FIL HUB

Babi na sha biyu

by @billysfari

Free page 12


        *FIL-HUB*♥️

               (Acikin so💘)

Paid Book: N5

    Written by

       Billy s fari💎

______________________________

A haka Hisham ya shigo ɗakin ya taddashi yan faman kai da kawo haɗe da suruttan da shi kansa ma baisan dalilin yin su ba, kallonsa ya yi cike da tuhuma kafin yace, "Wai lafiya kake Hisham? ko ka manta matsayin da Abbu da Mahmah ke dashi a wajenmu ne? Yanzu ka faɗa mun, me akayi najin haushi awajen da zakayi masu tsaki ka fito?"


"Look ya Haisam, bana son takurawa da damuwa, kaje ka ƙare abunda kake yi sai ka dawo muyi magana, amma ina so ka sani, ni ba Mahmah da Abbu nake yiwa tsaki ba.."


"Oh kenan Ni kake yiwa ko?"


"Akan me zanyi maka tsaki ya Haisam? Saboda bana da abunyi?"


"Yes upcouse, tunda har baza ka iya ɗauke idanuwanka ga abubuwan da nake yiwa Madiyam ba dake saka ka jin haushi to tabbas ba kada abun yi".


"Ok haka kake zato?"


"Eh haka ɗin ne Hisham, ni na rasa me yasa ka ɗauki karan tsana ka ɗorawa yarinyar can, gabaɗaya sam baka ƙaunar farincikinta da walwalarta.." Haisam ya faɗa rai a ɓace yana ware hannuwansa, cikin sanyin murya mai cike da ɓacin rai shima Hisham ya ce,


"Ok, shikenan na ji, kai da kake son farinciki da walwalarta sai kaje ka ci gaba da bata, in yaso ka maidata ciki idan zaka iya". Ya ƙare zancen tare da ɗaukar wayarsa da makullin motar da Haisam ya zo da ita dake ajiye kan gado ya bar ɗakin ransa a ɓace,


Bayansa Haisam ya bi yana kiran sunansa ya yi banza dashi haɗe da buɗe motar da ƙarfi fizga ya bar ƙofar gidan, tsaye Haisam ya yi riƙe da kunkuru kafin ya koma cikin gidan, tsaitsaye ya tadda su Mahmah a tsakar gidan jin ƙarar yanda Hisham ya tada motar haɗe da sunansa da Haisam ke kira ya ƙi saurararsa.


"Lafiya Haisam? Me ke faruwa tsakaninku?" Abbu ya tambaya yana riƙo hannunsa, murmushi ya saki haɗe da cewa,


"Ba komai Abbu, ku ƙyalesa haka yake da baƙar zuciya akan ɗan abunda bai kai ya kawo ba, ya tafi duk inda zai je ALLAH ya kiyaye".


"A'a Haisam kada kace haka, baka ji yanda ya tada motar ba ne?"


"Ba abunda zai faru Mahmah ina sha ALLAH, kuje ku kwanta ni zan jira dawowarsa".


"ALLAH ya kyauta" Abbu ya faɗa tare da komawa ciki, don idan har zai ce bai ji zafin abunda Hisham ɗin ya yi ɗazu ba, to ya yi ƙarya, Mahmah kuwa kallon Haisam ta yi haɗe da cewa,


"Ya kamata kai da Abbu ku fahimci Hisham da kyau, abubuwan da kukewa yarinyar nan ne dake shagwaɓata suna sakata sakalci ne baya so, sai yake ganin kamar yana tubƙa ne kuna walwala, kana gani dai da idanuwanka, in ba shi ba babu wanda Madiyam ke tsoro agidan nan, ga rashin ji da rashin kunya tab cike da cikinta, kuma idan muna da rayuwa gidan wani zata je bai kamata abarta tana cigaba da rayuwarta haka ba..."


"Haba Mahmah! Me yasa kullum kike goyon bayan abubuwan da Hisham ke yiwa Madiyam, shin ita ba ƴa bace da baza a barta tayi rayuwarta yanda take so ba? Wannan takurawar da Hisham keyi mata tayi yawa wlh"


"Na sani Haisam, amma duka yana yi ne don tasan ciwon kanta da kuma gyaran gobenta, ka ga kuwa bai dace a hanasa ba tunda ɗan uwanta ne".


"Koma dai meye abun nashi ya yi yawa Mahmah, shi kansa yana buƙatar a gyara masa saitin rayuwa saboda a wani baibai yake tafiyar da tasa, sai kuma yace yanda rayuwarsa take haka yake buƙatar wasu suyi tasu? Bazai yuyu ba kawai ku ƙyaleni dashi". Ya ƙare zancen tare da koma wa wajen ya zauna, tun suna dubin dawowar Hisham har ƙarfe sha biyu ta wuce bashi ba labarinsa, abun da ya matuƙar tayar wa da Mahmah hankali kenan, don ko ƙarfe takwas da rabi na dare nayi Hisham na dawowa gida, bai taɓa kaiwa ko ƙarfe goma a waje ba inba abokinsa Ashafaq ya zo ba ya je yi masa rakiya, gabaɗaya ta kasa zaune ta kasa tsaye akan rashin dawowarsa haka ma bacci ya gagara ɗaukarta saboda rashin sanin halin da yake ciki, har ga ALLAH tana jin wata irin soyayya da ƙaunar Hisham a ranta da baza ta taɓa iya jurewa wani abun ya samesa ba.


A ɓangaren Hisham kuwa yana fizgar motar bai tsaya ko ina ba sai can bayan gari, ba tare daya damu da dare bane ya yi parking motar haɗa da fitowa ya samu waje ya zauna, ba by abunda yake buƙata a yanzu sama daya ganesa shi kaɗai, shi yasa ya baro gidan ya dawo nan ya zauna saman wani dutsi ko zai samu natsuwar zuciya, don yanzu haka wani irin zafi take yi masa tamkar zata huda ƙirjinsa ta fito, ya fi ƙarfin mintuna goma sha biyar a haka kafin ya miƙe ya sake komawa cikin motar, nan ma wasu mintuna biyar ya sake kwashewa kansa na jingine ajikin kujerarar motar daya zauna kafin ya tayar da motar ya yi gaba, gidansu Ashfaq ya nufa don dare bai wani yi sosai ba ya tadda shi ƙofar gida tare da wasu abokanansa suna fira, motar ya yi parking ya fito haɗe da wuce ta gabansu ba tare da ya ce dasu uffan ba ya wuce tsaye cikin ɗakin na Ashfaq daya gani a buɗe don dama a ƙofar gida ɗakin nasa yake, kallo ɗaya Ashafaq ya yi masa ya girgiza kai tare da maido hankalinsa wurin abokanan nasa suka ci gaba da fira, ɗaya daga cikinsu ne ya ce,


"Mtsss..ni fa gaskiya bana son gayen can Ashfaq saboda girman kansa ya yi yawa". Ya faɗa a hasale haɗe da miƙewa tsaye cikin ɓaci rai, "wallahi ka riga ni faɗa ne kawai Jamil, amma nima sam bana son shi, mutum sai kace ya fi kowa kana ganin mutane amma baza ka iya yi masu magana ba sai dai ka raɓa su ka wuce kana wani cin magani, ko da yake ba laifinsa bane, laifin ka ne Ashafaq da ya ga kana kula shi, shi yasa har yake yiwa mutane wannan faɗin ran tsiya".


"Look Khalid, Jamil kuyi haƙuri, kunsan kowa da irin rayuwarsa, ba wulaƙanci ne Hisham keyi maku ba, kawai haka rayuwarsa take, kuma kunsan baza mu iya sauya masa ita ba". Ya ƙare zancen tare da kallon Khalid da Jamil dake tsaitsaye cikin ɓacin rai, tsaki Jamil ya ja haɗe da cewa, "Dallah gafara, ko haka rayuwarsa take ai ya yi wa mutane sallama idan har bazai iya tsayawa a gaisa ba, kai dake iya wa da halinsa sai kaje can kayi ta haƙuri dashi, Khalid wuce muje". ya faɗa tare da taɓa Khalid suka bar wajen, shiru Ashafaq ya yi haɗe da duba agogon wayarsa yaga ƙarfe goma da rabi na dare, ajiyar zuciya ya saki tare da juyawa ya shiga cikin ɗakin, kwance ya isko shi idanuwansa a rufe ya ɗora hannunsa ɗaya a saman goshinsa ɗaya kuma akan ƙirji tamkar mai bacci, gefen ƙafafuwansa ya zauna tare da kallonsa ya ce,


"Hisham lafiya? Me yake faruwa?". Kusan mintuna biyar ya kwashe yana yi masa magana amma ya yi banza dashi hakan ya sa ya miƙe ya shigewarsa cikin gida don inda sabo ya saba da irin wannan murɗaɗɗiyar halayyar ta Hisham dake bala'in wahalar dashi, musamman akan Madiyam daya yi ta ƙoƙarin fahimtar dashi amma yaƙi fahimta, shi yasa wasu lokutan yake fita batunsa ya saka masa idanuwa, yasan duk ranar da giɗa ta ji gashi ita za tayi ɗaɗo da kanta.


Har ƙarfe sha biyu ta buge Hisham na kwance a wajen bai ce dashi ko uffan ba shi ma kuma bai sake bi takansa ba ya ci gaba da yin abunda ke gabansa, ganin yana shire-shiren kwantawa ya sa Hisham miƙewa yana faɗin, "Sai da safe" ya amsa masa da "mu tashi lafiya tare dayin tsaye bakin ƙofar ɗakin nasa yana kallonsa har ya shiga motar ya tayar ya bar ƙofar gidan sannan shima ya shige ɗakinsa ya rufe ya kwanta yana jinjina zurfin ciki irin na Hisham.


Ganin hasken mota ya nufi wajen ya sa Haisam dake zaune yan latsar wayarsa ya koma cikin gida, "Mahmah to kije ki kwanta ga ɗan renin wayon nan ya dawo" Haisam ya faɗa ganin Mahmah zaune saman bencin dake tsakar gidan ta rafka tagumi lokaci ɗaya kuma tana faman gyangyaɗi.


Bata bar tsakar gidan ba sai da ta ji shigowar Hisham tare da rufe gidan, duk da haka tsaye ta yi har sai daya ƙaraso, ganinta zaune a saman bencin ta zubo masa idanuwa ya sa shi jin ba daɗi haɗe da rashin kyautawarsa, wajenta ya ƙarasa ya zauna kusa da ita haɗe da cewa, "Mahmah baki kwanta ba.." kafin ya ƙarasa ta ɗaya hannu kamar zata maresa ta ce "yimun shiru, taya kake tunanin zan iya kwantawa a yanayin da naji kafita gidan nan, taya kake tunanin bacci zai ɗauke ni awannan yanayin da ka fita ba tare da nasan wane hali kake ciki ba?"


"Kiyi haƙuri Mahmah muje ki kwanta". Ya faɗa tare da riƙata har cikin ɗaki ta zauna a gefen gado, hannunsa ta kamo shima ta zaunar dashi tare da tallabo fuskarta suna kallon juna ta ce,


"Hisham, idan akwai abunda ke damunka ka sanar dani, bana son ganinka cikin irin wannan yanayin da kuma saurin fushin da kake yawan yi, hakan baya mani daɗi sai naji kamar na gaza wajen baka irin kulawar daya kamata ace kowace uwa na bawa ɗanta, a ko yaushe ina yimaka kallon wani haske kuma alkhairi a tare damu, shi yasa bazan iya jurewa ganinka cikin ko ƴar ƙanƙanuwar damuwa bace".


"Kiyi haƙuri Mahmah, in sha ALLAH zan dena, nima bnsan me yasa nake tsintar kaina cikin ire-iren wannan fushin ba, amma zanyi ƙoƙarin nisanta kaina daga abubuwan dake haifar mani dashi".


"Ka tabbata?".


"In sha ALLAH Mahmah". Ya faɗa haɗe da ɗora hannunsa a saman nata dake kan fuskarsa yana sakar mata murmushi, ajiyar zuciya ta sauke sannan ta gyara kwanciyarta tana faɗin, "ka ja mun ɗakin idan ka fita, sai da safe".


"To" ya faɗa haɗe da juyawa ya kalli Madiyam dake kwance ƙwaƙume da tedinta tana baccinta hankali kwance, ji yakeyi kamar ya fincike tedin daga jikinta ya je ya ƙona amma ya san yin hakan babban kuskurene, don ko shi aka yiwa haka sai ya ji zafi sosai, tsaki ya ɗan ja cike da jin haushin kansa ya kashe wutar ɗakin sannan ya fice haɗe da rufo masu ƙofar, ajiyar zuciya Mahmah ta sauke haɗe da gyara kwanciyarta don tana kallon duka mintunan daya kwashe tsaye a wajen yana kallon Madiyam kafin yabar ɗakin.


Ko daya shiga ɗakinsa kuwa ya tadda Haisam har ya yi kwanciyarsa akan gadon bacci ya soma ɗaukar sa, ba tare daya bi takansa ba shima ya ɗauko pillow ya jefa kan doguwar kujerar dake ɗakin shima ya yi kwanciyar sa, baccin da gabaɗaya rabi da rabi ya riƙa zo masa tsabar tunani har sai da aka kusa kiran sallar asuba sannan ya ɗaukesa.


A ɓangaren Najlah kuwa tana shiga gidan Ammie da ta ji tana waya da Haisam akan idan bai taso ba ya bari sai gobe ya dawo ta ji wani irin zazzaɓi da kishi sun taso mata lokaci ɗaya, kasa ɓoye hakan ta yi har sai da ta ce, "Ammie saboda me zaki ce ya kwana acan, ai ƙwanda ya dawo gida tunda kinga Abbie baya nan".


"A'a Najlah, hanyoyin nan basu da kyau kema kin sani, ALLAH ya kare ba fata ba idan yace ya kamo hanyar nan yanzu ya taho kafin ya iso dare ya yi, kuma zai iya haɗuwa da miyagun mutanen nan da idan har basu kashe mutum ba za su iya garkuwa dashi, to wahala ake gudu ba abunda zasu tambaya ba shiyasa na ce yayi zamanninsa sai gobe kin fahimta".


"Kuma Ammie a gidansu Madiyam zai kwana".


"Eh mana, banda abunki Najlah yana da wani waje ne a can wanda ya fi masa gidansu?"


"Hotel mana Ammie, ba sai yaje can ya kwana ba da safe sai ya dawo". Zaro idanuwa Ammie ta yi haɗe dayin dariya kafin tace,


"Hotel kuma Najlah, ga gidan baffan nasa inda ɗan uwansa yake zai wani je hotel ya kwanta, ai bazai yuyu ba".


Kallonta Ailat dake zaune tana kallo ta yi haɗe da cewa, "Tab..ai aunty Najlah babu hotel a Giwa, kuma ALLAH NI gani nakeyi ɗan iska kawai ke kwana a hotel, sai kuma dole idan ta kama, ai ƙwanda ya yi kwanciyarsa a gidan Abbu wlh, babu wata takura kuma zai ma fi sakewa acan sosai bisa ga hotel.."


"Dalla rufa mana baki, to waya tambayeki ne?" Ta kwatse Ailat ranta a ɓace sannan ta miƙe tana yiwa Ammie sai anjima ta bar gidan.


Dariya Ailat ta saki haɗe da cewa, "Kai! Wlh aunty Najlah akwai kishi, don fa Madiyam ta daɗi hakan Ammie".


"Ina ruwan Najlah, ai akwai aiki gaskiya don matuƙar akayi auren nan nasu da Haisam to fa daƙyar in zata amince ya auri Madiyam, gashi Abbie ya ce sunyi magana da Dady idan ya dawo daga Abuja za a tsaida maganar aurensu".


"Amma Ammie kina gganin ya dace haka? Wlh da gaske ya Haisam keyi yana son Madiyam sosai"


"Na sani Ailat, itama Najlah ɗin zai so ta tunda akwai shaƙuwa da fahimtar juna tsakaninsu, sannan baza mu ci gaba da zuba masa idanuwa haka ba aure ba, kuma daya je ya ɗauko mana bare ai ƙara Najlah ɗin, in yaso daga baya sai ayi maganar Madiyam idan tana sonsa, tunda itama ba a san ra a yinta akan shi ba".


"To ALLAH ya sanya alkhairi, wlh ina son ya Haisam ya auri Madiyam saboda ba kaɗan yake sonta ba".


"Ai abun farin ciki ne idan ya aureta don sake ƙarfafa zumunci ne haka".


Dariya Ailat ta yi haɗe da cewa, "oh ya Hisham, shi kuma ko sai yaushe zai zaɓo matar da zai aura? ALLAH ba don basu shiri da Madiyam ba da ma shiya aureta don sunfi dacewa".


"Kar ki bari ya ji wannan zancen, in ba haka ba zaku ɓata dashi".


"Na sani Ammie, amma dai baisan ya Haisam na sonta ba ko?"


"Zai sani ne tunda kinsan halin Haisam bai iya ɓoye abuba a ransa, inda dai shine to bazai bari kowa ma ya ji ba balle shi".


"Aikuwa, to ALLAH ya bashi ta gari shima".


"Amin ya ALLAH, kema ALLAH ya baki na gari"


"Amin Ammie, amma fa ya Nau..." Sai kuma ta kasa ƙarasawa haɗe da miƙewa ta bar wajen cike da jin kunya, don tuni sun jone da ya Naufal ba tare da kowa ya sani ba sai yanzun da ta yi suɓul da baka, da idanuwa Ammie ta bita haɗe da cewa, "Tooo... Kunji yaran zamani, wato suna can suna sha'aninsu bamu sani ba, kinga ikon ALLAH, to ALLAH ya tabbatar mana da alkhairi". Ta ƙare zancen cike da jin daɗi da farinciki a ranta, don kuwa ta yaba da hankalin Naufal dashi har mahaifiyarsa, ta kuma tabbata ba ƙaramin farinciki ƴarta zata samu ba idan ta auresa, fata dai kawai ALLAH ya sanya alkhairi a cikin lamarin.


*****.     *****.     *****

 Kamar yanda Hisham ya saba ako yaushe idan ya yi sallar asuba bai fiye komawa bacci ba, yakan littafansa ne ya duba ko kuma ya hau karatun ƙur'ani har safiya ta fara wayewa, yauma haka, text books ɗinsa ya ɗauko ya ɗan dudduba topic ɗin da zai yiwa ɗalibbansa sannan ya miƙe ya faɗa toilet yayo wanka, zaune ya samu Haisam shima ya tashi baccin daya koma bayan sallar asuba, "Morning brother". Ya faɗa a daƙile yana goge kansa da ɗan ƙaramin towel daya fito riƙe dashi, "morning Hisham, ka tashi lafiya".


"Fine" ya bashi amsa a taƙaice tare da rataye towel ɗin ajikin ƙofar shiga toilet sannan ya nufi wajen wadrobe ɗin kayansa ya fiddo kayan da zaisa haɗe da shafa mai, cikin mintuna kaɗan ya gama shirinsa cikin wani rantsattsen boyel fari tas ɗaya matuƙar karɓar jikinsa, kai tsaye ɗakin Mahmah ya nufa ya tadda Abbu yana karyawa, 


"Abbu ina kwana" ya faɗa yana Sadda kai ƙasa saboda abunda ya faru jiya, murmushi Abbu dake kallonsa ya yi haɗe da cewa,


"Lafiya klw Malam Hisham, anfito?"


"Eh Abbu". ya faɗa yana warar idanuwa, dariya Mahmah ta yi haɗe da cewa,


"A haf! Tana ciki tana aikin, ka ganshi nan shi yace na ƙyaleta sai zuwa anjima".


"Me yasa Abbu?"


"Hisham ko bakwai naga bata yi ba, kuma ga alama baccin bai isheta ba shiyasa"


"To amma Abbu idan bata tashi dawuri ta shirya ba, taya kake tunanin zata isa makaranta cikin lokaci? Sannan idan yaro ya yi lattin zuwa makaranta hakan na nufin ya rasa darasi na farko da akeyi, wanda hakan ba ƙaramin cutar da yara yakeyi ba".


"Kamar ya Hisham?"


"To Abbu da safe koda yaro zai tashi ƙwaƙwalwarsa fresh take, duk abunda aka karanta ko aka faɗa masa zai ɗauke, haka kuma akwai msimaicin darasin jiya da akeyi wanda idan ɗalibi bai fahimta ba yau idan anyi zai fahimta, ka ga rasa wannan a wajen ɗalibi abune da zai cutar dashi sosai".


"Haka ne gaskiya, to ai bansan haka abun yake ba, shiga ki tafi da ita" Abbu ya faɗa yana nuna ƙofar, 


Kusan mintuna biyar Mahmah ta kwashe tana fama da Madiyam ta tashi amma taƙi hakan ya sa Abbu zuwa da kansa shima ya yi yayi taƙi tashi, da an ɗaga ta sai ta koma luuuu.ta sake yin kwanciyarta tana faman ƙwakume tedinta, hakan ya sa Mahmah fitowa cike da takaici ta ce,


"Je ka tadota da kanka shima ya yi yayi taƙi tashi".


Dama kamar jira Hisham keyi ya shiga cikin ɗakin tana kwance saman gado ta naɗe cikin tedin, wani irin takaici ne ya rufesa ganin Madiyam fa ba ƴar shekara bakwai bace ko goma, shekaru kusan sha huɗu cikin ta sha biyar take dasu amma ace sai abubuwan yara takeyi tsabar shagwaɓawr da kayi mata, tedin ya fara fizgowa da ƙarfi aikuwa Madiyam tayi wani zallo ta riƙe tedin tare dayin kwance ajikinsa tana faɗin, "wayyo Abbu kabrmun babyna" tana sake gyara kwanciyarta akan ƙirjinsa, runtse idanuwa yayi jin wani irin abu kamar anyi masa shocking a jiki tare dasa hannu ya fizgota da ƙarfi daga jikin nasa ya dire ƙasa yana faɗin.


"A gidan uwar wa wannan abun ta zama babynki? Zaki buɗe idanuwa ne ko sai na ɗaukeki mari tare da ƙona wannan abar". Ya faɗa yana wurgota falo haɗe da taso ƙeyar Madiyam a gba yn mangarar mata kai, karaf tedin ta faɗa a hannun Haisam daya shigo falon yanzu, cike da ɓacin rai ya nufo kan Hisham ya ɗaukesa mari tare da riƙo hannun Madiyam ya maida a gefensa haɗe da miƙa mata tedin yana watsawa Hisham wani irin mugun kallo haɗe da cewa, "Kai wane irin mugune marar tausayi Hisham, wane irin zalinci ne haka kake yiwa yarinyar nan fisabilillahi, ka kuwa san irin matsayi da soyayyar da nake yi mata azuciya ta?, Kasan irin ɓacin ran da kake saka ni aduk lokacin daka musguna mata? Look daga yau ina so ka fidda hannunka a lamarin Madiyam kafin mu samu matsala dakai domin Madiyam rayuwata ce" ya ƙare zancen haɗe dasa hannu ya rungumota a jikinsa sannan ya ci gaba da cewa "saboda haka ka ƙyaleta tayi rayuwarta yanda take so ni ina sonta a duk yanda take kuma aduk yanda zata tashi, shagwaɓa, sakalci da duk wani rashin jin maganarta basu dameni ba kuma a haka nake sonta, don haka babu ruwanka da lamarinta na faɗa maka". Ya ida zancen yana nuna sa da yatsa.


Cikin ɓacin rai shima ya yo kansa ya ce, "Baka isa ba wlh, kai meka sani akan so da har zaka furta cewa kana son Madiyam, wai a tunaninka duk abubuwan da nake yi mata saboda bana sonta ne? To kayi kuskure ya Haisam domin wannan abun da nake yimata shine so, shi ake kira da ƙauna kuma duka ina yimata su ne *A cikin so*, me ma kace? Madiyam rayuwarka ce? To tabbas zaka mutu domin baza ta taɓa zama mallakinka ba, ni ne nan na dace dana kira Madiyam rayuwata domin duka tawa rayuwar mallakinta ce ita kaɗai, sannan zanci gaba da gina rayuwarta izuwa yanda nake so don ta tabbata cewa ni ɗin da ita mallakin juna ne ta hanyar cuɗanya a cikin halaye ɗaya". Shaƙo wuyan rigarsa Haisam ya yi haɗe da cewa.   


"Karya kake Hisham kai ba masoyinta bane, dubeka a haka kake kiran kanka masoyi kana neman muzguna mata akoda yaushe, da wuɗan nan munanan halayen naka da kake nuna mata kake sa ran zaka iya zama masoyinta? You Are just playing Hisham, idana kana tunanin wuɗannan abubuwan da kakeyi duka *A cikin so* ne, You fail Hisham, domin tuni suka maida kai zero behind a decimal point (0.00) a zuciyarta, idan kuma baka gane ba to ina nufin fanko kake a zuciyar Madiyam.." kafin ya rufe baki Hisham da idanuwansa suka kaɗa suka yi jajir saboda tsananin ɓacin rai da ɗacin maganganun da Haisam ya faɗa masa ya shaƙo wuyan sa tare da haɗewa ga ginar ɗakin yana faɗin,


"Waye fanko a zuciyar Madiyam? Kana tunanin zamowarka yayana zai sa ka faɗi irin wuɗannan kalaman akaina kuma in ƙyaleka? Bazai yuyu ba don idan har ban mallaki Madiyam ba kaima baza ka taɓa mallakar ta ba" kafin ya rufe baki Abbu dake tsaye sake da baki yana kallon ikon ALLAH ya ɗaukesa wani irin Zazzafan mari ganin yanda Haisam ke kokuwa da lumfashinsa yana neman taimako, don ba ƙaramar shaƙa Hisham ya yi masa ba da kaɗan ya rage ya leƙa barzahu ya dawo, cikin ɓacin rai Abbu ke magana haɗe da cewa.


"Hisham kana da hankali? Yayan naka kake yiwa haka? To bari kuji in faɗa maku, kana son Madiyam ko ba ka sonta, kai ne ke sonta ko shi ke sonta duka ba damuwata bane, Madiyam ƴata ce kamar yanda kuma kuke ƴaƴana, saboda haka haƙƙin zaɓa mata miji na akaina sai wanda naga dama kuma ya kwanta mani arai na kuma aminta da irin soyayya da kulawar da yake yimata sannan zan aura masa ita". Ya ƙare zancen tare da karɓar wayarsa dake hannun Mahmah ya fice daga gidan.....


_Hmmm tirƙashi!, Ko ya wannan wasar zata kaya tsakani Haisam da kuma ɗan uwansa Hisham? Ina labarin Najlah da kwanaki kaɗan suka rage a tsaida maganar aurenta da Haisam? Shin Haisam zai amince ko kuwa? Tsakanin Hisham da Haisam wa Abbu zai zaɓawa Madiyam a matsayin miji, shin ya Madiyam zata karɓi kalaman Hisham da suka yimata dirar mikiya acikin kunnuwa cewa duka abubuwan da yake yimata *A cikin so* ne, shin zata yarda da hakan ko kuwa? Idan kina son jin yadda labarin zai kaya to maza ki hanzarta biyan kuɗinki domin ayi wannan kyakkyawar tafiyar mai cike da kyakkyawan salo da kuma kyakkyawan tsari a tare dake.💃💃💃💃_