Babi na uku
by @billysfari
Free page 3
*FIL-HUB*♥️
(Acikin so💘)
Paid Book: N500
Written by
Billy s fari💎
______________________________
Ammie na cikin ɗaki tana shiryawa ta jiyo sallama daga falo, amsawa ta yi haɗe da gyara mayafin doguwar rigar data saka ta feshe jikinta da turarukka masu ƙamshi sannan ta fito fuskarta ɗauke da murmushi gani Najlah tsaye a tsakiyar falon. "A'ah wai dama kece muryar taki ta ɓacemun?, zo ki zauna kin wani tsaya anan sai kace baƙuwa". ta ƙare zancen tare da ɗaukar remote ɗin dake kan center table ɗin dake tsakiyar makeken falon ta kunna tv sannan ita ma ta nemi waje ta zauna, murmushi Najlah dake kallon irin kyau da haɗuwar da Ammie tayi ta yi kafin tace, "Ammie ina wuni?"
fuskarta a sake ta amsa da "Lafiya klw Najlah, ya su Hajiya Raheema, da Zeenatu duk suna lafiya?"
"Lafiya klw suke, gashi suka ce na kawo maku". Ta ƙare maganar tana ajiye mata wata ƙatuwar leda agabanta, sai da Ammie ta ɗan buɗe ledar ta ga abunda ke ciki sannan ta ce,
"Ko ƴan ƙasar Parisa sun dawo ne?"
"Su yaya Irfan?"
"Eh, ko ba satinnan Hajiya Zeenat ta ce zasu dawowa ba?"
"Eh wannan satin ne, amma yaya Irfan kaɗai ne zai dawo, shi ya Naufal ya ce sai ya biya ta indiya wajen budurwarsa tukuna, Dady dai ne yadawo". Ta yi zancen murmushi ɗauke akan fuskarta, murmushin itama Ammie ta yi haɗe da cewa, "To angode sosai, ina ruwan Naufal, inaga ai duk sai ya doke yaran nan ya yi aurensa ya huta tunda su sun tsaya shashanci, badai kamar wannan babban kobon Haisam". Faɗaɗa murmushin dake kwance akan fuskarta tayi jin Ammie ta ambato sunan marurun zuciyarta haɗe da sinne kai tana wasa da ƴan yatsun hannuwanta,
"Kai Ammie, ai shima zai yi in sha ALLAH, kwana biyu ma na dena ganinsa?"
"Ko? Ai kuwa yana nan, halan ya dena shiga wajen su Hajiya?"
"Eh, tun bayan tafiyar Dady Umrah na dena ganinsa".
"Yanzu nan kina ganinsa shi da Abbie sun shigo tunda angama sallolin ishah, ya Dadyn naku ya dawo lafiya?"
"Lafiya lau, yana gaisheku".
"Muna amsawa, ai yanzu ne zaki ga Haisam agidan naku tunda ya dawo". Tana rufe baki yana shigowa falon bakinsa ɗauke da sallama, ɗaure fuska ya yi haɗe da kau da kansa gefe ganin Najlah yana faɗin,
"Ammie na dawo". Tare da haye upstairs ɗin ya nufi ɗakinsa, "Haisam, ina Abbie naga ka shigo kai kaɗai". Ammie ta faɗa haɗe da juyawa tana kallonsa, ba tare daya juyo ba daga hawan upstairs ɗin da yakeyi ya ce,
"Yana can tare da Dady suna gaisawa?"
"To halama baka ga Najlah bane zaka wuce baku gaisa ba? Ko baka ji gaisuwar da takeyi maka bane." Oh my God ya faɗa cikin zuciyarsa ganin Ammie na neman kwafsa masa haɗe da juyowa daga kan matattakalar fuska a ɗaure ya ce, "Sannu Najlah banji bane, kina lafiya?"
Ƙin amsa shi itama tayi don ya bala'in bata haushi, ko don yaga tana son shi ne shiyasa yakeyi mata haka? Tayi maganar cikin zuciyarta haɗe dajin haushin kanta, shi kuwa ɗage kafaɗa ya yi irin ko ajikinsa tare da juyawa ya ƙarasa hayewa sama abunsa, Muryar Ammie ta ji data dafata ganin yanda fuskarta ta sauya tana cewa
"Kiyi haƙuri Najlah, kin san halin yayan naki, ni kaina wani lokacin idan ya yi wani abu sai naga kamar bashi ba, shi da Hisham kamar suna musayar halaye nake gani wani lokacin, don wannan halin na Hisham ne ba nasa ba."
"Ai ƙwanda ya Hisham Ammie da Haisam, sam shi baya da wulaƙanci irin na ya Haisam ko don yaga ina son shi shiyasa." Ta ƙare maganar tana share ƙwallon daya zo mata, rungumota Ammie ta yi haɗe da cewa,
"Ba haka bane Najlah, kiyi haƙuri zanyi masa magana kin ji ko?"
"To Ammie, bari na wuce"
Ta miƙe tare da gyara mayafinta, dai dai lokacin Ailat ta fito itama ta watso ruwa earpiece laƙe a kunnenta ta nufi kitchen ba tare data kallin inda Najlah ɗin take ba,
"Ke zo nan". Ammie ta faɗa tare da ɗaure fuska, wajen ta ƙaraso haɗe da cire earpiece ɗin dake kunnenta tana kallon Najlah ta ce, "ina wuni Aunty Najlah, Ammie gani". Ta ƙare zancen tana dariya don tasan zancen da Ammie zata yi mata kenan, hararar ta Ammie ta yi haɗe da cewa, "ALLAH Ailat sai na saɓa maki akan Najlah, wannan ai rashin kunya ne ace kana ganin babbanka baza ka gaishesa ba sai anyi maka magana"
"Yi haƙuri Aunty Najlah". Ailat ta faɗa tare da ɗan rissinawa tana haɗe hannuwa waje ɗaya tare da rungumo Ammie ta ɗora kanta asaman kafaɗarta ta ce,
"Keyi haƙuri bazan ƙara ba kin ji Ammie na".
"ALLAH yasa, ni ɗagamun a kafaɗa" ta ƙare zancen tare da ture mata kai, ganin haka yasa Ailat riƙo hannun Najlah tana faɗin "muje na rakaki zuwa gate aunty Najlah, nasan shi ɗai zaisa Ammie ta dena wannan fushin nata". ta ja hannun Najlah da dama tun ɗazu ta matsu ta wuce saboda wani irin ɓacin rai da take ji yana sake taso mata, musamman yadda taga Ailat na dariya sai taga kamar da ita take saboda abunda ya faru, a bunda bata sani ba ma Ailat bata san meke faruwa ba, asalima bata san da zuwanta gidan ba sai yanzu data fito ta ganeta, to kuma dama ba wani shiri sukeyi da ita ba shiyasa ta wuce abunta ba tare data kulata ba, don ita kam ta tsani ɗaukar kai da isar da take nuna mata,
"Najlah kicewa Dadyn ku angode, ina na nan shigowa ko zuwa gobene nayi masa sannu da zuwa, ina gaida su Hajiya."
"To Ammie zasu ji". Najlah ta faɗa sannan suka fice har lokacin Ailat na riƙe da hannunta, suna kawowa wajen gate ta fincike hannunta daga riƙon da Ailat tayi mata tare da watsa mata wani mugun kallo gami da harara tana cewa,
"ALLAH kika sake ƙoƙarin riƙon hannuna kamar haka sai na baki kyakkyawan mari a fuskarnan taki, ni sa'ar kice ko angaya maki ni tsararki ce?"
"Easy Aunty Najlah, Nima ai ba son haka nakeyi ba, kawai nayi ne don Ammie ta dena jin haushin abunda nayi maki, amma ALLAH ya baki haƙuri tunda kinji haushi".
"Dallah rufamun baki, in sha ALLAH sai nayi maganinki tunda kika rena ni". Ta faɗa tana nunata da yatsa sannan tabar wajen, dariya Ailat ta yi haɗe da tafa hannuwanta kafin tace, "sai da safe aunty Najlah" cikin ɗaga murya,
juyowa ta yi shaye da toka haɗe da sake nunata da hannu ta ce "Zanyi maganinki ne very soon". sannan tabar gidan, Ailat na dariya itama ta koma cikin gida tana bin waƙar da take sauraren a kunnenta.
Ammie kuwa Najlah na wucewa takira Haisam ta rufesa da faɗa akan abunda ya yi mata bai kyauta ba, ta kuma nuna masa rashin dacewar hakan da yayi tunda baisan inda rana zata faɗin ba tsakaninsa da ita, kuma ko ba haka ba ya ci ace kodon irin alaƙar dake tsakanin gidansu da gidansu ta maƙwabtaka da yanda iyayensu suke ya girmamata, yanda yaga ran Ammie ya ɓaci ya sashi saukowa haɗe da cewa "Kiyi haƙuri Ammie in sha ALLAH hakan bazata sake faruwa ba, kawai Ni abubuwan da take yimun ne yanzu bana so shiyasa na dena bata fuska"
"Au, saboda ta nuna maka so shine kake yimata haka?, Ashe da gaskiyarta abunda ta faɗa".
"No Ammie ba haka bane, Ni akwai wacce nake so shiyasa bana son sakar mata fuska kar ta zata ko nima ina sonta".
"ALLAH Ammie kar ki yadda dashi, shima yana sonta kawai baya son faɗa maku ne." Ailat data shigo falon yanzu ta faɗa tana yimasa dariya, ɗaure fuska ya yi tare da ɗago kai ya ce,
"Ke, ina wasa dake ne?"
"Sau nawa kuma? Ai saidai kar a ƙara" Ammie ta faɗa tana dariya ganin yanda ya ɗaure fuska yana zarowa Ailat idanuwa, dariya itama Ailat tayi haɗe da ɓuya bayan Ammie tana cigaba da cewa, "kuma wlh Ammie sun bala'in dace wa da ya Haisam, har fa kama sukeyi da juna wlh"
Kafin ta rufe baki ya ciro pillow kujera ya jefeta dashi haɗe da yo kanta ta bar wajen aguje tana yimasa gwalo, zagaye falon suka shiga yi tana dariya shi kuma yana biye da ita yana cewa "yau sai kin faɗa mun ta inda muke kama da ita ko nayi maki shegen duka a gidan nan". Dai dai lokacin Abbiey ya shigo tayi saurin ɓuya bayansa haɗe da riƙe shi don har ga ALLAH ba ƙaramin shammatar ya Haisam ta yi ba, don shi kyakkyawane sosai chocculate colour dake da wasu irin narkakkin idanuwa masu matuƙar ɗaukar hankali, Najlah kuwa fara ce sosai ƴar siririya marar hanci da ƙananun idanuwa, sak idan ka ganeta ba tada maraba da ƴan China don har haka wasu ke kiranta (Ƴar china), lokacin da tana ƙarama kyakkyawa ce sosai amma bakin mutane yasa tana girma kamanninta suka sauya, duk da hakan ba laifi ko yanzu tana da irin nata kyau daidai gwargwado, tun suna yara tare suka tashi dasu Haisam da Hisham don makaranta ɗaya ma sukayi karatu lokacin Abbie na aiki a Lagos, sai ya zamana mahaifinta shike kula da kaisu makaranta da ƴan sauran abubuwan da ba'a rasa ba, sun shaƙu sosai dasu Hisham amma kuma tafi shiri Haisam, mahaifinta shahararren mai kuɗi ne, wanda ke da mallakin gaba ɗaya kamfanin NaNa rice da aka fi sani da suna Alhaji Asim mai dala (cikin littafin WASU MAZAN 😍), gidansu laƙe yaƙe dana su Haisam, ma'ana maƙwabta ne, maƙwabtaka ce ta haɗa su da Mahaifin su Hisham wato Alhaji Sani Naira, inda sannu a hankali mutuntaka da sanin yakamata da kuma kyautatawa dake tsakaninsu ta juye izuwa ƴan uwantaka, don dukkanninsu sunsan darajar ɗan adam da kuma haƙƙin maƙwabtaka, shiyasa zamantakewar tasu tayi kyau da kuma ƙarfin da duk wanda ya ganesu zai ɗauka ƴan uwa ne, Najlah itace ƴarsa macce tilo da yake da ita duniya wacce ƙaddara ta shiga tsakaninsa da mahaifiyarta aka samu cikinta ta hanyar daba halas ba, inda bayan wasu shekaru ya yi tunanin gyara kuskurensa ya nemo inda mahaifiyarta take Hajiya Raheema ya roƙeta gafara sannan kuma ya aureta, a ɗaya ɓangaren kuma yana tare da matarsa Hajiya Zeenat da yake matuƙar so da ƙauna, mace mai haƙuri da kuma kirki da yadda da ƙaddara, sosai ta shiga damuwa lokacin daya labarta mata tsakaninsa da Hajiya Raheema da kuma cikin dake tsakaninsu, tayi kuka ta shiga damuwa ta kuma tuhumi kanta sosai akan wannan jarabawar da mijin nata ya tsinci kansa a ciki, in da ƙarshe ta ɗauki abun a matsayin ƙaddararsa, ta kuma tashi tsaye wajen taimaka masa don ganin ya gyara kurakuran daya aikata na baya, wanda hakan ya sa lokacin daya gano inda Raheema take da cikin data haifa, ta bashi ƙwarin guiwar aurenta ɗari bisa ɗari, lokacin itama tana da ƴaƴanta biyu a gabanta Irfan da Naufal, Irfan ɗan ta ne na cikinta data haifa, shi kuma Naufal ɗane ga aminin Alhaji Asim wato Imran, wanda adalilin irin mu'amalar da sukeyi ta masha'a tare matan banza ya auri wata mata Azeema ta haifa masa a matsayin ɗansa, ya zamana ta ci amanarsa ne ita da abokinsa Imran, wanda sai daga baya da tazo rasuwa ta sanar dashi gaskiya, ko data rasu ta bar Naufal yana jariri wanda hakan ya sa Hajiya Zeenat ta haɗa su duka shi da Irfan ta cigaba da shayar dasu don babu wata tserewa tsakanin su, yanzu haka suna ƙasar Paris sun kammala karatunsu suna shire-shiren dawowa gida nageria. (Ga mai son jin yanda labarin na family ɗin Alhaji Asim Mai dala yake, sai ya biya N300 na littafin WASU MAZAN ta hanyar wannan account namu da muke amfani dashi tare da tuntuɓar wannan lambar *** domin mallakar nasa).
Dariya Abbie ya yi tare da riƙe shi lokacin daya ƙara so yana faɗin, "Haisam nima fa na kusa komawa bayan ummina tunda bazaka bari ta sakata ta wala ba, don haka dole ma satin nan ka fiddo da mata na aurar dakai mu hutu".
"Ai Abbie har ma ya fidda, shi da Aunty Najlah ƴar gida za a yi"
"Haba ummina! Da gaske kike yi?" Abbie ya faɗa with so much excited akan fuskarsa yana kallon haisam, zancen da suka gama yi kenan yanzu shi da Alhaji Asim, ALLAH yasa hakan ta kasance, da yafi kowa farinciki don Alhaji Asim mutumne, ya ƙare zancen cikin zuciyarsa yana riƙo hannun Haisam daya samu sa'ar kaiwa Ailat ranƙwashi akai ya nufi wajen dining dashi yana faɗin,
"Ammiensu zo ki zuba mana abinci muci, ina so mu sakaya nida yarona idan mun gama" ya jawo masa ɗaya daga cikin kujerun dining table ɗin ya zaunar dashi, yanda yaga ya sha toka ya sashi yin dariya tare da cewa, "menene yarona?"
"Abba ƙarya fa Ailat keyi, ni Madiyam nake so gaskiya ba Najlah ba"
"Common..Madiyam kace fa? Yarinyar dako Ailat ta fita girma, yaushe zaka tsaya zaman jiranta? ka dai san ko way Abbu, bazai taɓa aurar da ita ba yanzu ko ana maza ha mata".
"Abbie to ba saina jirata ba har lokacin da Abbu zai shirya aura da ita, nidai gaskiya ita nake so". Ya ƙare zancen yana tura plate ɗin gabansa, zaro idanuwa Abbie ya yi yana maido masa da plate ɗin agabansa haɗe da cewa, "To meye na ture plate ɗin? Ai abun bai kai can ba, indai kwantar da hankalinka in sha ALLAH kamar ka sameta ka gama, amma kuma bazai yuyu kayita zama a haka ba dole kayi aure kafin lokacin tunda kai mijin macce huɗu ne sannan shekarunka ja suke yi ba raguwa ba".
"A'a Abbie nidai..."
"Ya isa haka". Abbiey ya faɗa shaye da toka yana nuna masa yaci gaba da cin abincinsa da Ammie ta gama zuba masa, sanin halin Abbie ya sa Haisam ɗaukar cokalin ya fara cin abincin ransa a ɓace ba tare daya koma cewa uffan ba, bai wani ci abincin sosai ba ya ture plate ɗin gefe haɗe da miƙewa ya bar wajen, ɗago kai Ammie ta yi zata yi masa magana Abbie ya ɗaga mata hannu, hakan ya sa ta kama bakinta tayi shiru ta cigaba da cin abincinta,
"Good night Abbie, night Ammie." Ailat ta faɗa itama tare da miƙewa ta bar wajen ta nufi ɗakinta dake nan ƙasa Abbie na cewa tayi addu'a kafin ta kwanta.
Sai da suka gama cin abincin Abbie ya riƙawa Ammie suka kwashe kayan ta ɗauraye shi kuma ya wuce ɗakinsa ya watso ruwa sannan ya sake saukowa ƙasa ya sameta a falo tana kallon drama, gefenta ya zauna tare da amsar remote ɗin ya sauya channel zuwa ta labarai sannan ya mayar mata yana faɗin, "yau dai ya kamata mu kalli labaran nan tare dake.
"Ai kuwa bazan kalla ba don bacci nake ji".
"Ai tunda na kashe maki drama ɗinki ba?" Ya faɗa yana dariya kafin can ya ɗan riƙe fuska yana kallonta, hakan ya sata natsuwa sosai tana kallonsa itama don tasan tunda ya yi haka akwai maganar da yake son yi da ita mai muhimmanci, murmushi ya saki ganin yanda ta tattaro duka natsuwarta gareshi haɗe da cewa,
"Shiyasa nake ƙara ƙaunarki a zuciyata saboda kina fahimtar duk wani yare dazai fito daga kan fuskata, koda kuwa ban furta komai ba a bakina". Sai daya yi ajiyar zuciya sannan ya ci gaba da cewa, "wai me kika fahimta a zancen yaron nan ɗazu, wlh daga ni har Alhaji Asim mun zata suna son junansu ganin yanda suka shaƙu juna."
"Nima haka na ɗauka daga farko, amma daga bayan nan sai na fahimci kawai shaƙuwace shi Haisam baya sonta, amma ita tana son sa sosai, gashi ya ɓullo da zancen Madiyam yanzu, kuma kasan Abbu na ji babu abunda zai hana ya bashi aurenta".
"Hakan ba laifi bane, amma shekarunsa na ja, idan aka ce ya zauna zaman jiranta tofa yayi mata tsufa alokacin."
"Alhaji kenan, ai shi namiji baya tsufa da aure, indai tana son sa ba wata matsala bace, sai ya haɗa su su biyu ya auresu".
"Abunda nake ƙoƙarin nuna masa kenan ɗazu yake nema ya yimun gaddama".
"Haƙuri za muyi mu lallaɓasa, kuma muyi masa addu'a ALLAH ya zaɓa masa alkhairi, nasan in Sha ALLAH itama Najlah zai amince ya aureta."
"ALLAH yasa".
"Amin, ya batun yaronki shi kuma, ya faɗa maki yana da wacce yake so?" Sai da tayi dariya sannan ta ce,
"Ina ruwan Hisham, ai ni ko ga mafarki banji ba kuma ban gani ba".
"Ai shikenan, gashi ga iyayensa su suka san yanda za suyi dashi, don yanzu ina magana Abbu zai ce takurasa nake son yi, kinsan halinsa da son ƴaƴa"
"Ai sai ka zuba masu idanuwa, idan tayi tsami ma ji"
"Hakane, kindai hanani kallon labaran nan, bari naje na kwanta gobe muna da mitin ƙarfe bakwai na kwamishinoni idan ALLAH yakai ranmu da maigirma gwamna." Ya ƙare zancen tare da miƙewa ya nufi sama yana yimata sai da safe, kayan kallon ta kashe itama ta wuce ɗakinta tana buga hammar dake nuna baccin na cinta itama sosai.
Abbu da Abbie wa ne da ƙane kuma uwarsu ɗaya ubansu ɗaya, dukkanninsu haifaffin garin kaduna ne a ƙaramar hukumar Giwa dake cikin jahar, sun taso cikin maraicin iyaye lokacin Abbu mai suna Awwal yana da shekaru goma sha tara aduniya shi kuma Abbie Sani yana da shekaru sha biyar, sai ƙanwarsu Fatima tanada shekaru bakwai aduniya, inda tana cika shekara goma bayan rasuwar iyayen nasu itama ALLAH ya yi mata rasuwa ya rage daga Abbu sai Abbie, ganin yanda Abbie ke son karatu ya sa Abbu jajircewa wajen kasuwancin saye da sayarwa na hatsin da suke nomawa da kansu a gonar da mahaifinsu ya bar masu a kasuwanne don taimakawa ɗan uwan nasa ya yi karatu, cikin taimakon ALLAH kuwa Abbie ya maida hankali sosai ya yi karatun da har ALLAH ya kawosa a babban matsayin da yake yanzu a cikin gwamnati na commissioner of health a jahar, sosai ya so ɗan uwan nasa ya dawo su zauna tare amma fir Abbu ya nuna masa yafi don zamansa acan ƙauyen yana ƴan harkokinsa daya saba dasu na yau da kullum, hakan ya sa Abbu ya gyara masa gidansa ya kuma buɗe masa wani ƙaton ma'ajiyar hatsi da yake siye ga manoma idan sunyi girbi shi kuma yana saidawa manyan ƴan kasuwa dake zuwa siye daga birni, shiyasa in ya fita tun safe baya dawowa sai marece, tun da Abbu ya auri matarsa Fatima (Mahmah) bata taɓa haihuwa ba har Abbie ya zo ya yi aure sai gashi cikin iyawar ALLAH shekara na zagayo wa matarsa Amina(Ammie) ta haifi Haisam inda Abbu ya yi murna sosai da samun ƙaruwar ɗan uwan nasa, bayan shekara uku ta sake haifo ɗan ta ya ci suna Hisham har lokacin Mahmah ko ɓatan wata bata taɓa yi ba, sosai Abbu sukayi zuwa yawon asibiti har cikin Kaduna da taimakon Abbie aka duddubasu akace basuda matsala su dukansu lokacine kawai baiyi ba, hakan yasa Abbu ya kwantar da hankalinsa ya cigaba da addu'a ALLAH ya kawo masu nasu lokacin suma.
Kamar yanda Abbu da Abbie ke tsananin son junansu haka Haisam da Hisham ke matuƙar son junansu tun suna ƙanana, babu mai yadda wani abu ya sami ɗan uwansa ba tare daya tare masa ba, komai nasu iri ɗaya akeyi masu haka ma suna da kamanni sosai, hasken fata kawai ne ya banbanta su inda Haisam ya ɗauko kalar fatar mahaifiyarsa, shi kuma Hisham ya ɗauko ta mahaifinsa don kuwa farar fata ne Fulani ƙauye na asali, sai kuma banbancin halayya da suka samu, inda Haisam keda son wasa da dariya sosai shi kuma Hisham miskiline ko magana bata damesa ba, hakan yasa rana ɗaya yana gama jlc ya daka tsalle Abbu na zuwa ya laƙesa yace shi wajensa zai koma da zama, wanda hakan ba ƙaramin farinciki ya saka Abbu ba tare da jin soyayyar Hisham sosai a ransa, shi kuwa Abbie ya tattara komai nasa ya barwa Abbu shi, komawar Hisham wajen Abbu sai ya zama alkhairi, don kuwa a watan ALLAH ya bawa mahmah cikin Madiyam, murna awajen su Ammie da Abbie ba a magana, lokacin Ailat nada shekara biyu da haihuwa, yanda su Mahmah suka ga su Abbu na son junansu haka suma suke son juna ita da Ammie, shiyasa Mahmah ta zama ƴarlici ta ko ina data samu cikin, don ko yaushe Ammie na kan hanyar zuwa dubota, Hisham kuwa har girki da shara duka yimata yakeyi lokacin da cikin ya tsufa saboda tausayi, watan haihuwarta na kamawa ta haifi kyakkyawar ƴarta taci sunan mahaifiyarsu Abbiey wato hawwa'u amma sai ana kiranta da Madiyam da yake cikin damana aka haifeta, su kuma Fulani sukan kira wacce aka haifa cikin damana da Madiyam musamman ma idan za ayi mata laƙani.
Sosai Madiyam ta taso cikin kulawa da soyayyar ƴan uwa musamman Hisham da har goyata yakeyi, yanayin karauniya da irin ƙiriniyar data taso da ita da sangartawar da Abbu keyi mata ya sashi sauya mata saboda gudun kar ta koma ɗaya daga cikin sangartaccin yaran dake lalacewa ana yi masu kallon marasa tarbiya da kuma mafaɗi...
*****. *****. *****.
Tun da asuba da Madiyam tayi Sallah ta ɗauko madubi tana faman jujjuya fuskarta aciki har safiya ta fara wayewa, don ba laifi ƙafar tayi mata sauƙin sosai, kallonta Mahmah ta yi haɗe da cewa, "Wai lafiyar ki Madiyam, me kikeyi da madubi tun asuba har yanzu"
Turo baki ta yi haɗe da cewa, "To ba ya dodo bane ya ce wai ƙarin baki ne dani, shine nake dubawa na gani wai don ALLAH da gaske ne Mahmah? ta ƙare maganar tana wani kimtsa bakinta haɗe da kallon Mahmah, dariya Hisham daya shigo ɗakin da sunan gaishe da mama ya taddata tana wannan shirmen ya kwashe da ita haɗe da ƙaraso wa cikin ɗakin ya karɓe madubin ya ɗora saman chest of drawer ɗin dake gefe haɗe da cewa,
"Ai kima hutar da kanki yarinya da dubawa, kowa agidan nan ya san ƙaton baki ne dake, matso nan naga ƙafar taki".. ya ƙare zancen yana ɗaure fuska tamkar ba shi ya gama dariyar ƙera ba yanzu tare da zuba mata kyawawan idanuwansa yana kallon yanda ta fara kyaƙƙyafta idanuwa haɗe da tumɓure fuska za tayi kuka...
*ALLAH KA JIƘAN IYAYENMU 👏😭*