Thirty
by @maikosai53
Shafi na 59-60.
A hankali take zira kayan hawaye na malala kan kumatunta. Matsawa ta yi gaban madubi ta shiga mulkawa kanta wani turare da yaya Saudat ɗin ta ba ta ta ce ta goga,sai wata haɗaɗɗiyar humra ta tashiga shafawa kai ka ce mai take shafawa jikinta. Duk abin da take yi tana yi tana hawaye,hannayenta biyu ta ɗora kan madubin ta sunkuyar da kanta tana mai kallon kan madubin ruwan hawayen suna zuba saman kan madubin.
"Ba zan iya ba, ki yafe min yayata." ta faɗa tana haɗiye wani yawu.
Kamar mai aljanu haka ta yi wata iriyar zabura ta saka hannunta ta goge hawayen fuskarta ta fice daga ɗakin bayan ta saka ƙatan hijabi.
Tura ƙofar ta shiga yi a hankali ta saka ƙafafuwanta cikin ɗakin ta soma tafiya saɗaf-saɗaf kamar wata ɓarauniya. Dai-dai wajen kayan abincin da ta ajjiye masa ta ƙarasa,ta saka hannu ta soma buɗe flask ɗin,ga mamakinta sai taga anci fiye da rabi. Ji ta yi kawai ta saki wani ƙayataccen murmushi wani sanyi ya ratsa zuciyarta,ta soma tattara kayan cikin nutsuwa dan kada ya jita.
Yana kwance ya juya baya sanye ya ke da singlet sai wandon da kaɗan ya wuce gwiwa gaɓoɓin jikinsa suka bayyana, yalwatacciyar kyakkyawar fatarsa ta bayyana. Kallo ɗaya ta masa ta kau da kanta ganin yadda gashin jikinsa ya kwanta luf-luf sai kuma ta sake ɗaga idanuwanta ta kalleshi kafin ta saukesu ƙasa tare da sakin ajjiyar zuciya.
Duk abin da take yana jinta ba barci ya ke yi ba,ya so tashi amma sai ya waske ya ga inda za ta dosa.
Rumtsa idanuwanta ta yi ta soma tattara kayan, ba ta yi za tao ba kawai ta ji hannunta ya yar da wani kofi har sai da ya fashe . Ta buɗe idan tana mai zaro su kamar za su faɗo,ta soma kiciniyar yadda za ta gyara wajen, miƙewa ta yi ta shiga bayi ta ɗakko mofa ta dawo ta saka mofar tana sharewa kafin ta tsugunna tana tattara glass ɗin. Bisa tsautsayi wani daga ciki ya caki yatsanta ɗaya da ƙarfi ta saka ihu har sai da ya saka shi juyowa yana mai kallonta.
Ganin yada ta yi wuri-wuri da ido sai kawai ya soma bin fuskarta da kallo, ƙamshin turarenta tun shigowarta ya soma bugar da shi sai ya kuma shiga hancinsa lungu da saƙo yana zagayawa.
Sakkowa ya yi daga kan gadon ya riƙo yatsan nata da take ta kurma ihu a kansa, ga mamakinsa sai yaga ma ba wani ciwo ne mai yawa ba jini kaɗan ne ya soma zuba ,wani hankici ya samu ya samo ruwa ya shiga dannan mata shi yana mai hura iska akan yatsan ,sosai ta ji sanyi na ratsa ɗan yatsan nata.
"Sai shegen kinibibi amma akwai raki." Ya faɗa yana ƙarewa fuskarta kallo. Ita kam sunkuyar da kanta ƙasa ta yi ba ta ce uffan ba.
Miƙar da ita tsaye ya yi, ya zaunar da ita kan gefen gadon ya soma tattara wajen.
Sai da ya gyara shi tsaf ya shiga bayi ya watsa ruwa sannan ya fito, har lokacin tana zaune wajen da ya ajjiyeta.
Wajen adana kaya ya wuce ya soma saka wasu kayan marasa nauyi. Miƙewa ta yi ta soma laluban hanyar fita kamar wata makauniya.
"Dawo ki zauna " Ta tsinkayo muryarsa.
Ba ta jiyo ba , ba ta kuma ƙara gaba ba ta ƙame a wajen.
Sannu-sannu ya taka har in da take, ya saka hannayensa biyu ya tallafota zuwa jikinsa yana mai hura hanci yana sinsinar ƙamshin da ke jikinta. Hannunsa ɗaya ya saka yana zagaya wuyanta da shi ,cak ya ɗauketa ya direta kan gado, ya soma yi mata wasu irin wasanni masu wuyar faɗa.
Ramlat kuwa ji ta yi lamarin ya soma fin ƙarfinta ,take ta ji ƙirjintana bugawa fat-fat ba za to ba tsammani ta ji saukar bakinsa cikin nata. Lokaci guda ya sauya salon da ya ke mata tun tana mutsu-mutsu har ta rissinar da kanta dan ya fi ƙarfinta. A wannan lokacin, a wannan ranar Mamman ya san Ramlat a matsayinta na ɗiya mace.
Kuka ta ke ba ƙaƙƙautawa rarrashin duniya yake mata amma kamar ba da ita ya ke ba.
Tsaki ya ja cikin ransa yana ayyana matsalar yara kenan.
Ficewa ya yi zuwa kitchen dan sama mata ruwan ɗumi, kafin ya dawo barcin wahala ya yi awon gaba da ita. Kallonta kawai ya ke yi yana jin wani nishaɗi na ratsa zuciyarsa hannu ya ɗaga sama yana mai godewa Ubangijin da ya azurtashi da ita.
Gyara mata kwanciyar ya yi, sai dai tunowa da ya yi ba ta gyara jikinta ba ya saka shi wucewa bayi ya soma haɗa mata ruwan ɗumi. Cak ya ɗauketa ya shige bayin da ita, Ramlat na barci ta jita cikin ruwan ɗumi da fari ta so ƙin zama amma jin yadda ruwan ke ratsata sai ta koma ta yi lamo a ciki.
Shi kam komawa ya yi ya shiga gyara wajen. Tas ya gama gyara shi yana shirin komawa ya ji motsinta a bayansa waigawa ya yi yaga yadda take takawa a hankali kamar mai koyan tafiya sai kawai ya ji tausayinta na ratsa sassan jikinsa.
Ita kam Ramlat cikin zuciyarta ba abin da ta ke yi irin tsinewa yaya Saudat duk ita ta ja mata wannan azabar ba ko tausayawa.
Ɗakinta ya wuce dan sama mata suturar sakawa, san da ya dawo ya isketa sai rawar ɗari ta ke yi. Da sauri ya ƙarasa inda take yana mai tallafo kanta zuwa ƙirjinsa.
Sosai ya ji jikinta ya yi zafi, ga shi sai rawar sanyi ta ke yi, shayin da ya haɗo mata tun ɗazu ya ɗakko ya soma ba ta a hankali sai dai kurɓa biyu ta yi ta shiga kwaro masa amai jikinsa.
Hankalin Mamman ya soma tashi kaddai wani abin ne ya faru da ita?, Wayarsa ya ɗauka ya soma kiranq Dr.Jawad.
Har sai da ta kutsa katsewa sannan ya ɗaga.
"Wai kai wani irin gaula ne a yi ta kiranka ka na ji ba za ka amsa ba." Mamman ya faɗa a zafafe.
Sai da dr. Jawad ya yi ƴar dariyar tsokana kana ya ce, "To ai kaine gaula na farko ni na biyu ka manta? Malam mene ne ka ke faman kirana lokacin da na ke tsaka da hutawa da matata."
Da hanzari Mamman ya katse shi ta hanyar faɗin,
"Kar ka kawomin duniyanci ni ma ba wanda ban sani ba yanzu, malam ka hanzarta zuwa matata ba lafiya sai rawar sanyi ta ke yi." Yana ji ya soma masa tsiya ya yi maza ya kashe kiran.
Ramlat kam duk hirarsu tana ji har lokacin da Mamman ya kira ta da matarsa kenan ta tabba ta ita ɗin MATAR MAMMAN ce, da gaske shi ma yana santa.? Sai dai ta rasa mai ba ta amsa, amma tabbas ta ji wani sanyi ya ratsa ƙasan maƙoshinta.
Yana ajjiye wayar ya kuma janyota jikinsa sosai,yana mai shafa kanta a hankali.
Sai da suka ɗau kusan rabin awa kafin dr Jawad ya iso. Da yake ya sanar masa tana zazzaɓi wannan ya sa ya taho da first aid box(Akwatin taimakon gaggawa.) Allura ya soma mata wacca sai da Mamman ya riƙeta sannan a ka yi, ba tafi mintuna ukuba ta soma zufa take wani wahalallen barci ya yi awon gaba da ita.
Kallon Mamman ya yi cikin tsokana ya ce,
"Malam itafa yarinya ce dole sai ka riƙa bi da ita a hankali, bawai lokaci guda za ka sauke mata tsufantakarka kanta ba."
Mamman ya maka masa harara gami da furta,
" Ko kuma dattantaka ba, matarka ko matata.?"
Dr. Jawad ya murmusa ka na ya ce,
"Ni dai na gaya maka, idan kuma ka kuma aikata makamancin haka to babu ruwana dan kasan ni ba ɓangaren nan na karanta ba kawai dai na mata iya abin da zan iya ne a to."
Mamman ya ja tsaki kan ya ce,
"Hy you, yanzunma ruɗune ya sa na kirawoka ,kai a suwa da za ka dubamin matata."
Dr Jawad dariya kawai ya ke yi bai ce masa komai ba.
Sai da suka kusan shafi awa suna hirarsu ta abota. Bayan tafiyar Dr.Jawad da mintuna goma Ramlat ta farka, sai dai wannan karan ta ɗanji sauƙin jikin nata.
Ganinta zaune ya saka Mamman ƙarasowa da sauri tare da faɗin,
"Sannu kin farka?"
Gyaɗa masa kai kawai ta yi. A hankali ta soma furta,
"Zanje ɗakina."
Murmushi kawai ya yi kafin ya ce,
"Me za ki yi a can? Ki zauna ki kuma samun hutu."
"Ni dai zanje ɗakina" ta rausayar da kanta.
Ganin yadda tanarke a lallai sai taje sai kawai ya sunkuceta ya fice da ita daga ɗakin.
Mai Ƙosai.