Babi na sha ɗaya
by @billysfari
Free page 11
*FIL-HUB*♥️
(Acikin so💘)
Paid Book: N500
Written by
Billy s fari💎
______________________________
Ɗago kai Mahmah ta yi ta kallesa ganin ba komai cikin plate ɗin haɗe da cewa, "Au ashe ka ci"
"Eh Mahmah" ya faɗa tare da sha fa kansa cike da jin kunya sannan ya wuce ɗakinsa.
Murmushi ta yi haɗe da wucewa kitchen tana mai addu'a ALLAH ya sa hasashenta ya zamo gaskiya, da tafi kowa jin daɗi saboda gabaɗayan su renonta ne kuma tana jin soyayyar kowanensu a ranta,
Yau Haisam ya so wucewa gida saboda ganin Abbie baya nan don kar ya bar su Ammie su kaɗai a gida, amma da ya yi waya da ita sai ta ce indai bai taso ba ya bari sai gobe don ba ta so marece yayi masa a hanya saboda yanayin da ake ciki yanzu na rashin tsaro, sosai hakan ya yiwa Haisam daɗi don dama haka yake so, faɗar kalar farinciki da kuma shauƙin da yake jin kansa aciki kuwa bazai misaltu ba, ko ba komai zai kasance tare da Madiyam ɗin sa daga yau har gobe da safe kafin ya wuce, kuma hakan zai bashi damar bayyana yanda yake fama da dakon soyayyarsa ko da baza ta fahimta ba, ya san sannu a hankali wata rana zata fahimci hakan, yana gama wayar da Ammie ya ga Madiyam ta fito cikin shirinta na uniform za ta wuce islamiya, ƴar gayaran murya ya yi haɗe da cewa, "cutie makaranta zaki je?"
"Eh ya Haisam."
"Bari nazo na raka ki". Ya faɗa haɗe da miƙewa daga kan kujerar da yake sannan ya bi bayanta, Kallonta ya yi tun daga sama har ƙasa yana yaba yanda kayan suka yi matuƙar karɓarta haɗe da cewa,
"Tubarkallah cutie kayan nan sunyi maki kyau, sai kace ba na islamiya ba".
"ALLAH ya Haisam?"
"Sosai kuwa, yayanki bai taɓa faɗa maki ba?"
"Tab..ya Hisham ɗin? Ai sai dai na mutu in sai ya ce nayi kyau, wanda baida aiki kullum sai kushe ni"
"Jininku ne bai haɗu ba shiyasa, ai ni babu wacce nake ganin kyanta da kuma yaɗuwar ta a duniya sama gake ƴar ƙanwata, shiyasa duk lokacin da nake tare dake nake jin wani irin daɗi tare da tsintar kaina cikin farinciki marar misaltuwa". Dariya ta saki haɗe da ce
"ALLAH ya Haisam?"
"Sosai cutie, ke baki ga hakan ba."
"Na gani mana, ai shiyasa nima nake jin daɗi idan ka zo tare da tsintar kaina cikin farinciki sosai"
"Da gaske cutie?"
"Wlh kuwa ya ya Haisam"
"Faɗa mun naji me yake saki cikin farinciki idan na zo" Ya faɗa yana kallonta cike da so da ƙauna, sai da ta yi ƴar dariyarta dake matuƙar tafiya da hankalinsa sannan ta ce,
"Saboda yanda kake sona, kake zauna wa kayi fira dani, kake sake mun fuska, kana siyo mun abubuwa da kuma yanda ba ka sakani kuka, amma shi wancan ya dodo ɗin ba abunda ya gwane kamar ya sakani kuka ko ya yi mun mugunta". Tayi zancen haɗe da turo baki, murmushi ya saki tare da cewa.
"To me yasa yake yi maki hakan?"
"Wai bana jin magana yake cewa, don ALLAH da gaske ne ya Haisam bana ji?"
"Gaskiya a'a, cutie ɗina na jin magana sosai." Dariya ta saka haɗe da cewa, "yauwa, dama na sani kawai yana faɗa ne don baya so na!"
"To ni fa?"
"Kana so na mana shiyasa ba ka cewa haka," shafa kansa ya yi yana kallonta cikin idanuwa haɗe da jin wani irin shauƙin sonta da ƙaunarta na sake fizgarsa kafin yace,
"Tabbas ina sonki sosai Madiyam, duk duniya banda Abbie da Ammie babu wanda nake so sama dake, zan iya ƙarar da rayuwata duka saboda in dinga ganinki cikin farinciki tare da wannan kyakkyawan murmushi akan wannan fuskar taki a koda yaushe". Ya ƙare zancen yana nuna fuskarta da yatsansa, cike da jin kunya ta sa tafin hannunta ta rufe fuskar tana cewa, "kai ya Haisam, kar kasa na fara yiwa ƙawayena kuri akan nafi kowa sa'ar samun yayan da ke matuƙar so na aduniya".
"Ki faɗa da kyau duk inda kika shiga cewa yayanki yafi kowane yaya aduniya son ƙanwarsa, don tabbas zan iya bada rayuwarta ga duk wanda ya nemi taɓa mani ke".
Dai-dai lokacin suka kawo bakin gate ɗin makarantar tasu ya ja ya tsaya haɗe da cewa, "To my cutie, Bari na tsaya anan, ayi karatu lafiya, kuma ki kula mani da kanki"
"To ya Haisam in sha ALLAH"
"Yauwa, na manta ban faɗa maki cewa ba ina sonki sosai"
"Nima ina sonka sosai ya Haisam". Ta faɗa tare da rugawa ta shige ciki saboda kunya da ta ji, wani irin jiri ya ji ya ɗebesa jin kalmar data fito daga bakinta haɗe da jin wani irin farinciki marar misaltuwa na ratsa dukkanin sassan jikinsa da kuma ruhinsa, wai da gaske ne Madiyam ɗin sa na son sa? kuma ita da kanta ke faɗar hakan da bakinta? Ya tambayi kansa haɗe da zaunawa daga gefen makarantar yana murmushi, "what a happy moment!" Ya faɗa a fili haɗe da sakin dariyar dake nuna tsantsar farincikin da yake ciki.
Ya jima a zaune wajen kafin ya miƙe ya nufi wajen Abbu da ƙafa, don ba wani nisa ne da inda shagon Abbu yake da makarantar ba, haka ma tsakanin makarantar da gidansu Madiyam ɗin ba wani nisa bane sosai, shiyasa ma da ƙafa ma mutum zai iya zuwa makarantar.
Hisham kuwa tun daya koma ɗaki ya yi kwanciyarsa, babu abunda yake yi illa tunanin Madiyam da yanda take motsa ɗan ƙaramin bakinta ɗazu da yake kallonta da tana cin abinci, dariya ya saki hango lokacin data turo bakin haɗe da janyo wayarsa daya ɗauke ta hoto lokacin ba tare data sani ba, hoton ya jawo haɗe dayin zooming ɗinsa ya sake sakin wata dariya yana kauda kansa gefe ya ce "trouble girl" A hankali Sannan ya gogesa zuwa trash box, dama haka yakeyi duk lokacin da take yin wasu abubuwan dake saka shi dariya, yakan saita wayarsa ya ɗauke ta hoto ba tare da kowa ya fahimci hakan ba, wanda a zahiri idan ka gani zaka ɗauka latsar wayarsa kawai yakeyi, aduk lokacin da kuma ya gaji da kallonsa a wayarsa sai ya goge cike da jin haushin kansa.
Bai fito ɗakin ba har sai da aka kira sallar la'asar, lokacin har Madiyam da Hisham sun fita don tun ƙarfe uku ake zuwa islamiyar, arwala ya farayi sannan ya wuce masallaci, bayan ya dawo ya zauna tsakar gidan yana danna wayarsa, lokaci kaɗan kuma yana yi yana ɗago kansa yana kallon ƙofar ɗakin Mahmah, so yakeyi ya tambayi Mahmah ina Haisam don ya san dole Madiyam ta yi makaranta tunda lokacin zuwa islamiyarsu ya yi har ya wuce amma ya kasa, kallonsa Mahmah ta yi haɗe da cewa,
"Wani abu kake nema Hisham?"
"A'a Mahmah". Ya faɗa haɗe da miƙewa ya koma cikin ɗakinsa, wayar Haisam ya kira har kusan sau uku bai ɗaga ba, hakan ya sa ya sake fitowa yana faɗin,
"Mahmah Haisam fa?"
"Ya fita tare da Madiyam wai zai rakata islamiya".
"Ok" ya faɗa tare da komawa cikin ɗakin ya yi zaune gefen katifar tasa yana ci gaba da latsar wayarsa, ji ya yi bazai iya ci gaba da zaman ba, don haka ya tashi ya fice daga ɗakin haɗe da jawo ƙofar ya fice daga gidan gaba ɗaya, tsintar kansa ya yi da bin hanyar makarantar tasu yana tambayar kansa me yasa ma tun farko baya rakota zuwa islamiyar, gashi yanzu lokaci ɗaya Haisam ya tsiri rakata, wanda hakan zai sa Ammie taga rashin kulawarsa agareta ta wannan fannin, tsaki ya yi tare da ja ya tsaya yana jin haushin kansa, don yanzu idan ya tsiri yin hakan za a ga kamar don Haisam ya yi ne shiyasa shima ya yi, da wannan tunanin ya juya ya koma ƙofar gida ya yi zaunensa, ya yi tsaki tsaki ya fi a ƙirga cike da jin haushin Madiyam ɗin, don a cewarsa ita ta ba Haisam damar hakan amma shi daidai da rana ɗaya bata taɓa nuna masa tana so ya rakata ba, da wannan marece ya yi masa a wajen har aka taddo su Madiyam a islamiya, tunda ya hangota ta doso ƙofar gidan ya ƙura mata idanuwa har ta ƙaraso, kauda kansa ya yi haɗe dayin tsaki ya miƙe ya wuce cikin gida.
A jiyar zuciya Madiyam ta sauke ganin yabar ƙofar gidan don tunda ta hangosa gabanta ke faɗuwa, tana shiga cikin gida ta ji muryarsa yana faɗin, "kizo ki gyara mun ɗakina". Ya ƙare zancen tare da ƙarasawa cikin ɗakin, turo baki ta yi haɗe da cewa,
"Na rantse bazan zo ba, kawai daga dawowar mutum sai a tsiri sakasa aiki".
"To marar kunya, yi niya ya jiki".
"ALLAH Mahmah ni na gaji bazan gyara ba sai dai ya kashe.." kafin ta ƙarasa Mahmah tayo kanta tana faɗin,
"Zaki ajiye ki tafine ko sai na saɓa maki rai, wai ke wace irin yarinya ce haka? Shiyasa sam bana tausayinki tunda ke marar kunya ce, zaki wuce ne ko sai na saɓa maki".
"Mahmah.." ganin ta yo kanta ya sa tayi saurin shigewa ɗaki ta ajiye jakar ta nufi ɗakinsa tana ƙunƙuni, zaune ta iskesa saman doguwar kujerar dake gefe cikin ɗakin ta ɗage labulen ƙofar saboda kar yaci zalinta idan yana hango Mahmah na ka'ida kawo a tsakar gidan,
"Fitarmun ɗaki kuma ki sake mun labule tunda ke ba musulmai bace, in yaso duk randa kika zama musulma sai ki shigo ki gyara".
Sanin inda ya dosa da kuma idan ta tafiyarta me hakan zai haifar mata ya sa bayan ta saki labulen ta yi sallama a bakin ƙofar ɗakin haɗe da cewa, "in shigo?"
Can cikiciki ya amsa sallamar haɗe da cewa, "zaki iya". Ba wani datti ne a ɗakin ba kawai rashin son zama lafiya ne ya sa shi sata gyaran ɗakin tare da son ƙare mata magana, yana kallonta ta fara cire bedsheet ɗin katifar haɗe da kakkaɓeshi sannan ta sake shimfiɗasa da kyau ta gyara filallan ta aza, tana ƙoƙarin shiga toilet ta wanke masa ta ji ya ce,
"Beyi ba".
Juyowa ta yi.ta kalli katifar sannan ta kallesa haɗe da cewa, "meye?"
"Miya" ya bata amsa yana kallon katifar, hakan ya sa ta sake sauke filallan ta sake gyara zanen gadon da kyau sannan ta maida pillows ɗin ta aza, tun kan ta cire hannunta ya sake cewa,
"Bai yi ba shima" ba tare daya ɗago kansa ba a wannan karon, tsaye ta yi tana turo baki haɗe da cewa "to ya zanyi ya Hisham? Ni haka na iya".
"Kina macce baki san yanda zaki gyara common gado ba balle ɗaki, amma kin iya fita anguwa tare da namiji kowa na kallonki, sai kace ba ƴar Fulani ba da aka sani da kunya, fitar mun ɗauki ni na gyara abuna". Ya ƙare zancen tare da ficewa ya bar ɗakin jin ankira sallar magrib, kallon yanda ta luluye katifar ta yi amma don tsabar ganin laifi wai yace bata yi ba, to ya yake so tayi? Ta tambayi kanta haɗe da cewa, "kar ALLAH yasa yayi" ta faɗa a fili tare da haye katifar ta dinga juyi akai har saida ta turmuju zanen gadon tas, kamar ance ta juyo ta gansa tsaye ya zaro idanuwa yana kallon ikon ALLAH, sumui sumai ta miƙe haɗe da raɓawa ta gefensa zata wuce, fizgo hannunta ya yi tare da cewa, "idan na dawo yana haka saina ɓallaki biyu tunda ke marar kunya ce" ya ƙare zancen tare da tura ƙeyarsa sannan ya wuce masallaci, tafe yake yana murmushi haɗe da dariyar yanda ya iskota tana birgima akan gadon har ya kai masallacin, acan ya tadda Abbu da Haisam suma sun dawo sun tsaya yin sallah, tare suka bi jam'i suka gama aka kira sallar isha itama suka yi sannan suka shigo gida tare, abinci suka fara ci sannan Haisam ya je ya buɗe mota ya ɗauko saƙon Hisham dana Mahmah daya manta dashi tare da abunda ya koma ya siyowa Madiyam lokacin da zai zo, saƙon Mahmah ya fara bata sannan ya miƙawa Hisham nashi, kallon Madiyam data takure waje ɗaya ya yi haɗe da cewa, "cutie rufe idanuwanki kema na baki naki sauƙin." Murmushi ta saki tare dasa hannuwa ta rufe fuskarta, wata ƙatuwar tedi fara tas da takusa rabin girmanta ya ɗauko a ƙofar ɗaki daya ajiye haɗe da cewa, "oya to buɗe idanuwanki" ya saita tedin a daidai fuskarta yana dariya, waro idanuwa ta yi haɗe da cewa, "wowwww ya Haisam kamar kasan ina son Baby". Ta ƙare maganar tare da rufe bakinta saboda tsabar farinciki, dariya Mahmah da Abbu suma sukayi ganin yanda ta karɓi tedin ta wani sa a jikinta ta rungume tana faɗin, "Na godiya ya Haisam, babyn so cute". tana wani tattaɓa fuskar tedin,
"Yes she's so cute like you cutie, ta yi maki ko?"
"Sosai ya Haisam ina sonta".
"Ahh..to nifa?" Ya faɗa shaye da toka yana harararta irin da wasa ɗin nan, dariya ta saki haɗe da cewa,
"Kai ma ina sonka ya Haisam sosai"..
Wani irin tsaki Hisham ya ja cike da takaici yabar ɗakin, shiyasa sam baya son wani lokacin Haisam na zuwa don gabaɗaya shi ke ida lalata Madiyam, fisabilillahi yanzu meye na siyo mata wata tedi sai kace ƙaramar yarinya, wannan ai salon ya hanata karatu ne kawai ya sa ya siyo mata ita, ya dinga faɗa shi kaɗai cikin ɗaki haɗe da cilla saƙon da Dady ya aiko masa dashi saman katifar zuciyarsa cike da takaici ba tare daya duba ba.
*ALLAH KA JIƘAN IYAYENMU 👏😭*