MATAR MAMMAN.

Twenty six

by @maikosai53

 51-52

"Tabbas ni ba mahaifiya ce a gareki ba wacca ta fito da ke daga tsatsonta, amma ni mahaifiyace gareki wacca ta raineki tun kina jaririya sannan kuma wacca ta ke muradinki cikin ranta, mafi soyuwa gareta fiye da na ta ƴaƴan da ta haifa. Ina sanki ƴata zan iya komai a kan ki muddin bai saɓawa shari'ar musulunci ba. Amma idan har ba kya san auren na yi miki alƙawari ba wanda zai tursasa ki zauna da shi a yau ɗin nan , a yanzun nan zan saka ya sake ki."

"Ta yaya ma za ta iya haka ga Amminta mafi soyuwarta? , ba za ta taɓa yarda ta watsa mata ƙasa a ido ba ko da kuwa ba ta san shi to za ta zauna da shi har ajalinta ya risketa. Ammin da ta sota fiye da kanta, ta raine ta ,ta juri duk wata ƙiriniya ta ta, ina sam ba zai yiwu ba." Ta furta hakan cikin ƙasan zuciyarta.

Ba ta iya dogowar magana ba sai dai kalmomi uku kawai da iya faɗa "Na amince Ammi."

Ammi ta janyota jikinta tana mai kuma dukan bayanta kaɗan-kaɗan.

"To kai muke jira." Abi ya watsowa Mamman maganar.

Mamman ya ɗan sosa kai kafin ya ce,

"Na amince."

Kowa murma ya ke yi cikinsu, Ahmad kuwa ji ya ke kamar ya rungumi mutuniyar ta sa dan taya ta murna.

Nan kakale ta kuma yi musu nasiha mai ratsa jiki ,da gaya musu irin girma da matsayin da aure ya ke da shi.

Jikinsu ya yi sanyi sosai ba ma ya Ramlat.

"Anjima kowacce za a miƙata gidan mijinta dan haka inawa kowa fatan alheri, Allah ya haɗa kawunan ku." Ammi ta ce.

Nan Abi ya kuma yi musu ta sa ƴar nasihar kafin ya sallami kowa.

Mamman ne ya soma miƙewa ,sannan su ma suka take masa baya. Ramlat na shiga ɗaki ta kife kan gado tare da sakin wani marayen kuka, "Daman ita ba ƴar Ammi ba ce, ashe ita ɗin marainiya ce? " Ta shiga tambayar kanta da kanta.

Saudat ce ta shigo ɗakin bakinta ɗauke da sallama, ganinta kwance tana kuka ya saka ta dosar inda take tare da furta,

"Mene ne na kukan to,? Me ya faru kuma?"

Ta ɗago a hankali fuskar nan shaɓe-shaɓe da ruwan hawaye duk ta jagwale, cikin muryar kuka ta ce,

"Shi kenan ba ni da iyaye ko? Ni da man marainiya ce? Ashe Ammi ba ita ce mahaifiyata ba.?" Ta watso mata tambayoyin.

Saudat ta ja tsaki kafin ta ce,

"To mene ne a ciki? Wani abin ki ka rasa ?,Iyaye ne ki na da su har biyu sai kuma kaka guda ɗaya, to mene ne abin damuwa ,tabbas na san rashin iyaye akwai sosowa cikin rai amma ki tuna Allahn da ya fi mu san su shi ne ya amshi kayansa, ni wallahi na za ta ma kan aurenki da yaya ki ke kukan?" 

Ramlat ta goge hawayen kan fuskarta, kafin ta ja tsaki gami da furta,

"Ni ko a kwalar rigata wallahi, can ta matse masa ya yi kiɗansa ya yi rawarasa, damuwata ɗaya ban taso da iyayena ba, ban san su ba ban yi rayuwa tare da su ba."

Saudat ta tuntsire da dariya kafin ta ce,

 "Au ko a kwalarki ko? Lallai ma wuyanki ya isa yanka, bari na je na sanar da su Ammi abin da ki ka ce." Ta ƙarasa tana mai miƙewa dan aiwatar da abin da ta faɗa.

Da sauri Ramlat ta riƙota fuska a haɗe ta ce, "Ni daɗina da ke har yanzu duhun kai, wallahi auren nan sam baya gabana yanzu, a da na damu da rashin malam amma a yanzu zan iya yin komai kodan cikar muradin iyaye na, amma ba hakan yana nufin wai ina san shi ba, har a bada bazan so shi ba kamar yadda shi ma ba ya so na."

Saudat ta dafa kafaɗunta ka na ta ce,

"Ba namijin da zai ganki ya ce ba ya so wannan ma ganganci ya kewa kansa, ke ko da a ce muninki ya kai na gwaggwon Biri to muddin kin iya yadda ake siye zuciyar maza to za ki siye ta sa, abu biyu zan ce miki shi ne; Ki riƙe addu'a, sannan ki zama mai biyayya garesa to ko da ba ya sanki wata rana tabbas zai so ki ni na faɗa miki wannan."

Ramlat ta sauke ajjiyar zuciya ba ta iya furta mata komai ba ta kifa kan gadon tare da yin zugum. Ita kam ci gaba da ɗan nasihohin da ke kwanyarta ta riƙa mata. 

Sai bayan magrib Ammi ta shigo saman ta tadda ta tana barci, a hankali ta soma tashinta, bayan ta farka ta umarceta da ta shiga ta yi wanka ruwa na jiranta a bayi.

Bayan ta fito ta shiga shiryata, tare da ba ta wani maganin sanyi ta kuma sha, sai kuma haɗin kankana da ya ji ingantacciyar madara.

Ammi ce ta shiryata tsaf ,wayyo! Zo kuga Ramlat kamar ba ita ba. Duk wanda ya ganta sai ya yaba, Saudat kam da Ahmad sai tsokanarta suke yi.

Bayan komai ya kammala aka kuma tara su a falo tare da jeranta musu wasu nasihohin masu kama zuciya da tsuma jiki. Abi kam sai jawa Mamman kunne ya ke a kan ya kula masa da ƴa, Ammi kam wajen masa kashe di ai ba a magana.

Nan Abi ya ta sasu zuwa ɗakinsu, Aunty Rahma ya fara miƙawa da kansa ba rakiyar kowa sannan ya kai Ramlat na ta gidan da ba su da ta zara mai yawa.

Sai da ya tabbatar Mamman ya zo sannan ya bar gidan bayan ya kuma yi musu nasiha.

Tun da Abi ya fita take zaune kan kujera mai cin mutum ɗaya, ba abin da take yi sai kuka yau ga shi an raba ta da Amminta, yau ba za ta kwana da ita ba. Ta kuma fashewa da wani sabon kukan.

Mamman da ke ta latse-latsen waya jin muryartana amon kuka ya tsayar da abin da ya ke yi ya fuskance ta sosai kana ya ce.


Mai ƙosai.