FIL HUB

Babi na tara

by @billysfari

Free page 10


    *FIL-HUB*♥️

           (Acikin so💘)

Paid Book: N500

  Written by

     Billy s fari💎

______________________________

  Yana wannan tunanin kiran Najlah ya shigo wayarsa, da har bazai ɗauka ba sai kuma ya yi sauri ya ɗaga ganin kiran ya kusa katsewa,


"Hello Hisham".


"Na'am Najlah ya kike?"


"Lafiya klw Hisham, ya Haisam ya iso lafiya?"


"Lafiya klw, dama nasan don shi kaɗai kika kirani".


"Ba haka bane, kai ɗin ne ayita kiranka ba a samu, gabaɗaya ka yafe kowa".


"Ba haka bane, ya su Hajiya da Dady?"


"Duk suna nan lafiya, ka faɗa masa na kira wayarsa ban samesa ba".


"Ok. Riƙe wayar bari na kai masa ai muna kusa". Ya faɗa tare da komawa cikin gidan cike da son rabo Haisam a wajen, kamar dai ɗazun, yana shiga ya tadda Madiyam na ƙarashe robar icecream ɗin da take sha Haisam na goge mata gefen bakinta daya ɓata yana faɗin, "Cutie na gano bakin nan naki ya iya shan daɗi". Ita kuma tana dariya, ɗaure fuska ya yi kafin ya miƙa wayar haɗe da cewa,


"Matarka na magana, ta ce ta kira bata sameka ba".


Harararsa ya yi kafin ya karɓi wayar haɗe da cewa, "for where matata, kai ka ɗaura mun aure da ita?" 


Yana kallon yanda Madiyam ta ɗan sha jinin jikinta tana kallon yanda Haisam ke magana, "Oh my God Najlah, Wai me yake damunki?" Ya faɗa tare da miƙewa ya bar ɗakin, harara Hisham ya dalla mata ita kuma haɗe da cewa, "ALLAH yasa naji kin ɓarewa mama wannan ƙarin bakin naki kina faɗin cikinki ke ciwo, sai na tattakaki a gidan nan, acici kawai" sannan ya fice shima ya bar ɗakin, cuno baki ta yi haɗe da cewa, "oho dai kanka ake ji" ta miƙe itama tare da har haɗa kayan dake gabanta ta saka cikin fridge.


A can ɓangaren Najlah kuwa kuka ta sakawa Haisam haɗe da cewa, "Duk abunda zaka yimun ya Haisam ba laifinka bane nawa ne don na ce ina sonka, kuma ka sani tsangwama da kyarar da kake yi mani wallahi baza su taɓa sa na sauya ba, ina sonka, ina sonka har iya ƙarshen rayuwata".


"Najlah kenan! ALLAH sheda ne akan ni ban yi maki komai ba, amma dai na faɗa maki gaskiya ni ina da wacce nake so, saboda haka ki bari alaƙar dake tsakaninmu taci gaba da wanzuwa a mutunce, idan kuma ba haka ba..." Tayi saurin katsesa haɗe da cewa, "me za ka yi? Yanke alaƙar ko kuma cire mani sonka a raina".


"Ko wane zai iya faruwa".


"Ƙarya kake yi Haisam domin dukansu ba huruminka bane, ni nake da damar daina sonka kuma na ciresa azuciyata idan naso haka, alaƙa kuma daga iyayenmu ne, matuƙar suna tare kai baka isa ka yanke ta ba".


"Ok! Gaskiya kika faɗa, amma ina so ki sani ba a so dole".


Dariya ta kwashe da ita dake nuna cike take da ɓaci rai kafin tace, 


"Tabbas ba a yi Haisam, amma za a fara kanka in sha ALLAH, don sai na zame maka ƙarfe ƙafa ko kana so ko ba ka so, tun wuri ƙara kayiwa kanka ƙiyamullaili ka koyawa kanka da kanka soyayyata, in ba haka ba.."


"Sai kiyi me?" Shima ya katseta cikin jin haushin maganganunta, wata dariyar ta sake yi sannan ta ce, "Oh relax my feature husband, ba abunda zan yi illa ni da kai na in sa kaso ni by force".


"By force!"


"Yes upcouse, ko ka manta cewa ni macece kuma na cancanci a so ni kamar yanda ka faɗa da bakinka".


"Mtss..You are not serious Najlah". Ya faɗa yana ƙoƙarin kashe wayar.


"Kar ka fara, ai ni nakira ba kai ba sannan ko ka manta wayar ba taka bace? Kai mashi abussa akwai maganar da zanyi dashi". Ta faɗa cikin gadara da nuna isa, tsintar kansa ya kasa yi da yimata musu har ya ya kaiwa Hisham dake ɗaki wayar, tana jin alamun zai bashi ta ce,


"Wait my feature husband, yaushe zaka dawo?"


"Wannan matsalar ni ta shafa ba ke ba, saboda haka babu ruwanki da ranar da zan dawo". Ya ƙare maganar cikin jin haushi haɗe da miƙa masa wayar, ba tare da sanin haka ba ta ce "Bye tunda baza ka faɗa mun ba, ka kula mani da kanka sosai i love you" ta ƙare maganar haɗe dayin dariya tana jefo masa kiss a wayar, da sauri Hisham da har ya kai wayar a kunnensa ya yi saurin janyewa yana kallon Haisam da zai fita ya ce,


"Ungo wayarka ba a gama baka saƙonka ba fa".


Banza Haisam ya yi dashi ya fice abunsa yana tunanin yanda zaiyi da Najlah ta raba shi da zancen soyayyar nan ta ta da take iƙirarin tana yi masa, a can ɓangarenta kuma dariya ta yi jin abunda Hisham ya faɗa tare da kashe wayar, duk da a zuciyarta tana jin haushin abubuwan da Haisam ke yi mata amma a zahiri tana matuƙar tsintar kanta cikin nishaɗi aduk lokacin da suke haka dashi, tana da ƙwarin guiwa sosai akan cewa tunda har yana saurarenta to tabbas wata rana zata yi winning heart ɗinsa, musamman idan ta tuna yanda take dashi da yanda tasan wasu halaye nasa na jin tausayin mace, shi yasa baza ta taɓa hasala ko kuma yin zuciya dashi ba don yana faɗa mata maganganu, sannu a hankali wata rana zai daina.


"Wai ni kam baza kuzo kuci abinci ba Hisham? Sai faman yawo da hankali kuke yimun in wannan ya yi nan wannan ya yi can, kun kasa zaunawa kuci abinci kuma nasan dukkaninku yunwa na damunku" Mahmah ta faɗa tsakar gidan ranta a ɓace, hakan ya sa Haisam wuce wa ya zauna yana bata haƙuri, cigaba da faɗa ta yi ganin shi Hisham yaƙi fitowa, tasan halinsa kar tunda bai fito ba to lallai bai da sha'awar zaunawa aci abincin tare, hakan yasa ta ce Madiyam ta zuba masa nasa a plate ta rufe ta ɗauki cokali da ruwa takai masa a ɗaki, shi kuma Haisam ta zuba mashi na shi ta tura masa a gaban shi tana faɗin,


"Ka dena biyewa waccan ɗan uwan naka, zai iya kai dare a haka baici komai ba indai ba nayi masa magana ba, nayi faɗa har na gaji amma ya kasa dena wannan halin nasa".


Murmushi ya yi haɗe da cewa, "A yi haƙuri Mahmah zai dena ne in sha ALLAH, ai yunwa ba uwar kowa bace balle ta raganmasa". Ya ƙare zancen yana kallon yanda Madiyam ke loda abinci cikin plate ɗin tana turo baki har tana sake dannawa, wani murmushin ya saki saki haɗe da cewa, ashe akwai ƙura yau, cikin zuciyarsa,


Har zata fita ya yi tunanin wulaƙancin Hisham ya kira Madiyam ya ce ta rage abincin, "a'a ta kai mashi hakan, tun safe ruwan tea kaɗai ne acikinsa ƙara yaci ya ƙoshi". Mahmah ta faɗa tana ɗauko wani haɗaɗɗen zoɓon data sake haɗa masu ta ajiye mashi a gabanshi, ta ce Madiyam ta jeka takai abincin ta dawo ta ɗaukar masa nashi soɓon da ruwa.


A natse ta tura ɗakin tare dayin sallama sannan ta shiga ta kai abincin ta ajiye masa ta koma ta ɗauko ruwan da zoɓon ta kawo masa ta ajiye, har lokacin ko motsawa bai yi ba daga inda yake zaune yana latsar wayar dake hannunsa, sai daya ga zata fita sannan ya ce,


"Azo mun abincin annan". Ya nuna mata gefensa saman katifar ba tare daya ɗago ya kalleta ba, sai daya ga zata aza zoɓon da ruwan akai sannan ya ɗago kai yana faɗin, "A ina kika taɓa ganin haka?" 


"Yi haƙuri" ta faɗa shaye da toka sannan ta saukar dasu ƙasa, abincin dake cikin plate ɗin daya buɗe ya ga yawansa ya ƙurawa idanuwa haɗe da ɗago kai ya kalleta tana ƙoƙarin fita ya ce,


"Zo nan!" Jin tayi kamar ta saka ihu don gabaɗaya ta tsargu da wuɗannan abubuwan da takeyi mata, dawowa cikin ɗakin ta yi haɗe da cewa


"Gani".


"Waya zubo wannan abincin, ke ko Mahmah".


"Ni ce" ta faɗa kanta na sunkuye a ƙasa, ɗago kai ya yi ya kalleta haɗe da sakin murmushin mugunta sannan ya ce, "Saboda gani jaki ko? Shiyasa kika kofi mun wannan abincin haka tunda an faɗa maki ni acici ne kamar ki, to zauna ki cinye sa". Sai alokacin ta ɗago kai kamar za tayi kuka ta ce,


"To ka kawo rago maka, ni na ƙoshi bazan iya ci ba".


"Baki isa ba, zauna nan sai kin canye sa" ya ƙare maganar tare da nuna mata ƙasan wajen shaye da toka, ƙyaƙƙyafta idanuwa ta farayi tana so tayi kuka ya daka mata tsawa haɗe da cewa, "duk kika samun kuka sai na ɓallaki a wajen, meye ɗazu banganki kina ci ba ko gajiya bakinki ba ya yi, ai sai ki ƙara da wannan" ya dangware mata plate ɗin abincin aƙasan, yanda ya yi da huska ba karamin tsoratata ya yi ba, hakan ya sa dole ta zauna tana cin abincin tana ƙwalla, a zahiri za kaga kamar idanuwansa akan wayar suke amma gabaɗaya hankalinsa nakanta, yanda take cin abincin da yanda idanuwanta suka sauya kala cike da ƙwalla ba ƙaramin burgesa ya yi ba, ganin ta ɗago kai ya sa ya yi saurin maida idanuwan nasa ga wayarsa yana sake ɗure fuska, "Ya Hisham wlh na ƙoshi, wlh zan iya yin amai".


Banza ya yi da ita ya ci gaba da latsar wayarsa, hakan ya sa taci gaba da tura abincin yana kallonta ta ƙasan ido har sai da ya ga ya kai daidai yanda zai iya canyewa sannan ya ce,


"Rufe ki tashi ki bani waje". 


Ba musu ta jawo ɗayan plate ɗin ta rufe sannan ta fita tana yi masa ALLAH ya isa a zuciya, dai dai lokacin Haisam shima ya gama ya fito, kallonta ya yi haɗe dayin dariya ganin yanda ta fito tana kumbura fuska ya ce,


"Ya akayi cutie!? Ko ke yasa kika cinye abincin?"


"Eh, kuma fa na faɗa masa cewa na ƙoshi, wlh da na sani bazan kai masa abincin ba sai dai Mahmah takai masa".


"Eu'uhm rufe bakinki kar ya jiki, haka yake yiwa Ailat itama, don haka daga yanzu ki kula".


"Kar ma ta kula". Ya faɗa riƙe da plate ɗin ya fito dasu, da sauri ta shige ɗaki Haisam ya bita da dariya yana kafin ya maido kallonsa ga Hisham ya ce, "ALLAH Hisham ka rage mugunta, ina laifin wanda ya baka abinci kaci ka ƙoshi?"


"Babu shi, ai shiyasa kaga nima na sata taci ta ƙoshin". 


Mahmah dake tsakar gida ta girgiza kai haɗe da amsar plate ɗin tana cewa, "ALLAH ya maka maganin wannan hali naka, da na sani ai sai a ƙyaleka kayi ta zama da yunwarka tunda haka kake so" ta ƙare zancen tana buɗe plate ɗin, ganin ba komai ya sa ta dena faɗa da takeyi, don a tsammanin ta baici abincin ba, shi kuma Haisam ya zata yanda yake wa Ailat yasa ta canye abincin duka haka ya yiwa Madiyam, abunda bai sani ba rabi ta ci shi kuma ya canye rabin amma ya fito yana wani matse fuska.....





*ALLAH KA JIƘAN IYAYENMU 👏😭*