Twenty one
by @maikosai53
Page 41-42.
Ramlat ta soma furta, "Ammi lokacin da na ƙware ina ɗago ido na ga tana yi mini gwalo, sannan tana ƙyasta yatsu biyu tare da sanya yatsanta ɗaya kan wuya alamar yanka ni za ta yi."
Saudat kam zaro idanuwa ta yi tana mai mamakin irin sharrin Ramlat. Yanzu tana tsaye amma har ta shirya wannan zance.
Ammi ta dubi Saudat kana ta ce, "Da gaske anyi haka ko kuwa?"
"Ammi wallahi ni sam ban sani ba ,yanzu dai ni ma na keji a bakinta."
Saudat ta ce.
"Ba na san shashanci na gaya miki, ki riƙa kama kanki kija girmanki."
Ammi ta ce.
"To Ammi"
Saudat ta faɗa tana mai ɗan rissinawa.
A hankali Ramlat ta ci gaba da kai lomarta baki, fakar idan Ammi ta yi ta yiwa Saudat gwalo.
Ƙwafa Saudat ta yi, kafin a hankali ta furta,
"Da ni kike zance"
Tsawon mintina goma ba abin da suke yi sai faman kaiwa junansu harara. Ammi tana jingine da jikin kujer har bacci ya soma ɗibanta.
Dr.Jawad ne ya shigo bakinsa ɗauke da sallama.Jin sallama ne ya sanya Ammi motsawa daga baccin da ya soma a rangama da ita.
Gaisawa suka sake yi.Cikin salon ƙwarewa irin nasa na aiki ya shiga sake duba ƙafar Ramlat ɗin.
Magunguna ya umarceta da ta sha in ta kammala cin abincin yana mai ficewa daga ɗakin.
Sa'ilin da ta kammala ta fake idon Ammi ta soma baccin ƙarya Ganin haka ya sanya Saudat buɗe murya da ƙarfi tare da furta,
"Lah! ki ka kwanta ba ki sha maganin ba.?"
Sai a lokacin Ammi ta lura da hakan. Kallon Ramlat ta yi ka na ta ce,
"Ƴa ta tashi ki sha maganin ma na ko ba kyaso ki warke da wuri.?"
Buɗe idanuwanta ta yi a hankali ta marairaice fuska kamar ƙaramar yarinta ta soma faɗin,
"Ammi ai na warke yasin."
Ammi ta matso kusa da ita sosai ta ɗauki magungunan ta soma ɓallo mata dan ta sh.
"Ammi wallahi na warke,dan Allah ka da ki bani wannan abun.'
Caraf Saudat ta cafe da faɗin,
"Ta ina ki ka warke ɗin, salon anjima ki damu mutane da ihun ciwo-ciwo. Ammi wallahi in ba za ta sha ba ki kirawo yaya kawai."
"Haka ma za ayi "
Ammi ta ce.
Jin maganar Ammi ya sanya Ramlat ƙara haɗe fuska da sake marairaicewa harda haɗa hannaye wahe guda ka na ta ce,
"Dan Sayyadis-sadati Ammi ki yi min rai, wallahi maganin nan ba daɗi ko kaɗan in na sha amai zan yi "
"To ai daman shi maganin ba dan daɗi ake sha ba sai dan neman lafiya. Ammi wallahi kada ma ki tsaya tausaya mata ki kirawo yata kawai in dai ba so ki ke ta zama gurguwa gaba ɗaya ba kinga muma mun huta ai da fitina."
Saudat ta ce tana mai yiwa Ramlat gwalo.
"Kin ga kirawo min shi kawai Saudat." Ammi ta furta.
Cikin ƴan sakanni Saudat ta soma kiran layin wayarsa. Yana ɗagawa ta shiga rattaba masa saƙon Ammi.
Mamman da ke zaune office ɗin Dr Jawad ya ja tsaki kafin ya miƙe.
Dr.Jawad ya kalleshi da mamakin tsakin kafin ya ce,
"Me ya faru kuma sarkin tsaki.?"
Harara ya jefa masa kafin daga bisa ni ya furta, "Zanje kiran Ammi ne tare da ɗaukar wani babban mataki."
Taɓe baki Dr.Jawad ya yi ka na ya ce,
"Allah ya bada sa'a."
Ficewa Mamman ya yi daga office ɗin ya nufi ɗakin da Ramlat ke kwance.
Ku yi haƙuri yau sai a slow na ke jina.