Nineteen
by @maikosai53
Page 37-38.
Ammi ta ce:"Kai ka sani sai shegiyar baƙar zuciya ,a haka za ka ƙare ai."
Dukkansu miƙewa suka yi suka bar falon , sai ya rage daga Ammi sai ƴarta Ramlat.
Sai da suka gama kallonsu har film ɗin ya ƙare sannan suka ta shi.
Washe gari, Mamman ne ya shigo ɗakin Ammi hannunsa ɗauke da wasu takardu.
Bayan sun kuma gaisawa da Ammi ya kalleta tare da furta:"Yawwa Ammi daman foarm ne na amso na makaranta."
Ammi ta ajjiye littafin da ke hannunta ta ce: "Na wa fa? Wacca makaranta?"
Mamman ya ce:"Na ƴarki, boarding school da ke Kazaure."
Da ƙarfi Ammi ta ce:"Ka me? Ko Ɓazaura ne wallahi ba inda za ta ,ƴar tawa za ka kai mini boarding salan a kashe mini ita."
"Haba Ammi ya kamata fa ace yanzu tana makaranta amma tana zaune a gida saboda Allah, kuma mai za'a mata a can ɗin ba cinma ita ce za ta yi da wannan banzar fitinar ta ta."
Mamman ya ce.
Ammi ta kalleshi cikin san yarda da zancansa kana ta ce:"Amma kana ganin in aka kaita boarding ɗin za ta sami nutsuwar karatun.?"
Ya girgiza kai cikin san ƙarfafa mata gwiwa na barin yarinyar ta yi karatu ya ce:"Ina da tabbacin haka in sha Allahu Ammi a
Amincewarki kawai na ke nema."
"To ubangiji ya sa haka ameen. Yanzu yaushe za'a kaita.?"
Ta tambayeshi.
"Ammi na kammala komai na tafiyarta daman amincewarki kawai na ke jira, kuma ga shi kin bada goyon baya alhamdulillah zuwa jibi sai na kaita."
Mamman ya furta.
"A'a har da ni za aje.Allah ya kaimu jibin."
Ammi ta ce.
"Ameen Ammi. Amma dai kada ki sanar mata gudun tawayenta."
Mamman ya ce.
"To na ji ta shi kaje ɗan tsari master"
Ammi ta ce tana saita masa hanyar ficewa daga ɗakin.
Ficewa ya yi yana ƴar dariyarsa a hankali.Har ya hayi sama abinsa yana dariyar muguntar da ya shiryawa Ramlat.
Ramlat kam ba ta san wainar da ake toyawa ba. Hurumunta kawai ta ke yi da zallar taɓararta.
Ita kaɗai ce ba ta san da rafiyarta makarantar kwana ba, amma kaf ɗin mutum gidan sun sa ni.
Rana ba ta ƙarya sai dai uwar ɗiya ta ji kunya; yau ce ranar da Ramlat za ta tafi makaranta.
Zaune ta ke gaban Ammi sai faman zuba mata nasiha ta ke yi.
Ramlat ta marairaice fuska kamar za ta yi kuka ka na ta ce:"Wai Ammi me ke faruwa ne ki ke ta yi min nasiha kamar za ki mutu."
Ammi ta yi ƴar dariya ,tare da shafa kanta kafin ta ce:"Ramlat ko ɗaya ba abin da zai sameni mutuwa ba yanzu ba da izinin Allah sai na ga aurenki.Ki nutsu ina so ki sami wadatacciyar nutsuwa domin za ki ci gaba da karatune a makarantar kwana da ke Kazaure, kuma yau ɗin nan za ki tafi yayanki zai kai ki da ni za'aje amma wani uzuri ya tasomin ba zan sami zuwa ba.Ina so ki kula da kanki, ki kama kanki banda shiga sabgar da ba taki ba kin ji ko? Ki kula da addini ki daina wasa kin ji ƴa ta."
Gaba ɗaya saman fuskar Ramlat ta jiƙe da ruwan hawaye, duk da cewa sautin kukan bai fito ba amma fuskar ta cika da ruwan hawaye.Shiru ta yi ba ta ce uffanba hakan ya sanya Ammi faɗin:"Ƴa ta ko ba kya so ne?"
Ta tambayeta.
Girgiza kai kawai ta yi.
"A'a ƴa ta in baki so kawai sai a haƙura, amma zan yi farin ciki in aka ce ƴa ta ta ci gaba da karatu."
Murmushi ta yi kana ta ce: "Ammi ina so zan je."
Ta furta hakan a hankali tamkar ba Ramlat ɗin da aka sani mai tsiwaba.
"Yawwa Allah ya yi maki albarka ɗiya ta, ayi karatu lafiya kada a yi wasa kin ji ko"
Ɗaga kanta kawai ta yi.
Har bakin mota Ammi da sauran ƴan gidan suka rakata, Saudat sai dariyar mugunta ta ke mata, har sai da Ammi ta daka mata tsawa kana ta tsagaita.
Ramlat kam abubuwa da dama ta ke ayyanawa wanda ta ke ta saƙawa tana warware kayanta cikin ranta.
A hanya Ramlat ce ke ta faman rusa kuka kamar wacca aka yiwa wahayi da lokacin mutuwarta ko aka aiko mata da saƙon mutuwar Ammi.
Tun da ta fara kukan nata yake dukan dodon kunnuwansa yana ratsa kwanyar ƙwaƙwalwarsa .Cikin jin haushinta ya taka wani wawan burki ji ka ke "Ƙiiiiiiiƙiiiiiiii"
Kallonta ya yi a fusace kana ya ce:"Fi ce mini a mota."
"Lallai ma ka ji ɗan rainin wayo, ka sanya Ammi ta kaine makaranta kuma ka zo kan tsakiyar hanya ka ce na sauka ka ji rainin wayo."
Ta fa ɗi haka cikin ƙasan zuciyarta.
A tsawace ya kuma furta:"Ki fi ce min a motana ce, tun da ke wawiya ce."
Turo ba ki ta yi ba ta furta kanzil ba ta sanya hannunta ta murɗa murfin motar ta fice.
Ji ka ke "Fuuuuuuuu" ya ja motar.
Hawaye suka kuma zuɓo mata akan kuncinta ,"Da man na san kaine babban maƙiyina, ni da man na sani sai da ni kawai ka yi."
Ta durƙusa wajen ta yi zaman ƴan bori "Wallahi ina nan koma mene ne zai zo sai dai ya zo ,inma cinyeni za ayi ko ayi gutsi-gutsi da ni to a zo a yi."
Ta furta tana mai dukan ƙasa.
Ku san mintina goma ta ga mota ta tsaya gabanta Murfin motar baya a ka buɗe mata alamar ta shiga.
Ita kam ɗauke kanta ta yi tamkar ba da ita ake yi ba.
Ganin tana nan zaune ba ta motsa ba ya sanya shi furta:"Shigo "
Yi ta yi tamkar ba za ta shiga ba, komai ta tuna sai kuma ta miƙe ta kyakkyaɓe jikinta ta shiga tana taɓe baki.
Ammi zaune ta yi tagumi da hannayenta biyu.Saudat ce ta zauna kusa da ita tana mai furta:"Ammi wai ni kam yau lafiyarki ƙalau? ,Tun ɗazu naga jin aza hannaye biyu kin rafka tagumi mai ya faru Ammi?"
Ammi ta sauke ajjiyar zuciya kana ta ce:"Gaba ɗaya ba na jin nutsuwa a tattare da ni, ni inajin kamar wani abu na faruwa da ita fa."
Saudat ta ɗan yi murmushi ta re da sauke ajjiyar zuciya kafin ta ce:"Haba Ammi yanzu daga tafiyarta har kin soma rafka tagumi da kuma tunanin ana mata wani abun? Ammi mai za'ayi mata alhalin na san ko isa ma ba su yi ba. Dan Allah ki kwantar da hankalinki kawai ba abin da zai sameta in sha Allahu rabbi."
"To shi kenan na ji Allah ya sa hakan."
Ammi ta ce.
Saudat ta cafe da "Ameeen".
Sun isa cikin makarantar Kazaure lafiya.Yayin da Ramlat ta buɗe idanuwanta tana mai ƙarewa makarantar kallon tsaf.
Offishin shugaban makarantar suka wuce.Nan Mamman ya soma gabatar da ita a matsayin ɗalibar da ya kawo .
Shugaban makarantar ya yi murmushi kana ya ce:"Madalla mene sunan ɗalibar ta mu?"
"Ramlat " Ta furta a hankali tana mai ƙarewa malamin kallo.
"Ah masha Allah" ya ce.
Nan suka tattauna da Ramlat akan karatu ba laifi ta ɗan san wasu abubuwan tun da daman ai ta yi karatun.
"Masha Allah, Ramlat akwai ƙoƙari hakan ya sa zamu kaita aji biyu kuma in sha Allahu za ta sami kulawa sosai"
Shugaban makarantar ya ce .
Sosai Mamman ya kuma tattaunawa da shugaban makarantar bayan an kai Ramlata ajinsu wanda kafin ta tafi sai da Mamman ya ja mata kunne ya fi babu adadi.
San da ta shiga ajin bencin ƙarshe ta je ta zauna ba ta kula kowa na ajin ba.Sai faman kallonsu da ta ke yi ɗai-ɗai sai ka ce mai nazar tarsu.
Mamman kam godiya ya yiwa shugaban makarantar tare da ƙara jajjada masa akan dan Allah ya kula masa da ita kafin ya tafi.
Har malamin da ke cikin ajin ya gama karatunsa amma ba abin da Ramlat ta ɗauka aciki illa kawai bin kowa da ta ke da kallo.
Tsawon mintina goma a haka har wani malamin ya shigo.Bayan ya soma darasi Ramlat ta tambayi uzurin fitsari ta fice daga ajin.
Aunty Rahma ce ta fito falon nan ta tadda Saudat da Ammi su na taɓa hirarsu.Zama ta yi kan kujera tana mai furta,
"A'a hira a ke sha ? Maimakon a ce ni ma a zo ayi da ni."
Ammi ta ce:"Ina wata hirar tun da ba daɗi ta ke min ba babu Ramlatu na"
Aunty Rahma ta yi ƴar dariya kafin ta ce:"Kai Ammi ai inaga ta mu sai ta fi tun da mu dai munfi waccan hankali."
Harara Ammi ta maka mata kafin daga bisa ni ta ce:"Ko kuma shashashai ba"
Dariya suka kwashe da ita.
Saudat ta ce:"Kwantar da hankalinki Ammi gobe ba sai ki shirya ki je ki ganta ba."
Ammi ta lumshe ido tare da furta:"Ni dai ba wannan ba na fison a ce inama su dawo na buɗe ido na na ganta gabana hankalina sai yafi kwanciya akan na je na gano ta."
Har Aunty Rahma ta buɗe baki za ta yi magana suka ji motsin shigowa falon a tare suka kalli wajen da ido dan ganin mai shigowa harda Ammi da idanta ke rufe ta buɗe.
A razane dukkansu suka miƙe har da Ammi cikin rawar murya da nuna ɗan yatsa suka furta...