FIL HUB

Babi na biyu

by @billysfari

 Free page 2

 

    *FIL-HUB*♥️

           (Acikin so💘)

Paid Book: N500

  Written by

     Billy s fari💎

______________________________

  Dole Madiyam ta zauna ƙasa tare da miƙawa Sadi mai ɗori ƙafar tana faɗin, "don ALLAH kaji tausayina kada kayi mun da zafi ka ji sadi?, ALLAH gobe zan kawo maka wani abu idan Abbu na ya siyo mun".


Dariya Sadi mai ɗori ya yi yana mammatsa kafar haɗe da cewa, "To ƴar gidan Abbu kidai tsaya kurum kinji ko?" ya ƙare zancen tare da danna wajen da yake tunanin taji ciwo, yarfi ta shiga yi da hannuwa tana kiran Abbu shi kuma Sadi mai ɗori ya cigaba da aikinsa, sai daya mammatsa kafar ko ina ya gama gano inda matsalar take sannan ya ɗago kai ya kalli Hisham daya juyar dakai gefe yana latsar wayarsa ya ce. "Targaɗe ne taji, don haka sai an ɗan tsaga ƙafar saboda jinin daya kume mata a ciki yafita, ka anso mana reza a wannan shagon". Ya ƙare zancen yana nunawa Hisham wani shafi dake tsallake yana kallon na Sadi dake saida kayayyakin abinci.


"To" ya faɗa a miskilance haɗe da miƙewa ya juyo yana kallonta murmushi ɗauke akan fuskarsa wanda kana gani kasan na mugunta ne sannan yabar wajen, ko mintuna uku ba ayi ba ya dawo da reza guda biyar a hannunsa ya miƙawa Sadi, dariya Sadi ya yi yana miƙa hannu ya ɗauko ɗaya yana faɗin, "Ai ɗaya ma ta isa malam Hisham".


Ɗago kai ta yi ta kalli rezojin dake hannun Hisham sannan ta kallesa ya maka mata harara tare da ajiye su agaban Sadi yana faɗin, "idan yaƙi tsayawa kasa duka rezojin ka tsage Mata ƙafafuwa don tsaf zata iya cewa guduwa za tayi". Ya yi zancen kamar bashi ke maganar ba haɗe da yi gaba yanaɗaga kiran daya shigo a wayar tasa sannan ya kara a kunne, Madiyam kuwa tana ganin Sadi ya nufo ƙafarta da reza ta tsala ihu haɗe da miƙewa tana ɗingisa ƙafar zata bar wajen da sauri da sauri don baza ta iya gudu ba, Hisham kuwa dama wayar kawai yake yi amma duka hankalinsa na akan Madiyam, hakan yasa taƙa biyu zuwa uku ya yi ya damƙota tare da maidota wajen Sadi dake faman dariya, har lokacin wayarsa na a kunnensa ba tare daya tsinke taba, haɗe hannayenta waje ɗaya ya yi ya riƙe yana sake ɗaure fuska tare da galla mata harara, wanda hakan ya sata natsuwa haɗe da runtse idanuwa lokaci ɗaya, Sadi na riƙo ƙafar ta shige jikin Hisham jikinta na rawa, lumshe idanuwa ya yi haɗe da buɗe wa ya saukar dasu akan kyakkyawar fuskar tata data kame idanuwanta ta runtse sosai, yana tsagawa ta saki wata irin ƙara haɗe da saita bakinta akan hannun Hisham ta cije sosai, ba tare da ko gezau ya yi ba yaci gaba da amsa wayar yana kallonta har aka gama tsagar sannan ta cire bakinta daga cizon data yimasa haɗe da zubewa ƙasa wajen tana kuka, yanda ta wage baki ya sa Hisham sakin dariya har yana riƙe cikinsa haɗe da kallon hannun nasa da har shape ɗin haƙwaranta da suka shiga cikin fatar jikinsa ya fito tare da fasawa, yarfar da hannun gefe ya yi tare da ɗago kai ya kalleta, dai dai lokacin Haisam yayansa dake waya dashi ya shiga tambayarsa ko lafiya jin yanda yake kwasar dariyar da mawuyacin abune kaga ya yi irinta, sake yarfar da hannun ya yi don ba ƙarya yana jin zafi wajen data kai masa cizon ba kaɗan ba haɗe da cewa "Wannan baƙauyar ce Madiyam, baka ji ƙarar kukanta ba?".


"Naji, Me kayi mata ne halan kuma ka koma kana yimata dariya?". ya tambayesa cikin muryar dake nuna rashin jin daɗin abunda ya faɗa, taɓe baki ya yi haɗe da kallon Madiyam data gaji da kukan ta koma kalar tausayi sannan ya ce "Me dai ta yi mani zaka ce, ALLAH yarinyar nan ina ganin kura ce".


"What ever dai Hisham kaji tsoron ALLAH kadena cin zalinta, ko da yake laifin Mahmah ne wlh ita ke ɗaure ma kana takura mata".


"look ya Haisam, baza ka gane bane wlh, trouble girl ce yaƙin ƙari..." nan ya shiga labarta masa abunda ya faru har lokacin idanuwansa na akantanta yana kallonta, yana gamawa Haisam ya yi murmushi haɗe da cewa "Sosai naji daɗin wannan cizon data yimaka, don wlh ko nine sai nayi maka fiye da hakan, haka kurum kabi ka takura yarinya ba tada wata wal...." Kafin ya ƙarasa Hisham ya katse kiran don ya fara gajiya da surutun yayan nasa, da ace shine ke zaune gidan ya tabbata ba abunda zai hana sakalcin Madiyam yafi hakan, don bazai taɓa ganin lifinta ba idan tayi laifi sai dai kawai ya goya mata baya kamar yanda Abbu keyi, juyowa ya yi ya kalleta haɗe da cewa,


"Natafi ne na barki anan zaki iya zuwa gida da kanki idan kin gama hutawa?"


Girgiza kai ta yi haɗe da miƙewa da ƙyar ta wuce gaba, shi kuma ya ciro ɗari biyar ya miƙawa Sadi mai ɗori dake miƙo masa wani magani daza a riƙa shafa mata awajen, godiya ya yi masa bayan ya karɓi maganin shi kuma ya ƙarɓi kuɗin sannan ya bi bayanta, so yake ya taimaka mata ganin yanda ta jan ƙafar amma yanda ta kumbure fuska yasa ya yi banza da ita yana cigaba da binta a yanda take tafiyar har suka isa gida ya bawa Mahmah maganin sannan agurguje ya ɗibi ruwa ya yi arwal saboda har antada sallah ya nufi masallaci, Abbu dama shima lokacin daya shigo har an kira sallah shiyasa ya yi arlwala ya wuce masallaci tun kafin su dawo, Mahmah ma sun sameta tana arwalar itama ta yiwa Madiyam dake faman jan ƙafa kallo ɗaya ta ɗauke kai haɗe da karɓar maganin tana ƙumshe dariyar dake zo mata ganin yanda duk tayi sanyi ta marairaice fuska, turo baki Madiyam tayi kafin ta duƙa ta ɗauki butar ta soma yin arwalar itama, tana kaiwa ga ƙafar da aka yimata tsagar ta yayyafa ruwa kawai ta miƙe abunta ta nufi ɗaki, zaune ta yi haɗe da miƙe ƙafafuwanta santal sannan ta kabbarta sallar daga zaune tana yi tana russuna kanta idan ta zo ruku'u haka ma wajen sujada tana sake duƙar da kanta sosai fiye da yanda tayi a ruku'u, haka tayi sallar har ta gama ta sallame, da yake kuma ba laifi tunda anhalasta yin hakan sai Mahmah bata ce da ita komai ba, sannu ta yimata haɗe dayin murmushi sannan ta ce,


"In Jin da sauƙin ko Madiyam?" Ta ɗaga mata kai ba tare da ta ce komai ba tana ci gaba da laziminta don ko magana bata son yi saboda yanda take jin zafin ƙafar, da haka aka kira sallar ishah da yake babu wani dogon lokaci tsakanin sallolin yanzu saboda sauyawar lokaci, nan ma a zaune Madiyam ta sake yin sallar ishah ɗin jiki a mace, tana gamawa ta koma tayi baya ta jingina da kujerar dake bayanta, ita kuma Mahmah ta miƙe ta je kitchen tana ɗauko abincin da za ayi na dare tana jerewa akan dardumar dake can gefen kujeru inda suka saba cin abinci gaba ɗayansu, Madiyam kuwa tuni baccin wahala ya soma ɗaukarta, tana jin sallamar Abbu ta wartsake tare da fashewa da kukan da tunɗazu take tanadinsa kafin ya ƙaraso, dai dai lokacin kuma aka kawo wutar nefa data haske gaba ɗaya falon dake ɗauke da ƴan madaidaitan kujeru saiti ɗaya masu kyau da kuma fridge a gefe, da sauri Abbu ya ƙaraso wajen don Mahmah bata faɗa masa komai abunda ke faruwa ba ganin yanda ya shigo gidan a gurguje yana so ya samu jam'i.


"Madiyam ɗin Abbu! Wa ya taɓa mun ke haka kuma?, me aka yiwa yarinyar nan?" Ya faɗa yana kallon Mahmah ganin yanda idanuwanta suka kumbura, har za tayi magana sai ga Hisham ya shigo haɗe dayin gyaran murya ya ce, "Ba abunda akayi mata Abbu, wajen rashin jin maganarta ta je ta faɗa a kwalbatin ƙofar gida, shine fa ta jima ƙafarta". Ya ƙare maganar tamkar bashi keyi ba haɗe da zaunawa saman kujerar dake facing ɗinta yana jifarta da wani irin kallo dake nuna ki shiga taitayinki, sai data haɗiye wasu yawu masu ƙarfi haɗe da tsaida kukan da takeyi sannan ta tura kanta cikin jikin Abbu daya rungumota. "Haba mamana, meyasa kikeyin abunda zai wahalsheki haka?"


"Abbu to ba shi bane!" Ta faɗa can cikin jikin Abbu data tura kanta,


"Waye? Hisham ko?" Ya tambayi kansa tare da bawa kanshi amsa yana kallon Hisham.


"Eh Abbu". 


"Ahaf dama ai nasan kwanan zancen, yanda na ji yayi karaf ya amshe zancen daga shigowarsa ya sa nasan shiga taɓa mani ke, ƙyalesa ni dama tunda ya kirani a waya haɗe da cewa yau zai dawo nasan sai anyi ta tsakanin ke dashi, yi haƙuri zanyi masa faɗa bazai sake ba kin ji ko?"


"To Abbu, bacci zanyi" ta faɗa a shagwaɓe tana ƙara narke masa a jiki, ɗagota ya yi ya ce,


"Kinci abinci ne?"


"Ai Mahmah bata bani ba, kuma yunwa nake ji sosai".


Ɗago kai Abbu ya yi yana kallon mama dake zaune gefe tana kallonsu haɗe da cewa, "yanzu fisabilillahi kinsan halin da yarinyar nan ke ciki zaki bari ta kawo wannan lokaci bata ci abinci ba, haba maman Hisham wannan wane irin abune haka?"


"To ai basu jima da dawowa gidan ba daga wajen Sadi mai ɗori, kuma suna shigowa Sallah muka tsaya yi daga ni har ita, da ina yimata magana ma ƙyaleni tayi balle naji ko zata ci abincin, gata nan zaune agabanka in ƙarya nayi mata".


"Wai haka ne mamanah".


"Abbu to ƙafar kemun ciwo fa, ALLAH wancan Sadin mugune, dafa reza biyar ya tsaga mun ƙafata".


Gaba ɗaya buɗe baki sukayi haɗe da cewa, "Reza biyar Madiyam?" Lokaci ɗaya, in banda Hisham da tun ɗazu takaici ya sashi fiddo wayarsa yana latsa, juyowa Abbu daya gama dudduba ƙafar Madiyam ya yi haɗe da kallon sa ya ce,


"Yanzu don ALLAH Hisham a gabanka Sadi zai fiddo reza har biyar ya tsattsagewa ƙanwarka ƙafa haka..." Bai ƙara sa ba da sauri Madiyam ta ɗora hannunta akan bakinsa haɗe da ƙwalo kyawawan idanuwanta ta ce,


"Kayi shiru Abbu, ai shine ma ya siyo rezojin fa ya kawo masa, kuma ya riƙeni har ya gama yimun tsagar, baka ji ya yi shiru ba? ai shima yasan gaskiya na faɗa". ta ƙare zancen tana turo baki haɗe da naɗe hannayenta saman ƙirji, ɗago kai Hisham ya yi tare da kallon yanda take maganar tamkar wata sakarya shi Abbu na biye mata, girgiza kai kawai ya yi tare da maida kansa ƙasa yana ci gaba da latsar wayarsa don baya son ya shiga shirginta yanzu, amma yana addu'a ALLAH yasa cikin daren nan ta shiga nasa sai ya koya mata hankali, Abbu kuwa lallaɓa ta ya yita yi har ya samu ya riƙata suka nufi wajen cin abincin yana yi yana yimata sannu.


Cike da natsuwa kowa ke cin abincinsa da Mahmah ta zuzzuba masu a plate amma banda Madiyam data karɓi wayar Abbu tana faman buga game tana dariya, a gefe kuwa sai faman mutsunniya takeyi da ƙafar tata mai ciwo ta rasa inda zata ajiyeta, Mahmah tayi magana har ta gaji ta ajiye wayar taci abinci amma ta yi banza da ita, data nemi ɗaga mata murya Abbu ya dakatar da ita da hannu dole ta saka mata idanuwa, ai kuwa kamar an bugo ƙafar Madiyam sai cikin abincin Hisham, dai dai lokacin kuma wani yaro ya shigo ya ce ana yiwa Abbu sallama, dama ya gama cin abincinsa don haka ya miƙe ya fita, Hisham kuwa da tuni ransa ya gama ƙololuwar ɓaci akan abunda Madiyam tayi masa Abbu na fita ya fizge wayar hannunta tare da sakar mata wani mugun ranƙwashi akai yana faɗin,


"Ba kya ganin abunda kika yimun ne zakiyi tamkar baki san kinyi ba, halama ke makauniya ina ce? to wallahi na rantse sai kin cinye abincin nan ko nayi maki ɗan banzar duka a gidan nan".


Ya ƙare zancen haɗe da juye sauran abincin nasa acikin plate ɗin dake gabanta.


"Kamun daidai Hisham, ALLAH ya yi maka albarka". Mahmah ta faɗa haɗe da miƙewa tana tattara kwanonin abincin ta bar falon a fusace, wage baki Madiyam ta yi tana kallon ƙofar fita ko Abbun nata zai shigo ya bala'in daka mata tsawar data sata juyowa a razane ta saka hannu ta fara cin abincin, ci takeyi tana hawaye har ta ci fin rabi, ba tare data ɗago kan ba ta ce, "ya Hisham na ƙoshi"


Banza ya yi da ita wanda hakan yasa ta cigaba da cin abincin har saida ta cinyesa tas sannan ya miƙe yabar ɗakin ransa a ɓace,


"A'ah, ina kuma za kaje ga wani na zubo maka?" Mahmah ta faɗa dake riƙe da plate ɗin wani abincin data sake zubowa, 


"Na ƙoshi". Ya bata amsa a taƙaice tare da barin gidan, yana fita ya samu Abbu na sallama da baƙin nasa, bayan ya wuce ya riƙo hannunsa haɗe dayin murmushi ya ce,


"Hisham ya bautar ƙasar, angama lafiya ko?" Ya ƙare maganar yana janyo hannunsa suka dawo cikin gida, sai da suka zauna akan wani benci dake tsakar gidan tukuna Hisham ya ce "Lafiya klw Abbu, mun sameku lafiya?"


"Lafiya lau Hisham, ya mutuniyar taka? Wato daga dawowa saida kukayi halin, ko dai ƴar gida za ayi Hisham?" Abbu ya faɗa yana kallonsa haɗe dayin dariya, ba tare da Hisham ya ce komai ba ya sadda kai ƙasa, shi kuwa Abbu dama da zolaya ya faɗa don ya san Hisham da Madiyam tamkar wayar positive ne da negative, baza su taɓa haɗuwa ba, wata firar ya ɗauko masa suka ci gaba dayi har kusan sha biyu na dare ya yi sannan sukayi sallama ya wuce ɗakinsa dake can gefe shi kuma Abbu ya wuce cikin nasu ɗakin, ko daya shiga har Madiyam data gama cin duka agun Mahmah saboda kukan banzan data aza mata tayi bacci, ɗaya ɗakin nasa dake laƙe cikin falon ya nufa bayan ya tofawa Madiyam ƴa tilo a wajensa da yake matuƙar ƙauna addu'a haɗe da yiwa Mahmah seda safe.


*****.     *****.     *****

  A ɓangaren Haisam kuwa yana jin Hisham ya katse masa kira ya yi dariya haɗe da cewa, "Dama nasan za a rina Hisham, indai kan zancen Madiyam ne bazaka taɓa tsayawa ka saurara ba, na rasa me yarinyar nan tayi maka ka fiye tsangwamarta da yawa, gashi kuma yayanka na masifar sonta, bansan ya zamuyi dakai ba idan kasan haka!" Ya ƙare zancen tare da kwashewa da dariya yana faɗin "case" sannan ya jefa wayar cikin aljihun dake gaban rigarsa ya miƙe ya nufi cikin toilet ɗin dake cikin ɗakin nasa ya ɗauro arwalar magrib tare da ficewa cikin ɗakin, yana fitowa Abbie wato mahaifinsa na fitowa daga cikin ɗakin nasa shima, da alama shima arwalar ya yi ya fito zuwa Masallaci saboda yanda yake ƙoƙarin faman saukar da hannun rigar tasa, ɗan russunar dakai Haisam ya yi haɗe da cewa, "Barka da marece Abba?"


"Barka Haisam". Abbie ya faɗa yana miƙa masa hannu tare da saƙalo kafaɗarsa suka shiga saukowa daga kan upstairs ɗin gwanin ban sha'awa, murmushi Ammie dake fitowa daga kitchen ta hangosu tayi tana faɗin, "A'ah, kike father like son, wato dai na fahimci kun haɗewa yarona kai ko tunowa bakwai dashi ko, ALLAH sarki Hisham bawan ALLAH."


"Mu kuma fa?" Abbie ya faɗa lokacin da suka sauko tare da janyo Ailat dake kusa gareta ya yi mata kiss a goshi yana faɗin,


"Ummina bye bye, munyi masallaci" murmushi Ailat da baza ta wuce shekaru goma sha shidda ba a duniya tayi haɗe da cewa, "ok Abbie bye, ALLAH ya kiyaye." "Amin" Haisam ya faɗa yana mangare mata kai sannan yabo bayan Abbiey dake dariyar Ammie dake faɗar, "kuma bayin ALLAH ne amma ba kamar yarona ba Hisham, shi wannan ja'irin yaron naka ba abunda ya sani inba tsokana da ɗaukar magana ba, duk ya bi ya hana autata sakewa." Ta ƙare zancen tana ƙoƙarin kai masa duka ya yi saurin ficewa daga falon shima yana dariya, juyowa ta yi ga Ailat data turɓune fuska haɗe da dafe ƙeyar kanta da Haisam ya mangare ta rungumota tana dariya haɗe da cewa, "Srry my Baby, ƙyalesa ni nasan hukuncin da zanyi masa kinji ko?" 


"Ammie ni dai don ALLAH ya Hisham ya dawo nan shi kuma ya Haisam ya koma can gidan Abbu."


"Tirƙashi! Kar ma ki sake Hisham yaji wannan zancen a bakinki ku ɓata, ai shi yafi jin daɗin zamansa acan saboda baya son hayaniya, shiyasa tun yana ƙarami yabi Abbunku a can."


"To amma ai Madiyam nada rashin ji da karauniya kuma."


"Ai shiyasa basa shan inuwa ɗaya dashi, wlh Ni har tausayi take bani don ba ƙaramin takurata yakeyi ba, gashi itama Mahmah ɗin na biyesa suyita takurata."


"To Ammie ki ɗaukota ta dawo nan mana, nima kinga na samu ƙanwa muriƙa zuwa makaranta tare ko."


"Ai Abbu bazai yarda ba, sai dai tazo mana hutun data saba zuwa, Abbiey ma yaso haka amma idan mukayi hakan kamar munyi amai mun lashe ne."


"Ammie to..." Kafin ta ƙara sa Ammie ta katseta haɗe da cewa, "oh my God Ailat, nifa matsalata kenan dake tambaya ta yi maki yawa, maza jeki kiyi Sallah kafin Abbie ya dawo ya iskoki bakiyi ba, kinsan sai kinsha faɗa sosai ko?"


Tmɓure fuska ta yi haɗe da cewa, "Ammie idan zan kwanta zan haɗe da ishah duka nayi."


"What..?" Ammie ta faɗa tana zaro idanuwa kafin tayi kanta kamar zata doketa, dariya Ailat ta yi sannan ta riga da gudu ta wuce ɗakinta ta faɗa toilet, bayanta Ammie ta bi har sai da taga ta fito ta shimfiɗa abun Sallah haɗe da saka hijab ɗinta ta tayar sannan ta bar ɗakin nata itama ta wuce nata don ta samu ta watsa ruwa kafin su Abbie su dawo don fashin sallah takeyi...


*


*ALLAH KA JIƘAN IYAYENMU 👏😭*