ZULFAH

page 15

by @rabiattu0444

_Typing🤳🏼_




  *_....🌪️ZULFAH🌪️...._*



_UMMU MAHER_

    *@MRS GREEN🍏*



_GAWURTATTU 3_



Book 2 page 15


*_follow Zulfah on Arewa books_*

https://arewabooks.com/book?id=64ff0277d73b80a18ea59540


*_VIA GROUP ZULFAH FANS_*

***

gSsodCRZGcEjERSEsBY


_*AMMA ARAB!AMMA ARAB!!

AMMA ARAB!!!*_


_kai daga jin sunan kasan

sunan ya amsa sunansa,

AMMA ARAB ta kawo muku

wani supplement na gyaran jiki

mai sanya daɗi da ƙamshi AMMA

ARAB gidan ƙamshi_


*MUSUK*

*MADARAR TURARE*

*KAJIJI*

*ROT*

*SANDAL*

*HUMFUR*

*SANDAL FLASK*

*SANDAL WUD*

*AALUT*

*GAF-GAF*

*JANNAMI*

*ƘWALAKCA*

*MAHAHABSUFYAN*



*WANNAN SHINE GRP

ƊINA NA WHATSAPP,KI ANTAYO

SABODA KADA AYI BABU KE*

👇🏻👇🏻👇🏻👇🏻👇🏻

***

mBHnDN6KUJYnkBDT7S


*ADDRESS👇🏻👇🏻👇🏻*

Zaria road kwankwasiyya sabon gari ɗangwauro house number 224

  Kano


OR CALL MY CONTACT

***


*AƘWAI WANI SUPPLEMENTA NA GYARAN JIKI DA TAZO MUKU DASHI KE DA KANKI IDAN KIKA YI ZAKISAN EH LALLAI ZAKI GIGITA ME GIDA,KINSAN MAZA SAI DA ƘAMSHI DUK MATAR DA BATA SAYI WANNAN SUPPLEMENT ƊIN BA TO AN BARTA A BAYA*


*AƘWAI BABBAN MAGANI NA INFECTION,WANDA ZAI DAWO MIKI DA MARTABARKI NA ƳA MACE,ZAI CIKO MIKI DA NI'IMARKI KI KOMA ƳAR GATAN MEGIDA*


*AƘWAI BABBAR KAMBASA,TA TURARA KAYA HAJIYA KI BUƊE BAKIN ALJIHU KI JIƘO DA ƘAMSHI,KINA ZAMA AN SAN KIN ISA MACE HAJIYA DON AMMA ARAB TA SHARA SOSAI WAJEN KAWO MUKU KAYAN GYARA NA MATA*


*AƘWAI SABULAN GYARAN JIKI SUNE KAMAR*


*MULATO SOAP*

*FACE CREAM*

*FACE SOAP*

*MULATO WHITENING LOTION*

*HAIR GROW OIL*

*HAIR GROW CREAM*

*KAR-KAR OIL*

*MINT LEAVE OIL*

*ANTI PIMPUS SOAP*

*AƘWAI SABULUN NANKARWA*


sannan ina harkar👇🏻👇🏻👇🏻👇🏻

*ABIN BUKI*

*ABINCIN OFFICE*

*SNACK*


KAMARSU👇🏻👇🏻


*WAINAR MASA*

*SINASIR*

*MEAT PIE*

*CINCIN ƊAN LAUSHI*

*CUP CAKE*


DA DAI SAURANSU.

AMMA ARAB GIDAN GYARAN AURE😄👏🏻



_BILAL_


______"Umma Zulfan kike kira da shegiya?a ina kika taɓa jin wannan maganar mai muni haka?".wani irin mugun kallo hjy Maryam tabi ɗanta dashi sannan ta ce"awajen ubanka naji wannan maganar,kasan dai ba zai maka ƙarya ba ko?saboda hakama nake son kaima ka fita daga sabgarta tun kafin in yafe ka acikin ƴaƴana,saboda ni bazan haɗa zuri'ata da shegun ƴaƴa ba."

Sosai maganar mahaifiyar tashi tayi masa ciwo sosai,hankalinsa yakai ƙololuwar tashi ya ƙara kallon mahaifiyarsa akaro na biyu ya ce"Umma idan har Zulfah ƴar shege ce,ya kamata mu dakanmu mu aibatata?ya kamata mu da muke ƴan uwanta muƙi aurenta?kuma shin aƙwai hadisin da aka rawaito cewa a daina auren shegu?........."tun kafin ya ƙarasa ta ce"kai don ubanka kada ka zageni,ka koma ka zagi wannan tsohuwar najadun kakar nan taka,amman ni kul ɗinka don ruwa ba sa'an ƙwando bane,duk son da nake maka zan iya ajjeshi agefe inyi maka abinda za kayi nadamar son Zulfah,saboda haka ka kiyaye ni banza salamamme".

da ido yabi bayan mahaifiyarsa,kansa na wani irin sara masa yana kiran sunan Allah,ji yake dama ya koma ƙasar daya fito saboda sam baya son tention,saboda Zulfah ya dawo ƙasar nan amman kuma sai gashi tafi kowa tsanarsa,ya rasa me yasa Xulfah ta tsanesa yasan yarinyar tun tana ƙarama,yarinyace me son mutane musamman ma shi da suka shaƙu sosai tun kafin a kaita U.S karatu,bayan an kaita karatu ne yasa shima ya nemi ya bar ƙasar don yaje ya ƙaro karatunsa,sai gashi dawowar da zaiyi ya tarar da gidansu acikin wani irin hali,wanda duk da lalacewar da gidansu yayi ada bai kai yanzu ba,ya rasa abinda mutanen gidansu suke nufi da mahaifin Zulfah,dukkaninsu babu ƴan uba a tsakaninsu amman kuma sai gashi acikinsu aka samu waɗanda sukayi masa wata irin muguwar tsanar da sai ka ɗauka waɗanda ba suda alaƙar komai a tsakaninsu,tabbas ya zamar masa tilas ya kawo ƙarshen wannan babbar tsanar dake tsakanin mahaifin Zulfah da ƴan uwansa,cikinsu kuwa harda mahaifinsa acikin masu wutar rura tsanar ɗan uwansu azuciyarsa,tunda gashi har ya fara sheganta Zulfah yarinyar da aka haifa agidansu,kusan ma zai iya cewa shine ya fara sanin anyi haihuwar,tunda hjy Innah ce ta karɓi haihuwar da kanta da taimakon wata likita,duk da likitan ce ta karɓi haihuwar amman bai hana hjy Innah shelar cewa itace ta karɓi haihuwar ba,yana jin kukan jaririya ya faɗa ɗakin,tare da rungume Zulfah a ƙirjinsa ko wanketa ba'ayi ba da ƙer aka koresa daga ɗakin,amman kuma yau wai Xulfah ake cewa shegiya,afili ya ce"oh duniya ina zaki damu ne?Allah ka shiryamin iyayena bisa tafarkinka da manzonka,ya Allah ka ganat dasu ganewar da zata zame musu nutsuwa da sanyi game da ɗan uwansu".

daga bayansa yaji an amsa da "Amin".a hankaki ya juya don ganin waye?ƙanwarsa ce Amira,ta kallesa tana murmushi sannan ta zauna kusa dashi ta dafa kafaɗarsa abinda bata taɓa yi ba,saboda yayan nasu aƙwai shi da bin dokar ubangiji ba shida wani tsare gida kamar yadda sauran yayyi ke yi,yana da sakin jiki da ƙannensa sosai idanuwanta cikin nasa ta ce"Yaya bai kamata ka dinga damuwa kan wannan maganar ba,abu ɗaya ya dace kayi ka xama mai gayawa Allah matsalarka,sai kaga ya kawo maka komai da sauƙi sannan ya kamata ka ƙara bawa Zulfah lokaci,don kuwa har ayanzu banyi tsammanin an bar Zulfah haka ba saboda yadda take samun masoya masu sonta tsakani da Allah,amman fur sai ta sanyawa idonta toka ta gurza musu rashin mutunci,wanda ni a ganina addu'ah ce zata sanya Zulfah sonka don Allah ka cire damuwa aranka,kasan fa kana da heart bit(ciwon zuciya)saboda haka ka daina damuwa kada ciwon ka ya tashi".

murmushi ya yi sannan ya ɗan shafa gefen fuskarta ya ce"to naji zan kiyaye ƙanwata,kema ki tayani da addu'ah akan Allah ya karkato da hankalinta kai na".Amira ta ce"to yaya me zan dafa maka"?.murmushinsa mai ƙayatarwa yayi sannan ya ce"komai ma my sis".yana faɗar hakan yayi ɓangarensa,ta tsaya ƙuri tana kallonsa har ya ɓacewa ganinsa,tana tausaya musu saboda sam Allah bai basu iyaye na gari ba,su biyar iyayensu suka haifa amman su biyu ne nagari acikinsu sauran duk halinsu suka biyo,ta girgiɗa kanta hawaye na silalo mata saboda wani abu da ta gani yau a dangane da iyayen nata,wanda ya zamar musu sirrinsu a tsakaninsu kuma ba iya iyayensu kaɗai ne ke yi ba kusan duk hakan ƴan gidan nasu suke,sai dai wanda Allah ya bawa zuciya tsarkakkiya acikinsu wanda sune sukafi ƙaranta acikinsu.

tausayin Zulfah take sosai,saboda aƙwai wasu abubuwa masu tsoratarwa acikin rayuwarta gami da abubuwan mamaki sai dai hakan ba zai bayyana ayanzu ba,domin kuwa iyayensu sunyi nisa basa jin kira sunyi nisan da bazasu iya nutsuwa su fuskanci alƙibla ba,sunyi nisan da basajin kira ayanzu sai dai lokacin da zasu gane gabas da arewa yana nan zuwa.




    *¢¢¢¢¢¢¢*



Hajiya Maryam tana shiga ɗakinta ta saki ajiyar zuciya,don da alama tana ganin nan gaba Bilal zai iya kafe mata don tana hango son Zulfah tsantsa acikin ƙwayar idonsa,tana masifar son ɗanta Bilal bata haɗashi da kowa aduniya saboda shi kaɗai ne ɗanta namiji,sannan yana yi mata tsananin biyayya baya son duk abinda zai taɓa zuciyarta balle kuma har tayi fushi dashi,tabbas tarihi zai maimata kansa don kuwa mahaifiyar Zulfah a gaba gaban goshi take a idon mijinta,don sam bata wasa da lamarinsa musamman ma da ta fito daga tsatson shuwa arab,shiyasa ko da aka aurota don asirin Hjy Raihana sai data zama bora agidan,don ko kallon arxiƙi bata samu a idon mijinta saboda haka itama take tsoron kada yaronta ya zama mijin tace,ya zama sai abinda wata take so shi zaiyi mata ita kuma ya daina jin maganarta,ba ƙaramin artabu akasha a familyn Alfas ba alokacin da mahaifin Xulfah ya auri mahaifiyarta,tana ɗaya daga cikin waɗanda suka sanya hannu wajen ganin bayanta,don su kansu ba jin daɗin gidan sukeji ba saboda mahaifiyar Zulfah tabi ta kanainaye komai,su da suke facalolinta sai ta sanya Super ta dubu ɗari a wannan ƙarnin su basu sanya ta dubu hamsin ba,don duk da asalin Alfas ɗin yana da kuɗi kuma ƴaƴansa ma sunyi gadonsa,amman kaf cikinsu babu wanda ya kai mahaifin Zulfah kuɗi,ya shahara sosai aduniya ko ina an sanshi da kuma Business ɗin da yake yi,na sarƙoƙin gold na nigeria da kuma sauran ƙasashen turai da asia,sunsha gwada yin wannan kasuwancin amman sam baya yiwuwa saboda haka sai suke ganin kamar aƙwai wani abu da yake yi yasa yake wannan kasuwancin.




      *¢¢¢¢¢¢¢*



_HAJIYA RAIHANA_

      manyan mata😉


waya takeyi da wata ƙawarta mai suna NANA gidan kuɗi,ta ƙara da ce wa"oh ke Munira ranar taso janyo min masifa,yarinya daga ganina da wannan kayan ta rusa ihu sai ga mutanen gida sun fara tururuwar zuwa ganina?ai da sauri na canja kayan daman aƙwai atamfa a ƙasan kayan nayi sauri na ɗaura ɗan ƙwalina na fesa turare,na fito falo kafin suzo ai wallahi ko Munira ƴata ce idan har ta nemi ta tona min asiri babu yadda za'ayi in barta haka,saboda haka tuni na rufe mata baki ko da sukazo harda wannan tsohuwar mayyar kakar tasu suka fara tambayarta abinda ta gani,ai kawai shiru tayi ta tashi ba tare da tace komai ba nima don in nuna musu bansan abinda ke faruwa ai sai nabi Munira ina muxurai ina tambayarta abinda ta gani".sosai NANA ke dariya tana ce wa"oh ai ni da kika ganni ba nida sakaci irin naki,na iya tafiya ta sosai ta yadda ba kowa ne zai gane abinda nakeyi ba,saboda haka ki ƙara tsare komai ki kula da kyau saboda kada a ƙwace madafan yaƙi daga hannunki kamar yadda aka yiwa BIBI".

Shiru tayi don tuno da aminiyarta BIBI wacce suke komai tare amman yau ta zama ba tada komai ta zama abar tausayi tana yawo bola bola ta zama mahaukaciya,saboda haka gwara ta ƙara dagewa sosai don ganin bata wulaƙanta ba.

har wayarta zata katse wayar don sun gama wayar sai kuwa ta ce"yau wa NANA inason yin magana dake,kinsan fa wannan yarinyar yau naji labarin ta koma America saboda haka ayau ba sai gobe ba,inason ayimin abinda zata dawo ƙasar nan saboda inason in shayar da ita wutar baƙin ciki,sannan in wulaƙantata kowa ya tsaneta tsana mafi muni arayuwa,ta zama mujiya mafi muni arayuwa sai na wulaƙantata tamkar yadda na yi wa uwarta".sheƙewa sukayi da dariya NANA ta ce"yauwa ta hannun dama a janyota ta dawo muyi maganinta mu nuna mata Allah da girma yake".


Uhm ni kuwa Ummu maher na ce oh sai kace sunsan girman Allahn,uhm Allah ka tsarkake mana zuciyoyinmu baki ɗaya.


NANA ta ƙara ce wa"yauwa ya maganar bikin Salman ni banji kince komai ba har yanzu?".

Sai da ta gyatsina fuska sannan ta ce"ta yaya zanyi miki wata magana?bayan yana shirin tonamin asiri ya auromin ƴar gidan malam iro?ni wallahi banga abinda ya gani wajen ƴar matsiyata ba?yanzu duk arziƙin babansa ya rasa wacce zai aura sai wannan yarinyar?ga ƴar wajenki nan Safina amman ya maƙale sai wannan matsiyaciyar yarinyar yake so,ke ba abinda banyi ba don inga na rabashi da wannan yarinyar amman yadda kika san turasa nake,saboda haka tunda yace sai wannan yarinyar wallahi babu ni babu shi."da sauri NANA ta ce"a kul ɗinki Raihana kada ki sake kice zakiyi masa baki ko ki juya masa ba,hakan zaisa ayi miki dariya ke da kike da mahasadda da yawa?ki janyo sa ajiki sosai ta hakanne zaisa duk wani sirrinsa ya faɗa miki,daga nan ke kuma sai ki shiga ganin bayan wannan shegiyar yarinyar,kinga daga nan shikkenan kin kawo ƙarshen matsalarki amman ayanzu idonsa ya rufe sosai,kinsan ƴar malamai ce sun riga da sun bashi rubutu ya tanɗe a shinkafa ko a lemo,saboda haka kiyi musu ƙwantan ɓauna daga haka ki kaisu ki baro su" .

Dariya sosai Hjy Raihana ke yi sannan ta ce"kinsan kuwa ni banyi wannan tunanin ba,shiyasa ko da akazo batun lefe dana tashi wasu shegun atamfofi na sanya guda goma don bazan kashe kuɗi a ƴar gidan matsiyata ba".haka dai sukayi ta hirarsu ta yadda zasu ga baya mutane amman su basa tunanin tasu rayuwar.




     *¢¢¢¢¢¢¢*



_ALIYU_


Ranar banyi wani barcin kirki ba,saboda yadda matsalar ƙanwata Harira ta sanya ni agaba bana son inga wani ɗan uwana acikin matsala sam.da ƙer barci ɓarawo yayi awon gaba dani ina saƙawa da warwarewa.

da safe kuwa na daɗe ban fita ba,ina zaune muna hira da Baba yana ta shi min albarka akan abubuwan da yake yi musu agidan aka aiko kirana

yaro ya shigo ya ƙwala sallama tare da ce wa"wai ana kiran Aliyu awaje".

da sauri na ce"waye yake kirana?".

yaron ya ce"wanine dai ya aikoni".

Ban ƙara cewa komai ba na fita,daga nesa na hango Ahmad na ce"shegen kaya ashe kai ne".murmushi kawai yayi sannan ya ce"eh nine dama ina sane nace a ɓoye sunana,don idan ƴan rashin kirkinka na kanka ba lallai ka fito ba".da sauri na ce"rufamin asiri ai kai yanzu yaya ne,saboda haka dole ace da mijin iya Bba".muka tafa muna dariyarmu ta shaƙiyancin abokai musamman ma aminan juna.

sai kuwa Ahmad ya ce"kasan kuwa mutuniyarka tayi tafiya"?.da sauri na kallesa na ce"haba yanzu Ruƙayya ce tayi tafiya shine baka faɗamin ba?sai bayan da tayi tafiyar?amma baka kyautamin ba".

Ahmad ya murmusa don ya fuskanci abokin nasa bai fuskanci wacce yake faɗa ba?.

sai kuwa Ahmad ya ce"kai ba fa Ruƙayya nake nufi ba ZULFAH........"tun kafin ya ƙarasa naji wani irin mummunan bugawar ƙirji,wanda har ya sanya ni riƙe ƙirjin nawa don ambato sunan maƙiyiyita ZULFAH...........✍🏻




_MRS GREEN CE_



domin chart dani kai tsaye ***


*_GAWURTATTUN UKU🔥🔥🔥2023 SEPTRMBER._*




_1-ƘWAI A BAKA...!!!🥚_

👇🏽

*(Ummu Affan)*



_2-NA FAƊO DAGA BENE NA ZARCE RIJIYA...!!!🫗_

👇🏽

*Badi'at Mrs bukhari*



    _ZULFAH_🍏

👇🏽

*Ummu maher(mrs green)*



_Littafi ɗaya;400_

_Littafi biyu;800_

_Littafi uku;1000_


Ga masu son tura kuɗinsu ta acc sai su tura a wannan acc ɗin👇🏽👇🏽👇🏽👇🏽


0037219728

Fatima Rabiu Sunusi

StanbicIBTC Bank


Sai ka tura da shaidar biyanka ta wannan no ɗin👇🏽👇🏽👇🏽


***


Masu tura kati kuma sai su turo screenshot na katinsu Mtn ta wannan no ɗin👇🏽



***


Ƴan Niger zasu turo katin Moov ko Airtel ta wannan number.


***


*GA MASU SON A TALLATA MUSU HAJARSU A DUKKANIN SHAFINMU na facebook,whattpad,telegram,youtube,group da status,zamu tallata muku ne akan farashi me rahusa*

10K ne kacal.

Sai ku tuntuɓe a numbobinmu kamar haka👇🏽👇🏽👇🏽


***

***

***


Domin tallata muku hajojinku a cikin littafinmu na sati ɗaya ya kama👇🏽👇🏽👇🏽


2K

sati biyu

3k


idan kuma kanason har mu gama book muna ɗora maka ya kama

10k kacal.




Mun gode da zaɓar gawurtattu uku ako da yaushe.🙏🏼