MATAR MAMMAN.

Twenty nine

by @maikosai53

 57&58

Ya jima a ciki yana mai fancala wankansa san ransa.

Ramlat kuwa tana ƙarasawa ɗaki ta faɗa kan gado tana mai lumshe idanuwa gami da sakin ajjiyar zuciya.

 "Kai anya juwa zan iya?" Ta tambayi kanta.

"Me zai hanaki Ramlat? Wannan aurenfa farin cikin iyayenki ne,muradinsu ne. Ba abin da zai gagareki muddin kina tare da Allah,ki cire kunya ki nutsu shifa mijinki ne ki yi masa duk abin da zai saka shi cikin farin ciki." Wani sashi na cikin zuciyarta ke ayyana mata hakan.

Miƙewa ta yi da sauri ta sake gyara jikinta sannan ta fice daga ɗakin. Kai tsaye wajen cin abinci ta nufa ta hau tattara kayan abincin zuwa ɗakinsa.

Sai da ta kammala kai masa komai sannan ta koma nata ɗakin tana mai fata da addu'ar Allah ya sa ya ci abincin.

Shi kam sai da ya kammala shirinsa ka na ya fito,turus ya yi yana mai bin kayan abincin da kallo. Ƙarasawa ya yi ya soma buɗe kwanukan ƙamshin abincin ya karaɗe hancinsa bai shiryawa ci ba amma sai ya tsinci kansa da san ci, nan ya hau zubawa ya soma ci yana ya tsina baki, abin da baifi mintuna ba sai ga Mamman ya gyara zama yana mai ɗurawa cikinsa abinci.

Sanda Saudat ta koma gida ba ƙaramin tambaya tasha wajen Ammi ba akan lafiyar Ramlat. Ita kam murmushi kawai ta yi tana mai tabbatarwa da Ammi komai lafiya.

Ammi ta sauke ajjiyar zuciya tana mai furta,

 "Ubangiji ya haɗa kawunansu. Ina san jin muryar ɗiyata."

Saudat ta ƙyalƙyale da dariya kafin ta ce,

"Ammi to ki kira ta mana."

"A'a ƙyale ni babanku ya hana wai zan takura musu." Ammi ta ce.

"To ai sai kawai ki haƙura Ammi." Ta faɗa tana mai gimtse dariyarta tare da hayewa sama abin ta.

Ammi ta ce,

 "Ja'ira za ki dawo ki sameni ne." Ta shige ɗaki cikin zuciyarta cike fal da tunanin sahibarta.

Saudat na shiga ɗaki ta zaro wayarta ta soma latsa lambar Ramlat. Bugu ɗaya ta ɗaga tana sauke ajjiyar numfshi.

"Malama me ya faru?" Saudat ta watso mata tambayar.

"Hmm! Babu komai, amma ni dai na kasa yaya Saudat."

Sai da ta ja tsaki kafin ta ce,

"Kina nufin ki ce min babu abin da kika aikata cikin abubuwan da na gindaya miki.?"

"A'a yaya Saudat ba haka nake nufi ba, na kasa zuwa tarɓarsa wallahi kunya nake ji, na dai kai masa abinci na baro shi a ɗaki can ya ƙarata.'

"Ramlat" Saudat ta faɗa da wata iriyar murya har sai da Ramlat ɗin ta ɗan tsorata.

"Na rantse zan fita daga sabgoginki, ki yi abin da zuciyarki ke so, amma ki sani duk sanda kika kaso aurenki ki ka fito to sunanki bazawara ragowar kwantai ' tana ida faɗa ta katse kiran ranta a mugun ɓace.

Sosai jikin Ramlat ya yi sanyi, tabbas ta san abin da take gaya mata gaskiya ne, to amma ita yaya za ta yi,tana matuƙar jin kunyarsa fiye da za to ba za ta iya aikata abin da ta saka ta ba. Amma ba ta san fushin yayyenta duk da fitinar da take addabarsu da ita.

A hankali ta soma danna lambar yayarta ta sai da ta kusa tsinkewa sannan ta aka ɗaga.

"Ki yi haƙuri yayata zan aikata duk abin da kika ce dan farin cikinku kawai ke da iyayena ,zan yi saboda soyayyar AMMI cikin ƙahon zuciyata." Ta ƙarasa cike da sakin marayan kuka.

'To mene ne na kukan? Ki tashi ki shirya kamar yadda na ce miki, kada ki tsallake ko da da silin kara ɗaya ne, ki yi haƙuri hakan shi ne dai-dai ƴar uwa,bazan taɓa cutar dake ba, dan Allah kada ki saɓawa umarni na."

"Zan yi yayata, zan yi saboda farin cikinki ." Ta ƙarasa da kashe wayar tana mai cusa kanta cikin cinyoyinta, a hankali ta miƙe ta buɗe wajen ajjiyar kayanta tana hawaye tana zaro kayan da ƙwaƙwalwarta ke raya mata wasu saƙonni kala-kala ciki.

Tofa ko me Saudat ta saka ta ?

Shin za ta iya aikatawa ɗin ko kuwa za ta fasa?

Farin cikin ƴan uwanta ko kuwa nata?

Ku ci gaba da bibiyata cikin littafin MATAR MAMMAN.