguntar da za ta yiwa Saudat.
Ko da Ammi ta dawo ba ta yi gigin sanar mata da abin da ya faru ba, saboda tasan ca za ta yi "Allah shi ƙara."
******
Bayan kwana biyu.
Kowa yana falo Ammi, Abi da shekaran jiya ya dawo da dare, sai Aunty Rahma, Mamman ,da kuma oganniya Ramlat.
Saudat ce ta sakko daga bene tana tafe tana ƴar waƙarta, dai-dai kan wata kujera da ke gefe ta nufa da niyyar zama.
tana ɗora mazaunanta ta jita daram a ƙasa, nan ta sanya ƴar ƙara.
Sai a lokacin kowa hankalinsa ya kai wajen.
Ammi ce ke tambayarta ko lafiya?.
"Ammi na zo zama ne na ji ne a ƙasa, kuma wallahi kujerar tana wajen san da na je zan zauna."
Kafin Ammi ta yi magana Ramlat ta ƙyalƙƙyale da dariya kana ta ce,
"One five kenan, yanzu ma ki ka soma gani."
Ammi ,Abi da oga Mamman duk suka zuba mata idanu, Abi ne ya yi jurin tambayarta ta hanyar furta,
"Me ta miki ɗiyata ake gasata?"
Ramlat ta cuno baki kafin ta ce,
"Abi sa wa ta yi yaya ya kamani ya yi mini ɗan banzan duka har sai da na kasa ta shi, akan kawai na ciro Ayaba na zo zan ci, kuma ji na yi an faɗa a redion Baba an ce ,"In mutum na cin Ayaba jikinsa na yin kyau ya yi ƙiba ya zama lukuti" shi ne fa na ɗakko zanci ƙarshema ita ta kwashe Ayabar ta je ta ci."
Abi ya kalli Saudat ya ce,
"To ke yaya garin ya ya hakan ta faru?"
Saudat ta yi rau da ido ta ce,
"Wallahi Abi sharrinta ne kawai ba haka akayi ba, tabbas na cinye Ayaba kuma gani na yi tana ɓoyewa ni kuma daman ta yi min laifi shi ne na mata hukunci."
Ammi ta yi caraf ta ce,
"Allah shi ƙara, gobe ma kya kuma sawa a dakar min ƴa, kai kuma"
Ta juya ta kalli Mamman ta ci gaba da faɗin,
"Duk randa ka kuma dukar min ƴa sai na ɓalla ka gida goma ka ji na gaya maka."
Kafin kowa ya yi magana Ramlat ta bushe da dariya ta ce,
"yeeee! ba ka ce za ka ɓalla ƙafata gida ɗari ba, ni ma ga shi nan Ammi za ta rama min."
Ammi ta ce,
"Ƙwarai ma kuwa, wani ya kuma taɓa ta sai ransa ya matuƙar ɓaci."
Ba wanda ya kuma cewa "Uffan" har Abi ɗin da ke zaune,kallonsu suka ci gaba da yi.
Dai-dai wani waje da wata yarinya ke faɗin,
"Sai ni Jamila ta kamilu bada kan ki a sare ki je gida ki ce ya faɗi, sai ni Jamila ta kamilulu na abin ƙaunata da begena"
Ta washe baki tamkar gonar auduga.
Ramlat ce ta yi sowa gami da faɗin,
"Hoo! sai ni ta Ramlat ta Mamman bada kan ki a sare kije gida ki ce ya faɗi, sai ni Matar Mamman ,shalelen Mamma........."
Mauje mata bakin da Mamman ya yi ne ya sanya maganarta katsewa.
Ganin hakan ya sanya kowa na wajen kwashewa da dariya.
Ammi ce ta ce,
"Ba yanzu na maka iyaka da taɓamin lafiyar ƴa ba?"
Mamman ne ya sha mur tare da furta,
"Amma Ammi ba ki ji sakarcin da ta ke yi ba."
"Ta yi ɗin sai me dan firta hakan tunda ba sunan wani gardin ta kira ba, ita ɗin ba ƴar uwar ka bace sai me na ce ta yi."
Ammi ta ce.
"Yawwa Ammita ai daidai na faɗa ko, ni matar Mamman ce ko?"
Ammi ta shafa kanta ta ce,
"Ƙwarai ma kuwa, amma ba wannan Mamman ɗin ba.Mamman ɗin ki mai sanki ne ɗan ƙwalisa kin ji Matar Mamman."
Abi ne ya ce,
"Ya kamata ki rage shagwaɓa yarinyar nan tafa girma shekara goma sha uku ba wasa ba."
"Ba ruwanka bana san sa ido"
Ammi ta ce.
"To ai shi kenan, mu dai namu kallo ne."
Abi ya ce.
Mamman kam ta shi ya yi fuuuu ya bar wajen zuciyarsa na masa suka.