Chapter 7-8
by @autarmama
👑👑ƁOYAYYEN YARIMA👑👑
(MUTANEN DAJI).
BY.
ƳAR LELEN ROYAL STAR.
*🌟ROYAL STAR WRITER'S ASSOCIATION🌟*
{ROSWA}
***
*_Marubuta masu aiki da fasaha da zallar amana, Fad’akarwa, ilimantarwa da kuma nishad’antarwa_*
_(ROSWA) _Ruwa kad’ai ke maganin k’ishi__
*Alƙalaminmu Ƴancinmu*
It's Paid book.
PIt's Paid Book.
P.11-12.
Cikin wani Zafin nama suka jaa baya tare da sara masa, inaa baya ma ganinsu, burinsa ya ga Uban waye ya tare wa Mutane hanya, wanda har ya haddasa Go-slow haka, Kamshin Turaren Roja and Giorgio Armani, da ya dake hancinta ne, yasa ta wani jaa numfashi, tare da lumshe golden Eyes nata.
Jikinta ta ji yay wani irin sanyi, kasala ta saukar mata, "Uban waye ya tare hanyar nan?", ya fada cikin tsawa, inda-inda suka fara yi dukkansu, ita kuwa kasalar da ta saukar mata ce ta hanata ko motsawa , Sandar hannunta ta fara dogarawa da som komawa Mota sakamakon wani sanyin zazzaɓin da ya saukar mata
, bata An kare ba ta ji an jaa gyalen Abayarta, juyawa tayi, tana juyawa taji an kifa mata wani wawan mari, da yay sanafiyar kifawarta jikin mota kanta ya bugu da jikin mota, "Ke Yar gida Uban waye da zaki zo kiyi Locked Hanya, ki tsaya kuma kina hurawa Mota Hanci , Ana miki magana kina wucewa, ?", ya fada ranshi na tafarfasa, take idanunshi suka kaɗa suka yi jaa, Abin ka da mutumin da bai iya fushi ba, in kuma yay saukarshi wahala ce, Naman jikinsa har wani rawa, yake jikinsa na Ɓari , tura motar yay iya ƙarfinsa, sai gashi ta koma gefe, Umarni bawa Motocin bayansu , dan-danan gurin ya koma ba kowa, shiga motarshi yay ya bar gurin.
Tun da ta kifu bata dago ba, saboda muguwar buguwar da kanta yay, wanda ya haddasa mata wani fitinannan ciwon kai, marin da yay mata kuma ya haddasa mata wani irin kuɗar kunne, take yanke jijiyoyin idanunta suka fara mata wani Amsa kuwwa, ji take suna mata wani zut-zut-zut ga wani yaji-yaji da take ji , glass dinta kuwa tuni ya watse a ƙasa.
Dakyar ta iya laluɓar sandarta ta dauka, miƙewa tayi tare da fara dogarawa zuwa gurin motarta, da sauri Aka tayar da motar suka matso mata da ita,buɗe mata suka yi ta shiga.
Gidan Uncle Aseef din da bata je ba kenan sai dai suka koma gida, Rana Yini tayi kanta na mata wani irin masifaffan ciwo ga zazzaɓi da ya rufeta, ko numfashi bata iya yi, kunne kuɗa idanu na ra zubar da ruwan hawaye.
10:00pm Sitti ta turo ƙofar Bedroom din, ganinta kuɗunɗune a cikin bargo, ga numfashinta na fita a wahalce yasa da sauri ta nufi inda take, zama tayi a gegen bed din tare da fara yaye mata Bargon, cikin kulawa ta sanya hannunta jikin wuyanta, da sauri ta dauke hannunta, Cikin tausayawa tace "mai yake damunki ?", Cikin kukan da tun dazun bata samu damar yinsa ba sai yanzu, tace "Kunne kuɗa, zazzaɓi, ciwon kai", ta fada idanunta a rufe.
Cikin damuwa da tashin hankali, tace "wannan cieo kan ba na zama bane, bari na kira Yayanku muje Asibiti" ta fada tana ficewa.
Bata dauki lokaci mai tsayi sosai ba ta dawo ita da wani kyakyawan Saurayi mai jini a jika, son kowa kin wanda ya rasa, Sitti ce ta kamata suka fita zuwa mota, babu nisa sosai tsakaninsu da Medical Hospital din garin, hakan yasa cikin sauri aka Amsheta,Doctors ne suka rufu a kanta , basu dade ba sosai suka fito.......Haushi da ya ishi Rayuwarsa ko inda zai je din fasa zuwa yay ya koma gida, yana zuwa ya yi parking motarsa a Parking space, ta ƙofar baya ya shige part dinsa, yana shiga ya wuce Bathroom dinsa , ruwa ya sakar wa kansa, yana jin zafin zuciyarsa na sauka, jikinsa har wani zafi yake fitarwa, idanuwanshi kwa ruwan zallar ɓacin rai ne kwance a cikinsu, bai san mai yasa yake ƙara jin ɓacin rai ba, wani tuƙuƙi yake ji yana kara turnuƙesa.
bayan ya fito, vest da Wani Three quater ya sa, turare ya fesa, tare da sanya Bluetooth A kunnansa, wayarsa ya dauka ya fito, yana magana A fiffisge.
"Zaki!".Amma ta fada tana kallonsa, A hankali ya juyo ya zuba mata Idanuwansa da suka dan fara washewa daga jaan da suka yi, "Ga Abin cin ka fa", ta fada tana nuna masa Dining, hannunsa ya dan kaɗa mata kafin yace "Coffee!", yana faɗar haka ya zauna Akan kujerar da ta zaunar da shi ɗazun.
da Kanta ta haɗa masa
Coffee'n Cikin wani kyakyawan Mug mai kyau, ta zuba masa Coffee'n yana turiri ta kawo masa, cikin kulawa tace "Gashi" Miƙa hannunsa yay ya ƙarɓa, cikin jin dadi yace "Thanks Amma", shafa tulin gashinsa tayi, tare da zama kusa da shi.
Shan Coffee'n ya shiga yi da zafinsa,gefe daya kuma yana Amsa wayar da taƙi ƙarewa, time to time yana duban Babban Agogon da take Saƙale a Bango.
Tun yana Amsa Wayar cikin jin dadi, har ya kai ga ya gaji da wayar, yana Amsata ne kawai ba dan jin dadi ba, har ya kai ga sai ya jima sosai kafin ya furta magana daya, Kusan 1 hour kafin ya gama wayar da yake, bayan ya gama ta tambayesa a kawo masa Abin ci, girgiza kansa yay Alamar ya ƙoshi, "Na kusa fara Maka ɗuran Abin ci tunda baka ci ", ware manyan idanunshi yay da matuƙar Mamaki, "Eyyi ka kalle ni da kyau, Ɗure zan fara ma".
"Ana wa Manya ma ?", ya fada yana kama hannunta, Cikin tsokana tace "ko ba'a musu kan ka za'a fara ", kwaɓe fuska yat, kafin ya furta "ni kam na Girma Amma", dariya tayi tare da cewa "No har yanzu Small Boy ne kai", murmushin da ya bayyana loɓawar Beautiful Point nasa, da kuma ya bayyana Fararan Siraran Haƙoransa masu wani irin sheki na musamman ga Kamshin Mouth Freshener da yake fita a Ciki ya washe, "Na girma ni kam", jinjina kanta tayi tare da cewa "I see. na ga ka koma Babban Mutum, Sai Aure", dandanan ya mayar da fuskarsa kamar yarda yake ɗazun kadaran kadahan.
Numfashi ta fesar , tana kallon yarda ya chanja yana yin fuskarsa lokaci daya, ta lura duk yarda yake Nishaɗi da ta masa maganar Aure dandanan Annurin Fuskarsa yake daukewa, Hannayensa, ta kama tare da gyara zamanta Alamar zata mishi magana mai matuƙar Muhimmanci.
Idanunshi gaba daya ya zuba mata, yana sauraron Abun da zata faɗa, "Mene Matsalar ?", kallonta yay da rashin fahimta, "I don't have Any Problem with that, " ya fada yana lumshe idanunshi.
"Ya zaka ce You don't have Any problem, ina ga sai na samo wata na Aura maka , tunda kai ba zaka iya dubawa ka fitar ba", taɓe bakinsa yay, chan ciki yace "Uhmmm Aure dai.!", "Mai kace ?" ta fada tana harararsa, tura karamin bakinsa ya yi, tare da kwantar da kansa A bayan kujerar .
"Hayaniyar Mai ake yi haka ?", Abdel Fattah Al-burhan ya faɗa yana shigowa cikin parlor, "ni da Zaki man, shi kullum baya son Maganar Aure, ya faɗa mana in basa da lafiya mu nema masa magani, ko kuma Aljana ce ta Auresa", Ware manyan idanunshi yay a kanta, sai kuma ya kalli Abdel Fattah Al-burhan.
"Haɗi yake son mu nema masa", Abdel Fattah Al-burhan ya faɗa yana kallonsa ta ƙasa ido, "Abba bana so", ya fada idanunshi a Lumshe, "mai din ?", ya fada yana gyara zamansa, kasa faɗar komai yay, "Ina yar gidan Gen.Abideen Course Mate nasa, ina ga da ita zamu haɗasa", da Azababben Sauri ya buɗe idanunsa, har bai san sanda ya wuntsila zuwa Gaban Abdel Fattah Al-burhan , ya zauna a Ƙasansa , tare da dafa ƙafafunsa ba, "Abba Bana son Mumu Girl din nan, Wlh da na Aureta gwara na mutu ban Aure ba", kallon kallo suka yi A Tsakaninsu don sun bala'in sanin yarda ya tsani Mutuwarsa Haka ya tsani Yarinyar .
"Maganata babu Fashi gobe ma zan je na tambayo maka Aurenta", kamar zai yi kuka, ya furta "Amma!". " Nima Tuni na Amince", "Auzubillah!", ya fada yana rumtse idanunsa, kamar wanda ya ga ko yaji wani tashin hankali, "Tana da wani Matsala ne da baka sonta har haka ?", ta fada tana kallonsa.
"Amma dan baki san Yarinyar nan bane", wani kallo ta masa kafin tace," kai ne ma ka haifeta ƙarewar sani ai, ka bani Amsar tambayata kawai", jujjuya kansa yay tare da tsuke bakinsa.
Zuba masa idanu duk suka yi suna ganin yarda yana yinsa gaba daya ya muzanta, wani ƙunci ya kama zuciyarsa, sai numfashi yake saukewa da ƙarfi-ƙarfi
.
Da sauri ya tashi ya fita, Garden din gidan ya nufa, domin shaƙae Sanyayyiyar Iska, don gaba daya Yana yinsa ya Gurɓata.
Yana shiga ciki wata sanyayyiyae iska mai tattare da feshin ruwa ya bugesa, wani numfashi mai matuƙar dadi ya jaa, yana jin wani iri,bai san mai yasa ba baya son Ana masa wata maganr Aure, ba wai dan bashi da Abun da zai riƙa mace na A'a, yarda abun da zai iya riƙa mace goma ma in Ana yi, Amma shi yanzu yana gani he's too young da yay Aure, ban da ma haka, bai taɓa ganin macen da ta kwanta mishi har yake ji zai iya Aurenta ba.
Sanyayyen Numfashi ya fesar, tare da shafa kyakyawan baƙin bear dinshi, hannayensa yasa cikin Bear ya shiga dan jaansa, idanusa a lumshe, yana jin daddanan sautin kukan tsutsaye mai dadi......"Jijiyoyin kunnanta ne suke son taɓuwa sakamakon bigewa ko kuma marin da aka mata, Wanda hsr yay sanadiyar taɓa babbar jijiyar idanunta, Wanda muna tunanin ƙillan sakamakon hakan zai iya dawo mata da ganinta, za dai mu daurata akan maganin da ya kamata ta ci gsba da Amani da shi."
"Mari!", Sitti ta furta kalmar tana kallon Yaya Ahmad da shima kalmar ta shiga har cikin kansa, "Eh mari!".Zazzafan Numfashi mai dauke da Zallar ɓacin rai Sitti ta jaa , tare da cewa "Zazzaɓim fa ?", jim ya dan yi kafin yace "Firgici ne ya haddasa mata Zazzaɓin har ma da ciwon kan, zamu ɗan riƙeta na yan kwanaki , domin muga kamun ludayin jikin".jinjina kansu suka yi, bayan sun masa godiya suka fito.
Suna fitowa Hafiz Ahmad Al-bashir ya shigo cikin Asibitin, da sauri ya ƙaraso garesu, cikin damuwa da Amanarsa yace "Ya dai ?. mai yake faruwa da ita", kaf Abun da ya faru suka faɗa masa, cikim zallar ɓacin rai shima ya ƙara furta kalmar 'Mari' .
"Ai kuwa ko Ɗan Uban waye A ƙasar nan ya jawa har Ahlinsa da gaba daya Danginsa jafa'i, domin babu wanda ya isa ya yiwa Ƴar cikin Ahlina wannan Mumman Dukan kuma ya lalas, in bai yi prison ba to lallar zan dauresa , har sai naga gatan Ahlinsa