Thirty one end
by @maikosai53
Shafi na 61-62.
END.
Kan gadanta ya sauketa. Kallonshi ta yi tare da kwaɓe fuska ka na ta ce,
"Ni dai ka fita." Ba musu ya fice daga ɗakin.
Yana fita ta miƙe a hankali ta shiga bayi, haɗa ruwan zafi ta kuma yi ta kuma shiga sai da ta gasa kanta sosai sannan ta fito ta shirya cikin dogowar riga ta atamfa ta mata kyau sosai.
tana zama wayarta ta soma ruri, sunan Yaya Saudat ya fito ɓaro-ɓaro kan gilashin wayar.
Hannu ta sa ta ɗaga tare da karawa a kunnenta, sai kuma ta fashe da kuka.
Saudat ta yi saƙaƙe tana mai bin wayar da kallo da yake handsfree ta sakata.
"Ke mene ne kike yi mini kuka.?" Ta tambayeta.
"Yaya Saudat shi kenan na zama gurguwa, shi kenan yaya ya yi mini......"
Saudat ta katseta da hanzari ta hanyar faɗin,
"Ke mene haka? Kin yi haukane sirrin mijin naki za ki riƙa faɗa? Kin manta iliminki za ki watsar da karatunki, sau nawa ki ke karantawa haramune bayyana sirrin gidan aure. Koma dai mene ne dai ina so ki nutsu duk abin da ya faru da ke da yaya to shi ne rayuwar auren,da wannan kaɗai zai sa ki gane banbancin rayuwar da da ta yanzu. Ki nutsu ki kama kanki. Jiya Aunty Rahma ta kirani da naje zan taho ta bani saƙo gobe zan shigo na kawo miki in sha Allahu, kuma ta ce ki kirawota a waya. Dan Allah Ramlat kada ki bayyana sirrinki ga koma wane ne ko da kuwa Ammi ce, ina so ki bawa Ammi mamaki ko da yaya ba ya sanki bakwa zaman mutunci kada ki bari ta fahimci hakan dan Allah ki yi ƙoƙarin gyara mu'amalarku, duk abin da ya miki ki yi haƙuri kada ki bari shirmenki na baya ya dawo, yanzu ke babbace mace mai daraja da ƙima."
Cikin kuka ta ce,
"To yaya Saudat zan yi, amma ki yi haƙuri jiya na ɗan tsine miki kaɗan."
Saudat ta tuntsire da dariya tare da zaro ido kana ta ce,
"Lallai ma ashe ni ma zan tsine miki kibi rariya. Ki dai kula ,ki zama mai tsafta a ko da yaushe."
"To yayata."
"Dalla! ki tsayar da kukan nan haka malama, ki kashe wayar ki tashi kije ga mijinki ki yi masa duk abin da yakeso wanda zai saka shi farin ciki." Ta kashe wayar dan kada ta kuma ba ta damar magana.
Ramlata ta yi ɗan murmushi kafin ta ce,
"Yayata kenan ta kaina."
Ɓangaren Saudat kuwa ji take kamar ta zuba ruwa a ƙasa tasha,wani daɗi ya mamaye zuciyarta, addu'a kawai take yi Allah ya ƙara haɗa kawunansu.
Ta jima a ɗakin kafin ta fita zuwa falo, yana zaune yana kallon zeeworld. Kujera mai cin mutum ɗaya ta samu ta zauna tana mai sunkuyar da kanta ƙasa.
Kallonta ya yi yaga yadda take ta faman wasa da yatsunta biyar, ya saki wani murmushi sanyi na ratsa zuciyarsa. A hankali ya miƙe ya koma kusa da ita tare da faɗin,
"Ni ma zan iya sami wajen zama a nan?"
Ta ɗago da kanta ta kalleshi kafin ta saukar da shi ƙasa ,cikin ranta faɗi take,
"Kai ka jima wani rainin hankali, to a kaina zai zauna."
A fili kuwa gyaɗa masa kai kawai ta yi.
Ya saka hannunsa ɗaya ya ɗago da fuskarta tare da kusantowa da ita jikinsa har su na shaƙar numfshin juna ka na ya ce,
"Magana za ki yi min ba gyaɗa kai ba, daga yau har yaumuttanadi nanne wajen zamanki ko a ina ne." ya faɗa yana mai nuna cinyarsa. Wata kunyace ta rufeta ta kasa ko da ci gaba da kallonsa. Da sauri ta miƙe dan barin wajen ya sa hannu ya fizgota sai ga shi ta faɗo kansa.
Bin ta yake da wani irin kallo, haka kawai yake jin wani abu game da ita na sake fusgarsa bai san mene ne dalili ba amma yana jinsa cikin nishaɗi, duk da dai shiyasan bawai santa yake yi ba amma yana jin farin ciki tattare da ita.
Sun fi mintuna biyar a haka, idanuwanta a lumshe shi kuma sai bin ta yake da mayataccen kallo yana mai shafa sumar kanta.
Ita ce ta yi hanzarin miƙewa ta wuce ɗaki da sauri. Sauke ajjiyar numfshi ya yi yana mai shafa kansa.
"Wai meke damunka ne?" ya tambayi kansa. Tsaki ya ja kafin ya kashe tibin ya wuce ɗaki. Makullin mota ya ɗauka ya fice daga gidan.
tana ɗaki ta jiyo tashin motarsa sai ta ji wani sanyi ya ratsa zuciyarta. Wayarta ta ɗauka ta latsa kiran wayar Aunty Rahma, tana shiga ta ɗaga bayan sun gaisa itama ta shiga jerantamata kalamai da nasihohi masu kashe jiki.
Ramlata har da kukanta ji take wai duk a kan auren ne a ke mata haka, me ya sa shi ba za a riƙa masa ba sai ita kaɗai.
"To baki gani ba ai shi Ammi ce ke yi masa, ba kiga yadda shi ma yanzu ya ke sanki ba." Wani sashe na zuciyarta ya ce mata.
Ko da suka kammala wayar da Aunty Rahma hayewa gado ta yi ta yi kwanciyarta tana mai lumshe idanuwa.
Mamman kam gida ya nufa kai tsaye. Ammi na ɗakinta ya shiga da fara'a take hau faɗin,
"Ina ƴata?"
Murmushi ya yi, yana jinjina irin san da Ammi ke yiwa Ramlat.
"Ammi tana gida, da ita zan taho to ba ta ɗan jin daɗi ne shiyasa."
"Me ? ba ta jin daɗi? Me yake damunta? ma za kaine naga jikin nata."
Sai yaji ina mai bai gaya mata,ginin yadda hankalinta ya tashi lokaci guda.
"Ammi dan Allah ki kwantar da hankalinki, bafa wai rashin lafiya ce sosai ba ɗan zazzaɓi ne kuma anmata allura yanzu haka ma na barota tana hutawa, Ammi ta ji sauƙi wallahi."
"Ni dai ka kaine naga ɗiyata ma za ta shi." Ammi ta ce.
Duk yadda ya so dakatar da Ammi taƙi amincewa harta Saudat da ta sakko ta iskesu suna fafatawa ta tsoma baki amma ta ƙi yarda. Ƙarshe dai sai da Mamman ya ɗauketa zuwa ga Ramlat.
Har lokacin barcinta take yi hankali kwance. Ammi ta soma shafata a hankali tana mai ƙara jin ƙaunar ɗiyarta cikin ranta.
Kamar a mafarki ta ji ana shafa mata jiki, a hankali ta soma buɗe idanuwanta, tas ta sauke su kan Ammi hannu ta sa ta sake murza idanuwan nata kodai gane mata ba dai-dai suke yi ba, taga dai da gasken Ammin ce sai kawai ta miƙe zaune ta rungumo Ammi tana faɗin,
"Ammi ta." cikin washe baki.
Ammi itama ta murmusa tana mai shafa kanta, "Na'am ɗiyata, ya jikin?"
Ramlata ta sunkuyar da kanta ƙasa ka na ta ce,
"Ammi na ji sauƙi, yaya Saudat ce ta gaya miki ko? Ta sa kika taso babu shiri."
Ammi ta yi ƴar dariya kafin ta ce,
"A'a ko ɗaya mijinki ne ya sanar da ni bakya jin daɗi." Tafaɗa tana mai nuna mata Mamman dake tsaye kansu.
Sai lokacin Ramlat ta kula da shi tsaye ya harɗa hannayensa biyu.
"Ni ba abin da ke damuna Ammita, gaskiya bai kyauta miki ba ya kamata a masa hukunci."
"Duk yadda ki ka ce ƴata." Ammi ta ce.
Mamman kam faɗi yake cikin ransa,
"Kut yarinyar nanfa ta rainani, ko dan taga na kusanceta.?"
"A'a ko ɗaya, kamanta da halayyarta ce hakan.?" wani sashi na zuciyarsa ya ce masa.
"Ni dai Ammi ki ce ya fita ya bamu waje zamu zanta." ya jiyo sautin muryar Ramlat na faɗin haka.
"Malam ka bamu waje ,ka ji dai me ta ce ko?" Ammi ta ce.
Ƙyasta yatsu biyu ya yi, yana mai kallonta kafin ya ce,
"Ai dai Ammin ba kwana za ta yi ba ko? Za ta tafi za kuma ki yi bayani."
Karaf Ammi ta ce,
"Me za ka yi mata ,wallahi na ji ba dai-dai ba saina saɓa maka kamanni."
Ramlat ta ƙyalƙyale da dariya tana watsawa Mamman harara gami da murguɗa masa baki.
Ficewa ya yi yana mai yin ƙwafa. Su kam ci gaba da hirarsu suka ci gaba da yi cikin nishaɗi, a wasa-wasa Ammi ta riƙa shigar mata da nasiha mai ratsa zuciya,tana kuma ba ta wasu hikimomi yadda za ta siye zuciyar mijinta ,yadda za ta yi zamantakewa da mijinta lafiya. Sai bayan azahar sannan Mamman ya mayar da ita gida, bayan ta kuma yi musu nasiha.
Bayan wata uku.
Shaƙuwa mai ƙarfi ce ta shiga tsakanin Mamman da Ramlat, wacca ta haifar musu da kyakkyawan so mai cike da tsagwaran ƙauna. Duk inda Ramlat ta yi nan Mamman ya ke yi, duk wani farin cikinta shi ya keso.Haka zalika itama farin cikinsa take so,duk abin da zai ɓata ransa tana ƙoƙarin gujewa.
Malamin Ramlat ya zo ya nemi soyayyar Saudat kuma ta amince masa, yanzu haka ya kawo kuɗi an saka rana shekara guda mai zuwa in da rai.
Murna, farin ciki wajen ahlin ba a magana.Ramlat kuwa ji take itama yayarta za ta yi aure ta daina zaman gida.
Shiri suke yi sosai zasu kaiwa Kakale ziyara. Ramlat sai hada-hada take, siyo wancan shirya wancan.
Mamman ne ya shigo ɗakin na ta da sallama ɗauke a bakinsa. Bayanta ya je ya rungumeta da duka hannayensa.
Cikin murmushi ta ce,
"Za fa ka karyani Kakale ta yi mini dariya."
Ya juyo da ita, yana mai sakin murmushi kana ya ce,
"To an sanar miki da cewa za ki je ne."
Ɓata fuska ta yi, ta shagwaɓe kamar za ta yi kuka tukun ta ce,
"Bangane ba ,fasa zuwa a ka yi kome?"
Ganin yadda ta ci kunu ya saka shi tuntsirewa da dariya,
"A'a mayar da wuƙar taki, me zai hana kiƙi zuwa ai in bake ba tafiyar. Zo ki ji" Ya ƙarasa faɗa yana mai janyota jikinta. Ta riga ta saba da wayonsa ,duk sanda ya keson biyan buƙatarsa in tana aiki to zai jata da wayo da wasa, ko da kuwa ba abin da take yi, ita kuma duk lokacin da yazo ba ta taɓa juya masa baya balle ta hanasa wannan horon Saudat ne. Shi kuma ya riga ya horar da ita kan komai nasa ,ta saba da jikinsa da nauyinsa kanta.
Bayan sun kimtsane suka ci gaba da shirin tafiyar ta su.La'asar suka ɗau hanyar Azare Ammi, Saudat ,Mamman dake tuƙasu,Ramlat da Aunty Rahma wacca ke fama da ɗan ƙaramin cikinta wanda take ta laulayinsa duk da cewa bai fito ba dan wata biyu ne da sati ɗaya,sai dai wahalar da yake ɗan ba ta.
Ammi ta so hanata zuwa ma amma ta riƙa lallaɓata har sai da ta amince.
Isarsu Azare ya saka Ramlat farin ciki sosai, ko ba komai ta haɗu da ɗan uwanta Ahmad. Ita acewarta ba ta girmaba za su fice yawon na su. Sai da Ammi ta mata jan ido sannan ta nutsu.
Kwanansu biyu a Azare Ramlat ta soma zazzaɓi amai da gudawa, sosai hankalin Mamman ya tashi matuƙa. Aunty Rahmace ta shiga kula da ita ka'in da na'in.
Gwaji ta mata na masu juna biyu tashin farko ya nuna tana da shigar juna biyu. Zo kuga farin ciki wajen Mamman wai shi ne zai zama uba kuma da Ramlat? Ammi da Kakale kuwa abin ba a magana. Kakale kuwa faɗi take,
"Ni daman tunda naga ta ɗashe ta yi ƙiba na ce a rina, kawai dai na yi shiru ne gaskiya ta yi halinta, to ga shi nan kun dai ji kun gani." Kowa na wajen ya sa dariya. Saudat kuwa rungume Ramlat ta yi tana faɗin,
"Ina sanki ƙanwata, kin gamamin komai za ki bani ɗa." Dariya sosai suka saka.
Kulawa ta musamman a ka shiga bawa Ramlat, ita dai kawai bin su take da ido, sai kunne da ke saurarn zantukansu. tana kallon yadda kowa ke cikin farin ciki itama sai kawai ta ji tana san abin da ke cikin na ta.
Ahmad kuwa tsokanarta kawai ya ke yi ya kance mata,
"Mai ciki?" Har sai da suka yi faɗa, sannan ya daina.
Satinsu guda a can suka baro Azare Kakale ta so su bar mata Ramlat amma Mamman ya kafe akan ina ba za ta saɓuɓa.
"Ka jimin ja'irin yaro, sadda aka maka auren ba ca ka yi a'a ba,shi ne yanzu an ji daɗin aure ko? Za ka zo ka sameni ne."
Shi kam dariya ya ke yi yana faɗin,
"Ni dai ban bayarwa ai matata ce ko?"
Har sai da Ammi ta saka baki sannan su ka yi shiru.
Bayan dawowarsu ya kaita asibiti aka shiga duba ta, aka bashi tabbacin in cikin ya kai wata uku za ta soma zuwa awo dan a riƙa duba lafiyarta. da kuma ganin ƙwarin cikin.
Sai da ya sama mata likita mai kula da ita sannan suka baro asibitin.
Kullum Ramlat cikin rashin lafita take, yau zazzzaɓi gobe ciwon kai ko baya. Har ya sa Ammi tasa ya dawo mata da ita kusa da ita. Baiso ba amma ba yadda ya iya haka ya ɗauketa ya mayar da ita gaban Ammi.
San da Abi ya dawo ya ji daddaɗan labari ba ƙaramin farin ciki ya shiga sosai ba.Komai Ramlat ta ce tana so yi mata ake yi.
Bayan sati biyu.
Jikinta ya soma warwarewa sosai. Ji ta yi kawai tana sha'awar shan mangwaro kai tsaye ta nufi lambun Mamman wanda take shiga a da dan tsokana.
Mai bawa shukokin ruwa na zaune yana ƴar hutawarsa ta ratso cikin lambun.Kai tsaye ta wuce wajen Abarba da ta hango.
"A'a matar Mamman ai ba su ƙarasa nuna ba."
Harara ta galla masa tare da murguɗa baki ka na ta ce,
'Me ye ruwanka ? Ba ka ji cewa Matar Mamman ka ce ba, kaga kenan ko ita gonar ko da ba ta nunaba zan iya ɗaukarta haka na yi gaba da ita."
Dariya ya yi cikin ransa na ayyana.
"Har yanzu dai hali ba zai canza ba." A fili kuwa faɗi ya ke,
"Yadda ki ka ce haka za a yi Matar Mamman."
Gaba ta yi ,tana mai ɗan murmusawa, tana jin daɗi in aka kirata da suna Matar Mamman.
Wajen Baba mai gadi ta wuce bayan ta fito daga lambun.
"Baba barka da hutawa."
"Yawwa barka dai ƴata, ya ƙarfin jikin? Ya kamata ki riƙa hutawa dan samun cikakkiyar lafiya." Baba ya ce.
Dariya ta yi sosai kafin ta ce,
"Haba Baba sai ka ce baka san irin ƙarfin da nake da shi ba, kamanta ni wai baba ne.?"
Baba ya riƙe haɓa ya na faɗin,
"Ina ni ina manta Matar Mamman ɗinmu."
Sosai ta yi dariya. Hira suka sha da Baba kafin ta koma cikin gidan.
"Har yanzu dai kina nan da halinki, ba za ki canza ba, daman mai hali ai baya fasawa." Baba ya ce sa'ilin da ya hangeta tana ƙoƙarin shiga cikin gidan tana leƙe.
Bayan wata takwas da sati biyu.
Cikin Ramlat ya tsufa sosai haihuwa yau ko gobe dan cikin watansa Tara cikin na goma. Yanzu ta koma gidanta tun sa'adda cikin keda wata shida.
Addu'a suke yi mata akan Allah ya sauketa lafiya. An kawo kayan lefen Saudat in da aka saka bikin nan da sati guda.
tana zaune ta tasa kafu-kaza a gaba tana sha, wanda Saudat ta yi mata shi. Mamman kuwa sai baza na mujiya yake yana ƙare mata kallo yawon bakinsa na tsinkewa kuma ta hanasbi sha.
Ji ta yi cikinta ya murɗa ya bada wani irin sauti mai ƴar ƙara. Ya mutsa fuska ta yi.
"Ya dai ƴan matana.?" Mamman ya jefa mata tambayar.
"Babu komai ɗan saurayina." Ta ba shi amsa tana ƴar dariya. Shi ma dariyar ya yi kafin ya ce,
"Watakam kin raina ne ko? Ki faɗamin meke faruwa?"
Sai da ta kanne ido ɗaya sannan ta ce,
"Babu komai fa."
"To ni ma a sammin mana na sha na ji da daɗi."
Mamman ya ce yana mai saka hannu kan farantin da kafu-kazan ke ciki.
Tura masa farantin ta yi gaba ɗaya sai kawai ta ji ya ma fita daga ranta.
Ta miƙe a hankali tana ɗan takawa zuwa ɗaki. Ji ta yi bayanta ya riƙe ƙugunta ya ƙame ta kasa motsawa.
Ƴar ƙarar da ta saki ce ya saka Mamamn bin ta da kallo. Da sauri ya miƙe yana mai nufarta. Kafin ya cimmata har ta zuɓe a wajen.
"Ramlat" ya faɗa da ƙarfi, gaba ɗaya ya ruɗe ba ta ko motsi, da sauri ya shiga laluben lambar Saudat bugu ɗaya ta ɗaga .
"Ka da ki sanarwa da Ammi ki yi maza ki zo yanzu Ramlat ba lafiya." Ya kashe kiran.
Da sauri ta sakko daga benen Allah ya taimaketa Ammi na ɗaki ta yi hanzarin ficewa daga falon zuwa waje.
Mintuna ashirin ne suka kawo ta gidan, Mamman na ruƙunƙume da Ramlat jikinsa yana ta faman jijjigata.
tana isa ta isa garesu ta tallafo kanta.
"Yaya ka fidda mota muje asibiti inaga haihuwa za ta yi, haka naga Aunty Rahma ta yi kwatankwacin haka sanda za ta haihu."
Bai jira ƙarashen maganarta ba ya fice da sauri, bayan ya fidda motar ya dawo ya sunkuceta zuwa mota.
"Ku je zan taho da kayan buƙata." Saudat ta ce.
A guje yake jan motar kariyar Allah ce ta kai su asibitin. Yana zuwa aka amsheta zuwa labour room.
Duk yadda suka so ta farfaɗo ko dan ta haihu abin ya ci tura, har sai da likitan da ya amsheta ya bawa Mamman tabbacin sai dai ayi mata aiki a ciro babyn dan samun ceto rayukansu ,a gwajin da suka yi kuma yarinyar ta jigata sannan a juye take kai a sama ƙafafuwa a ƙasa.
Take ta saka hannu a ka shiga da Ramlat ɗakin tiyata. Dai-dai da isowar Saudat. Ganin abin da ke faruwa ya sakata sanar da Ammi abin da ke faruwa.
Lokaci guda Ammi ta tashi hankalin direban gidan ya kawota asibitin. Addu'a kawai suke yiwa Ramlat a kan Allah ya ba ta lafiya.
Bayan awa ɗaya ana ta abu ɗaya kafin a sami kan matsalar sai dai har lokacin Ramlat ba ta farfaɗo ba, ko da a ka sanar da su a guje Mamman ya shige ɗakin ana hanashi amma ina ko jinsu bai yi ba ya faɗa ɗakin.
Likitoci burjik suna san shawo kan matsalarta. Ganinsa ya saka wani likita sakawa a dakatar da shi amma ya yi wurgi da su ya iso gareta. Hannunta ya riƙa ya soma faɗin,
"Ka da ki tafi ki barni cikin rashinki ni ma ba zan zauna ba, ki buɗe idanuwanki ki kalli mijinki abin ƙaunarki, ki ta shi ki kalleni Ramlat ɗina, ki farka ki ci gaba da rayuwa tare da ni kada ki yimin haka."
"Ki ta shi na ce, in kika tafi saina kashe kowa, in kika tafi sai na ƙauracewa kowa, a kanme ? Dan me? Me ya sa? Ki ta shi." Ya soma jijjigata yana surutai yi yake kamar mahaukaci, duk likitan da ya zo tsayar dashi to mangareshi ya ke yi, ya hana kowa taɓa masa mata.
Suna haka suka ga abin motsawar bugun numfshinta tafiyarsa ta ƙaru, a she Ramlat ce ta sauke ajjiyar numfshi tana jin muryar Mamman na zuba surutan hauka amma ta gaza cewa komai. Da ƙyar ta saka hannunta ta soma shafa sumar kansa da ya kwantar da kan nasa gefen ruwan cikinta.
Da murmushi ya ɗago bakinsa washe kamar gonar auduga ya gaza rufesu. Sai kuma ya koma sunbatun ganin farkawarta.
Da ƙyar likitocin suka ya ki ce shi zuwa waje. Su Saudat kuwa jin ta farka sai hamadala da godewa Allah.
Jinjiri na hannun Ammi,ta hana kowa shi, tun bayan fito da shi da mai kula da majinyata suka yi ta amshe shi, yanzu kuma da ta ji Ramlat ta farka sai ta sake ruƙunƙume shi.
Komai ya lafa Ramlat ta sami lafiya ta dawowarta cikin duniyar hayyacinta.
Mamman kamar ya cinyeta haka ya ke ji. tana jin daɗin yadda Mamman ke nuna mata so da ƙauna shiyasa itama ba ta san yin nesa da shi ko kaɗan. Duk da bai taɓa gaya mata baki da baki ba amma ta san yana santa sosai,ita kuma za ta juri komai sannan za ta yi haƙuri har lokacin da Allah zai matse bakinsa ya furta mata kalmar so.
Satinsu guda a ka sallameta daga asibitin.Kulawa ta musamman ta ke samu daga wajen mijinta Mamman, Ammi da kuma ƴan uwanta biyu Saudat da Rahma.
Ammi gidanta ta sa a ka wuto da ita ta ce ba za ta koma gidan mijinta ba saboda tafi samun kulawa wajenta. Haka Mamamn ya haƙura ya barta dan ba yadda zai yi.
Abi ya dawo, dawowa ta musamman saboda jikan da aka masa. Satin da ya zagayo a ka ɗaura auren Saudat sakamakon ɗagawar da aka yi saboda Ramlat na kwance a asibiti, ranar suna aka raɗawa ɗan Mamman suna in da aka ba shi sunan Mahaifin Ramlat suke kiransa da Baba ƙarami.
Washe gari a ka kai Saudat gidanta, tare da mata fatan zaman lafiya.
Sosai Ammi ke kula da Ramlat har ta cinye kwanaki sittin gidanta. Da kanta ta mayar da ita gidan mijinta.
Ramlat zaune bakin gado tana bawa yaron mama yana sha.
Mamman ya turo ƙofar ɗakin bakinsa ɗauke da sallama.
Kusa da ita ya samu ya zauna, yana mai kallon fuskarta ganin yadda take matse fuska.
"Wai meke faruwa ne?"
Mamman ya jefamata tambaya.
"Za fi mana." ta ba shi amsa.
"Zafin me?" ya sake tambayarta.
Kamar za ta yi kuka ta ce,
"Haba dan Allah baka ga yadda yake ta faman tsotsa da zafi ba salon ya ciremin shi gaba ɗaya."
Mamman ya kwashe da dariya kafin ya ce,
" Me yake taotsa? Me zai cire?"
Sarai ta san ya gane me take nufi san tsokana ce kawai da neman magana. Sai kawai ta fashe da kukan shagwaɓa.
Janyota jikinsa ya yi ya na faɗin,
"Haba madam ,ya da haka? In kina haka su kuma sauran yaran da in sunzo fa ya za ayi da su.?"
"Me ? caab gaskiya a'a dai."
"Haba my matata ,ni da nake so mu yi mu samawa Baba ƙarami ƙanwa ko ƙani kusa-kusa."
"So kake na mutu kenan ko?" ta jefa masa tambaya.
"Ba wani mutuwa matata, in kin tafi ni ma na tafi tare dake na ke rayuwa, ina sanki zuci da ƙalbina, ni dai ki soni ta hanyar haifamin yara masu yawa yadda gidan nan zai cika da yara."
Daɗi ta ji ya ratsa zuciyarta, wai yau yaya ne da kansa ke furta yana santa, wayyo! Allah daɗi kasheta.
"Allah na gode maka, Allah ka barni da kyakkyawan mijina, Alhamdulillah Allah ka barmu tare har a aljanna ameen."
Yana dariya shi ma ya amsa da "Ameen kyakkyawar matata."
Alhamdulillah!
Ƙarshe.
Sai mun sake kasancewa cikin wani sabon littafin nawa.
Abin da na yi kuskure cikinsa Allah ka gafarta mini. Kar ku manta duk ɗan Adam tara yake bai cika goma ba. Kuma daidan wani karkataccen wani.
Bissalam.
Mai Ƙosai taku har abada.