BOYAYYEN YARIMA

chapter 13-14

by @autarmama

P.13-14.





     Daya daga cikin Sojojin da suke kamar Escort din Bim-bin yace , "Sir!. it's Lt Canal Aliyu Abdel Fattah Al-burhan", da sauri ya kallesa tare da ƙara furta "Lt Canal Aliyu Abdel Fattah Al-burhaaan!." ya fada cikin tsananin mamaki, ransa har lokacin A ɓace.




      "Yaushe Yaron ya dawo ?, mai kuma ta masa ?", jaan numfashi guy din yay tare da cewa "A titin Hafiz Ahmad Al-bashir Road ne motar ta ta samu matsala, a tsakiyar titi, shi ne aka samu tsaikon Cunkoson Ababen hawa, yana daya daga cikin Wanda Abun ya riƙe, shine har hakan ta faru".



    "Yanzu dama Akan titin Hafiz Ahmad Al-bashir Road hakan ta faru, Amma shine bai san ita wace ce ba ?", ya fada idanunshi har ruwa-ruwa suke.



     "Bani da Masaniyar yasan hakan ko bai sani ba Sir!", ya fada kansa a Ƙasa cikin bada girma, dogon tsaki ya jaa, tare da furta "Stupid Boy!." 



     bayan wani lokaci aka barsu shiga su ganta, ko da auka shuga har lokacjn barcin wahala take, Kunnuwanta an liƙe mata su da bandage .




      WASHE GARI.



   Tun da ya tashi Sallar Subhi bai koma barci ba, don daga Massalaci ma, ya wuce chan bayan gidan , inda Aka zuba musu kayan Game, Kwaɓe Jallaviyar jikimsa yay, ya rage daga shi sai Boxer da Singlet, Motsa jikinsa ya fara da wasu na'u'rorin zamani na motsa jiki, dandanan jijiyoyin jikinsa suka wani fito, cikin kankanin lokaci ya haɗa zufa jikinsa, har wani ƙara budewa yake, damtsen hannunsa yay wani irin ƙato, Six packs dinsa kuwa, ba'a magana, ya tara kwanji sosai yarda kasan dan Resiling .




    Ya kai kusan 1Hour yana motaa jikinsa kafin yaji an turi ƙofa , ɗaga kansa yay, yana sa idonsa kan ƙofar suka haɗa ido da Abdel fattah Al-burhan, shima cikin shiga irin ta motsa jiki, guys dinsa na bayansa, "Good Morning!", ya furta , Cikim dan zafin ran da har lokacin bai gama sakinsa ba, Ƙarɓa masa yay tara da tambayarsa yarda ya tashi, Amsa masa yay, tare da ci gaba da Abun da yake.



    Join nashi yay, shima ya fara Motsa jikinsa, sun dau lokaci sosai suna yi tare duk sun haɗa zufa sosai , Saymeerh ce ta turo Ƙofar ta shigo, Ta ci kwalliyarta cikin Wani dandatsattsen lass mai Azabar kyau, ya biyu sosai a jikinta, sai wani fitinannen kamshi take.



    Shigowa tayi Hannunta riƙe da madaidaicin Tray ,mai dauke da flask da wasu cups guda biyu, sai kuma sugar da take cikin kwali, "Oooh Yan Samarina Sannunku da Aiki", ta fada fuskarta da raha, Abdel Fattah Al-burhan ne ya Amsa , yana kallonta.




     Wani table ta ja tare da Ajiye tray din akai, Sauka duk suka yi daga kan Machines din da suke motsa jikim suka zo gareta, tare da zama gefe da gefenta, Towels na goge zufa ta miƙa wa kowa, goge fuskarsu da kirjinsu suka yi, tare da miƙa mata, Ajiyewa tayi kafin ta hau Haɗa musi Coffee'n ƙa'ida.



     Sugar ta fara zubawa, daya ta sanya tea spoon Huɗu dayan kuma tasa biyu, motsa musu tayi ta basu, ƙarɓa duk suka yi tare da kah wa baki, yana ƙurɓa ya haɗiye dakyar, Ajiye mata Cup din Coffee'n yana yamutsa fuska.



      "Ni fa na gaji da wanan Sangartar taka Zaki, yau kuma me ne ?", ta fads tanz kallonsa,nuni ya mata da ta sha ta ji, bb musu ta kai bakinta ta ƙurɓa, kallonta tayi tare da cewa "A wannan dai ko tested din Sugar babu", ta fada tana kara kallonsa .




     "Green tea", ya fada yana wani yamutsa fuskarsa yarda kasan mace, "bazan iya ba Zaki, Aure zan ma, gwara ma ka zauna ka fara tunanin mata in ba haka ba Wallahh Auro ma zan, ko ta ma ko bata ma ba, ko na ma Auro ma Ƴar gidan..."yarda ya tallafe fuska ya tsaya yana kallonta ne yasa ta kasa ƙarasa maganar tayi shiru, dariya ce ra kama Abdel fattah Al-burhan yana nuna su, suma duk Abun dariya ya basu.



Sudanese Amy....



   Da dukkan natsuwarta take tafiya kanta a Ƙasa, hannunta riƙe da wata Sanda mai kama da Sandar gold , an zuba mata wani zaiba-zaiba, "Mangana!", Chak ta tsaya zuciyarta na dukan ukku-ukku, dariya yay tare da riƙe hannunta,cikin kula yace "Your Highly Welcome Mangana!", cikin tausasa maganarta tace "Uncle Aseef!", cikin jin ta har cikin jinin jikinsa yace "kina lafiya ?", jinjina kanta tayi kafin tace "Alhmdulillah.Anty fa ?", " tana gida , mai kika shigo yi ne ?", kafin tayi magana, taji kamshin turaren da ba zata taɓa mantawa da shi ba, da wani irin sanyin mai shiga cikin ƙashin da shima ba zata manta da shi ba ya daketa.



     Cikin dan sauke sanyayyen numfashi, da wani dan tsoron da ya fara shigarta, ta ƙanƙame jikinta, lips dinta na ƙasa ta fara tsotsa a hankali, tana kallon guri daya.



     Tafawa suka yi da juna, Uncle Aseef ne ya ce "Yane Buddy ?", yatsina fuskarsa yay, cikin natsuwa yana shafa gefe dayan gashinsa, jela daya ta gashinsa ya kama yana dan jaa , yana lumshe idanu ,A gefen da Aka kwashe An yi wani shiga, An karshe gurin sosai, inda yay wani irin kyau na musamman

.



     "Alhmdllh!", ya furta a Gajarce, "My Lil!", ya faɗa yana nuna ta, bai ko kalleta ba ya ci gaba da tafiyarsa, shima bai ƙara tanka masa ba ya ja hannunta suka wuce.



      5pm ta fito daga Gidan Uncle Aseef zata koma gida, tafiya take kanta a Ƙasa bata , tana tafiya tana dogara sandarta wadda ita ce ta zame mata jagora idon gani.



    Shima dawowarsa daga Gida kenan zai dauki Wasu Files da ya manta, kuma Ana buƙatar yin Amfani da su Urgently, yana tafiya yana wani bonsing , ya chanjo wanka cikin wasu yan Ubansun ƙananan kaya da suka matuƙar dacewa da zubin tsarin jikinsa, ya sha wando pancil blue back , da wata farar riga da Aka mata tambarin Sudanese Amy, kansa ba hula, gashinsa da bai samu zarafin daurewa ba ya wani bazo masa, hat kan fuska, yana tafiya yana dan tattarewa,sai jaan tsaki yake,Yana tafe yana latsa waya kansa a Ƙasa.



    Wani Mummunan karon da suka firgita suka gwabza, kowannensu komawa yay baya, ya dafe kansa, don sun yi wani irin ƙaro, sosai, A harzuƙe ya Dago kansa, da niyyar suburbuɗar wanda yay masa hakan.



      Yana ɗaga idanunshi suka masa tozali da ita, ta koma gefe daya tana mulmula kanta, a wani side din kuma ga wani masifaffen sanyin da ya Addabawa rayuwarta, har wani zazzaɓi-zazzaɓi ne ya kamata, "Stupid.Idiot Gal!, na tsani ganin Mumu face naki", ya fada yana jaan wani kyakyawan tsaki Alamar ransa yay masifar ɓaci.




     Wani hawaye da bata san daga inda suke bane suka wanke mata fuska, "Tun da take a Rayuwar girman da tayi cikin Ƙasar Sudsn, bb wanda ya taɓa wulaƙantata balle ya mata cin mutumci kalar wannan, kullum kuma kowa ganin darajarta da girmanta yake, yarda Ake girmamata da ganin mutuncinta ma har ba'a magana, Amma gashi Yanzu Mutumin nan 2× yana shiga jikinta yana mata mummunzn yanka.



    Dakyar ta samu zarafin da ta iya ɗaga ƙafafunta ta bar gurin.



     Haka rayuwa ta ci gaba da tafiya, da dadi da ba dadi hat Aka ƙulla watanni masu dan dama.



Har Allah yasa ta gama karatunta tas a (KICS) bata sha wahalar neman Aiki ba kasantuwar dama Malamar lafiya ta karanta, gashi kuma tana tare da Manyan jiga-jigan sanannun Sudan, hakan yasa su bb abun da yake musu wahalar samu.



     Babbar Asibitin Khartoum aka kai ta, Uncle Aseef ne ya shiga ya fita ya mayar da ota Aiki cikin babbar Asibitin da take cikin Sudanese Amy.



     Dole Ta koma gidan Uncle Aseef da zama, haka take fita Aiki kullum da safe, sai Addu'a take kada ubangiji ya taɓa haɗata da shi, har ta samu ta bar ƙaddararriyar Asibitin.

haka har ta cika wata daya a Cikin Asibitin ,ko mai kalar kamshin turarensa bata ji ba

.



     Suna zaune duka A parlour suka ji Ana knocking sandarta ta dauka ta nufi gurin Kofar da ake knocking

., tana buɗewa ta ji An bankaɗata baya, "Blind!", kalmar da ta daki dodon kunnanta kenan, da sauri ta kama jikinta tana matsawa baya, don muryarsa kawai ta ji , taji gaba daya ta tsani kanta,tana kuma nadamar zanta A cikin barikin Sa boda yarda yake gasa mata maganganu




    Raɓata yay ya wuce zuwa ciki, "Aseef!", ya ƙira sunan Uncle Aseef yana furzar da huci daga bakinsa da hancinsa, Wani Ƙaramin Abu Uncle Aseef ya fito da shi a Hannunsa, kafin ya ƙarasa gurinsa, shi ya ƙarasa, ƙarɓe Abun yay, ya fita, sai da yazo dai-dai gurinta kafin ya jaa wani irin dogon tsaki, da ba shi wanda ya yi sa ba,har ita da yawa sai da ta rumtse idanunta, don tsokin ya tafi cikin wani irin fushi.




      Da daddare tana kwance a Bedroom dinta taji tashin kiɗa kamar A cikin Bedroom din Ake yi

, A zabure ta tashi, tana karanta dukkan Addu'ar da ta zo bakinta, ta tsorara sosai da yana yin yarda kiɗan ke tashi, ga wani irin duma na Musamman da yake dukan zuciyarta.




    Saitin zuciyarta ta riƙe tare da lumshe idanunta, Cikin wani yana yi, Ka jurewa tayi ta dauki sandarta, daga ita sai kayan barci ta fito, kan ta ko dan kwali bb , ta dauresa da wani baby peach .




     "Lafiya?.mai ya fito da ke yanzu?", Uncle Aseef ya fada yana kallonta

, A hankali tace "Tashin kiɗa, Hayaniya bazan iya barci ba", ta fada tana raƙi guiwar hannunta, "Zaki!", ya furta yaba furzar da iskar bakinsa, "Okay yanzu shiga Room din Maman Rafeeq , ni zan kwanta a Na ki", cikin ladabi ta Amsa masa.



     Wucewa tayi ta shiga, shima ya wuce nata, Kwanciya tayi Gefen Maman Rafeeq, Amma ta kasa barci duk inda ta juya sai ta ji kalmar "Blind!", din da ya kirata da shi ta daki dodon kunnanta,idan kuma ta rufe idanunta, to sautin kiɗan da kalmar ne suke mata yawo Aka.




       Rasa yarda zata yi tayi, ta kasa barci har dare ya raba tsakiya, har kuma lokacim kiɗan da yake tashi bb alamun za'a kashe ko a rage, sai ma sautin da ya ƙaru, sakamakon dare da kpwa ya natsu, bb hayaniya da cunkoso hakan yasa sauti ko ya yake sai ra ringa Amsa ƙuwwa.




     Sai kusa da Magrib sosai barci ya dauketa, hakan ne yasa dakyar ta tashi Sallar Asuba, tayi Sallah tana jaawa Zaki Allah ya isa domin shi ne nan ya jaa mata ƙasa barci har ta kasa tashi sai da kyar...."Jiya fa ka Hana min Ƴa barci don haka zaka biya tara", Uncle Aseef ya fada yana kallon Zaki, da yake gefensa, taɓe bakinsa yay bai ce komai ba, "ya kayi shiru ?, baka ce komai ba ?", ya tambayesa, yana hawa wani machine na motsa jiki.



     Kamar ba zai ce komai ba sai kuma chan yace "Who is she ?," "Ƙawar Faɗarka," Kallon ban fahimta ba ya masa, shi kuwa kallon ka gama raina Min hankali ya mishi.



     Har suka gama bb wanda ya ƙara magana, don shima Uncle Aseef din in yasa kansa Miskilin ƙin ƙari ne.



     Bayan sun fito Aka kawowa Uncle Aseef Mota , zai je Hafiz Ahmad Al-bashir Estate sakamakom kiran da Abier (Hafiz Ahmad Al-burhan) ya masa.



    "Mu je ka raka ni" ya fada yana Ƙarɓar key'n mota a Hannun Yaron da ya kawo masa mota, "You Know By 8 O'clock , zan shiga Meeting da Lt General Right ?", ya fada yana kallomsa da lumsassum idanunsa, "I no.

ba zamu kai lokacin bamu dawo ba".



      Bai son jayayya dan yanzu kansa ya fara ciwo, hakan yasa ya balle gaban motar ya shiga ya zauna, Jaa Uncle Aseef yay, shi kuwa kwantar da kansa ya yi A sit din motar, tare da jona Tafkekiyar Wayarsa , ɗaɗɗar Ƙira'a 'Sheikh Afif Muhammad Taj' ne ya fara tashi, cikin ƙwarewa da iya karya harshe.




     Lumshe idanunshi yay, yana saurarar karatun, har suka ƙarasa cikin Estate dim idanunshi a lumshe