MATAR MAMMAN.

Twenty five

by @maikosai53

Page 49-50.


Ranar da ya kasance ita ce mafi soyowar farin ciki acikin zuƙatan mutanen gidan, ita ce ranar da tafi ƙololuwar baƙin ciki a cikin zuciyar Ramlat. Wannan rana ta kasance ranar da aka ɗaura aurenta da Mammman ,sanarwar ya yi dai-dai da sumanta a ƙasa numfshinta ya ɗauke cak.

Mamman kuwa ba wanda ya kai shi kiɗimewa duk da shi daman ya san cewa ita ɗin ƴar uwace gareshi ba ƙanwa da suke uwa ɗaya uba ɗaya ba, amma bai taɓa tunanin wannan ɗanyan hukuncin daga wajen iyayen na sa ba harda kakale, yasan ma wataƙila ita ce ginshiƙin samar da maganar har ga shi an zantar da ita.

Mai zai yi da kucakar yarinya ƙarama wacca ba ta kai ga yadda zai sarrafata yadda yaransa ke so ba, hasalima shi kallon ƙanwa ya ke mata ko kaɗan bai tunanin zai iya aurenta balle ya zauna da ita amma wai sai ga shi su Ammi sun masa abin da ya juyar masa da lissafinsa, shi sam aure ma baya gabansa a yanzu.

Kakale kam ji ta ke kamar ta zuba ruwa a ƙasa ta sha, faɗi ta ke "Ku ƙyale ja'ira za ta farka ne , duk suman daɗi ne."

Su Ammi da Aunty Rahma kuwa ba su bi takan zancenta ba suka ɗauke ta zuwa asibiti, ko da Ammi ta kira Mamman ƙin ɗaukar wayar ya yi.

An karɓi Ramlat ciki kulawa ta irin likitoci, duk yadda su ka so ga ƙoƙarinsu na san ta farfaɗo sai da su ka tabbar da haka. Lokacin da ta farfaɗo ihu ta ke yi da zunduma kuka ita a kan lallai sai an raba ta da ƙaya, lallai ita sai an haɗa aurenta da malam, wanda har yasa Ammi ta ce a mata allurar barci.

Kiran Mamman ta kuma yi a karo na ba adadi har wayar ta kusa tsinkewa ya ɗaga, cikin faɗa ta ce,

 "Wato ga sa'arka tana kira ka na ƙin amsawa ko? Ma za ka zo asibiti ina jiranka ka da ka haura ko da minti biyar ne." tana ƙarasawa ta katse kiran sanin cewar ta san ya san asibitin ba sai ta yi masa ƙarin bayani ba.

Ko kaɗan ba ya san damuwar Ammi, fushinta ko ɓacin ranta, ba shiri ya miƙe ya canza kaya zuwa masu ɗan sauƙi ya fita amma zuciyarsa sai harbawa ta ke yi bai san dalili ba.

Yana isa ya iske su tsaitsaye, Ammi tana shafa fuskar Ramlat ka na ta kalli Mamamn ta ce,

 "Ga ƴa tanan ka kula min da ita, idan ka mata wani abu kuma ni da kai ne. Ka tuna shi aure ba wasa ba ne, kuma aure ibada ce ta Allah subhanahu wata'ala."

tana gama faɗin haka ta yiwa su Aunty Rahma alamun su tafi.

Shi kam bin ta kawai da ido ya ke yi har ta fice daga ɗakin, a hankali ya dawo da kallonsa ga Ramlat da ke kwance saman gadon tana barci abin ta.

Tsaki ya ja kafin ya ce,

"Sokuwa duk kan auren ne haka? To an gaya miki ni ma ra'ayin irinki na ke yi?"

Ya ja kujera ya zaune ya fidda wayarsa ya buɗe data, saƙonni su ka shigo masa rututu ta ɓangaren manhajar whatsapp da facebook kuma duk na ta ya shi murnar auren sa ne. Mamaki ya cika shi ta ya aka yi friend na shi su ka sa ni, ashe wai Dr.Jawad ne ya yi masa wannan ɗanyen aiki, ya watsa katin da hoton ranar ɗaurin auren kafar sadarwar.

 "Shasha-sha." Ya faɗa ya na taɓe bakinsa.

Su Ammi kam ko da suka isa gida kai tsaye ɓangaren Kakale ta wuce nan suka ci gaba da tataunawa kan lamarin, ya yin da Kakale ke kwantar mata da hankali akan Allah zai dubi lamarin tun da da niyyar alheri suka yi.

Su Aunty Rahma kuwa kowa da irin ta shi tambayr maƙale cikin zuƙatansu.

A asibiti kuwa Ramlat ta farka da kuka ,cikin kukan take furta kalaman da suka ƙona ran Mamman wanda cikin ƙunar rai ya soma faɗin,

"Dalla malama rufemin dagargajajjen bakin ki, an gaya miki kin kai mizanin da zan zauna dake ,na yi soyayya dake, na yi rayuwar aure da ke, da har za ki zo ki na gayawa mutane mahaukatan kalmominki."

Jin muryarsa cikin dodon kunnuwanta ya saka ta jin wani iri, ta rumtse idanuwa tana mai ɗan turo baki.

Mamman kam bin bakin ya ke da kallo, ya na mai jinjina jarumartar rashin kunyarta ,ga tsoro amma ga fitina, gadon asibitin ma da take kwance kansa ba za ta saduda ba.

Ficewa ya yi daga ɗakin ya tafi neman likita dan ya kuma duba ta, ya yi rantsuwa a ransa muddin lafiyarta ƙalau to zai saka a ba ta sallama, dan ba zai iya zaman jinyar wannan abar ba.

Tun a office ɗin likitan suka gama shirya jadawalin yadda lamarin zai kasance. Ilai kuwa da ya duba ta ya tabbatar ba wata damuwa nan take ya rubuta mata sallama.

A hankali take taka ƙafafuwanta, sai faman rumtse idanuwa take yi har ta isa bakin motar, gidan gaba ya buɗe mata ta shiga shi ma ya shiga mazaunin direba ya ja motar suka fice daga asibitin.

San da suka isa kowa yana falo har da Abi dukkansu. Da sauri Ammi ta taso ta tareta tare da riƙo mata hannu ta zaunar da ita kan kujerar.

Shi ma ƙarasawa ya yi ya zauna kan ɗaya daga cikin kujerun. Ya sake gaishe da iyayen na sa da kakarsa. Cikin fara'a kakale ta ce,

 "An gaida ango, ka ga shi kenan na yi maka maganin tuzurancinka."

Mamman ya taɓe baki gami da ɗan haɗe fuska kan ya ce,

 "Ki dai soma magance taki tukunna."

"Ka jimin ja'irin yaro, dan tsohonka ba fama ka ke da shi ba, sai faman wani raɓe-raɓe ka ke yi kamar ƙadangaren da ya maƙale jikin katanga."

Gaba ɗayansu suka kwashe da dariya ciki har da uwar ƙiriniya.

Bayan an lafa ne Abi ya soma magana kamar haka.

"Da fari muna baiwa mutane biyu haƙuri wato; Mammmn da Ramlat. Ba dan komai ba sai na shiga haƙƙinsu da mu ka yi ba tare da munji ra'ayin kowa ba. A bin ya samo asali ne tun sa'ilin da mahaifin ita Ramlat ɗin ya ke kan ganiyar mutuwarsa ya yin da ya roƙemu alafarmar dan Allah mu kula masa da ƴar sa sannan mu damƙata gareka kai Mamman ma'ana mu baka aurenta ya san ko babu komai za ka riƙe masa ƴa da amana za ka kula da ita sosai. Ke kuma ya ce ya san ba za ki taɓa watsa masa ƙasa a ido ba, za ki amince da wannan zaɓin na sa. Wannan ne dalilin da ya sa san da kai ka zowa mahaifiyarka da maganar tsayawarta da wani sai abin ya tashi hankalinmu, sosai mu ka shiga ɗimuwa sai kawai mu ka yanke shawarar a yi bikin kusa, a haɗa shi da na ƴar uwarku tun da abin ya matso. Shi kuma malamin har gida na je na same shi na ba shi haƙuri tare da gaya masa dalilinmu na hana shi, amma na masa alƙawarin muddin yana san zuri'armu to ga yayartanan."

Ya nuna Saudat, kana ya ɗora da faɗin,

 "Sosai ya yaba da hakan ,kuma ya yi amanna, amma ya bamu tsaikon a ɗan ƙara masa lokaci zuwa shekara ɗaya sannan ya kammala komai, na ce masa ya zo ya same ki ku dai-daita ko ya zo Allahu a'alam?."

Ya ɗan tsahirta kaɗan, kafin ya ɗora.

 "Mu na sake baku haƙuri a karo na biyu, kuma muna fata za ku cika farin cikin iyayenku dan muma muna san wannan auren musamman Kaka." Ya nuna kaka da har a lokacin bakinta cike da fara'a.

Ramlat ta sauke a jjiyar zuciya tana jin wani iri, ita abin da ba ta gamsu da shi ba kenan Ammi ba ita ce mahaifiyarta ba kenan? to wacece?

"Ammi kina mufin ke ba Ammi ta ba ce kenan, kina nufin ni ba jinin ki ba ce?" Ta ƙarasa cike da rushewa da kuka.

A hankali Ammi ta saka hannunta ta soma shafa bayanta cikin san kwantar ma ta da hankali ta ce.