Twenty eight
by @maikosai53
55&56
*FIRST CLASA WRITERA ASS.*
"Yanzu kina nufin in na mutu wuta zan tafi kai tsaye? Amma ni banji malaman makarantarmu na faɗa ba, kodai sharrin ki ne Yaya Saudat.?" Ta ƙarasa tana kafeta da idanuwa.
Saudat ta ɗan yi guntun murmushi kafin ta ce,
"Sharri kuma sai ka ce wata ke, gaskiya na ke faɗa miki saboda ke ai ba ki je ajin da za ki ji hakan ba.In kina son gasgata zance na ki mutu akan hakan kiga ni ko ƙarya nake yi miki. Ni dai shawarata ɗaya wallahi kada ki kuskura ki rasa wannan damar da Allah ya baki dan in ta wuce ta wuce ba kuma za ki sami wacca takaita ba. Ki riƙi mijinki hannu bibiyu, ki yi masa biyayya ko da zuciyarki ba ta so,ki ƙauna ce shi ko da bakya so,ki saka shi farin ciki ko da naki ran zai ɓaci shi ne kawai ƴar ƙaramar nashita gareki zamu iya kwana ina gaya miki haƙƙin miji akan matarsa kema nasan kin san wasu, Manzan Allah da kansa ya ce da zan umarci ɗayanku ya yiwa wani sujjada da na saka mata ta yiwa mijinta sujjada kinga kuwa miji yana da matuƙar falala da tasiri cikin rayuwar ƴa mace. Dan Allah ki nutsu ki yi min alƙawarin babu abin da zai haɗaki da yaya wanda bai kamata ba. A yanzu kin girma Ramlat ke ba yarinya ba ce kada ki bari ki kuma rasa damarmakin da kika rasa a baya lokacin da kika riƙa wasa da lokotanki wanda a yanzu ba zasu taɓa dawowa ba."
Ramlat ta yi jugum tana saurarenta, cikin zuciyarta na ayyana mata abubuwa da yawa; tabi shawarar Saudat ,kai amma in ya mata ba daɗi fa sai ta haƙura ya ci bulus kenan? Ina da sake.
Jin shirun ya yi yawa ya saka Saudat faɗin,
"Kada ki manta burin iyayenmu ne mu girma su aurar damu, wannan shi ne babban farin cikinsu,da kwanciyar hankalinsu sa'ilin da mace ta taso ta balaga ta kai munzalin aure shi ne su aurar da ita ga miji na ƙwarai wanda zai tsaya mata ya tallafi rayuwarta, kullum hankalinsu a tashe ya ke har sai sun aurar da ita. Ke yanzu me yafi miki wannan daɗi abu biyu sun cika na farko burin iyaynki na san haɗaki da yaya, na biyu burin su Ammi na san ganin sun cika alƙawari kuma sun kau dake daga gabansu zuwa ɗakin mijjnki na ƙwarai. Me ya rage miki wanda ya wuce ki yi ƙoƙarin faranta musu, ita ce hanya mafi daɗi da zasu san cewa lallai sun haifi ƴa ta gari mai san ganin farin cikinsu. Ni dai gareki dabara ta rage gamai shiga rijiya."
Ramlat ta share hawayen da ke shimfiɗe saman kumatunta dalilin ambatar iyayenta da Saudat ta yi, sosai ta mata fami a gyamɓon ranta.
Ta kamo hannun Saudat ta cusa nata ciki gami da furta,
"Na yi miki alƙawari Yaya Saudat ba zan taɓa baɗawa iyayena huɗu ƙasa a cikin idanuwansu, na yi miki alƙawarin zama da yaya duk rintse duk wuya da daɗi na yi miki alƙawari dan Allah kada ki gayawa kowa halin da muke ciki ni da kaina zan gyara na yi miki wannan alƙawarin."
Saudat ta damƙe hannunta sosai tana mai shafa kanta kafin ta ce,
"Na yi miki wannan alƙawarin kuma in kika yi hakan kin gama komai cikin ran ahlinki. Allah ya haɗa kawunanku ya sakawa yaya soyayyarki fiye da tunanin mai tunani."
Ta yi murmushi tana mai ɗan ɓoye fuskarta da tafin hannunta .
"Munafuka, to ba sai na fasa addu'ar ba. Yaya yana sanki kawai dai fitowa ne ya gaya miki ba zai yi ba saboda gudun kada ki raina shi, amma ni na gaya miki yana sanki, za ki gane hakan idan ki ka bishi sau da ƙafa." Saudat ta ce.
Sun jima suna shan hirarsu wacca rabinta kan yadda Ramlat za ta saito gidan aurenta ne, dan sosai Saudat ke fayyace mata abubuwa da yawa tana mai kuma nusar da ita akan abubuwa da yawa na zamantakewar rayuwar aurenta.
Ba ta bar gidanba sai da ta tasa Ramlat gaba ta yi wanka, ta zaɓa mata kaya marasa nauyi ta saka, ta fesheta da turaruka masu daɗin ƙamshi sai humrori da su kwalakca da mulketa da su, hatta da girki sai da ta yi mata wanda ta tabba tar Mamman na san cimar sannan tabar gidan bayan ta koya mata wasu dabaru kala-kala.
ba ta jima da tafiya ba Mamman ya shigo bakinsa ɗauke da sallama. Ramlat na ɗakinta wanda Saudat ta nuna mata shi tana mai karanta wani littafin addini ta jiyo sallamarsa.
Zama ya yi kan ɗaya daga cikin kujerun falon yana mai bin ko'ina da kallo ga wani sihirtaccen ƙamshi na ta shi cikin gidan.
Kamar ba za ta sakko ba haka take ji, dan ita kunya take ta fita ya ganta da kayan jikinta. Sai kawai ta tsinci kanta da jin kunyarsa, ƙarfin hali ta yi irin na ɓarawo ta yi shahada ta fice daga ɗakin bayan ta ajjiye littafin. Kai tsaye ɗakinsa ta wuce ta shiga bayi ta haɗa masa ruwan wanka kamar yadda Saudat ta umarce ta.
Yana zaune kamar wanda aka tsikare shi ya miƙe zuwa ɗakin na sa. Yana shiga tana fotowa daga bayin tana mai yarfe hannayenta.
Kallonta ya ke tundaga sama har ƙasa,ji ta yi kamar ana kallonta hakan ya sakata bin inda take zargi da kallo tsaye yake ya harɗe hannayensa biyu kan faffaɗan ƙirjinsa ya na mai bin ta da kallo.
Gefanshi ta raɓa danɗan sauri za ta wuce. Lumshe idanuwansa ya yi yana mai hura hanci tare da shaƙar ƙamshin dake tattare da ita. Daf da za ta fita ya saka hannunsa ɗaya ya fizgota ta faɗo kan jikinsa. Ƙoƙarin ƙwace kanta ta ke yi amma ta kasa ,shi kuwa sai faman shinshinarta ya ke yi yana mai sake hura ƙofofin hancinsa yana shaƙar ƙamshin jikinta. Da ƙyar ta fizge jikinta tana mai furta,
"Akwai ruwan wanka a ciki." Ta yi saurin buɗe ƙofar ɗakin ta fice. Sai lokacin ya dawo cikin hayyacinsa daga duniyar da ya lula. Tsaki ya ja yana mai ƙarasawa ciki.
Ya ajjiye agogon hannunsa da hularsa bayan ya cire takalmin ƙafarsa ya wuce bayin.
Ƙamasin dake tashi ciki ya hanashi fitowar da ya yi niyya bai san lokacin da ya saki wani ƙayataccen murmushi yana mai jin wata iriyar annushuwa na rasa duka sassan jikinsa.
Mai ƙosai.