1
by @zeeeyybawa
DA UBA AKE ADO
(Bada riga ba)
*بسم الله الرحمن الرحيم*
ZAYNAB BAWA
Marubuciyar
*BIBIYATA AKEYI*
*Y'AR FARI*
*YARIMA FAYAD* paid ₦300
*ƘADDARAR RAYUWA*
*BIBIYATA YAKEYI (WAYE SHI?)* ₦500
*IYALAINA (A'ilaty) ₦500
Cikin nutsuwa suke sauƙowa daga steps da zai sadasu da Babban palourn dake gidan, Sound ɗin Foodsteps ɗinsu kawai ake iya jiyowa dagashi sai ƙarar na'urori da ake jin sautinsu suma. Ƴan matane guda biyu wanda suke da ɗibin kamanni ko ba'a faɗa ba ansan cewa suɗin ƴan uwane ɗaya tana sanye da atampa wacce akayi mata ɗinkin riga da skirt sun zauna ɗass a jikinta ta yafa mayafi sai schoolbag dake bayanta, ƙafarta sanye da takalmi ƙirar toms wanda yasha adon duwatsu kalar atamphan dake jikinta, hannunta rayate da lab-coat ga dukkan alamu ɗalibar lafiya ce, yayinda ɗayar kuma tana sanye da Riga da skirts na kanti rigar farar t-shirt ce wacce akayiwa zane da baƙin flowers sai baƙin High waist skirt da ta ɗaura akan rigar ta yane kanta da ƙaramin black veil ƙafarta kuma baƙin high heel ne sai Suit data riƙe a hannu da alamu zata ɗaurata akan suturar dake jikinta, ita kuma alamun shigarta ya nuna itaɗin ɗalibar lawyer ce. Kowacce a cikinsu zallan gazal da White lip-gloss ne a fuskarta amma hakan bai hana sirrintaccen kyawunsu fitowa ba yayinda kowacce take ɗauke da kyawunta dai-dai gwargwado abune mawuyaci agane wanda tafi wata kyau a cikinsu saboda kowacce na ɗauke da Halittar kyawunta mai tasirin gaske, dukansu biyun sirara ne. A lokacin da suka ƙarasa sauƙowa daga steps ɗin suka nufi wata ƙofa, saida suka wuce wani ɗan corridor kafin ya sadasu da wata ƙofa, knocking sukayi haɗeda sallama ɗauke a bakinsu. Dag ciki aka basu umarnin shiga. Wacce ke sanye da atampha ta murɗa handle na ƙofar suka shige.
Magidanci kyakkyawan bafulatani ne zaune a bakin gado da yana kallonsu fuskarsa ɗauke da murmushi Cikin harshen fullanci suka gaisheshi ya amsa yana murmushi.
"Yau lokaci guda zaku fita kenan?"
"Eh Abba dukanmu fitar safe zamuyi amma ni sai 9am zan shiga lactures kawai dai naga yafi mufita tare saboda kafin driver yakaita yadawo lokaci ya ƙure" wacce ke sanye da atmpha tayi magana.
"Toh madallah hakan yayi, Chubaɗo ƙarasa jikin drawer ki ɗauko muku 4k kowacce 2k idan akwai wani abun buƙata sai kuyi amfani dashi cikin ladabi mai sanye da atamphar ta miƙe ga dukkan alamu ita akewa laƙabi da Chubaɗon ta isa gaban drawer taja kuɗine ƴan dubu-dubu aciki aƙalla zasu kai 8k ta kwasosu gabaki ɗaya ta juyo ga mahaifin nata.
"Abba kuɗin ciki ma yaƙare fa saura 8k kuma nasan kafin afita a ciro maka kuɗi zakayi amfani dasu kawai labarshi ni bawani jimawa zanyi a school ba kuma Ummi tabani dubu ɗaya dazan fito" Jijjiga kai yayi cikim jin daɗin kalamanta ya miƙa mata hannu tagane abunda yake nufi saboda haka ta miƙa masa kuɗin dake hannunta,
Murɗa ƙofar dake cikin ɗakin akayi wata matashiyar mata da bazata wuce 41years ba tafito hannunta da ruwa alamun wanke toilet ɗin tayi saboda tun shifowarsu sukejin alamun ana amfani da ruwa a ciki, zama tayi gefen mahaifin nasu da fara'a ɗauke a fuskarta take faɗin.
"Ƴan biyun Abba kun fito kenan?" Atare suka amsa da,"Eh" ta kalli mai baƙin kayan "Hameeda kin amshi kuɗin text books da kikace ina baki mance dasu ba?" girgiza kai tayi.
"A'a Mommy Ban amsa ba yanzu shigowarmu kuma Abbanma naga baida kuɗi a hannu dan baifi 8k bane duka kuɗin dake ɗakin"
"Uhm toh sai yayi miki tranfer aikoh? Tunda kinsan Abban ai bayason wasa da lamarin karatu" murmushi yayi kawai yana nazarin wani abun a duka kalaman da suke faɗa.
4k yazare cikin 8k data rage masa ya miƙa musu kowacce 2k, Jijjiga kai Chubaɗo tayi,
"A'a Abba ai nafaɗa maka mama tabni kabarshi kawai" Ki amsa kar kuyi latti nima zan shugo asibitin naku inaji da Yamma akwai patients da zan gani inaso ki jirani akwai abunda zaki tayani a asibitin sannan kafin naje zanbi asibitina acan asibitin naku za'a baki duk wasu Equipment da zaki buƙata naji akwai aikin da zakuyi ba?" jijjiga kai chubaɗo tayi dan tasan komai dake faruwa a asibitinsu a kunnen mahaifinta yake. Ya juya ga Hameeda.
"Baɗɗo zanyi miki transfer kafin ki isa kuɗin zaije" jijjiga kai tayi su dukansu sukayi masa godiya Chubaɗo ta sanya hannu ta amshi kuɗin taraba gida biyu tabawa Hameeda wacce mahaifinsu ya kira da Ɓaɗɗo" miƙewa sukayi suka suka yimasa godiya suka fice.
Sun rigada sun aika ƙaninsu ya sanarwa Driver ta tafiyarsu makaranta saboda Haka yagama shiryawa fitowarsu kawai yake jira.
Hameeda yafara sauƙewa a university ɗinsu saboda tafi kusa da gidansu Sannan yawuce yakai Chubaɗo wacce hankalinta yake kan waya tun fitar ƴar uwartata
Wata fantamememiyar private University wacce ke haɗe da kantamemen shahararren asibiti a cikinta. Makaranta ce wacce take ƙunshe asibitinta a taƙaice dai Private teaching Hospital ne wanda akayiwa laƙani da KAMFUT INTERNATIONAL TEACHING HOSPITAL tun daga layin da zai sadaka da mashigar makarantar wannan tambarinne ajiki har izuwa kan katafaren teaching Hospital ɗin. Ginin makaranta Ginine wanda ya tsaru iya ƙarshen tsari, yasamu zane daga manyen ARC yayinda suka miƙa gininsa a ƙwararru kuma fasahan magina' Makarantar tana ƙunshe da gates guda uku, ta main gate suka bi drivern bai tsaya ba saida ya sadata da gaban yanda take ɗaukan darasai sannan yayi parking saboda girman wajan yakai a kirashi girma zata iya ɓata 20minute batareda ta isa cikin wajanda zatayi lacture ba daga bakin gate. gefe guda daga Hannun dama na makarantar asibitine wanda suke tayen girma da Makarantar. Sai dai makarantar ta kasance mai hawa huɗu shikuma Asibitin mai hawa Uku.
ƙofar mashigar makarantar ta nufa wajene dayake rufe ciff-ciff kamar wani mall fararen kaya kawai suke wulgawa harma da fararen fata, cike da nutsuwa tafara taka steps ɗin amma hankalinta yana kan wayarsa sai dai kawai ta ɗaga idanuwanta ta kalli yanda take nufa, a hawa na biyu ta tsaya tayi hannunta na dama ƙofar wani lacture hall ta tsaya ta sanya lab-coat ɗinta ta saka wayarta cikin aljihu sannan ta murɗa handle na ƙofar ta ƙarasa ciki, kai tsaye seat ɗinta ta nufa wanda yakeda tambarin sunanta a jiki an rubuta AISHA AHMAD GIƊAƊO bag ɗinta ta ajiye a ƙan seat ɗin ta zauna a samansa sannan ta kai dubanta ga seat ɗin bayanta wanda itama itan take kallo.
"Zeezee Su Badiyya basu ƙaraso ba kenan?" tayi maganar tana canja kallonta zuwa seat ɗin da aka rubuta BADIYYA ABDULSAMAD dana bayansa , NADEEYA ALIYU JIKA Wacce aka kira Da Zeezee ita kuma naga an rubuta ZALAIHAT AMINU a jikin nata seat ɗin tace.
"Basu ƙaraso ba aida kin gansu zaune amma inaga a duk yanda suke yanzu kun kusa ƙarasowa" bata rufe baki suka shigo cikin class ɗin. Murmushi chubaɗo tayi.
"Ƴan halas kunƙi ambato yanzu nake tambayan Zeezee wajanku"
"Aikuwa gamu mun iso amma kema nasan baki daɗe da isowa ba dan yanzu naga drivern gidanku mun haɗu dashi zai fita daga school"
"Eh amma ai koma yaya na rigaku zuwa ba?" chubaɗo tafaɗi cikin zolaya. Suka ƙaraso ciki kowacce tazauna a seat ɗin banda chubaɗo wacce ta ɗaura bag ɗinta anata seat ɗin sukayi facing Juna.
"Uhm ai dole kizo dawuri kekam idan ba haka ba sai dai kijiki a ƙasa kawai kina shigowa" dariya dukansu sukayi. Chuɓaɗo tayi narai-narai.
"Nidai gabana har faɗuwa yake idan natuna zamu amshi wannan darasin"
"Mudai muyi addu'a Allah ya rabaki da wannan mutumin lafiya" nan sukaci gaba da hira kafin 8:40am gabaki ɗaya student da suka gama hallara lacturer kawai suke jira. 9:am yashigo cikin class ɗin. Yana shigowa Suka far dariya ƙasa-ƙasa banda Chubaɗo dataci murr gabaki ɗaya ranta yayi babu daɗi.
Tunda yashigo yafara musu lactures idanuwansa yake kan Chubaɗo, itakuwa chubaɗo tunda ta nemi wani wajan na daban ta ɗaura idanuwanta bata sake ɗagowa ba, kaff student dake cikin class ɗin sun daɗe da fahimtar abunda ke faruwa tsakanin chubaɗo da wannan lacturer dafarko daya fara sunyi zaton yanayi ne sahoda ta kasance student datafi kowacce ƙoƙari sai dai da abun ya juye wani iri suka fuskanci wata manufa ce ta daban yakeda ita akanta, a mintunan da bazasu gaza cikin awa biyu ba yagama yimusu lactures ya fice.
Ajiyar zuciya chubaɗo ta sauƙe tayi narai-narai nan da nan idanuwanta suka chiko da hawaye, ganin suna shirin sauƙowa akan kumatunta ya sanya ta kwantarda kanta akan bench sai hawaye sharr, Allah yagani tana cutuwa da kallon da wannan mutumi yake mata da tanada hali ko wata hanyar da zata guje masa da bazata sake shiga lactures ɗinsa ba saboda ƙunci da kallon dayake mata yake jefata gashi shi bawai ƙaramin yaro ba babban mutum ne aƙalla zai kai shekara arba'in da tara. taɓota" Zeezee ta dafata.
"Haba Aysha da'allah shareshi ki taso mushiga cikin Hospital Akwai aikinda zamuyi kafin 12 kuma nasan dole cikin ni koke akwai wacce zatayi assisiting Dr Hafiz a surgeryn da zaiyi kokuma ma gabaki ɗayanmu ma tunda naga dukanmu ya aikowa document kuma yayi mana bayani akan ciwon" girgiza kai chubaɗo tayi.
"Ina tunanin ke zakiyi dan Abbana yace zaizo zuwa yamma akwai aikin da zan tayashi, ina tunanin akwai patients da yayi referring ɗinta daga asibitinsa zuwa nan last 2days yabani file ɗinta nayi nazari akai abune mai sauƙi yace tare zamu shiga surgeryn So kije kawai kuyi tare da Dr" Jijjiga kai tayi na gamsuwa da maganata.
"Nima wata rana inason shiga Surgery da Abbanki Aysha please ki roƙamin shi ko sau ɗaya ne" cikin student fa ke kaɗai yake yarda yashiga surgery dake, daga ke sai cikakkun likitoci"
"Uhmm ai Abban Aysha akwai son kai wallh ita kaɗai yakeso ta iya bandamu shiyasa kullum take zama best a cikinmu" Nadeeya wacce tunda ake magana sai alokacin tasaka baki da cewa.
"Uhmm ku dama cam ai bakusan halin fulani bane haka fa suke koda yaushe son kan tsiya ne dasu ko yaransu basu bari wanda ba nasu ba ya koya yanzu kun taɓaji tayi yaranta suka damu?" Haɗe rai chubaɗo tayi sosai kamar bata taɓa dariya ba duk cikin ƙawayen nasu dama Jininsu yafi haɗuwa da ita sai dai kusan kullum sai sun samu matsala a tsakani shiyasa a zahir za'aga kaman sunfi shiri da Badiyya saboda kaff badiyya tafisu sauƙin kai.
Miƙewa tayi batareda tasake bi takansu su duka ba ta zari bag ɗinta ta saɓa abaya tayi waje tana faɗin.
"Akwai abunda zanyi cikin asibiti sai kunzo" su dukansu miƙewa sukayi sukabi bayanta."
ZAYNAB BAWA