MATAR MAMMAN.

Twenty two

by @maikosai53

Page 43-44.


Ya na isa ya tadda Ammi na kiciniya da Ramlat wajen cusa mata magani a baki.Sororo ya bi Ramlat da kallon mamaki a fusace ya ƙarasa shiga ciki.

"Mene ne haka kuma Ammi.?"

Jin muryarsa ya sanya Ammi dakatawa tare da kallonsa ka na ta ce,

"Ka gantanan tun ɗazu na ke fama da ita ta sha taƙi.'

Kallon Ramlat ya yi fuska a haɗe tare da furta,

"Karɓi ki sha."

Ta marairaice fuska gami da furta,

"Wallahi ɗac.........."

"Dalla malama karɓi ki sha ko na tattakaki a nan wajen wallahi ba ruwa na da rashin lafiyarki."

Ya ce cikin daka tsawa.

A tsorace ta amshi maganin da babu shiri ta antaya a baki ta haɗiye ko ruwa babu ji ka ke maƙuuuut.

"Ko kefa." Ammi ta ce tana shafa bayan Ramlat ɗin.

Ramlat kuwa baƙin ciki ne fal cunkushe cikin zuciyarta. Wai yau ita ce ake yiwa tsawa gaban Ammi amma ta gaza furta ko da uffan ce. Kenan ta daina sonta?" Ta tambayi kanta cikin zuciyarta.

"Ammi ina ga kawai a sallameta mu wuce gida zai fi kyau ta yi jinyar a can." Mamman ya ce.

"A'a Mamman barta a nan ka santa har yanzu ba hankali a nan za ta fi tsayawa wajen bada gudunmawar ganin lafiyarta ta ɗore, amma in an koma gida kaima kan ka kasan akwai matsala."

Ya ɗan numfasa kaɗan kana ya ce, "Hakane shi kenan Ammi Allah ya sawwaƙe."

Da "Ameen" Ammi ta bi shi da shi.

Baibi ta kanta ba ya fice daga ɗakin.

Tun da abin ya faru Saudat ke ƙunshe da dariyarta ai kam yana barin ɗakin ta ƙyalƙyale da dariya tana mai nuna Ramlat da ɗan yatsa.

"Kin ga ni ko Ammi, kin ga ko tana yi mini dariya."

Ramlat ta ce.

Itama Ammin gimtse dariyarta ta yi gudun samun matsala kana ta ce,

"Mene ne haka Saudat? Ba na so."

Saudat ta kuma gimtse dariyarta kafin ta ce, "Babu komai Ammi na daina."

Ammi ta matsa kusa da Ramlat tare da faɗin, "Yanzu me ki keso ƴa ta.?"

Kauda kai Ramlat ta yi, tare da cono baki ita ala dole ta yi fushi da Ammi akan ta sa an mata tsawa kuma an ba ta magani ta sha.

 Saudat ta kuma kwashewa da dariya ,musamman da idanuwanta suka haska mata yadda Ramlat ta turo baki gaba sai ka ce dogowar sakata.Ita kam oganniyar haɗe fuska ta yi kamar an bayyana mata saƙon mutuwa. Ammi dai rarrashinta ta ke yi kamar ƙwan da ba asan fasa shi. Da wannan damar ta samu ta riƙa zuba taɓararta san ranta.

Da yamma Aunty Rahma ta kuma dawo wa asibitin dan sake ganin jikin Ramlat ɗin.

A yadda ta iske ta sai kawai ta bawa Ammi shawarar a sallamesu su koma gida.

Jin hakan ya sanya mara lafiya turo baki tare da lafewa kan gadon.

Ammi kawai murmushi ta yi ganin yadda ta lafe kamar mage.

Wasa-wasa sai da Ramlat ta shafe sati biyu a asibitin tana jinyar jikinta.Abubuwa da yawa suka faru ,shagwaɓa, san jiki da ƙiriniya suka sake nunkuwa a wajenta.

Abi ya dawo ya iske halin da ta ke ciki, zo kuga taɓara wajen Ramlat, shi kam Abi ya biye mata duk abin da ta ce tana so yi mata ya ke yi.

Wata guda ta ɗauka tana jinya cikin hukuncin Allah ta soma samun sauƙi dan yanzu har tafiya tana iya yi babu abin dogarawa saɓanin da da take dogara sanda.

Ramlat an nutsu sosai ganin yadda take fama da ƙafa ,amma dai san jiki da shagwaɓa ba ta rage ko da da ƙwayar zarra ba.

Duk da rashin ƙafar ta kan yi ƴar tsama da Saudat ko da Mamman duk da yanzu shakkarsa ta ke yi musamman in ta tuna rinin muguntar da ya mata duk kuwa da ciwon dake jikinta.

Wata rana ne tana zaune tana shagwaɓa ya shigo ,ganinsa bai saka ta nutsu ba sai ma ƙara abin da ya zo mata.

Wani kallo ya watsa mata, maimakon ta ja jiki ta rungumi sori sai ma ta kuma narkewa jikin Ammi tare da masa gwalo.

Hakan ya fusata shi har sai da ya saka ƙafa ya take ɗan yatsan ƙafar da ke mata ciwon, wanda sai da taga giftawar taurari.

Ammi ta san yi ta yi ba dai-dai shiyasa ba ta tanka musu ba, kuma daman ta jima da dawo wa daga rakiyar ta.


Mai ƙosai.