BOYAYYEN YARIMA

chapter 15-16

by @autarmama

.P. 15-16.





     Har suka iso Get din Chan cikin gidan Hafiz Ahmad Al-bashir, idanunshi na lumshe, Uncle Aseef ya gama dauka barci yake, hakan yasa bayan gama parking nasa ya fara dan daddaɓarsa tare da cewa "Zaki! Zaki!! Zaki!!!", lumsassun idanunshi, irin na wanda ya shawu bai gama wartsakewa ba ya watsa masa, da ido ya masa A`lama da sun iso, siririn tsaki ya jaa, kafin ya buɗs motar ya fito, Uncle Aseef ya shiga gaba yana binsa A baya har suka shiga cikin babban Parlor'n bb kowa a Parlour'n Ƙasa hakan yasa suka nufi Upstairs

ko da suka Shiga Sitti kawai suka tarar, Hakimce a Kujera tana kallon Tashar Aljazeera A TV .

Cikin natsuwa ta juyar da kanta garesu, tana Amsa Sallamarsu, Da fara'a A fuskarta, tace "Lale Marhabun da Sojawa!", Uncle Aseef ne yay murmushi yana gaisheta, shi kuwa Ogan Fuskarsa kadaran kadahan Ya gaisheta, Kafin su gama Gaisawa Hafiz Ahmad Al-bashir ya fito daga Wata Ƙofa , yana sanye da wata Milk Jallabiya sai kamshi yake.



     Miƙewa suka yi Suka sara masa, tare da Zubewa cikin Girmamawa suka gaishesa, kasantuwarsa na Wanda ya Taɓa Riƙa muƙami shigen na Mahaifin Zaki, Ya yi Hafsan Sojoji, Sannan kuma A matsayin Yayan Mahaifiyar Aseef, Abubuwa dai iri-iri



 

     "Sannu da Fitowa Babu!", Uncle Aseef ya fada cikin ƙanƙar da kai, jinjina kansa ya yi, dubansa ya kai ga Aleeyou Abdel Fattah Al-burhan da tum bayan gaisuwar da ya masa bai ƙara ɗagowa da idanunshi ba, "Oh Hydar , naji Tsamar da kake da Bim-bim dina , me ne matsalar ka da ita wai, ko kana ciki ne ?", ya faɗa da dan zaulaya,kyawawan idanunshi ya ɗago yana wawwaresu, 'BIM-BIM' ya maimaita sunan cikin ransa, "Nop at all!", ya fada cikin ɗan karsashi, rausayar da kai yay , kafin ya juya gurin Uncle Aseef .



      Ba su wani jima a Gidan ba suka fice, Suna tafe yana ta ƙara tunanin Sunan da Aka kira Yarinyar da shi, sai ya ji sunan wani iri, kamar ma dai ya taɓa jin sa Amma a ina ?,yaushe ?, duk bashi da Amsar tambayar.



     7:30Am suka shigo cikin Barack din, Kowa yana harkar gabansa, Yara yan makaranta na tafiya, masu zuwa guri Aiki ma haka, Kamar dai itama , tana Sanye da fararen Kaya irin na Maluman Asibiti, tana tafiya cikim natsuwa, fuskarta manne da wani Sunglass , ƙafarta sanye da takalmi Combos , Tana rataye da wata jaka mai kyawun gaske, hamnunta yana riƙe da wata kyakyawar sanda, ba wacce ta saba Amfani da ita kullum da ko yaushe ba.sai faman Murmushi mai kyau tske, wanda yake bayyanar da kyakyawar wushiryarta da take tsakankanin kyawawan fararen haƙoranta , masu sanye da haƙoran Makka Har biyu, hakan kuma ne ya ƙarawa fuskarta wani irin sheƙi na Musamman.




      Gefen ta Wani kyakyawan matashin likita ne, mai jini a Jika,fari ne tas da shi kamar ka taɓasa jini ya fito, yana sanye da wasu Suit masu bala'in kyau, shima ya sha glass, suna tafe suna firarsu, kyawawan idanunshi ya lumshe yana furzar da iska.



     Idanun Uncle Aseef ne suka Faɗa kansu, Wani irin jaan burki ya yi, tsorata tayi, tayi gaba zata kifa, da Azama Kyakyawan Saurayin da yake gefenta ya riƙeta, ɗagota yay ya sanyata a jikinsa, hakan kuma yay dai-dai da buɗewar kyawawan idanuwan 'ZAKI' da sauri ya mayar da idamunshi ya lumshe.



     Uncle Aseef kuwa dakyar ya iya jaan motar suka ƙarasa gida, Ana zuwa ƙofar gidansa, ya fice ya bar Zaki a motar, shigewa ciki yay ransa a matuƙar ɓace yana huci.


   


      Oum Rafeeq ya gani Zaune tana Feeding Ƙaramar Ƴarta Naana, "Khadeeja Waya bawa Yarinyar chan damar Fita da wani Ƙato waje ?", Cike da Tsagwaron Mamaki tace "Wacce Yarinya ?", Cikin tsawa sosai yace "Ke bana son rainin Wayau, wacce yarinya ce kike zaune tare da ita, da har ina tambayarki kina tambayata, kin sha Omo ne ?" ya faɗa idanunshi Jaajir.



     Cikin Faɗa itama tace "Ka ga Malam ka dai na min Shouting Aka, ka Ajiye ni dama, dan na ringa bibiyar da wanda take tare ne ko kuwa ?." ta fada cikin nata zallar ɓacin ran.



     "Ni kikewa Tsawa Khadeeja ?"."Na maka tsawar Aseef taya zaka zo ka rufe ni da Faɗa Akan Abun da ban sani ba, Na farko dai Yarinyar nan tunda ka kawota ka Ajiyeta, ai kasa Aiki take zuwa, Rana daya ka taɓa binciƙar da wa take zuwa, ko sai yau zaka sauke min kwandon tijararka a ka ?" ta fada ido rufe .



    "Ni kikewa Tsawa ?". "Na maka ɗin. nace na Maka Aseef", 'Tasssss' kake ji ya wanke ta da wani irin mari, riƙe ƙunci tayi Cikin Ta'ajjudi take kallonsa, "Saboda Hauwa'u ka duke ni Aseef ?".



      "Na duke ki Khadeeja", kaɗa kanta tayi ta shige Bedroom nata.Dafe kai Yay, tare da faɗawa kan kujera, buga kansa yay da hannayensa, cikin dan ƙaraji yace "What's wrong with me ne ?", ya faɗa yana fesar da zazzafan numfashi daga bakinsa, tare da barbaza gashinsa har izuwa fuskarsa.




       Yinin ranar Haka suka yini tsakanin Uncle Aseef da Oum Rafeeq, bb wata fahimta a tsakaninsu, shi ya kasa fahimtar ita bata san da wa Bim-bim ta fita ba, ita kuma ta kasa fahimtar Mai yake faruwa a Tsakanin Mijin nata da kuma Bim-bim da har yake mata shouting akanta.



      Sai ta ji duk ta tsani Bim-bim, wani irin haushinta na zuwar mata, zallar kishi da kuma ƙunar rai ne ya zo mata a Wuya ya tsaya ya kasa wucewa.



     Da Misalin Ƙarfe Biyar na Maraice ta dawo daga Hospital tana tafe tana, dan sauri sakamakon iskar hadarin da ta fara kaɗawa Alamar gab Ake da fara ruwan Sama, tana tafiya tana sauri, Tsayuwar mota taji a gabanta, kafin ta yi wani yunkuri Aka dauketa ɗab tare da sanyata A bayan mota, da wani irin Speed aka jaa motar, direct fita yay daga ciki Barrack din ya dauki hanyar, shiga chan cikin Khartoum, gudu yake tsulawa na fitar hsnkali, ita kuwa ihu take tana dukan glass, tayi - tayi ta buɗe murfi ta Fita Amma ƙofar taƙi ta buɗu, Hankalinta yay matuƙar tashi, gashi sai laluɓen nema inda Driver yake ma ta kasa samu.



       Bai tsaya ko ina a sai cikin Babban Hotel din da yake cikin Babban Birnin Khartoum, sai da ya iso cikin Hotel din kafin ya yi parking A parking space, Kansa ya kwantar a Sit din , ya lumshe idanunshi, numfashinsa na matuƙar fita da sauri-sauri kuma zafi-zafi.



       Jin a Tsaya ne yasa ta fara dukan ƙofar iya ƙarfinta, ssndarta ta laluɓa ta fara dukan ƙofar, Kasantuwar Ƙofar bullet Proof ne yasa duk dukan da take mata ko Alamar fashewa ma Glass din bai yi ba.


 

      Buɗe motar Aka yi, sai ji tayi An dauketa ɗab , Ƙafafunta ta shiga haharbawa

, tana dukansa , don ya sauketa Amma ko gyzau, haka da ita Akan kafadarsa ya shiga Cikin Hotel din, kai tsaye VIP ya nufa, ko tsayawa Buɗe Ƙofar room dim bai yi ba, ya bankaɗa ya shiga, Parlour'n ya wuce ya shiga Cikin Bedroom .




        Yana shiga ya makata Akan Gado, ihu ta saki mai tattare da Salati Cikin tsorata, ta dafe Goshinta da ya mugum buguwa, kanta ya wani irin sara mata.




      Ciki wani irim kula tace "Who are you ?,mai na maka ? mai kake so a gare ni ?", ta jero tambayar cikin tsorata tana ƙanƙame jikinta.



      Banza Ya yi da ita bai Amsa mata ba, 

"Nace waye kai ? mai naka zaka dauko ni ?,mai kake so a gare ni ne?, " ta fada cikin tsawa, Ba'a kulata ba, Cikin tsantsar rashin ta ido tace "Wane iskanci ne zai sa ka dauko ni, mai kake shirin Aikata min , mai kake so ne ?" ta fada tana murguɗa baki da jaan tsaki.




     Matse mata bakinta ya yi, kuka ta saki mai cin rai, jin yarda ya matse mata baki, shi kuwa cikin rashin imani, ya shiga mammatse mata bakinta, yana jaa har sai da ya fara jini, idanunta na zubar da ruwan hawaye, ta shiga yayyarfa hannayenta, tana kuka, tana riƙe hannunsa ,Wasu Uwayen Jijiyoyi taji A hannun, kamar ba na mutane ba, wani irin babba, ga jijiyoyi.




      Sai da ya tabbatar da lallasuwarta kafin ya saki bakin, da sauri ta sa hannayenta ta riƙe bakinta, tana kuka, cikin takaici tace "Allah ya isa, mugu ,Ɗan iska, Mai hannun Gardawa, ban yafe ba, Azzalumi, kuma ka mayar da ni gidan mu, idan wani Abu ya sameni , Sai Babuna Ya kasheka da bindigarsa" ta fada tana kifa kanta a jikim pillow.



    Bai saurareta ba ya fice Abun sa, Key yasa ya datse Ƙofar ya tafi Abun sa.




    Har 9pm babu ita babu labarinta, Uncle Aseef sai zirga - zirga yake ya kasa zaune ya kasa tsaye, "Khadija ina Aysha?", wani kallo ta masa tare da tattarasa ta watsar, shima ganij irin kallon da ta masa yasa ya sha jinin jikinsa, sai yanzu ya fara tunanin rashin dacewar Abun da ya mata, haka ya ringa zagaye tana kallonsa ta sharesa.



     Har ta gama shirin barcinta ta kwanta bai sa natsuwa, sai ya fita, ba zai fi rabin Awa ba sai ya dawo, haka yake ta zagaye, ita dai ta zuba gaba daya Al'amuransa tasa a Shara.




      Yarda ya ga rana haka ya ga dare, ya kasa ko rumtsawa, sai juyi yake, kaɗan kaɗan ya leƙa window ya dawo, har garin Allah ya waye.



     Kamar kullum da suka fito daga Masallaci kasa zuwa gurin motsa jikinsu ya yi, gida ya koma,

Idanun Zaki Akan Uncle Aseef har ya shige gidansa, taɓe bakinsa ya yi, tare da sosa tsagun girarsa, wata iska mai sanyayyan kamshi ya fesar, tare da wucewa Gurin Motsa jikinsu.




      Ya dade sosai A gurin kafin ya fito ya nufi gidansa, Cikim sauri sauri ya shiga wanka ya fito, shirya kansa ya yi a cikin wasu Ƙananan kaya masu kyau da tsada, ɓarin turaruka ya shiga yiwa jikinsa, babu ƙaƙƙautawa har sai da ya fara jin turaren yana hawa kansa kafin ya Ajiye.




    Tsaf ya fito da shi cikin shirin fita, yana fitowa Aka buɗe masa Mota, shiga ya yu, tare da gyara zamansa, jaan motar Aka yi, kai tsaye

Second Sudanese Civil War suka nufa, suna zuwa motar ta koma shi kuma ya shiga ciki.




     10Am Ya turo Ƙofar Bedroom din, yana sanye da wani Three quarter  Baki da Wata Armless fara Qarrrr A jikin rigar An zana Damusa, A ƙasan damusan Aka rubuta 'Tiger' ,Hannunsa riƙe da Tabar Wiwi, gaba daya fuskarsa bata ganuwa sakamakon Hayaƙin da ya rufeta.




      Idanu ya zuba mata yana kallon yarda take tirje-tirjen Azabar ciwon da ya ishi rayuwarta, Ƙafarsa daya ya daura kan gadon da take dayar ƙafar kuma tana ƙasa hannunsa riƙe da Tabar Wiwin da yake ta zuƙa, Tari ne ya tsarketa , Cikin muryar da bata fita ta ce "Malam kai waye ?, kai wane irin marar imani ne ?, mai kake so tare da ni ? mai nai maka ?", ta faɗa A galabaice, shiru bai Amsa mata ba.




     Cikin kuka da hawaye sosai tace "Allah ya isa, in sha Allah kai ma sai An sace wani naka kaji in da dadi, Mugu Azzalumi , macuci , D....", kafin ta ƙarasa ya yarfa mata wani irin Masifataccen marin da yasa sai da ta ƙifa.



      kasa ɗagowa tayo sai kawai ta ƙarasa kwanciya tayi lebur, Ficewa ya yi daga Ɗakin ya ƙara rufeta, bai damu da ci da shan ta ba ya rufe yay tafiyarsa.......