Twenty four
by @maikosai53
Page 47-48.
Lokacin da ya ji batun daga bakin malamin ya yi matuƙar ƙuluwa jin yadda ita ba ma karatu ne ya kaita ba soyayya ce shiyasa ta daƙiƙance kenan? Har nawa ta ke ma da za ta tsaya yin soyayya,? Me ta sa ni game da batun soyayya.? Ya ji wani abu ya tokare maƙoshinsa.
Yana fushi ya shiga gidan tana ɗaki kwance ta yi shaɓe-shaɓe da ita ta ji saukar belt a bayanta.
Ihu ta saka tana neman maɓoya,sai da ya tabba tar nan gaba aka ce ta yi soyayya ba za ta yi ba ,bayan ya gaya mata laifinta ya kuma sanar mata da aurar da ita zai yi ga wani kuturu da ya gani a bakin titi.
Kuka ta ke yi sosai kamar ranta zai fita, me ya sa ba zai ƙyaleta ta yi rayuwarta yadda take so ba? Me ya sa ba zai ƙyaleta ta aure wanda ranta ya ke so ba? Wallahi muddin ya mata haka to kashe kanta za ta yi, tana jin ba za ta iya zama da kowa ba in dai ba Malam ba.
Mamman ya samu Ammi da maganar sosai hankalinta ya tashi, ƴarta ta ce take soyayya har da sakawa a zo neman izinin aurenta? Lallai lokaci ya yi da fallasuwar abin da ta jima tana ɓoyewa cikin ranta.
Zama suka yi ita da Abi suka ƙulla wacca za su ƙulla dan takanas suka je Azare wajen kakale tare da rangaɗa mata abin da ke wakana.
Itama ta basu goyan baya ɗari bisa ɗari daman ita ta gaji da yadda ake ta cukwikwiye abin.
Ba wanda ta yasan me suke kimtsawa daga su sai Allah.Ramlat kuwa jin shiru har yanzu ba a kira malam ba ya sa ta daina kula kowa a gidan, da yake ya ce mata "Ance za a neme shi."
Duk da sukan sha wayarsu ta soyayaya yana mai kuma ba ta tabbacin cewa za a nemeshin, amma hankalinta bai kwanta ba tana jin kamar yayan na ta zai aikata mata abin da ya faɗa.
Wata biyu da faruwar lamarin, Ammi ta sakata a gaba cike da nasiha kala-kala kafin ta sako mata zancen aure.
Ta miƙe a razane tare da dafe kanta ka na ta ce,
"Ammi aure kuma? Aure da wa? Dan Allah in dai ba da malam ba ne ba na so in ba haka ba wallahi sai na kashe kaina."
Ammi zuciyarta ta soso sosai cikin zafin rai ta ce,
"Ki mutu mana dan ubanki, in kin ga dama kada ki kai lokacin auren kuma ba da shi ba ne sai ranar da aka kai ke kya ga kowane ne."
tana gama faɗa mata haka ta fice daga ɗakin gaba ɗaya.
Ramlat kuwa ranar yini ta yi tana kuka taƙi cin abinci, ko da suka yi waya da malam ta sanar masa sa abin da ke faruwa haƙuri ya shiga ba ta tare da kwantar mata da hankali da ba ta tabbacin in sha Allahu za su yi aure.
Wannan ya sa hankalinta ya ɗan kwanta har ta samu ta ci abinci a wannan daren, wanda rabin cin abincin tana yi ta ma waya da malam da ya ke kasheta da ruwan kalamai ma su zafi.
A cikin sati biyu da maganar a ka saka rana in da aka tsayar da biki nan da wata ɗaya mai zuwa in sha Allahu.
Ammi da sauran mutan gidan suka soma shiri ba ji-ba-gani wanda bikin za a haɗa shi da na Aunty Rahma.
Kowa murna ya ke yi in ka cire Ramlat da duk ta rame ta yi wani iri da ita.
Hankalinta bai kuma ta shi ba sai da ta wayi gari in ta kira wayar malam ba ta tafiya kwana biyun a kashe a ke ce mata.
Duk hanyar da za ta bi wajen ganin ta same shi abu ya ci tura. Ko da Haulat ta zo ma ta gaya mata abin da ke faruwa kwantar mata da hankali ta riƙa yi amma ina ita sam ta tsohe kunnuwanta ba ta jin kowanne kira.
Duk abin nan da ake yi Ramlat na nata sabgoginta ,hankalintana kan ganin yadda za ta sami damar ganawa da Malam, amma duk in da ta ɓulla sai ta ga ko'ina a toshe ya ke. Duk da hakan ba ta yanke ƙauna ba, tana nan tana kimtsa yadda za ta isa izuwa gareshi.
Mamman kuwa shi ma ba a barshi ba ya ba, dan shi ma shiri ya ke yi sosai na bikin ƙannen na sa guda biyu, ba bikin da ya fi murna da shi irin na Ramlat ,cewarsa za su rabu da alaƙaƙai.
Cikin sati ɗayan da ya rage su kakale su ka iso garin ita da Ahmad, Ammi kuwa kullum sai ta kai amaren gidan gyaran jiki da kanta. Hakanan duk abin da ya kamata ace uwa ta yiwa yaranta wajen ganin ta inganta zaman aurensu ƙoƙarin yin sa ta ke yi.
Ita kuwa duk abin da Ammi ke musu ta ce,"Jin sa kawai ta ke yi". wai ya shiga ta dama ya fita ta hagu Amma muddin ba a aura mata Malam ba to kashe kanta za ta yi kowa ya rasa.