ZULFAH

page 2

by @rabiattu0444

_*Typing🤳🏼*_





_*💋....ZULFAH....💋*_




     Na

_*®UMMU MAHER(MRS GREEN)*🍏_




  *TEAM🔥GAWURTATTU 🤟🏻3*



*_AREWABOOK🤳🏼_*

https://arewabooks.com/chapter?id=65006c1d80342613407c880e




  *Page∆2*




_*ZULFAH*_




   News muke kalla ni da Hajiya Inna,muna zaune zaman kurmaye Hajiya Innah an ɗauro ɗaurin ɗanƙwali gaba ƙiris take jira ta fara masifa,ga masifar taf afuskarta amman babu wanda za ta yiwa,don Zulfa ko kallon inda take ma batayi ba balle tasa ran zata gane halinda take ciki.

Ana cikin haka Murassha ta shigo,ta kalli inda Zulfah take ta gwalo ido waje.

Mini siket ne ajikin Zulfah sai wata t.shirt iya cibiya me ɗan ƙaramin hannu,ta bazo uban gashi baya yayi wani yala yala, santala santalan cinyoyinta duk awaje sai wani ɗaukar ido suke,ita kuwa ko ajikinta ta tisa pop corn agabanta a wani babban mazubi tana ɗan ci ɗai ɗai tana kallonta.

Ƙafarta duk biyu akan ƙaton table ɗin da yayiwa falon ƙawanye me mugun tsada da kyau.

Hajiya Inna na masifar son wannan table ɗin, don duk jikanta daya shigo yasan inda yake zama sam ba'a zama ko kusa dashi gashi narkeke dashi yaji uban glass.

Ta juyo da akalar kallonta kan Innah wacce take ta cika tana batsewa amman babu halin yin magana,saboda ƴar gaban goshi ce tayi laifin.

Uwa uba gata da kaya matsatstsu wanda duk jikokin Inna sunsan ba'a shigo mata ɓangare da kaya matsatstsu ko da kuwa atamfa ce yadda ta tsani hakan har gaba sai ta ɗauka da mutum.

Amman yau babu damar yin magana saboda shalele ce tayi laifi,sai dai kawai ta girgiza ƙafa tana wani turo ɗam ƙwali ita a lallai tana masifa.ihi bayan hari don ita wacce ake abun don ita bata san ma anayi ba.

tintsirewa da dariya Murash-sha tayi tana ƙarasowa cikin tafkeken falon.

Tuni Hajiya Innah ya dawo da kallonta kan Murash-sha,daman yaya lafiyar kura haba sai kuwa ta fara faɗa.

   "Haba haba fisabilillahi,yanzu ni da ɗakina bani da wata dama Iye?sai azo ayi tamin dariya ta ɗibar albarka ana kassaramin kayan ɗaki?kuma babi damar kayi magana sai cibi ya zama ƙari?ni gaskiya bana son haka,haba haba Fisabilillahi".

maimakon ta daina dariyar har sai da ta tsugunna ƙasa,don ita mutum ce me saurin dariya ga fara'a saboda haka ta dawo wajen Innah da zama,saboda ɓangarensu kows takansa yake duk kuma wanda ya fita tun safe sai kuma yammah ko dare,shiyasa ma ɓangarensu sam yake ame baƙin jini awajenta,duk masifar Innah tafi son zama wajenta.


Duk wannan abin da ake haryanzu Zulfah bata ma nuna tasan abinda akeyi ba,Innah ta ƙara harzuƙa ta juyo tana huci ta ce"ke wai ni Muraisa Sale ne ya ginamin ɓangare?da akazo aka taremin kamar ɓangaren tasi no gareji?haba haba fisabilillahi don Allah Abarmin ɓangare a koma wajen wannan guzumar uwar taki me kama da giwa,aikin ɓur ayi ta cinyewa ƴaƴana abinci ana ɓarnar kuɗi ana kaiwa meduguri,haba haba fisabilillahi".

Me makon Muras-sha taji haushi sai kuwa ta dubi ɓangarenda Zulfah take ta ce"uhm uhm ni fa Hajiya Innah bani nakar zomon ba rataya nima aka bani".

Ta faɗi hakan da dariyarta wacce ta cika falon.

Zulfah ta ɗan kallesu tayi magana ahankali.



"I dont went hear noise please!".



Ta ɗan Faɗi hakan cikin iyayinta da ƙwaini,haba nan fa Hajiya Innah tahau kuka wiwi wai an zagi ubanta Ummaru dake ƙwance dama,don bata jin turanci ko kaɗan dayake ada ba damuwa akayi da karatun ba.

Murash-sha fa ta samu abinyi,Zulfah ta galla mata wani banzan kallo wanda ya haddasa shirun nata don tasan tsaf zata yi mata wani zagin da zai haddasa mata ciwon kai.


Hajiya Innah ta ƙara hawa sosai ga bukin zuwa babu zanin ɗaurawa don tasan bata isa tayi magana ba yanzu sai a tada musu tambotsai.

Ana cikin haka ta fara jin muryar wani matashi acikin tv,saboda lokacin hankalinta na kan cika da batsewar da Innah ke yi wanda tasan maƙasudin yin hakan,amman don ta manna mata sai ta kyaleta.


"Azzaluma ce,mara adalci sannan sam bata san martabar ɗan adam ba".

Sosai ta maida hankalinta kan saurayin da ake magana dashi.

Ƴan sanda na korar ƴan jaridan su kuma sun maƙale suna ɗaukar rahoto.

Ɗan jaridan ya ce"ko zamu iya sanin sunanta?".

Maganar da taji ce yasa kanta ya fara tartsatsin wuta me ci bal bal.

Sunanta"Zulfah Alfas family waɗanda ke cikin garin nan azzalumai masu ƙasƙantar da ɗan adam."

ba ita kaɗai ba,hatta Innah da Murash-sha sai da abin ya girgiza tunaninsu sosai,suka shiga rattabowa kawunansu to ayaushe ne hakan ya faru?kai wannan ma dagaji sharri ne.

Zulfah ta juya eyes ɗinta cikin ɓacin rai ta wuce ɗakinta.

Tsaye tayi bakin mudubi tana kallon kanta,from head to toe ta kasa tuna ranar da wani yayi mata irin wannan tuzarcin me kama da kamawar wuta.

Ta nuna kanta"ni Zulfah wani yakewa wannan zagin?".

Tuni ta fara shiga wanu hali,daman kuma aduk lokacin da ɓacin ranta ya sauka kasa gane kanta ake baki ɗaya.

Tuno da hakan yasa Hajiya Innah ta taho da sauri zuwa ɗakin jikarta Xulfah.

sai dai ko kafin tazo tuni an datse ƙofar gam Innah tahau bugawa iya ƙarfinta amman Zulfah bata buɗe ba.

Tsoro da fargabar abinda ka iya zuwa ya dawo tsoro da fargaba suka samu gurbi azuciyarta,tuni ta sau kuka don tasan yau sai ta Allah kenan.Murash-sha ma hankalinta ba ƙaramin tashi yayi ba,da ta tuno da gumurzun daya faru wasu ƴan ƙwanaki da suka wuce.

Hajiya Innah na kuka ta ce"Murash-sha miƙomin wayata ki dannawa Malik kira yazo yanzu yanzu".

Nan da nan kuwa ta kirasa,mahaifin Zulfah kenan yana cikin meeting aka kirasa sai da gabansa yaɗan faɗi dayaga number mahaifiyarsu.

Amman bai kawo komai ba ya ɗaga.

abinda yaji ne ya tsoratar dashi sosai nan da nan ya fito da ɗan sassarfa tuni ya fara jiƙewa da gumi,don tsabar tausayin halinda ƴar tasa take ciki.

kai tsaye ya shigo ɓangaren mahaifiyar tashi,hawaye sharkaf a kuncinsa ya fara doka ƙofar yana kuka yana magana haɗi da kuka tamkar ƙaramin yaro ɓaganarsa na sarƙewa

 "Zul. . . .Zul. . . . .Zulfah don Allah ki buɗe magana zamuyi".

Shiru babu amsa sai wani gurnani da suka jiyo Zulfahn nayi da ƙarfi,sai da masu aikin sukazo sukayi ta bugun ƙofar sannan ta buɗe,Hajiya Innah ce ta samu ta riga kowa shiga wai ita me jika.

Gam ƙofar ta rufe bayan hjy Innah ta shiga,sosai ta zato ido ganin Zulfah ta koma tamkar ba ita ba,gashin kanta ya barbazo har yana rufe fuskarta ga idanuwanta sunyi jawur,jini na fitowa ta idanuwanta tamkar an buɗe famfo tana zaune a saman gadonta ta naɗe ƙafarta tamkar wani boka me jiran siddabaru.

Hajiya Innah tsoro yasa ta fara fitsari tsuuuu awando tana ce wa"wayyo Allah na,yau shikkrnan na shigo hannu sai yadda akayi dani,don Allah Zulfah kiyi hƙr wallahi baza a ƙara ɓata miki rai ba".

Wani irin ihu Zulfah ta saki duk gidan nasu sai daya amsa,mutanen Alfas house duk suka firfito baki ɗayansu suwa sashen Innah wanda yake ta amsa kuwwar kiran jama'ah.



Hajiya Innah fa ido ya raina fata,sai ga gudawa ta fara samun wajen gudu tsuuu,faɗi take haba haba fisabilillahi tsabar mugunta a kulle ni aɗaki,wayyo Allah ni ƴar Abubakar jikar Ibrahim Ɗan magori Allah Ka kawomin ɗauki wayyo Allah na . . . . . . ."

Kowa yayi cirko cirko a bakin ƙofar ɗakin,kowa na faɗar albarkacin bakinsa gashi kuma an kasa zuwa bakin ƙofar,Dad Malik ne kawai awajen sai kuma Murash-sha wacce keta kuka yayinda suke jiyo ihun Innah acikin ɗakin har tana bugo ƙofat don azo akawo mata ɗauki.

Allah ya taimaki hjy Innah ƙofar banɗaki abuɗe take tayi wuff ta faɗa tana nishi ƙasa ƙasa.

Da ƙer aka samu ƙofar ta buɗu,sai dai ana shiga aka tarar da Zulfah ƙwance akan gadonta tamkar ma dai babu abinda ya faru.

Jin mutane acikin ɗakin yasa Innah ta fito da gudu har tana haɗawa da faɗuwa jikinta dama dama da kashi harda fitsari.

Chuchu ce ta fara dariya,yayar Zulfah wacce suke Baba ɗaya sai kuwa ta ce"oh yau Haba haba harda gudawa hhhhh".

duk da Dadynta yana cikin wani hali sai daya yi mata wani banzan kallo sannan ta kame bakinta,cike da jin haushin irin kulawar da mahaifin nasu ke yiwa ƙanwarsu.

Ƴaƴan Innah su shida ne,huɗu maza biyu mata duk kuma suna wajen abin ya faru saboda ranar weekend ce kowa yana gida.

Malik kallon Zulfah ya shigayi yana lulluɓe mata jikinta saboda yadda surar jikinta ta bayyana,su kuwa sauran iyayen nata ficewa sukayi suka zauna afalon Innah suna jimamin halinda Zulfah ke ciki.

wasunsu daɗi ne fal ransu,wasunsu kuma akasin hakanne azuciyoyinsu tausayin yarinyar fal aransu.

yarinyar da take da shekara 20 amman ace wannan muguwar lalurar ta same ta?wacce haryanzu aka rasa gane kanta.

hjy Innah dai babu bakin magana sai muzarai take,jikokinta kuwa sai danne dariyarsu suke saboda yadda Innah ta zama tamkar wata yakuwar da aka tsoma aruwa.

Tuni ta shige banɗakin don kunya,ta wanke jikinta tsaf sannan ta ɗora dayin wanka ta fito,har lokacin kuma waige waige kawai takeyi saboda tsabar tashin hankali,ko waccen karon da Xulfah tayi bai kai wannan ba abin yayi sauƙi.

Tana fitowa daga wankan ta iske Malik,zaune yana riƙe da hannun ƴarsa yana kuka wiwi tamkar ƙaramin yaro.

Sosai tausayinsa ya ɗarsu azuciyar Innah,tuni itama taji idanuwan nata sun kawo ruwa,don ta tabbatar da ayanzu dukkansu da za a auna jininsu to babu makawa sai ance jininsu ya hau.

Tasan ƙaddara ce ke zuwarma mutum aduk lokacin da Allah Ya kawota,amman bata taɓa tunanin wannan ƙaddarar ba,shiyasa idan zaka roƙi Allah Ka roƙesa akan kada ya ɗora maka ƙaddarar da bazaka iya da ita ba.

A hankali ta dafa kafaɗar ɗanta tana share hawayenda ya cika mata ido,suna buƙatar su samu sarari nan da nan suka shiga zuba murya a ɗan sarƙe ta ce.

"Malik inason ka daina damuwar nan,ka sanyawa zuciyarka salama ita dai ƙaddara ta riga da tazo,kuma babu yadda zamuyi da ita sai hƙr."

idanuwansa akan ƴarsa ya ce"babu abinda yake dawomin a halin yanzu sai Jidda . . . . . . ."


hjy Innah ta ce"tabbas Jidda ta tafi tabar baya da ƙura Allah dai ya jiƙanta da rahama yasa mutuwa hutuce agareta."

Malik ya amsa da amin amman zuciyarsa duk babu daɗi,musamman halinda Zulfah ke ciki wanda magani iya magani anayi amman kullum abin ƙara cutura yake.





*********


*ƳAR MAHAUKACIYA*


 

Adai dai lokacinda wasu suke cikin farin ciki,alokacin wasu suke cikin halin baƙin ciki,tabbas rayuwa ilimice duniya kuma makaranta ce daban ga bayi masu maida bauta tamkar abincinsu.

Adai dai lokacin da rana tayi zafi.wasu suna cikin inuwa saboda basa son zafi wasu kuma alokacin suke cikin matsin rayuwa,da tartsatsin wutar wahalar rayuwa.



Kuka na fashe dashi na janyo mahaifiyata jikina,alokacin da take tacin biredi na bola tana cinsa tamkar mayunwacin zagin daya shekara baici nama ba,wasu zafafan hawaye suka zubomin aƙwarmin idanuwa,na sanya bayan hannuna na sharesu,ta kalleni sosai tamkar dai me hankali ta miƙomin biredin hannunta ba tare da ta cinye ɗin ba.

Sosai nake ƙyanƙyamin biredin amman babu yadda zanyi,tunda dai da shi na girma ko abinci abola haka muke ɗauka munaci.

Haka na taso bansan ƴan uwan mahaifiyata ba?bansan kowa ba sai mahaifiyata,mun taso a matuƙar wahalar rayuwa ta yadda duk inda mukaje sai kaga ana mana waƙa ni da mahaifiyata wai ga ƴar mahaukaciya da mahaukaciya,wannan batu nasu yana matuƙar suya min zuciyata amman babu yadda zanyi,tunda na tabbatar da batunsu haka yake babu abinda zance sai dai Allah Ya kawo mana sauƙin rayuwa,nasha kuka da idanuwa na akan matsalar mahaifiyata amman sai dai inyi kuka inshare hawaye na,addu'ah kaɗai nake akan wannan halin da muka tsinci kanmu ni da mahaifiyata.

Zakuyi mamakin inda na yi ilimi,aƙwai makarantar allo akusa damu,don haka kullum ina zuwa amman jan hannun mahaifiyata nake mu shiga makarantar tare,takuwa zauna har sai an tashi in sake riƙo hannunta mu tafi.

Ina mamakin yadda haukan mahaifiyata yake?duk yadda akayi ita ɗin asalinta macece me nutsuwa.

Don bata tsokana,ita dai haukanta akaina ne don duk wanda ya taɓani duk abinda yasamo sai ta ƙwala masa.

Ana haka rannan na tafi samo mana ruwa,don a wani kango muke zaune abin mamaki tunda na taso muke cikin wannan kangon,amman ban taɓa ganin wano yazo yace kangonsa ne ba,muna dai zaune abinmu aƙwai banɗaki har ma da ƙofa agidan,kayanda muke sanyawa wani lokacin bara nake in samo mana su.



 Ƙaddarar da ta ƙara fuskanto rayuwata bata wuce wadda muka fuskanta ni da majaifiyata ba,wato abinda ya faru bayan na fita samo mana ruwa ina dawowa kawai sai naga wani mutum ya fito daga cikin kangonmu,ya hau wata rantstsiyar motarsa amman bai bari anga fuskarsa ba,yana hawa yaja motarsa da mugun gudu.


Da sauri na shiga kangonmu,abinda nagani ne yasa na ƙwala wani mugun ihu ina dana sanin ganin wannan ƙaddarar. . . . . . .✍🏽




Nasan zakuji labari biyu,to labarin de guda biyu ne na ƴar mahaukaciya da kuma Zulfah . . . .


*ku biyoni yanzu labarin ya fara aƙwai daddaɗar tafiya nan gaba* . . . .