BOYAYYEN YARIMA

1-2

by @autarmama

BOYAYYEN YARIMA(MUTANEN DAJI).



BY


ƳAR LELEN ROYAL STAR.



Alhamdulillah! Alhamdulillahi Allah Kulli Halin, Alhmdllh, ina mai ƙara Jaddada Godiyata ga Allahu Subhanahu Wata'ala da ya bani Rai da lafiyar Fara Rubuta Wannan Littafin nawa mai Suna Ɓoyayyan Yarima, Wanda na yi Tsawon Lokaci ina Nazartarsa da Son Fara rubutasa, Allah bai yi ba sai Yau, Ina fatan Jinkirin Rubutasa da Na yi ya zama Alkhairi ga ni ga Dukkan Wanda zasu Karanta, Ina fatan Ubangiji ya bamu Aron Rai da Lafiyar da Zan gamasa cikin Kwanciyar hankali da Salama.



*🌟ROYAL STAR WRITER'S ASSOCIATION🌟*

    {R.S.W.A}


***

 *_Marubuta masu aiki da fasaha da zallar amana, Fad’akarwa, ilimantarwa da kuma nishad’antarwa_*

_(R.S.W.A) Ruwa kad’ai ke maganin k’ishi_


*Alk’alaminmu ‘yancinmu



https://arewabooks.com/u/autarmama


P.1-2



Shimfiɗa..




Fur.



Wata Ƙabila ce Wacce Galibinta ke Zaune a Yammacin Ƙasar Sudan.

Sun fi karkata ne a Yankin Darfur, 

Haka wasu lokutan Ana kiransu da Suna Fora,Fordunga,Fuwali kojara ko kungara.

Mutane ne Masu Aikin Noma,suna iya yin kiwon Shanu, Wasu Dangin Fur wanda suka fara garken Shanu sun bunƙasa Salon Makiyaya kamar na Makwabtansu Makiyayan Larabawan Baggara(Baggara)A al`adance Fur din nan , na kiwon shanu, Yanzu ana daukarsu Baggara.Fur in suna ne na Musalmai Mabiya Sunni, Wanda ke bin Mazhabar Malikiya ta Shiri'ar Musulunci.

Sai dai Duk da Kasantuwarsu na Musulmai, suna Aikata Aiyuka Irin na Marasa Addini, Wanda ya Haɗa da Gine-ginen  Guraren Bautar Gumaka, Bautar Gumakan da sauransu.

 


Sune A Yammacin Ƙasar Sudan, Mutane ne da suke bin Sedentary herding da kuma Aikin gona,Mafi Noma gero.Al`ummarsu ta gargajiyace, Wacce Dattawan kauye ke Mulki.suna Magana da Fur ,Fur Wani Yare ne na Shahara, kuma Musulmai ne, Sun ƙarɓi Addinin Musulunci Ne Bayan Mamayar Yankin da Masarautar Kenam-Bornu ta yi A lokacin tsararru Wasu daga cikinsu, Sun so yin Magana da Larabci a cikin Yan shekaru.

Sunan Darfur ya fito ne daga Waka Ƙabila , ma'anarsa kuka 'Gidan Fur',Kamar su Deriege da Tegani Sei-sei dukkansu Mambobin Fur ne.Fur din ya Ƙafa Masarautar Darfur Mai Tarihi, Wacce take da Mulkin Darfur har zuwa 1916.


Harshe.

Suna Magana ne da Yaren fur, Wanda dangin Nilo-shaha ne.suna Magana ne da Larabci a Matsayin Harshen Yare.

Babu Rubutaccen Rubutu ko A`lamar A`lama Don Yaren Fur.

Sau da dama Suna Amfani da Ganga mai nauyi ya yin , yin Jawabai, Bayyanar da Sako, da Sauran Adiresoshi Jama'a.

Kiɗan Fur yana da Matuƙar Shahara A cikin Al`adarsu , Babban kayan Kiɗansu Sune Ganguna, Ana yin kiɗa tare da Amo mai nauyin gaske, Wanda Yake tare da Bikinsu Wasu Shahararrun Mawaƙan Fur Sune Abdallah Kioka da Marium Amo.



*****



Ƙarar Sautin Amon kiɗan Gangunansu ne ya shaidawa Jama'ar garin Lallai Akwai Wani Shararan Abun da yake Faruwa a Cikin garin, Sakamakon Duk idan Ana son Isar wa da Jama'ar Garin wani Sako, to Ana yin Amfani da Gangunan ne a Al`adance domin Isar musu da dukkan Saƙon da ya Iso.



   Tururuwar Fitowa daga Cikin Manyan Bukkukin da suke Kewaye da Babban Garin Mutane suka fara Tisasowa,Sautin Ƙarar Takun Dawakan da Suka fara Doso gurin ne, yasa gaba daya Mutanan da suke Gurin suka Ɗaga Kawunansu Zuwa Sama.



   Kururuwa Suka saki, tare da yin Hanyar Babbar Ƙofar Garin, cike da Farin ciki, gaba dayansu Fuskokinsu Yalwace suke da Wani Murmushi na Musamman.




     Tsaitsaye suke A Bakin Ƙofar Garin, suna Duban Yammacin Garin, inda Sautukan Takun Dawakai ke tahowa daga Chan nesa, Ga wani Ƙura da Yake tasowa, A`alamar Dawakan da suke tahowar ma sun wuce Gaban Kwatanci.



    Ƙurar da Take tahowa ce, ta riskesu, Dandanan ta fara washewa, Wasu Zaratan Dawakai ne, Ƙosassu Masu girman gaske suka Bayyana, Wasu Manya-manyan Baƙaƙƙen Mutane ne, Masu wata Iriyar Tufafi, Mai kama da Babu, Gaba dayansu suna Sanye ne da Wani kalar Yadi da yafi kama da Fatar Kura, Sun daurasa a Gabansu, sai kuma Wani ƙarami da suka daura a Kirjinsu, sai na Goshinansu, Suna Rarrataye da wasu Manyan Wuƙaƙƙe, Sanduna, Barandamaye, Da dukkan Wasu kayan Yake-yake na Gargajiya.

Guyawu a Sake Yan-garin suka Fara Kallon Mutane Biyun da suka Fara Bayyana, Cikin Alhini, Wasu daga cikin Mutane , suka fara Ƙananun Maganganu.




      Rage Gudun Dawakansu Sukayi.Buɗe Tsakiyarsu suka yi, An dauki yan Daƙiƙu Kafin wata Ƙura Mai duhun Gaske ta Mamaye gaba daya Gurin da suka saki, Bayan Wucewar Gaba daya Ƙurar Wani Farin Ƙosassan Doki Mai girman gaske ya Bayyana, An masa wani Irin Ado mai Daukar Hankali, Bayan Bayyanar Dokin ne kuma Mamallakin Dokin da ya kasance Lafiyayyan Mai kwarjini da Cikar Haiba, tare da Kamala ta Musamman ya Bayyana.



     Yana da girman jiki Sosai, Shima Baƙi ne kamar Sauran Mutanan cikin Garin, sai dai nasa Baƙin ba kalar na Sauran bane, Yana da Wani irin Baƙi mai daukar Hankali

, Yana da Faffadan Kirji Mai dauke da Manyan Ƙafadu, Jikinshi gaba da A Mummurɗe yake, ba'a Iya ganin Fuskarsa, Sakamakon Wani Farin Ƙyalle da ya Mamaye gaba daya Fuskar sai Kyawawan Idanuwansa da suka Kasance Blue kawai ake iya gani.

Gashin Kansa Da ya kasance Irin na Larabawa Mai yawan Gaske, da Cika Ya wani zubo masa, Girar Idanunshi na da Yawwa Sosai, sai dai daga Tsakiyarta kamar Ansa Wani Abu an Yasheta, ta Yarda har ake iya Ganin Baƙar Fatarsa.Yana sanye da Wasu Kaya na Sulke da suka Bayyana Zallar Jarumtarsa.



    Cikin Ƙasaita Suka Ringa tafiya akan Dawakansu, Ganguna kuma na Ci gaba da Kiɗa, har sai da Suka shigo cikin Garin Kafin kiɗan ya Fara Tsagaitawa kaɗan-kaɗan bawai don ya Rage duka ba, Sai dai An rage sautukansu ba Kamar da Fari ba.



Cikin natsuwa Sauran Mutanan da suke tare suka Bayyana Tafiya Suke Akan Dawakansu, da suka kasance Dark Coffee sosai, sun sha Adajensu Mai kyau, Dubana na kai akan Mutanan da suke kan Dawakan da Aƙalla ba Akasaru ba zasu kai kusan Mutum Saba'in Zuwa Tamanin, Gaba daya Shigarsu kala daya ce, gasu wasu irin Baƙaƙe na ƙin Ƙari, Baƙinsu irin Baƙin nan ne Marar kyan Fasali irin Baƙin da zaka ga Mutum har Wani mai-mai yake musamman in suka shiga rana.


Basu yi tafiya mai Nisa sosai ba suka fara Shigowa Cikin Wani gari, Mai dauke da Bukkoki a matsayin gidaje, Tun daga nesa suka hango yarda Uwayen Mutane suka taru A ƙofar shiga cikin Garin, Suna Riƙe da Ganguna, da kayan kiɗe-kiɗe, suna ƙara dososu Sosai aka saki Kiɗe-kiɗe irin na mutanen Da. Mutanen Da din ma Irin na 'Daji', wanda yake tayar da Tsumi,kiɗa suke sosai suna Rawa na Murnan Mutanansu sun Je Yaƙi sun Dawo, tare da Ɗumbin Nasarori, gaba daya Washe bakunan su masu dauke da Jajayen Haƙora Wanda aka musu Adon Wani Ɓakin Abu a Haƙoran Wanda su a Ganinsu Kyau suka yi da Abun.



Har suka iso kusa da juna suna Washe bakunansu, saukowa suka shiga yi daga kan Dawakansu, suna Gaishe da Sarki da Mutanan garin. duk Wannan Bidirin da Ake yana kan Dokinsa bai ko motsa ba, Sannan bai kalli gaba daya mutanan da suke gurin ba, haka zalika bai buɗe Fuskarsa da take Yane da wani Farin Kyalle ba.

Aƙalar Dokinshi ya fara Ƙoƙarin Juyawa domin Wucewa Cikin gari, babu wanda ya dakatar da shi, don sun san Kafiyarsa akan Abun da yake Buƙata, In yace zai yi Abu bb wanda ya isa ya hanasa, in kuwa kayi Ƙoƙarin hakan, bazai ji komai gurin Cire kan ka, kuma ya yi Abun da ya yi Niyyar yi.



Suna kallonsa ya wuce Cikin Garin nasu, mai kyan gani, Haka ya Ringa tafiya har ya ƙaraso Gurin Wata Babbar Bukka da tafi gaba daya Bukkokin Garin Girma, ko ta Sarki bata fi tasa ba sai dai su kara, sai da ya ƙaraso kafin ya sauko daga kan Dokinsa, Gurin da ya tanadar Domin Ajiye Dokinsa yaje ya Kulle Dokinsa A gurin. ya dawo ya shige Bukarsa, Kan yaloluwar Abun Shimfiɗar da yake Gefe ya kwanta, tare da sauke Sanyayyan Numfashi, lumshe idanunshi ya yi, dan-danan Barci mai nauyin Gaske ya daukesa, bai Farka ba sai da dare ya Ritsa sosai, Sai da ya ji Kiɗe-kiɗen da Ake sun cika masa kunnuwansa, ya yi ƙoƙarin toshewa Amma sautin yarda kidan ke shiga cikin kunnuwansa kai kace a ciki ake yinsa haka yake ji.



A dole ya tashi ya zauna, yana wawware Blue Eyes nasa, da suke Sheki ta Hasken Farin watan da yake Haskowa har cikin Bukar, Miƙa ya yi, cikin jin wata kalar Kasala. Cikin Izzarsa da ta zamar masa jiki a ko da yaushe, ya miƙe ya fice daga cikin Bukkar.


 Yana fita Ya ɗaga kansa, sama yana kallon Garin yarda yayi baƙi Wuluƙ sai hasken Farin wata da ya yi masa ƙawanya, ga Taurari Masu Haske sosai da suka Haɗu sukawa Saman Ƙawanya, Lumshe idanunshi ya yi, ya ƙara buɗewa akan Sararin Samaniyar wadda ta burgesa sosai, wanda har yaji kamar ya Dawwama yana tsura mata idanu, kar ya dauke.



Hasken Wutar da ya fara hangowa ta gefe da gefen idanunshi, da sautin Ƙiɗe-kiɗen Gangunan da suke Kaɗa kansu da kansu a duk Daren da Aka dawo daga Yaƙi kuma ya zamana Sune da Nasara.



Ranar Gaggarumin Biki ake yi a cikin garin, Randunan Giya, Da sauran Abubuwan Shaye-shaye na Mutanen 'Daji!' ake haɗawa, a tara Yan mata, da Samari, ga Wuta a Tsakiyarsu su ringa rawa, daga karshe bayan An gama, Za'a ajiyewa Zaratan Sojojinsu Mata kala-kala duk wadda kakeso ka dauketa a Matsayin Mai kula da kai, Wasu Daga nan suke Auren Hadiman da aka basu, Wasu kuma basa Samun Aurensu, to yau ma Abun da yake faruwa kenan, Sun fara gudanar da Bikin da suka saba yi, gaba daya mutanen Cikin Dajin suna gurin sun Zagaye da Wutar da take gurin.

Kowa na Jiran Isowar Kwamandan Yaƙi, Wanda ya jagoranci Yaƙin , wanda kuma Shine Yarimansu, Wanda ya kasance 'Ɓoyayye' a cikinsu, Ɓai taɓa Buɗe fuskarsa Wani ya gansa ba, kullum Fuskarsa tana a kulle, hakan ne ma yasa ake Masa laƙani da 'Ɓoyayyen Yarima!'. Wanda Asalinsa Ɗan Mutan Darfur ne, Kaura suka yi suka shigo cikin Ƙabilar Fur, wanda ya taso a cikinsu tun Yana Yaro, da haka Har ya tashi, Ya tashi cikin Zaƙwaƙuranci, ta yarda yake bige Gaba daya Sa'aninsa, baya da wasa baya son A masa, wasa baya son Abun da baya so, yana matuƙar girmama Abun da yake so kuma yana son a girmama masa, baya son raini baya son Zalumci, yana da tausayi sai dai ba Akan kowa ba.



Dirarre ne Mai kyan jiki , yana da Tsawo da Ƙibi da Faffaɗan Jiki Irin na Jaru......



COMMENTS✅

SHARE✅

EDIT❌



***




P.R.O SALMA🤙🏽