BOYAYYEN YARIMA

Chapter 9-10

by @autarmama

it's paid book



P.9-10




      Six Years Ago.



Kartoum Internation Community School(KICS).......



     Tafiya take cikin natsuwa, Cikin qata Rantsatsiyar Abaya Fara mai masifar kyau, gaba daya jikin Abayar Stones ne a jikinta, kafarta sanye da Modellerie Crystol Ankie-Stop Sondols ,Ƙafadarta Rataye da Jaka Ƙirar Satin Mini-bag With Crystais,Hannunta daya rike da sanda, fuskarta sanye da Baby pink Gucci Glass,tayi Rolling din Gyalen Abayar da yay masifar yiwa Ƙaramar Fuskarta kyau, bakinta sai glowing yake sakamakon White Lipstick da ta shafa, Fatarta da ta kasance Baka ta murje tayi kyau, bakinta mai kyau ya fito, kyakyawan Dogon hancinta ya fito sosai.



     Bata tsaya ba sai da ta ƙaraso Babban Parking Space din da yake cikin Makarantar, motoci ne burjik a gurin, Amma kai tsaye gurin daya daga cikinsu wadda duk ta fisu Haɗuwa ta nufa, Buɗe motar ƙirar Audi Baƙa sai shaning take.



     Da sauri Aka buɗe Mata Motar, shiga tayi aka rufe, kai tsaye aka rufe Motar, Da wani Irin Speed aka jaa motar , kai tsaye suka fita daga get din Makarantar, direct Hafiz Ahmad Al-Bashir Road suka nufa.




    Har suka ƙarasa tana Hakimce A bayan mota, sai Muah muah take da baki kamar mai son cewa wani abu, ko da suka Ƙaraso Cikib parking Space din gidan, buɗe mata mota aka yi, fitowa tayi tana gyara Riƙon jakarta,direct kuma ta nufi Babbar Ƙofar Glass din da take Kallon Get din babban Sashen, tana zuwa ta tsaya, hannunta ta sanya a dan wani abu dan danan ya gama daukar temprint din hannunta, da kuma scanning din face nata, Ƙofar ce ta buɗe, shi ga tayi bakinta dauke da Sallama , da murmushi a Fuskar Haj.Fatuha ta Ansa mata Sallamarta, Jin Muryarta ya sanyata Kwaɓe Fuska, cikin Sanin ko ina da ko ina na cikin Parllon ta Dimfari gurin da ta ji Muryarta, zama tayi a Gefenta tare da saura kanta akan Ƙafarta............



Sudanese Army has Called in reinforcements to aid in its fight with its rival, the paraminitary Rapid Support Forces (RSF) Sparking Fear Among Residents In the Capital of Khartoum that the Conflict will intensify....



    Nagartaccen Namiji wanda yake tamkar ingarmar Doki ne a tsaye kan ƙafafunsa, cikin wasu Kayan Sojoji masu duhu, ya juya bayansa da Wata P-cap a kansa, Amma duk da haka, bai hana kyakyawar Lallausar Baƙar Sumar kansa fitowa ba, baƙa ƙirin da ita sai wani shanning take kamar wadda aka sanyawa mai, hannunsa daya ƙame guri kunmansa da A`lamar sarawa, sarawa irin ta girmamawa, Abdel Fattah Al-burhan ne gabansu, yana basu tulin muhimman maganganu, gaba dayamsu kuma sun natsu yarda kasan Umarnin Ubangiji suke ƙarɓa, basu dade sosai suna maganar ba ya Sallamesu.




      Magana mai matukar muhimmanci suke sai su tashi, Wata Amy Toyota ce ta tsaya a gabansu, Da sauri wasu Kofura suka zo suka buɗe musi Motar , shiga suka yi, kao tsaye Driver da ya kasance Soja shima ya jaa, kai tsaye gidan Abdel Fattah Al-burhan suka nufa, tun daga bakin get zaka san cewar an ƙawata gidan iya ƙawatuwa, ga wasu Furanni masu kyau da kamshi da aka jajjare a ƙofar shiga gidan.



     Wani ne da Kayan Sojoji ya buɗe gidan, kai tsaye suka sulale cikin gidan , Chan cikin wata Ƙawatacciyar Rumfa mai kyan gaske aka yi parking.

da gudu aka buɗe musu Ƙofoffin motar , sun dan dauki lokaci kafin su fito a tare, Fuskar Abdel Fattah Al-burhan cike da wani ƙayataccen Murmushi, dai-daituwar junansu yay dai-dai da fitowar Mamma Saymeerh(Matar Abdel Fattah Al-burhan), fuskarta dauke da murmushi sosai, tana zuwa ta Rumgumesa tare da Pack din goshinshi, cikin matuƙar murna ta ƙara rungumesa, shima hug nata yay very tight , fuskarsa kadaran kadahan, ita ba a Murtuƙe ba, ita kuma ba murmushi yake ba.




    Jaan hannunsa tayi suka shiga chan cikin gidan, fuskarta da murmushi sosai, A ƙofar shiga cikin palon ta tsayar da shi, Jacket ɗin jikinsa da ta kasance ta Sojoji ta cire masa, zame takalminsa yay , jaan hannunsa ta ƙara yi cikin palon , shi dai Abdel Fattah Al-burhan yana biye da su, A baya har suka ƙarasa cikin tafkeken palon.



Wata Kawatacciyar kujera da ta kasance ta daban ta zaunar da shi, idanunshi ya ɗaga, bai saukesu a ko ina ba sai akan wani rafkeken photon sa mai kyawun gaske, babba sosai an masa wani packaging mai kyau, A jikin Photon an Rubuta Lt Canal Aliyou Abdel Fattah Al-burhan..

Lumshe Manyan idanunshi yay, tare da dan shafa tattausan bear din sa......"Sitti zan je gidan Uncle Aseef"Ta faɗa tana dan gyara Mayafin kanta, kallonta tayi kafin tace "Abin ci fa ?". Mitsitsin bakinta ta tura cikin shagwaɓa ta dan dira ƙafarta tare da cewa "am Full Maa!". ta fada tana shafa cikinta.

Bata ko kalleta ba, sai ma Kwaɗawa Safreen kira da tayi, jikinta na rawa, ta ƙaraso cikin Parlon , cikin bada Umarni tace "Jeki ki kawo min Abin cin Bim-bim!". ta fada ba tare da duk ta kallesu ba.



     Da sauri ta wuce Dining cikin minutes ta gama haɗa Abin cin ta kawo, center table ta jaa ta daura Abin cin Akai, Cikin bada Umarni tace, "zo!. ki ci " ta fada tana kallon TV .



      Kamar zata yi kuka , haka ta zauna tana cin Abin cih tana rarraba idanuwa, bai fi 3 spoon ba tayi, ta Ajiye Abin cin, direction din da Sitti take ta kalla cikin shagwaɓe fuskarta tace "Sitti na ƙoshi", kallon Abin cin tayi ta kuma kallon ta, bata ce komai ba ta juya da kanta, jin tayi shiru ne yasa, ta matsala, hannun Sitti ta riƙe ciƙe da shagwaɓa tace "Allah kuwa na ƙoshi", kallonta tayi kafin tace "Okay tashi ki je", da murna ta miƙe, Sandarta ta dauka tare da yin waje, tana fita aka buɗe mata Motarta da Aka Ajiye a Ƙofar parlor....Zama tayi a Gefensa tana tambayarsa Aiki, Cikin natsuwarsa yake Amsa mata dukkan wata Tambayar da ta masa, Gyaran murya Abdel Fattah Al-burhan yay, kallonsa duk suka yi, taɓe fuska yay tare da cewa "duk an wani basar da ni, ta Yaronki ma kawai kike", ya fada yana kallon gefe, dariya tayi tare da cewa "Afwan." ta fada tana kallon Abradeen , cikin sanyayyiyae muryarsa yace "let's Fresh Up" ya fada yana miƙewa, cikin kulawa ta jinjina masa kai.




    Cikin Wata iriyar tafiya ta Zaratan Maza, Direct Part dinsa ya wuce, yana buɗe Part din wani sanyayyan ni'imataccen kamshi mai sanyaya zuciya ya ɗaki hancinsa, lumshe idanunshi yay, tare da ƙara shaƙar ni'imtaccen kamshim mai dadin gaske.



     Dara-datan Royal Blue Eyes dinshi ya ware , a Lokacin da ya tabbatar da tsayuwarsa a cikin tsakiyar Makrken Parlor nasa mai dauke da kayan Alatu irin na More rayuwa, Parlor'n ya haɗu har ya gaji da haɗuwa, komai ƙyal-ƙyal very neat , gwanin sha'awa, Parlor'n bai cika Rankwachamai da yawa ba, kuma dai ba za'a ce bb abubuwa da yawa ba.




     Set din Kujeru ne guda biyu a Palon, sai Wani kyakyawan Carpet da aka balale Parlor'n da shi, sai TV dinsa da ta kasance Plasma mai girman gaske, sai wani TV Stand na glass mai masifar kyau, mai fidda wasu kalar kaloli masu kyau, wadda idan aka kunna TV take kawo hasken kallo, red, blue,black, green, purple, Coffee, kaloli dai , ga wasu Manya-manyan Speakers ma a Ajiye a gefe-da-gefen TV'n ga wasu Ams masu kyau,Wani Bango ya kafe da idanu hakan yasa nima na bi gurin da idanu, idona da na kai gurin ne, ya gane min, manya Award da manyan kyatutukan girmamawa da ya samu, ga wasu manya pictures nasa masu kyau, da aka mammana a jikin bango

n, wasu da Kayan Sojoji wasu da kayan gida, pictures dai ma ban-bantan gurare.



    Cikin izza ya nufi wata ƙofa, yana zuwa ya buɗe ya shiga, shima dai kyakyawan guri ne, Faffaɗan Royal Bed ne, ga ba daya jikin gadon madubbai ne da Aka wadata sa da wasu manyan Turaruka irin su Huge Boss, , gefe daya bedside drawer ne da Aka daura bedside lap a kai, dayan gefen kuma babban Mirro ne, wanda aka wadata samansa da turaruka irinsu , HUGE BOSS,KINGSMAN, MOHRA, ASAD,OUD TOUCH (franck Oliver), OUD WOOD(extreme),GUCCI,GIORGIO ARMANI,MR BURBERRY,CLINIQUE,GENTLEMAN, CREED,ROJA PARFUMS OUD.

 sai kuma Wata Wradrop daga bango har bango, Sai Shoes-ra wanda aka jera wasu yan Ubansun Takalma masu kyan gaske da tsada, bayan gama bin gaba daya ɗakin da kallo, ya ƙara nufar wani ƙofar, wadda yana buɗewa ta sadasa da Bathroom, wanda shi ɗin ma ba daga baya ba, don wani ko bathroom din Aka basa ya ishesa rayuwa.

ba tare ya da kwaɓe kayan jikinsa ba, ya sakar wa da kansa Shower , lumshe kyawawan idanunsa yay, yana jin yarda ruwan sanyin yake shiga cikin jikinsa, kyawawan Red lips dinsa ya dan taune, tare da sa Harshensa ya lasa lips din nasa, wani ziro harshi n yay, ya lashe gefe da gefen bakinsa.



      Wani Zazzafan Numfashi ya fesar, tare da furta "Ahhhhhh!", ya fada yana buɗe idanuwansa, zame ribbom din da ya tare tulin sumar kansa yay, tarwatsewa gashin yay ya bazu akan Fuskarsa

, ruwan da ya zuba Akan Fuskar ne ya bawa Gashin damar kwanciya Akan fuskar yay luf dashi, ya jima sosai ruwan na zuba akan fuskarsa kafin ya nanaɗe gashin, ya mayar da shi baya, kashe shower din ya yi, tare da matsawa gefe, kayan jikinsa da suka jiƙe lirif da ruwa, ya fara ƙoƙarin cirewa, Bottoms din riga ya fara zazarewa, har ya kai ga na Sama duka, yana zaresa gaba daya , rigar ta ware, cikin kyankyamin kayan ya fara zaresu, kyakyawar Farar Singlet dinsa ce ta bayyanawa, wadda ta rufe masa gaban sa, sai damatsan hanunsa kawai ake iya gani.wanda suka sha wani zanen Tatoo, wanda ya ƙarawa Baƙar Fatarsa duhu sosai.



     Belt din Wandonsa ya shiga zarewa, har zaresa gaba daya, zip din wanda ya kama, cikim natsuwa ya zugesa,cirewa yay ya haɗa da rigar da ya cire ya ajiye a gefe, tun daga ƙafarsa wanda suka kasance Baƙaƙƙe da Baƙar Gargasa ta gamawa Ƙawanya na fara ƙarewa kallo, zare Singlet dinsa yay, inda Atake a gurin Faffaɗan Kirjinsa mai dauke da Manyan Six packs ya bayyana, Abun har Abu tsoro, sun wani Kumbura sosai, lafafen cikinsa da zaka iya dauka ma babu hanji a cikinsa na dan kalla, Ramin Cibiyarsa da ya kasance Zurun-zurun na kafe da idanu, Boxer dinshi ya fara ƙoƙarin zarewa da sauri na fice daga Bathroom din inda dafe kirji, sakamakon ganin halittar da ban taba gani ba, don ko a Films di indiya bb mai irin wannan packs din, bale kuma a Hausa.



      Ina tsaye a tsakiyar bedroom din ya fito jikinsa na fitar da wani irin kamshin turaren wanka na musamman, ga ruwa na dan zuba, gashin ƙansa da ya kasance kamar na mata ya bi wuyansa ya lafe, kirjinshi da yake cike da gashi ya shafa, tare da fara ƙarewa kansa kallo, taɓe bakinsa yay, yana kallon kan Mirror da aka cikasa da Latest Mayuka And Turaruka masu kyan gaske, da kayan gyaran gashi, Cikin natsuwa da Yanga, ya dauki wani Lotion ya fara mulke jikinsa da shi, bayan ya gama Turare Giorgio Armani da na Clinique ya fesa a dukkan jikinsa, kafin ya fara gyaran fashinsa, baya ya busa da shi, yasa masa mansa, wani kyskyawan Ƙaramin Ribbom mai kyan gaske ya dauka a cikin drawer, Cikin wani yana yi ya tattara gaba daya sumar kansa ya daureta a guri daya, tare da daukar wani turare na musamman ya faffesawa gashin.




       Gurin Drawer ya nufa, buɗewa yay, yana kallon tsadaddun suturun da suke ciki , Wata Farar T-Shirt ya dauka, mai buɗaɗɗan wuya, wanda har ana iya hango gargasar da take kirjinsa, wani Ash Crazy Jese ya dauka, gaba Mirror ya daso, cikin natsuwa yake sa kayan  yana kallon Ƙirar jikinsa da ta kara sauyawa. ta wani mummurɗe.



Bayan ya gama sa kayansa ne, ya zari wasu Takalma masu kyan gaske da sukawa ƙafarsa kyau, Maƙulin mota ya dauka ta fita, ko da ya fito parlor babu kowa gaba daya sun gaji da jiransa sun shiga ciki.




     Waje yay, yana fira Gaba daya Sojojin da suke gidan Suka ƙaƙƙame suna fara masa , cike da bada girma , bai kulasu ba ya nufi wata mota kirar Toyota Benz kalarta kalar Amy Uniform , Da ganin motar zaka san sabuwa ce, komai nata na walwali da ƙyalli gwanin sha'awa, buɗe masa aka yi ya shiga ciki, kai tsaye ya fice daga cikin gidan Yana fita, ya ƙunna Karatun Al-qur'ani mai girma, gaba daya motar baka jin komai sai sautin ƙirar Sheikh Afif Muhammad Taj da take fita a Cikin Suratu Al-Burooj , Cikim sanyayiyyar muryarsa mai dadi da wani irin garɗi yake bin saurim karatun.



       Kai tsaye Hafiz Ahmad Al-Bashir Road ya nufa, da nufin zai je Omdurman.


      


      Go-slow din da ya tarar a hanyar ne yasa ya rage gudun motarsa, kusan 1 hour Go-slow baya raguwa sai ma ƙaruwa da yake, gashi sauri yake, hakan yasa ransa ya dan baci butsu-butsu ya duba Agogon Rolex din da take hannunsa, sai tsaki yake saki, ganin Abun yaƙi ci yaƙi cinyewa ne yasa ya ɓalle murfin motar ya fita, fuskarsa daɗe da Wani Jaan kyalle, idanunshi manne da Baƙin glass .Cikin takun Sassarfa ya nufi inda Cukowar Go-slow din yake .



    Tsaye take, Cikin Blue Abaya, An mata Jelling kanta, ga wani rolling da tayi da Gyalen Abayar, Fuskarta sanya da SunGlass , gefe da gefenta, Zaratan Sojoji ne masu jini a jika.



    

     Gefe daya kuma Motarta ce a Tsakiyar Titin , an daga gaban Motar, Haushi ne ya mugun kamasa, ganin yarda mutane suke ta matsa Horn Amma ko a jikinsu, Cikin Tafiyar Zaratan Maza ya dumfaresu.